Showing 375001 words to 378000 words out of 557259 words
gareni......na roqeshi kada ya baki ikon barina koda kina da nufin aikata hakan.......ya mallakamin rayuwarki gaba daya daga farkonta har qarshenta.......sannan na roqeshi ya bani 'ya'ya masu yawa ta jikinki.....duk shekara so samu ki haifemin tagwaye ko uku uku......"
"Please mana" Batasan sanda ta tsaidashi da fadin wadannan kalmomin ba. Tunda ya fara jero mata abinda ya roqa din zuciyarta ke wani irin bugu,ta sani gurin da yake wajene da babu wasa a cikinsa.....wajene da komai ka roqa amsashshe ne a wajen Allah......tana tsoron kada addu'arsa ta cita.....kada ta kamata,idan hakan ya kasance ina zata saka burin rayuwa tare da 'yan uwanta bisa kyakkyawar rayuwa?.
Dan qaramin murmushi ya subuce masa yana jiyo alamun tsoro cikin sautinta.
"Tsoron me kike haka?,akwai cutarwa cikin addu'ata?" Ya tambayeta yana ji a ransa inama hirar zatayi tsaho tsakaninsu.
Kai ta girgiza kaman yana gabanta,da gaske tsoro yana sake cikata.
"Wannan son kai ne.....zallar son kaine a cikin addu'arka,ka roqi Allah wani abun daban ba wannan ba" Tayi.maganar da dan hasala a muryarta tana ganin kaman da gayya yayi hakan. Boyayyen murmushi da bai bari taji sautinsa ba ya subuce masa.
"Me ruwanki da abinda zan roqa Allah yayimin?"
"Ina da ruwa dashi.....saboda a kaina ka roqi ubangiji...."
"Ke kuma kina tsoron hakan ya tabbata?.....to idan akan wata daban na roqa fa?" Shuru ya ratsa kunnensu na wasu sakanni kafin yaji tace
"Wannan kuma ruwanka bana sabreen ba" Ta samu kanta da fada,sannan ta gimtse wayar tana kasheta gaba daya.
Yaji saukar layin nata,sai ya zame wayar daga kunnensa murmushi yaqi barin fuskarsa. Me yasa tun asali baiyi dabarar bata waya ba kaman haka ya kuma kafa mata sharuda ba,haka hira da masoyi take da dadi dama?. To amma wani hanzari ba gudu ba.....me yasa tayi shuru sanda yayi mata tambaya ta qarshe kafin tace ruwansa?.
Maido fuskar wayar yayi saitinsa,ya rubuta mata gajeran saqo ya tura mata,ya koma ya kwanta rigingine wayar ba rungume a qirjinsa. Wani murmushi ke fita saman fuskarsa kadan kadan,zuciyarsa cike da fatan saisaita kansa akan yarinyar.....don da haka ne kawai zai saitata a hanyar da yakeso ta tabbata a kai.
Shidai baisan ya akayi bacci yayi awon gaba dashi ba,saidai ya cika mafarkansa duka,cikin kowanne gani da zai mata cikin qauna soyayya da kuma kulawa. Harda wanda ya gansu kewaye da yara qananu masu kama dashi sosai. Wannan mafarkin shi ya haska asubarsa,ya shiga bandaki ya daura alwala cike da wani kwantaccen farinciki qasan ransa.
Cikin jallabiyya 'yar Indonesia fara qal ya shirya ta maza,ya shafe jikinsa da lallausan turarensa ya saka hular tashi ka fiya naci saman kansa fara qal itama,ya dauki tasbaharsa counter data kasance farar itama.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 90
90
Wayarsa ya zura a aljihunsa bayan ya duba number dakin maamah. Kai tsaye can ya nufa yana tafiya da cikakkiyar nutsuwa a tare dashi,bakinsa dauke da ambaton Allah. Yanaso ya samu sahun gaba gaba,wannan ya sanya yake tashi da wuri koda yaushe,ya kuma isa masallacin da wuri.
