Showing 270001 words to 273000 words out of 557259 words
gurguje yasha,sannan ya zauna yana jawo wayar sadarwar yana kiran number dakin nata.
Ta gama komai tuntuni,ta kuma jima da kwanciyar saidai baccin da baizo ba. Tayi mamakin jin kiran,saita sanya hannu ta dauka tana tunanin zuwaira ce,ko meye kuma ya faru a daren nan oho?.
Muryarsa taji sabanin muryar zuwaira da tayi tunanin itace. Har tsakiyar kanta sautin muryar ta sauka mata da wani irin zuzzurfan amo
"Hello" Ya fada yana qoqarin hadiye bacin ran dake taso masa. Matsar da kan wayar tayi daga kunnenta da zummar sauke wayar,kaman yasan abinda take shirin yi ta tsinci muryarsa cikin zafi yana magana
"Kika kuskura kika sauken waya....zakisha mamaki na". Tsauri umarnin nasa yayi mata,saita samu kanta da gaza ajiye wayar. Sau tari tana mamakin yadda yake cin galaba a kanta haka da sauri,umarninsa yake saurin ratsata,wani abu guda daya da ta raina akan kowanne d'a namiji. Bata taba zato ko tunanin akwai wani lokaci da zaizo da wani namiji zai iya juyata ko ya canzata daga abinda yayi mata daidai cikin rayuwarta ba,sai ga abun yana tafiya cikin rashin zato bare tsammani.....kamar a cikin duniyar mafarkinta.
Ci gaba tayi da riqon wayar ba tare data ce komai ba,haka daga nasa bangaren bataji ya sake furta komai ba. Kusan minti daya wayar na a riqe a hannunta,sakannin kuma suna ci gaba da motsawa. Kaman daga cikin wayar taji an murda qofa an kuma budeta. Sauyin yanayin qamshin daya soma mata sallama ne ya shaida mata tabbas an bude mata qofa,ba kuma cikin wayar bane a zahiri ne.
Tana kwance ne rub da ciki,don haka ta waiwaya kadan don tabbatarwa da idanunta. Muhammad jadda ne,tsaye daga baki qofar dakin yana riqe da handle din,daure da lallausan farin towel wanda ke dauke da tambarin VERSACE baro baro a jiki. Gaba daya towel din ya daurashi ne daga iya qugunsa,ya kuma sauka sosai zuwa mararsa,abinda ya bata damar ganin full ginannen jikin nan dake cike da lallausar gargasa data kwanta tayi luf luf.
Fadin kafadunsa ya sanya bata ko iya hangen qofa,sai yau ta sake fahimtar GIANT ne na gaske,da murjajjen jiki da kuma ginannun tsokokin damtse dana qirjin wato(muscles).
Wani mahaukacin faduwa gabanta yayi,a yau taga abinda bata gani ba a wancan ranar data sameshi a parlor dinsa.....ko don yau din a tsaye yake da dukka tsahonsa da kuma wadataccen haske a dakin nata?.
Duk yadda take da kafiya da taurin rai sai data gaza ci gaba da kallonsa,wani irin tsoro ya kamata wanda ya tilasta mata maida kanta ta kwantar saman pillow tana baiwa qofar dakin baya,wato qeyarta ke kallon qofar kenan.
Gabanta ya sake yankewa ya fadi sanda taji ya maida qofar ya rufe gami da murxa key,ta fidda idanunta dukka biyun waje tanason yin hasahen abinda zai iya faruwa da ita,saidai bata gama wannan ba taji an sanya hannu an birkitota gaba daya,sai gata ta koma rigingine a maimakon rub da ciki da take a dazu.
Gaba daya ya zame mata rumfa saman kanta,tamkar me barazanar hanata ganin komai na dakin sai wannan mudadden jikin nasa.
Da hanzari ta sanya tafukan hannayenta guda biyu da zummar tureshi saboda yadda yake neman hade space din dake tsakaninsu,amma ko gezau kamar ma ba wani hannu daya sauka a jikinsa. Bai bata second chance ba ya kama hannuwan nata ya matse cikin hannunsa guda daya.
