Showing 432001 words to 435000 words out of 557259 words
Ya kirata a tausashe murya a karye kaman wanda baison kowa yaji sirrinsu. Kiran da yayi mata har cikin tsokar naman jikinta,ya kuma aike mata da saqo ta cikin jinin dake gudu a jijiyoyin jikinta. Labbanta ta motsa kadan tana amsa masa da
"Na'am" Sai ya lumshe idonsa labban nata suna daukan hankalinsa.
"Ina dauke da wani albishir ameenatu,yayi girma da nauyi sosai a qirjina" Ya qarasa fada yana zame hannunsa daga cikin nata,sannan ya maida kansa ya kwantar saman cinyoyinta kamar wani qaramin yaro.
A hankali ta daga hannunta ta dora saman sumarsa tana nutsa yatsunta a ciki,laushin sumar da santsinta suka ratsa yatsun nata,sai suka sauke ajiyar zuciya lokaci guda shi da ita kowa yana jin soyayyar dan uwansa tana keta jininsa.
"Ameenatu wannan zuciyar da wannan gangar jikin duka naki ne.....kulawarki take buqata kici gaba da bata muddin kinaso ta rayu yadda ya dace" Ya fada yana jin yadda bugun zuciyarsa ke daduwa daga yadda take yamutsa sumar kansa kawai.
"Zaka samu sabreen fiye da yadda kake fata.....zaka samu dukkan wani cikar burikanka a tattare da ita.....harma abinda tunani bai taba baka ba". Maganarta ta tsumashi sosai,ta kuma sakashi daga kanshi daga cinyarta. Idanu ya zuba mata sosai yana kallon qwayar idanunta,sai itama ta samu kanta da mannewa kallon nasa,kafin ya miqe a hankali tsaye a gabanta.
Hannuwansa ya miqa mata,sai itama ta aza nata ciki ya tashe tsaye sannan ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki ya maida hannuwansa ya lullubeta da kyau.
Ajiyar zuciya ce ta subuce masa,ya kwantar da kansa saman kafadarta.
"Sabrrrrr........kinsan kin bani wata kyauta da ba wani dan adam daya taba bani makamanciyarta?" Ya soma da jefa mata tambayar data kasa gane ma'anarta. Shurunta ya fahimtar dashi cewa ya sanyata a duhu,don haka ya zare jikinsa a hankali sannan ya juyata ya rungumeta ta baya yana sake nutsata sosai cikin jikinsa. A tausashe ya dora duka tafin hannunsa saman mararta,ya dora habarsa saman kafadarta yana saka tausasan labbansa saitin kunnenta.
"Sabrrrrr......you're pregnant......ciki ne dake,cikin muhammad jadda......zaki zama uwar 'ya'yana ameenatu". Wani irin abu ne ya tsarga mata tun daga tsakiyar kwanyarta har tafin qafarta,bugun zuciyarta ya qaru sosai. Samun kanta tayi da saka nata tafin hannun saman nasa dake mararta tun dazun,ta kasa fadin komai,don duk kalmar data kamo sai taji ta qwace mata,tana ci gaba da sauraren saukar numfashinsa cikin kunnenta.
"Are you happy sabrrrrr?" Ya tambayeta a raunane yana fatan ya sameta cikin irin yanayin da yake jin kansa shima.
Kai ta gyada a sanyaye,tanajin wani irin yanayi yana ratsata,mamakin yau itace wai dauke da ciki?,itama zata zama UWA?,zata haifi d'a ko 'ya a cikinta?,abun kamar cikin mafarki.
"Alhmdlh" Ya fadi yana sauke mata tattausan kiss a wuyanta,a hankali kumya ja dawo da ita tana facing dinsa sai ya rungumeta tsam a jikinsa.
Shuru ya ratsa tsakaninsu na sakanni,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa ta cikin kunnuwanta dame kwance a qirjinsa,sosai kaman akwai wani abu dake taba zaman lafiyarta,kusan minti biyu sannan ya sauke sassauqar ajiyar zuciya a sanyaye sannan ya dagata daga jikin nasa yana kallon fuskarta. Qwayar idanunta ya laluba ya saka nashi a ciki,da wani irin coolness ya sake kiran sunanta.