Kallon kallo suka yiwa juna shi da maamah din,alamu sun nuna tashinta kenan a bacci. Bata ce masa komai ba ta saki qofar ta juya zuwa ciki ya bita a baya. Guri ya samu ya zauna yana duban dakin dake cike da kaya wanda ya tabbatar tsaraba ce. Yaushe ma taxo?,yaushe ta samu daman yin ibada sosai har ta fada yin wata tsaraba?. Duk abinda zata siya din ba abinda bata dashi a gida,amma fadan hakan kaman laifi ne a wajensa.
Bandaki ta shiga ta daura alwala sannan ta fito,tana sauya hijabin jikinta ya soma gaidata kaman yadda ya saba cikin bata haqqinta na uwa daidai misali na girmamawa.
"Ka shigo tun jiya.....sai yanzu aka baka daman zuwa inda nake?". Idonsa ya kawar,shi yasan ko.meye zai faru tsakaninsa da maamah din bame sauqi bane,saidai ko meye ya gayawa Allah yana kuma da yaqinin komai zaizo masa cikin sauqi.
"Nayi qoqarin kiranki ban sameki ba,na aje miki saqo na dauka zaki amsa,banyi zaton a irin lokacin zan sameki a daki ba shi yasa na koma na huta,sai bacci ya daukeni" Ya fada a taqaice. Qwafa kawai taja tana qare masa kallo a fakaice. Ita kadai tasan me takeji a ranta,ita kadai kuma tasan me ta shirya zata aiwatar.....tana ji a ranta idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba lallai ta cika lusara asararra,wala'alla fareeda din itace wannan hasken nasarar guda daya da boka ya mata albishir dashi.
Har ya gama shiryawa suka fice tare bata sake cewa komai ba,dama ba wani sabo ko shaquwa tsakaninsu ballanta hira me kama da irin wannan ta biyo baya.
Zata iya cewa bata taba samun sallar asuba irin haka ba kaman yau,basu bar masallacin ba sai da gari yayi haske,suka hadu gaban hotel din nasu ya dauketa yin breakfast duk da akwai bada breakfast a tsarin hotel din nasu.
Ba wani abu ya karba ba illa coffee,itakam abubuwa da yawa yasa aka ajiye mata,yana sipping coffee din nasa amma hankalinta yana kanshi. Inama ace wannan kulawar ita daya a duniya yake bawa irinta?,inama yadda suka zauna a haka haka yake zama da ita koda yaushe yana kula da duk wani motsinta......yana jira yaji umarninta ko haninta?.
"Muhammadu" Ta krashi bayan ta gama tauna yadda zata fuskanceshi. Burinta a yanzu bai Gaza ganin fitar sabreen cak daga rayuwarsa ba. Da idanu kawai ya amsa mata ta hanyar kallonta.
"Wacce irin mace kake aura mara hankali da tunani kuma mara kirki Muhammadu?". Gaba daya sai maganar tazo masa a bazata,ya kasa kuma fahimtar abinda maamah keson cewa.
"Banda yarinyar nan bata da kirki bata da mutunci batasan girman uwar mijinta ba.....bata taba kirana ta gaidani ba?,bata taba tambayar lafiyata ba.....bata ma taba nemana ba wai sunan tana auren d'ana?,ni kuwa wallahi ba'a haifi diyar da tana auren dana kuma zata min riqon sakainar kashi ba" Ta fada cikin fada sosai tana dan dukan table din da suke kai kadan.
Zame hannunsa yayi daga jikin mug din yana zubawa maamah din idanu. Zaren tunanukansa suna qulluwa waje guda cike da wani irin mamaki. A nan dimma akwai wani qullin?, ya tambayi kansa da kansa. A abinda yake kallo akwai cikakkiyar fahimtar juna tsakanin maamah da sabreen wanda shi ya zama silar daukota zuwa rayuwarsa,a yanzun me ya bata wannan alaqar da jikinsa ya jima yana gaya masa gurbatacciya ce?,to kodai zai samu wani hint din a nan ne?.
