Showing 510001 words to 513000 words out of 557259 words

Chapter 171 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

432

yawancin lokuta idan tazo cewa take su zauna ayi hira,a nata lissafin wai ko hirar zata daukewa maamah din kewa.

Yanzun ma hira sukeyi lokaci lokaci suna kallon wani hausa film. Sunason kallo sosai,kuma bata hanasu ba indai sun gama duka ayyukansu.

Musaddiq ne yayi sallama,suka amsa masa,ciki harda sabreen cikin mamakin jinsa a irin wannan lokacin. Kwata kwata ba lokacin zuwansu bane,saidai kafin ta dauke idanunta amna ta biyo bayansa.

Doguwar riga ce a jikinta da qaramin hijab,kallo daya tayi mata taga kaman ta fada.

Yau din ba wannan tsoron sosai a tattare da ita,ta tako kaman yadda mijinta yayi ta qaraso gaban maamah ta gaisheta ta kuma dubata sannan ta matsa gefe kusa da sabreen ba tare data damu da ko idanu maamah din bata daga ta kalli amna ba.

Sun gaisa da sabreen kafin amnan tayi shuru. Sabreen ta daga kai ta kalleta da dan mamaki. Amna ba kasafai zata zauna tayi shuru haka ba,abune me wahala musamman idan akwai sabo tsakaninku. Dan tabota tayi,ta daga kai ta kalleta,sai ta sake mata murmushi,itama amnan ta maida ma sabreen

"Lafiya kuwa auta?" Sabreen ta tambaya. Kaman jirar tambayar aman da ya taso mata yakeyi sai ya qarasa fitowa zuwa sarari.

"Subhanallah" Sabreen ta fada a rude ta miqe tana riqe amna din dake sake galabaicewa.

Kaman ya mance a inda yake,gaba daya yayo kan amna din yana rungumeta ta baya hadi da riqeta sosai hankalinsa yana tashi. Sannu kawai yake jera mata,har zuwa sanda ta kammala aman,daya daga cikin masu aikin maamah din tuni harta dauko kayan aiki tahau gyara gurin,sauran kowacce sai jera mata sannu suke cikin kulawa da tausayawa.

Idanu maamah ta zuba mata tana jin qwayar idanun dama kewayenta gaba daya sun budade da yaji,tamkar an damqi garin yaji an watsa mata. Wani lafiyayyen gumi ya soma karyo mata,ta kasa dauke idanunta daga kanta zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa.

"Da ka sani musaddiqu ai baku fito haka nan ba"

"Daga asibiti muke......tun shekaran jiya bata da lafiya taqi kuma yarda aje asibitin saboda tsoron allura......ganin ban samu shigowa da safen ba sai nace bari mu shigo mu gaida maamah saimu wuce gida" Ya amsa mata yana goge mata jiki da tissue.

"Allah ya sawwaqe.......Allah ya inganta......mu saidai mu tayaku da addu'a ai,shekara ashirin rabona da haihuwa yanzu haka" Ta fada cikin raha tana murmushi.

Murmushi sabreen ta saki,sai a yanxun ta gano bakin zaren,wato shima musaddiq yayi nashi aikin. Murmushin da yazo wuyan maamah ya tsaye mata,sai taga kaman dariya sabreen take mata,kaman sabreen tana gaya mata KE DIN LOSER ce,kowa yaci nasara a kanki,abinda ya sanya wani tari ya sarqeta ta soma qoqarin zamowa daga saman wheelchair din saboda yadda zaman ya gagareta.156


"Subhanallah" Musaddiq ya fadi da sauri yana isa gareta ya tareta kafin takai qasa. Hawaye ne suka qwace mata,inama ace tana da ikon tureshi,ba shakka da sai tayi masa mummunar turewar da bazai sake sha'awar zuwa kusa da ita ko kawo mata dauki ba.