"Kinji yadda zuciyata take bugawa ko?" Ya jefa mata tambayar yana lalubar tafin hannunta ya matse gam cikin nasa. Kasa amsa masa tayi da baki sai kai data gyada mass,saboda cikin idanunsa abubuwa ne masu yawa ta gani suna yawo.
"Sabrrrr.....na gode da kika karbi ajiyata da sauri haka......inajina kaman ni kadai nake rayuwa cikin duniya......ashe rashin haduwa da tawa DUNIYAR shine sila......sabrrrr......bansan dame zan saka miki ba......bansan kuma da meye zan gode miki ba....kome na kalla sai naga kamar yayi kadan,alfarma daya kawai nakeso ki yiwa rayuwata.
Kallonsa da kalamansa gaba daya qara kashe mata jiki sukeyi,mamakin irin tsananin son da yakewa yara ne yake sake kamata,ta motsa labbanta a hankali
"Tame?"
"Kiyimin alqawari zaki rayu dani....kiyimin alqawari ba zaki taba rabuwa dani ba.....kiyimin alqawari zaki zauna dani,da dadi ko babu.....cikin wadata ko talauci.....sabrrrr kiyimin alqawari ba zaki taba tafiya ki barni da yara ba.....zaki zauna dani dasu a duk yadda nake ko suke,mu rainesu tare.......kiyimin wannan alqawarin sabrrrr cikin wannan garin me tsarki". Idan ba qarya idanunta sukayi mata ba hawaye ne kwance cikin idanun muhammad jadda din......taja numfashi sosai har kaman kayan cikinta zasu hade waje daya. Ita daya ce mutum na farko a duniya data taba ganin wadannan tsadaddun hawayen da suke zuba SILAR QAUNA daga idanun me jadda......tana fata ta zama mutum.na qarshe da zata gansu,kuma ta zama sila na goge hawayen daga idanunsa gogewa ta har abada.
Abu daya ta lura dashi har yanzu yana da tsoro game da halin mata......har yanzu wannan ciwon da maamah ta dasawa rayuwarsu yana masa zugi da radadi.....har yanzu yana jin kaman abinda ya faru da abbansu zai faru dadshi,a yanzu haka a shirye take ta goge masa dukkanin wannan fargabar da shakkun,don haka ta zame hannuwanta daga nashi,ta sulale tana duqawa saman gwiwoyinta,sai ya gaza tsaiwa ya silale shima ya bita.
Hannuwansa ta riqe da kyau tana kallonsa cikin tsakiyar idanunsa.
"Allah ya zama shaida.....annabin Allah ya zama shaida,ni ameenatu sabreen na shirya rayuwa dakai da dukka abinda zamu haifa......na sadaukar maka da dukka rayuwata sadaukarwa ta har abada......dadi ko wuya sunyi kadan su raba tsakaninmu.....zan zauna dakai tamkar dominka kadai aka halicceni,bazan barka ba muddin bakai ka buqaci hakan......". Ai bai iya barinta ta qarasa fada ba ya hade bakinsu guri guda.
Sai daya tabbatar ya kwashe ragowar maganar tass daga bakinta sannan ya zare bakinsa daga nata yana kallonta da birkitattun idanunsa.
"Ta yaya zan iya rayuwa ba'a duniyata ba?.......ta yaya dan adam zai rayu babu duniyarsa?,indai babu ta yadda hakan zata kasance....to ki sanya a ranki ni Muhammad jadda don ke kadai MAAMAH ta haifeni". Batasan sanda ta zube saman kafadarsa ba tana jin wani irin alfahari yana ratsata,tana jin tabbaci da yaqini suna ratsata.....ashe akwai sauran maza irin muhammad jadda din?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 117
117
Guri kawai ta samu ta zauna cikin dakin daya kasance ita daya ce qwallin qwal a ciki. Duk yadda taso ta cinye ta kuma jure ta kasa,bata ankara ba kawai taji ta fashe da kuka.