Tabbas inda a watannin baya da suka shude maamah ta fadi haka akan sabreen bazai dameshi ba.....in fact ma zai dauka ta fara gane wacece menene kuma halinta,amma kuma a yanzun sai yaji kalaman kaman sunyi tsauri da yawa. Ya shirya tare mata fada ko batanci kowanne iri ne kuma koda waye,don haka ya gyara zamansa yana fadin.
"Maamah.....inajin kinfi kowa sanin wacce iri ce sabreen.....tunda daga hannunki ta fito,kuma na tabbatar ba zakimin zaben tumun dare ba.....amma maganan waya bata da waya,duka wayoyinta suma hannuna". Har tsakiyar kanta taji wani abu ya tsarga mata,wato ita yarinyar zata gwadawa bariki ta bashi wayoyinta?,a tunaninta yin hakan shine zai sanya ta tsallake tarkunanta?. Ta jima tana zaton salwantar da wayoyin tayi,wannan yayi saving nata bata taba gwada Kiran layukan ba,inda ta kira din kenan yana iya zargar komai ko ya binciko komai?.
"Sannan kiyi haquri zan mata fada zata gyara" Ya sake fada yana kallon reaction na maamah din. Yadda ta daga kai da sauri tana dubansa ya sake bashi wani qarin percentage na zarginsa a kanta. Yaushe alaqa tayi nisa tsakaninsu da yake kareta?,yaushe ma duka duka ta kirashi ta masa jan kunnen ya kula da ita?,bariki ce ko nata kalar tsubbun ta shayar dashi kaman yadda jikinta keta bata zata aikata haka?.
"Ai karma ta gyara....ni d'ana bazai auri mace daya ba ballantana ta samu daman juyashi da zaton nata ne ita kadai,don haka ka shirya........na zabar maka fareeda mazaunin matarka ta biyu......muna komawa da sati biyu kacal zaayi komai a gama.....don banajin tafiyarka da sabreen zatayi nisan zango,akwai canje canjen dabi'u da halaye da nake ji a tattare da ita" Sosai yake kallonta,ba kuma don komai ba sai don maganganunta masu kama da almara. Auren fareeda wannan yasan wani abune da bashi da maraba da tatsuniyar gizo da qoqi,uwa uba ma fareedan dukkaninta ba damuwarsa bace,don tana under control nashi,kowanne motsi nata yana sane dashi.....abinda kawai yaja hankalinsa shine zancan sabreen. Wanne sauyin halaye take ji game da ita?,meye dalilinta dukka na damuwa da al'amuranta?. Wanne laifi mutumin da baka jinsa ko ganinka yayi maka da zata dinga zarginsa da aza masa laifi kacokam haka?.
"Kar kayi kuskuren cewa zakamin gardama akan auren fareeda,nasani sarai shurunka yana nufin abubuwa da dama.....muna dab da muhallin amsa addu'a,zanje gaba ga Allah na roqeshi ya fiddamin haqqin haihuwarka da nayi" Idanunsa ya lumshe maganganunta suna sukarshi. Baisan me yasa ako da yaushe barazanarta iri guda bace a kansu,yadda ta damu da neman haqqin Allah a kansu bata damu da nema musu albarka haka ba?.
"Relax.....cool down.....badai fareeda bane matsalar?" Kai ta jijjiga
"Itace"
"Done" Ya fada da wata ma'anar ta daban. Shi kadai yasan me ya sake shiryawa me kuma zaiyi. Binta da kallo yake kawai sanda taci gaba da cin abincinta,yana hangen tarin sassauci data samu can boye cikin fuskarta da karbar zancan fareeda da yayi. Wani irin quna zuciyarsa keyi musamnan idan ya tuna duk wannan abun da takeyi fa siyanta fareeda kenan tayi. TO TA YAYA TA HADU DA SABREEN?,MENENE SILAR HADASU AURE DA ITA?,MEYE MANUFAR?. Wasu tambayoyi da suke masa susa a qirji,ya tabbatar tunda take muradin hadashi da fareeda bisa wats manufar.....tabbas haduwarsa da sabreen ma akwai manufa,saidai ita sabreen yasan bata da kudin da zata siya maamah.....to meye SILA?. Ba wadda ta fado a ransa a sannan sai hajja,a take kaman an cillota cikin tunaninsa,saboda muhimmancin abun a take ya ciro wayarsa ya tafa qaramin massage ya tura yana cewa.