Ciccibarta yayi yana maidata saman wheelchair din sannan ya daureta da belt din da suke jiki. Komawa yayi gabanta ya zauna yana duban fuskarta yana kallon gumin da yake tsatstsafo mata. Ba ita ba.....shi kansa radadi zuciyarsa take masa,saidai akwai banbancin radadin da yakeji da kuma wanda ita yakeji. Ita nata radadin na baqincikin rayuwar wasu ne,qyashi da kuma baqar hassada. Yayin da nasa radadin ya ta'allaqa ne da yadda kullum zuciyarta ke sake gurbacewa,duk da irin yanayin da take ciki,duk da irin qalubalen da take fuskanta amma hakan bai sanya ta haqura ta ajiye koma meye da yake zuciyarta ba.

"Maamah" Ya kira sunanta kai tsaye da wani irin sauti bayan ya yiwa masu aikin alamar su fita. Jajayen idanunta ta daga ta kalleshi dasu,tana da magana fal bakinta saidai ba damar hakan.

"Kiyiwa Allah.....kiwa manzon Allah......na roqeki ko meye muka yi miki a rayuwa.....ba domin kanmu ba don lafiyar jikinki ki manta da komai........ki duba girman Allah ki sassautawa zuciyarki......haba mana!" Ta furta da wani irin bacin rai da yakeji yana taso masa.

Idanu tsaf ta zuba masa,abinda ke nuna inda bakinta a bude yake tabbas da yaji maganganu,saidai ko a iya kallonta a kansa kawai ya shaida masa maganarsa ta shigeta da wani kalar mamaki.

"Ba wanda ya isa ya canza qaddarar wani.....ba wata qaddara da zata sauya kanta da kanta sai wadda ubangiji da kansa yaso sauyata.......ba wani dan adam da zai tsarawa wani rayuwarsa......kowa da yadda Allah ya tsara masa.... Me yasa ba zaki hutar da zuciyarki ba?" Ya sake fadi yau din yana jin zuciyarsa takai maqura.......a yau din yana jin yana yanke dukkanin tsammaninsa da sauyawar halaye da dabi'un maamah.

"Ki yafe mana idan mun miki wani abun.....me zaki ragu dashi?" Ya qara tambayarta yana kallonta. Ba amsa,amma still hawayen basu daina fita ba

"Ko bayan an cuceka ka yafe.....ba zaka ragu da komai ba sai qaruwar daraja a gunka......ki yafe mana indai mun miki laifi muddin kedin ke kika haifemu" Ya qara fada yana hade hannayensa waje daya alamun roqo.

"Indai kun yadda ni din nice na haifeku me yasa ba zaku yimin abinda nakeso ba?,indai kun yarda nice na haifeku me yasa ba zakubi umarnina ba?,me yasa ba zaku kwanta nayi muku mulki irin na isassun iyaye ba?,me yasa ba zaku fahimci asiri akayimin ba?,me yasa ba zaku gane ba hawan jini bane wannan?!" Wadannan sune kalaman da suke ta kokawa a qirjinta suke koma neman hanyar da zasu fidda kansu,saidai kuma ba wannan damar,illa hawayen baqincikin rashin samun damar magana da batayi ba da suka sake wanke mata fuska.

Tsam ya miqe kawai,ya kama hannun amna da jikinta ya sakeyin laushi qwarai bayan aman da tayi,ya miqa mata takalminta ta sakawa qafafunta suka fice a parlor din sabreen da maamah na binsu da kallo,kowa da mabanbancin yanayi cikin zuciyarsa.

Tausayin musaddiq da hammanta kullum take kwana take tashi,bata tunanin duk yadda sukaso maamah ta shiryu idan har ubangijin daya halicceta bai shirya mata hakan ba saidai kowa yayi haquri. A zuwan da take dubata da duba yanayin gidan da masu kula da ita.....ba kalan lokutan da bata kebe ba zaune da ita,daga ita sai maamah din ta karanta mata dukkan kalar wata nasiha me ratsa jiki da zuciya......amma bata taba ganin alamun rusuna ko sanyi daga idanuwanta ba.