Ta yaya haka zata kasance?,bata tsira da komai ba sai hawan jini?. Wanne irin kafaffen yaro ta haifa?.....aure tsakanin musaddiq da amna?,wacce irin asara ke bibiyarta har haka?,da gaske kamam yadda boka ya gaya mata taurarin nasararta ke bacewa?,taurarin nasararta ke dakushewa?,ina dukka kaifin hankalinta da zallar iya takunta suka tafi?(ta mance cewa shi Allah gwanin hikima ne,yana iya yiwa bawa talala,yayi shekaru aru aru yana zalinci,a nasa hangen da tunanin nasara ce,sai Allah ya barshi da wayonsa da tunaninsa,ya turo.masa nasara a gabansa,plan dinsa yayita tafiya daidai,kwatsam idan yaso kamashi zai da damqeshi a tsakiyar wannan plan din da shirin nasa da yake tunanin sune mafita a gareshi,sai ya zurma yayita bundum bundum. Idan yana da rabo sai ya gane zunubansa da kuma kusakurensa yayi gaggawar tuba....idan baida rabo kuwa,zaiyita ganin INA DA SAURAN DAMA,INA DA SAURAN LOKACI yana tsaka da wannan lissafin sai ubangiji yayi ram dashi,dauri gaba dauri baya,me kwanceshi kuma sai ubangijin daya qulle abinsa. Duk runtsi.....duk tsanani,duk yadda za'a je a dawo karka yadda ka cuci kowa,daka cuci kowa gwara kowa din ya cuceka. Duk juyin da za'ayi ka tabbatar zuciyarka wankakkiya ce......kana bacci amma sai ubangiji ya zama jinka ya zama ganinka,ya zama me jagorantar al'amuranka,ubangiji ka barmu a naka duniya da lahira,karka bari duniya da abinda yake cikinta ya rufe mana ido don girman zatinka,karka bamu damar cutar kowa don isarkaππ½ππ½ππ½).
Abune a rayuwarta data manta rabon data yishi wato kuka,shekaru masu yawa da suka shude mata,amma sai gashi yau tana zubda hawaye sanadin anni amna da sabreen.
"Lallai dole fansa ta biyo baya.....lallai dole ku biya bashi da fansar zubar wadannan hawaye......dole sadaukarwa ta biyo baya.....wala'alla akwai rayuka da zasu salwanta......rayukan da shudewarsu shine silar wanzuwa da samun nutsuwar zuciyata" Ta fadi a fili tana kallon idanunta da suka tasa saboda kukan data share mintuna tana yi.
A gaggauce ta sake goge fuskarta ta,sannan ta koma wajen luggage dinta ta soma ninke kayan ciki tana zuba wadanda suke gefen gado da kuma cikin toilet din dakin. Tanajin ta qagauta gari ya waye,tana jinta.kaman saman qaya,a jikinta da ruhinta takejin bata da wani sauran zama a garin,bata da sauran abinda ya rage mata da zata zauna tayi cikin qasar(subhanallah).
β
Sau tari wata soyayyar tana zamewa madubi kuma abar sha'awa ga wanda ke gefe yana kallo. Wani memories din na wasu masoyan kan samu wajen zama na din din din cikin kwanya ya kasa gushewa saboda girman tsumammiyar soyayya zallar kulawa da qauna me gusar da hankali saboda tsananin kusanci da kulawa tsakanin masoya.
Fu'ad da sabreen......soyayyarsu ta zamewa wasu tamkar makaranta.....ko kuma allon da zaka kalla ka karance ilimin dake shimfide a kanshi.
Wucewar maamah Nigeria ya samar da nutsuwa me tarin yawa ga wasu zukata,wadanda sam basusan gaibun dake tattare da tafiyartata ta barsu ba. Wani lullubabben gaibu me cike da duhun sirrikan da ita kadai ta barwa zuciyarta shi.