_ina buqatar kowanne motsi na rayuwarta ya zama abun bi kafin na qaraso,bata buqatar kamu,amma ina buqatar ayi mata daurin talala_ sai daya tabbatar da shigar saqon sannan ya maida wayar aljihunsa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 91
91
Sosai maamah tayi amfani da wannan damar ta dinga karbar kudade daga hannunsa tana tsaraba. Baice komai ba don ba wannan muhallin bane,bai kuma hanata siyan abinda duka take so ba.
β
*_makka to Maldives_*
Kwanaki shida sukayi a maimakon kwana biyu ko ukun da ya tsara zasuyi. Kusan ita ta dinga jan kwanakin duka a nufinta na tafi da tsarinta yadda takeso. Abu daya ne kawai yake dan bata mamaki,yadda take kasa samun wayar fareeda kwata kwata,ta gwada dukka layukanta amma ta gaza samunta,mamakinta yana sake daduwa idan ta irga kwanakin taga ko sau daya bataga gilmawar kiran fareedan ba.
Sun sauka Maldives dab da sanda rana ke shirin faduwa,wannan ya sake haska tsibirin ma'abocin ruwa da wani irin yanayi me daukan hankali.
Baki kawai maamah ke tabewa,a zahirin gaskiya ba zata ce island din baiyi mata ba,saboda guri ne da yafi kama da aljannar duniya,amma baqinciki da bacin rai suna cikata idan ta tuna cewa ahalin alhaji hamza suka zabi wajen. Ranta ya sake baci sosai cikin wani irin baqinciki da fushi sanda taji tsadar da rayuwa cikin tsibirin yake dashi,da kuma yawan adadin kudaden da ake kashewa kowanne kwana daya cikin resorts da sauran guraren dake kewaye da wajen.
"Nikam banga abun burgewa a nan waje ba.....guri duk ruwa,koda yake ba lafinka bane.....kai ka zama dan amshin shata ne kawai sai abinda aka tsara maka,kuma tsabar zallar mugunta ne saboda basusan zafin dukiyar ba,ba tasu bace......dolla million nawa ka kashe musu?" Ta maida tambayarta ga fu'ad dake zaune a gefanta cikin motar da Jordan yazo daukarsu.
Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana rufe idonsa gami da budesu,tunda yake bai taba jin kwanaki masu wahalar wadannan ba,wadansu irin kwanaki ne da sam babu armashi a cikinsu. Ya sanya ran samun nutsuwa daga wajen sabreen tun ranar farko data daga wayarsa,saidai kuma bai sake samunta a waya ba har yau da suke dawowa qasar.
"Farouq ne ya dauki nauyin komai" Ya bata amsar da azahiri haka take,gida ne kawai zai iya cewa nashi sai jet din da suka taho a ciki. Idanu ta dauke tana tabe bakinta.
"Haka dama zaka ce,saboda kana qoqarin basu kariya,ina jiye maka ranar nadamar damqa ragamar rayuwarka a hannun mutanen da basusan ciwon haihuwarka ba.....gefe daya ga matar da nake kyautata zaton zuwa yanzu sun hada baki da ita don su sake cimma manufofinsu" Gaba daya maganganunta baya qaunar jinsu,baya iya daukan kowanne mummunan kalami a kan ahalin alhaji hamza kibiya din. Sun masa komai a rayuwa,idan yace komai yana nufin komai din,don wataqila idan bacin su da yanzun baisan rayuwarsa a wanne matsayi take ciki ba.
Duk maganganunta yayi shuru yana jinsu,qananun mitoci ne da basu da tushe ballantana makama. Banda zata fassara abun da wani yanayi na daban tabbas da gida daban zai kamata tayi zamanta ita kadai,saidai hakan yasan ba mafita bace,ba abinda zai sake jawowa sai wani damuwan na daban.