β˜…"laila" Hajja harira ta sake kiranta karo na biyu. Daga kai lailan tayi wadda ke zaune qasan carpet din dakin ta kalli mahaifiyar tata.

"Na'am hajja" Ta fadi dukkanin wani lungu da saqo na zuciyarta dama gangar jikinta suna azalzalarta,tana jin kaman wuta ake hurawa sassan jikinta dama zuciyarta.

"Wacece ni?"

"Mamana ce" Ta amsa mata Kai tsaye idanuwanta kafe a kanta.

"Alhamdulillah" Hajja ta fadi tana sakin murmushi. Cikin zuciyarta cike fal da godiya ga bokan da yayi mata aikin farraqu tsakanin maamah da laila,ya gaya mata cewa wannan din qaramin aiki ne da zai iya aiwatarwa,ya mata alqawarin sai yazo duk duniya ba wanda laila taqi jini taji koda sunansa sama da hajiya mariya.

"Zaki koma wajen maamah mariya?" Hajja ta gwada tambayar laila. Shuru ta danyi na wasu sakanni,sai kuma ta girgiza kanta da qarfi.

"Bana so,bazan koma ba,ina wurin hajja na". Ta fadi bawai don tana nufin abinda ta fada din bane da gaske har zuciyarta.

Da dariya ta qyalqyale sosai,farinciki yana cikata,lallai laila dinta ta dawo,ta dawo hayyacinta.

" Na godewa Allah daya dawomin dake hayyacinki laila" Murmushin qarfin hali ta sakarwa hajjan,tanason ta sake bata tabbaci da yaqinin ta warke don ta ware mata takunkumin hana fita da sanya masu gadi su hanata fita ko nan da can. Ba abinda takeso irin taje wajen maamah,ta duqufa tayi ta mata bauta iyakar qarfinta.

"Na warke hajja in sha Allahu,kawai zaman cikin gidan nan ne hajja na gaji.....ko cikin layinnan kya barni na tattaka da qafafuna ko?" Ta fada a shagwabe kaman yadda take mata a baya.

Fuska hajja tadan bata tana dubanta.

"Aah......ba yanzu ba laila,matar nan makira ce,duk da ance tana can tana jinya amma ba Allah a ranta,kina kallon yadda take kidnapping 'ya'yan jama'a fa?" Hajja ta fadi tana nunawa laila girman ta'addancin maamah.

Wani irin tashin hankali da kuma bacin rai ne suka bijirowa lailan,ta tabbatar yau ko gobe Hajja ba zata barta ta fita ba bare ta koma wajen maamah,kenan ba amfanin rayuwarta ba tare da maamah ba?". Ta yiwa kanta wannan tambayar.

A take taji indai za'a yanke alaqarta da maamah bata da wani amfanin rayuwa,don haka ta miqe tsam.

"Bari naje kitchen nasha ruwa"

"Ki tahomin dashi" Ta fada hankalinta kwance don tasan a kitchen din dai ba wata hanyar fita daga sassan ma bare akai ga gidan.

Idanu kawai take warawa sanda ta shiga kitchen din,gaba daya kwanyarta a birkice take,neman abinda zatayi amfani dashi kawai take yi idanunta suka sauka kan gas.

Da sauri ta qarasa wajen,ta saka hannu ta kunna dukka makunnansa guda hudun da yake dasu. Fita ya fara yi sosai,kafin kace meye wannan warinsa ya mamaye kowanne sashe na part din hajjan.

Hancinta sosai hajja ta dinga budewa tanason tabbatarwa warin gas dinne?. Da wani irin sauri ta duro daga saman gadon tayi kitchen da mugun sauri. Duka masu aikinta ba kowa yau ballantana tayi tunanin wani ne a cikinsu,laila kawai tasan ta shiga kitchen din.

Cak ta tsaya daga bakin qofar falon,qafafuwanta suna rawa zuciyarta na wani irin gudu mara fasali. Laila ce tsaye a kitchen din riqe da lighter,idanuwanta fes kan hajja dake tsaye daga can bakin qofar kitchen din.