Samun sararinta da gushewar wanzuwarta a family din ya bada damar baje kolin soyayya masu dauke da nau'ika kala kala. Sabreen da fu'ad,suna rayuwa da nunawa juna soyyaya da kulawa tamkar sun manta da akwai wasu halittun dake gewaye dasu suna tasu rayuwar.
Sau tari idan fu'ad yayi wani abun saidai kowa ya runtse idanunsa,don ba wanda yake gani sai sabreen da cikinsa dake manne a jikinta. Gaba daya kaman ya mance da kowa sai ita sai hidimarta,wani lokacin hankali yafi zuwa jikinta akanshi,don takan tuna da anni a wajen ta rage wani abun.
Duk da abun ya zowa anni a sabo,amma saita zama suruka me yawan bada uzuri da dauke kai. Bata shiga tarayyarsu ko kadan,saita dinga nesa nesa dasu gudun ji masu kunya duka ita dasu.
Wannan soyayyar sai ya hura wuta biyu......tsohon tsumin soyayya ya balle tsakanin musaddiq da amnansa,duk da cewa daga nesa nesa ake komai don anni bata bari abun ya zurfafa da yawa. Su dinma duk yadda sukaso su boye dole ita soyayya bayyana kanta takeyi koda an boyeta. Sannu a hankali sai wata wutar munafukar soyayyar ta soma kunnuwa kuma daban tsakanin saddiq da huda. Duk wani nuqu nuqu da sukeyi hakan bai hana sabreen karantar komai ba,ranar sun dawo daga masallaci take tseguntawa fu'ad hancinta ya lakace mata.
"Kin iya sa ido duniyata.......banda nidin ina da qarfin kurwa banjin zan qwace filin soyayyar da akewa su huda.......Allah ya taimakeni nayi hasashen tsaf zaki iya guduwa ki barni.......nayi miki yankan baya na kawo miki su.....to me ya rage?". A mamakance ta zare idanu dariya tana qwace mata,sai ta boye kanta cikin qirjinsa tana qoqarin musanta maganar.
Saidai kuma a zahirin gaskiya cike take da mamaki,wanne irin mutum ne fu'ad din me tsananin kula har haka?,ta yarda dari bisa dari baya wasa da duk abinda yakeso.
Duk wadannan abubuwan da yake faruwa bai hanasu ibada ba tuquru........zamansu tsakanin makka da madeena yafi yiwa fu'ad dadi sama da kowa,tunda ko banza yace za'a qiri halittar danshi ko 'yarshi a guri me tsarki da tsarkakken ruwan zamzam wanda shine komin sabreen. Komai da zamzam takeyi,shine ruwanta nayin komai,iya falalar ruwan zam zam kawai ya sanya yake qara jin nutsuwa da zamansu a nan.
Tuni ya mata register da komai na zuwa awo da haihuwa,don yace indai yana da rai da lafiya to tabbas a garin madeena yakeso a haifa masa yaransa,ya tsara komai ba tare daya gayawa kowa bama.
*_K'ADDARA KO GANGANCI?_*
_KALLON KALLO_
Sau uku tana rolling sassalkar luxury Egyptian abaya din tana warewa. Kawai sai tayi zaune gaban madubin tana ware hannuwanta gami da binsu da kallo.
Batasan me yasa ba......batasan kuma me yake faruwa ba,shagwabata da yayi da yi mata hidimar komai ne sila ko kuma cikin jikinta ya sanya ta zama raguwa?.
A karo na hudu ta sake gwadawa sai veil din ya sabule salin alin daga hannunta. Ido ta zubawa fuskarta,sai taji hawaye kawai ya kubce mata.
Murmushi ya saki yana qarasa sanya link din hannun kuftan jikinsa,ya soma takowa a hankali zuwa bayanta. Tun daxun da taketa drama ita da dankwalin yana kallonta,yasan qarshen maganar dama ta sanya kuka tunda ta zama rigimammiya ta gaske.