Tun anesa ya hangi musaddiq da saddiq zaune daga gaban gidan. Sanye suke da kaya iri daya black jeans da white din t.shirt. Tsaf zakayi tunanin twins ne saboda yadda komai nasu ya kusan zama iri daya.
Sosai maamah ta qanqance idanu tana dubansu,wani irin abu yana tsarga mata
"Turqashi" Ta furta qasa qasa. Da alama ameenatu tana ci gaba da mamayar komai daya kasance mallakinta. A sanda hankalinta yayi nisa,ta dogara kuma da sabreen hakan sai ya zamana kaman ta bawa ameenatu wata qofa ko dama naci gaba da baza mallakarta tsakanin yaranta. Ba zata iya tuna watanta nawa bataga musaddiq ba,jininta.....tsatsonta,ya gaya mata fu'ad dinne ya aikeshi wani aiki dubai da Qatar,amma yanzun gashi tare da ameenatu,gashi manne da ahalin alhaji hamza kibiya.
Tsaiwar motan yaja hankalinsu su duka,motar ba baquwarsu bace don haka dukkaninsu suka miqe zuwa gaban motar.
"Barka da zuwa maamah" Musaddiq ya fada yana niyyar karbar jakar hannunta. Kasa jurewa tayi ta jefeshi da harara duk data sakar masa jakar.
"Uwarka ta taso daga wani gurin amma ka gaza zuwa airport tarbarta kana nan manne da uwar wasu?". Maganar ta masa ba dadi har hakan ya bayyana saman fuskarsa. Yadan basar yana amsar jakar sannan yace.
"Hamma ne.....bai bada assurance na yau din zaku taso ba".
" Barka da zuwa maamah ina yini?" Saddiq ya fada yana dan matsowa kusa da musaddiq. Waiwayowa tayi,ta aje masa wani kallo tun daga sama zuwa qasa kafin ta amsa masa sheqeqe tana bin bayan fuad zuwa cikin gidan. Koda riga ta gani a jikinsu baqincinta takeyi,gani takeyi kudin fuad ne ya siya musu wannan riga takalmi da kuma daular da suke ciki ma gaba daya. Tana ganin sunyi amfani da nasibin danta ne kawai suna morarsa bayan sun rabata dashi.
Tunda ta idar da sallar la'asar take manne da earpiece a kunnenta tana sauraron karatun littafin umdatul ahkam. Sanye take da Indonesian set skirt ne da hijab dinsu madaidaici sai rigar da iyakarta qugunta. Dark green ne da suka haska fatarta sosai,ta tattare gashinta ta daureshi tsakiyar kanta bayan amna ta gama jagwalgwala matashi da sunan zata mata kitso. Ta kasa kitson saboda santsinsa,don haka ta bisu da hair clips ta tattare mata shi,ita kuma ta daureshi da ribbons don tace ba zata saka mata hair ppin ba. Kayane masu taushi da sakewa a jiki,duka anni ce ta saya mata su kusan kala shida.
A kwana biyar din sauqi ya samu sosai,ita kanta a jikinta takejin ta warke da taimakon wasu irin herbs 'yan Indonesia da anni ta bata.
A kwana biyar din ta wani murje,hankalinta kwance bata ganin wulgawarsa bare fargaba ta dameta. Hatta anni ta karanci yadda hankalinta ya sake kwanciya,ta daiyi murmushi kawai saboda tasan tsakanin miji da mata sai Allah,bare wadannan data fahimci yanzu ne yake fafutukar gina gwamnatinsa.
Batasan me za'ayi ba a gidan,don duka hankalinta yana kan karatunta,itadai ta shiga kitchen tana taya amna da anni girki. Annin ta fara fita ta barsu a ciki,amna ta fidda Warmers din tana shiryawa,ita kuma ta tsaya tana gyaran kitchen din.
Idanunta d'ai d'ai cikin parlor din tana kallon wata sabuwar duniyar. Fuad ya dauke idonsa a kanta