Qoqarin qwatar kanta sosai ta farayi tana tureshi,amma baiko motsa ba,yana riqe da hannuwanta gaba daya yana kuma ci gaba da zube mata idanunsan nan
"Ka sakeni......ka cikamin hannu" Ta fada sanda ta fahimci ko kusa ko alama bata da qarfin da zata iya amsar kanta a hannunsa. Ta cikin idanunta ya fahimci laushi tayi,hakanan qarfinta ne ya fara qarewa. Bayajin zai qyaleta haka sai ya bata mummunar barazanar da ba zata qara kai qararshi wani guri ba. Duk dabaya tunanin wani tsoro me yawa a tattare da itan duba da ita din WACECE?. Ba wani sabon abu bane a wajenta cudanya da maza,duk da maza suna suka tara kamar yadda mata suma suka tara suna.
"Inajin a matse kike a sauke miki jarabar da take damunki ko?,wannan ya sanya ba kunya cikin idanunki kika je kina kai qara a inda kike tunanin za'a sanyani sexual affairs dake ko?". Duf wuta ta dauke mata,daga iya kalmar sex data shigo maganar ta tabbatar lallai babbar magana aka baro. Yaushe takai qararsa?,kuma gurin waye?,me tace tana da buqata?,duka wadannan tambayoyin sune suka soma mata yawo saman kai,kuma inda tana da hali tana da buqatar amsarsu,saidai a yadda komai yake a hautsine bata jin tana da tattararriyar nutsuwar nemansa da wadannan amsoshin.
Tana aje wannan tunanin yana sakin hannun nata,ya miqa hannu da wani irin zafin nama zuwa Coller din rigarta,wadda tsaurin riqon da yayi mata ya bawa bottom daya damar tsinkewa fit. Fitarsa sai ya zamana kamar ya hada da fitar nutsuwa daga gangar jikinta,wani tashin hankali ya rufto mata har kala biyu. Na farko yadda yayi kusa da ita da towel din da kadan ya rage marabarsa da tsirara,don babu abunda ya lullube illa mararsa zuwa gwiwarsa,na biyu kuma fitar maballin rigarta sai ya tuna mata waccan ranar a kitchen. Ranar da har yau idan ta dauki rigar data sanya a ranar sai taji qamshin wannan mayataccen turaren nasa,abinda ya sanyata kenan tayi adabo da rigar duk kuwa yadda take sonta. Saboda duk sanda ta sakata haka yadda abin ya faru zai yita dawowa kanta,hakanan kuma zatayita tuna yadda ya azabtar mata da lips haushinsa yayita kai komo kenan a ranta har sai ta raba kanta da ita.
Matse hannunta yayi yana saukar dashi daga gaban rigar don so yake ya tsinke maballi na biyu,kafin ta iya komai har ya samu nasarar yin hakan,ya kuma wuce zuwa maballi na gaba,abinda ya sakata saka hannuwanta dukka biyun ta cukuikuye gaban rigar,cikin fushi kuma taci gaba da magana
"Don't touch me.......ka daina tabani mana.... Wai mene haka?!". Ta qarasa fadi sanda ya tattara hannuwanta da zummar turesu,cikin rashin sa'a hannuwan nasa suka samu nasarar sauka daidai saman tudun qirjinta wanda ke tsaye car babu bra. Sabonta ne idan zata kwanta dukka saita ciresu,don tana jin kamar suna hanata cikakken bacci.
Daga shi har ita ba wanda baiji kaman an yarfa masa wuta a jikinsa ba,yayin dashi ya hada wani azababben shock daya ratsa jininsa da wani irin mahaukacin gudu ya aike saqo qwaqwalwarsa ya kuma dawo da saqon yana rabawa zuwa sassan jikinsa gaba daya.