"Laila.....laila baki da hankali ne!!!" Hajja ta fadi a birkice ganin lailan tana qoqarin motsa yar robar data tare bakin lighter din wadda ita zata bata damar tashi. Wani kalar murmushi ta saki tana duban hajjan

"Kina tunanin zan iya rayuwa ba tare da umarnin maamah ba?,ko kina tunanin zan iya rayuwa a inda babu ita?.....sai watarana hajja" Laila ta fada cikin qwarin gwiwa.

A gigice hajja ta bude baki tana son gaya mata cewa.

"Kada ki kunna laila.....indai mariya c na bar mata ke har abada,ki hada kayanki ki koma gareta" Saidai dukka wadannan kalaman basu samu damar fita daga bakinta ba sai hucin tsananin atsabar zafin wuta da qarar bindigar fashewar tukunyar gas din da suka cakude waje daya aka wullota waje,wanda daga nan bata sake sanin abinda yake faruwa ba.

Qarar fashewar taja hankalin sassan matan 'ya'yanta da masu gadi dake waje,kafin balbalin wutar ya tashi hankalin kowa suka nufo sashen hajja din.

Duk saurinsu turus kowa yayi,saboda wata irin muraddiyar wuta ce me azabar duhu da Zafar tana harshe ke cin kowanne sashe na hajja din. Babban sashe da yafi na kowa cikin gidan girma kyau da tsaruwa,sashen da idan ka kalleshi ka kalli na matan 'ya'yanta saika dauka su din duka sashen ma'aikatan gidanne wato boys quarters,duk kuwa da cewa mudin na mazajensu ne,dasu akayi wahalar nema da kuma samu.

Tashin hankalinsu waye da waye a ciki?,suna tsaka da son tantancewa sukaci karo da hajja yashe a qasa,wadda babban jikanta ne kawai ya iya gane itace,saboda shi dinma ya shiga dazu kai mata wankinta ya gane atamfar jikinta,fuskarta kaf da kafadunta zuwa qirjinta sun koma jazur kaman an shafeta da jar hoda saboda yadda wutar ta kwaye asalin fatarta.

"Na shiga uku......wayyo Allah na..... Wayyo laila......laila kada ki mutu ki barni......laila bansan kanki abunnan zai koma ba,wallahi laila bake nace a bawa kici ba......laila don Allah ki fito laila......naci buri a kanki,na shiga uku" Sune maganganun data dinga fada tana ihu tana kururuwa gami da zabura,azabar zuciya dana gangar jiki duka sun isheta aka wuce da ita asibiti cikin ambulance bayan anyi kiran fire service suzo su tsaida watar kada ta soma lasar sassan gidan.

Abun kamar film kamar almara,ana fita da hajjan sanda wutar ta cinye sassan sarai,surukanta dukka dake tsaye a wajen sai kowacce ta dafe kanta.

"Wayyo Allahna.....wash Allah na.... Wayyo kaina" Shine abinda suka fara fadi a jejjere,kafin kace meye wannan sai gasu duka su ukun a zube warwas a qasa sun sume.

Akwai wani malamin makarantar almajirai dake a wajen,kallo daya yayi musu yace basai an kaisu asibiti ba,babban falon gidan yasa aka ajiyesu,ya karbi ruwa yayi musu tofi sosai ya bawa mazajensu yace a yayyafa musu idan sun farka a bawa kowacce tasha.

Cikin qasa da minti biyar sai gasu a zaune,kowaccensu kuka takeyi wiwiwi

"Wallahi saika sakeni......wallahi bazan sake zaman bauta ba..... Idan ta dawo kuma me ya rage mata?,inajin sujjada zata saka mu koma yi mata" Shine abinda matan kowacce ke gayawa mijinta cikin kuka. Duka falon sai ya rikice,ga gobara a waje ga tashin hankali a cikin gidan,su kansu mazan a rude suke,don sam duka abinda matan ke iqirari akai ba wanda yasan anyi a ciki.