Kafadunta ya kama ya tasheta tsaye,suka hada ido sai yayi qoqarin danne dariyarsa,saidai tuni ta riga ta gani.
Daga hawaye sai ta sakar masa kuka me qaramin sauti.
"Subhanallah......me kuma nayi?" Ya fada yana dora damuwa saman fuskarsa duk da da gasken dariya yakeson yayi.
"Ya isa....am sorry if I offend you" Ya fada yana sakata a qirjinsa. Shaqa daya ta yiwa turarensa nutsuwa ta fara saukar mata,sai ya bata lokaci sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya dagata yana duban fuskarta.
"To mene ne?,.....uhmmm.....tell me" Tabe baki tayi,ta miqa hannu taja kumatunsa.
"Ba mayafinne yaqi dauruwa ba,sannan kuma kai kazo kanamin dariya saboda ina ramewa kai kuma kina qiba". Wannan karon kecewa yayi da dariya sosai harda riqe ciki. B wani bane ya jawo masa wannan jagwal din ba sai amna,haka kawai ta sashi gaba vanilla ice cream takeson sha,suka yiwa anni wayo suka fice wadda ta jima da hanata shan kayan zaqi da sanyi. Koda sukaje kasa sha tayi.ma gaba daya sai ya fita a ranta,shi kuma duk da bai dameshi ba amma sai yaji ya masa dadi,yasa aka kawo masa ya soma sha,ashe tana ankare,ke amna kika ce
"Hamma madeena ta karbeka Allah,ka karbe jikin adda ka hada da naka,kanata kumatu" Ta fada tana dariya.
"Lovey dovey.....kin manta ni yayan mijinki ne kenan?" Ya fadi hakanne don shine abu daya yanzu da yake kashe bakin amna,ya kuma fadi hakanne don ya fuskanci sabreen din har ta kumburo fashewa kawai take jira tayi. Ashe abun dashi ta kwana sai yanzu ake fashe masa shi.
Sulalewa yayi ya durqusa gabanta,ya zagaye hannunsa a bayanta yana dora fuskarsa saman mararta.
"Kazo mu bawa mama haquri....mun hanata qiba mun hanata cin kayan dadi....mun tuba....zamu gyara halinmu" Ya qarasa maganar yana hade hannuwansa guri daya.
Da ido ya bita ganin daga kuka ta koma buga murmushi,ya girgiza kai kawai a ransa yana gulma,wato me ciki sai a barta kawai.....abun kuka ko bacin rai baya mata kadan,cikin dabara ya jata ya sauya mata yalwataccen mayafin rolling din ya daura mata da kanshi,don bayason wani sashe na jikinta ko kadan ya fita wani ya gani.
Yana gama mata ana knocking qofar,yasan waye farouq ne,qiri da muzu ya zama fusataccen qarfi da yaji,yace fu'ad ya jawo masa raini,ya hada tuxurantaka da aure da qannensa,in fact ma qanin bayansa ya rigashi amsa sunan me aure,wannan ta saka dole qasa daya data rage musu akayi cancelled trip din sai bayan wani lokaci,aka aikewa da iyayen fanna date na bikin sati biyu masu zuwa wato sati biyu da komawarsu nigeria kenan.
Hannunta cikin nashi yadda suka saba suka fito a dakin,ta zame hannun nata a dabarance ta qarasa gaban anni ta gaidata,ta gaida momma wadanda zasu sauka duka a nigeria,da yammaci kuma jirgi zai wuce dasu mali saboda washegari huda zatayi ton prints na jarabawar kammala secondary school.
Haka suka wuce airport cikin motocin da a nan qasar yake barinsu sai kuma zuwa na gaba.
Anata zuba soyayyar munafunci tsakanin amna da musaddiq,huda da saddiq daketa babbasarwa kaman ba komai tsakaninsu,angon gobe farouq kuwa anata sallama da fanna ta waya shima ya bude wuta sosai don shirye shirye sun gama kammaluwa,ranar kawai suke jira.
Ita kuwa kanta yana kwance kawai saman kafadarsa. Tun bata saba ba har