Taji komai har cikin jinin jikinta,sai taji kamar an zare mata dukka wata laka tata da wani irin firgici da tsoro bakinta ya furta
"Please......don Allah ka bari" Kalaman nata na qarshe ya fito da zirarowar hawaye zuwa saman kuncinta.
Duk yadda yaso ya zarce da tsoratata gami da gigitata cikin mugunta sai yaji ya kasa,haka ya sake mata rigar yana dauke idanunsa daga kanta ba tare daya bari sun sauka a inda take boyewar ba tamkar sulalewar ruwan kalkashi a tafukan hannun mutum. Zuciyarsa ta cika da wani irin mahaukacin mamaki......daga ina wannan weakness din ya taho?,ya tambayi kansa da kansa can qasar zuciyarsa. Bai taba niyyatar zai dauki mataki akan wani abu ba tare daya qarasa aiwatar da qudurinsa ba,bai taba jin rauni akan duk wani abu daya sanya a gaba ba sai akan wannan dan qaramin aikin.
Tattare jikinta tayi waje daya tana neman hanyar sauka daga saman gadon,amma sai ya sanya gwiwarsa ya take gefan rigar,ya waiwayo a nutse ya zube mata idanunsan nan masu dauke da wani kakkaifan maganadisu,wanda duk yadda sukakai ga haske sun surka launi a yau din.
"Kina zaton zan hada jiki dake ko?,over my dead body......duk randa zan hada jiki dake ki sanya a ranki ranar mutuwarki ne kawai yazo,don zan niqaki da kyau kaman yadda engine ke niqa tsaba ya koma gari....." Yatsunsa ya murza saman fuskarta sannan yace
"Sharadi guda biyu ne zan baki idan kin kiyaye shikenan.....na farko....kada ki kuskura ki sake kaiwa maamah qarata koda akan meye kuwa....ban hanaki kaiwa anni ba idan kinga zaki iya fine.....sharadi.na biyu duk randa na sake miki umarnin yin wani abu kika watsar kina daukan kanki wata tsiya.....zakiga abinda zai biyo baya,sai na sanya an sako Michael yayi dambu da namanki,ki tashi kizo ki gyaran sassa.....ki kuma samu note pad ki rubuta day one don lissafinmu yafi tafiya daidai" Yana kaiwa nan yaja jikinsa yana sauka daga gadon,ya kuma fara takawa hankali kwance yana fita daga dakin.
Da sassarfa yake haurawa saman cikin tuhumar kansa da kansa. Baisan kanshi da kasawa ko gazawa ba,ya akayi ya kasa bata mummunan punishment yadda ya kamata?. Koda ya tsaya gaban mirror na toilet din,sai ya dinga jin haushin kansa da kansa. Baisan wani weakness nasa ko kadan ba......amma sai ya samu kansa yana tsoron kada fa wannan ya zama shine weakness dinsa?.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 40
_Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_
_harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_
________________________________
Moroccon cotton jallab ya saka ta maza maroon color me gajeran hannu,wadda aka yiwa ado da gold din zarurruka masu kauri. Har hantar cikinta sai data kada sanda taji fitowarsa zuwa falon,amma ta dake bata nuna ba,tana duqe tana goge stand tv lokaci lokaci tana goge 'yan hawayen daketa qoqarin lallai sai sun sake karya mata zuciya.
Kai tsaye ya wuce saman minotti sofa dinsa yana lumshe idanunsa,wata azababbiyar kasala nason saukar masa. Dole yana buqatar wani abu da zaiyi awakening dinsa for some hours don yana da aiki.
"Ke..." Ya kirata idanunsa suna lumshewa kadan. Kiran ya mata ciwo,amma kuma dole ta nuna tasan da ita yake maganar.
"Bring me some coffee" Ya furta yana dauke idonshi a kanta ya lumshesu don kaucewa kallonta.
Ajiye duster din hannunta tayi qirjinta na mata wata suya,ta fara takawa don isa qofar da zata saukar da ita daga saman
"Hey.....ina zaki?" Ya furta da rashin qwarin murya. Sai kuma ya mata nuni da nasa kitchen din da idanunsa,kai tsaye ta gane me yake nufi,ta kuma canza akalar tafiyar tata zuwa can din.