Gyaran murya malamin yayi ya kuma nemi su bashi hankulansu. Bayani ya musu me ratsa jiki game da lamarin,kusan abune da kaf unguwar ake magana akai yadda take bautar da uban kowa cikin gidan,kusan duk me hankali yasan aikin sihiri ne.

"Indai har zaku yarda da shawarata ku yafewa mazanku,ku sake sabon zama dasu don ba cikin hayyacinku dukka kuke ba,wataqila wannan gobarar ta qone duk wani binne binne ne shi yasa komai ya warware kansa.....sai ku bita da addu'a Allah ya bata lafiya ya sake fahimtar da ita ainihin rayuwa.....". Da wannan bayanin nasa ya kashe wannan qurar,hankula kuma suka koma kan wutar dake ci wadda an fara samun daman kasheta.157


β˜…Tana kwance saman kyakkyawan gadon,sanye da fara qal din abaya har veil din da tayi rolling dashi,kaman yadda siraran abun hannun azurfa da zobensa da set din dan kunnensa suka sake qawata mata shigar tata.

Duk da tsufa da nauyi da cikinta yayi hakan bai hanata ado ba......duk da yadda take komai da qyar amma bata yarda ta bari tayi mummunan kama ba.

Ko a yanzunma akan gadon scanning take,daga daidai kanta kuma muhammad fuad jadda ne. Sanye yake da farar jallabiyya ta maza saqar morocco wadda ya yiwa ado da farin hirami daya zauna sosai a kansa,saika rantse da Allah dan asalin qasar saudiyyan ne. Wani irin ajiyayyen kyau na musamman shigar tayi masa,jikinsa da fatarsa dukka suna nuna zallar hutu da jin dadi gami da cikakken sukunin rayuwa da Allah ya bashi. Saman kujera hake,hannunsa cikin tsakiyar tafin hannunta,ya sarqafe yatsunta cikin nasa.

Daga shi har sabreen din idanuwansu suna kan allon computer din,wanda balarabiyar ke yawo da kan na'urar saman cikin sabreen din da yayi wani irin girma.

Sai data kammala scan din tsaf,sannan ta dora hannunta saman board din computer ta danna tana maidashi 3D scan gami da cewa cikin harshen larabci.

"Sa'ureekum shai'an" Ta fada tana murmushi.

"Na'am" Ya fada yana matse hannun sabreen cikin nasa. Maida mouse din tayi saman cikin sabreen din,ta matse hoton cikin take yara guda uku suka fito sosai.

"Allahu akhbar.......subhanallah" Fuad ya fada muryarsa tana rawa. Damqe hannunsa sosai sabreen tayi itama cikin nata,ta kasa magana kaman yadda fuad shima ya kasa cewa komai face tasbihi ga Allah buwayi gagara misali. Yaran na kwance irin kwanciyar jarirai uku cikin mahaifiyarsu,kamanninsu sosai ya fito,har ya dinga jin kaman ya saka hannu ya daukosu.

Cikin qwarewa take juya na'urar tana zoom in musu yaran daya bayan daya. Qosassu kuma lafiyayyu ko a ido,wanda ko daga yanayin girman cikin sabreen din shi kansa yasan qosassunne,duk da akance abun ba daga girman cikin bane.

Murmushi ya subuce masa wanda ya taho da taruwar hawaye cikin idanunsa ganin daya daga cikin yaran da tayi zoom in din babban yatsansa na cikin bakinsa kaman me shan hannu.

"Astgafirullah......alhamdulillah......subhanallah walhamdulillah wallahu akhbar" Abinda ya dinga fadi kenan,yana jin kaman kada ta daina nuna masa fuskokinsu,saidai kuma dole saboda ayyukan da suke gabanta.

Sauke na'urar tayi itama murmushi yana qwace mata,ita kanta yaran sun burgeta,ta kuma jima bataji jariran da taji tanason ta gansu fuska da fuska ba irin yaran. Bata sani ba,ko hakan yana da alaqa da yadda ma'auratan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login