Tayita dube dube da tsoron kada ta tabo wani abun duba da yanayin machine da utensils din dake kitchen din daya sake shan bamban dana qasa nesa ba kusa ba. Da qyar ta samu ta kammala,duk da bata da guarantee din yayi ko baiyi ba,don itadai ba damunta yayi ba,koda ya dameta ma ba irin wannan bane.....nasun irin nasun ne wato daidai matsayinsu yaku bayi.
Saman tea tray ta hado da cups. Ta qasan idanu cikin lumsassun idanunsa yake kallonta sanda take nufoshi da wani irin kallon da zaka rantse da Allah bacci yakeyi. Yana qoqarin binciken kansa me yasa yaketa tunawa da abinda ya faru?,amma ya rasa dalili,haushin kansa sosai yakeji a yanzun,yana ganin kamar wannan hanyar ta sanya tsoro a zuciyarta bazatayi aiki ba.....zata iya dasa masa matsalar da zata gagari gangar jikinsa watan watarana.
Yadda jikinta yayi laushi sosai yake karanta,yana mamakin macen data saba mu'amalantar maza kala daban daban me ya sanyata jikinta yayi laushi don ya mata wani qaramin riqo da bai taka kara ya karya ba?.
"Kana murzata ne ta hanyar da ba haka su suke mata ba,da ta irin tasu hanyar ce qila ba abinda zai sanya jikinta laushi" Wani sashe na zuciyarsa ya bashi amsa.
A gabansa ta ajiye tana jin inama zata samu wata dama ta zuba masa wannan abun cikin tea dinsa?,qila cikin kwanaki uku ta samu nasarar da zata cika aikinta,ta tattara tabar wannan DUNIYAR tasu ta koma tata ainihin duniyar.
"Serve me" Ya fada da murya can qasa. Sake baci ranta yayi,gaba daya a hankali yana son canzata ta koma 'yar aikinsa kenan kome?. Tsugunnawa tayi a nutse ta soma zuba masan tana qoqarin danne zuciyarta amma ta kasa jin relief. A sanda parlor din ya dauki shuru,wayarsa da tafi kusa da ita ta soma kuka alamun shigowar kira. Kallo daya ta yiwa wayar ta dauke kanta,yarinyar kullum ce dai wato fareeda khaleed mustapha. Qaramar tsuka taja,ita ta sani zaa rina,mutum kamar muhammad jadda ace yana zaune lafiya bisa kyawawan dabi'u?,ai ta qalubalanci wannan. Banda akwai wata gurbatacciyar alaqa me zai dinga shigo da kiranta cikin wayarsa a kowanne dare?,a daidai lokaci irin wannan da mafi yawan lokuta yake kebancewa shi kadai?.
Tana miqa masa coffee din yana daukan wayar yana kallon screen din ransa yana baci,ya dauke dubansa daga kan fuskar wayar da yakeji kamar ya bugata da bango saboda yadda tsananin nacin fareeda ya soma shallake hankalinsa,ya aje dubansa akan fuskarta dake a dinke sosai.
"Fara sha kafin ki bani" Yace da ita a taqaice. Duban rashin fahimta tayi masa,sai ya kafeta da idanu kafin yace
"Do you think am a fool?,kina zaton zan karba nasha any how?....." Ya qarasa maganar yana daidaita zamanshi sannan ya tura mata teatray din
"Take a sip first" Sai data ja numfashi sosai ta aikawa hunhunta sannan ta samu zuciyarta taci gaba da aiki yadda ya dace,me yake nufi data fara sha?,ta tambayi kanta.
"Kada ki barwa kanki qofar zargi" Wata zuciyar ta shawarceta. A nutse ta dauka mug din ta kurba kadan sannan ta ajiye masa,zata motsa yace
"Hang on for a bit" Ya fadi cikin halin shariya yana maida hankalinsa kuma kan fareeda tare da tunanin ta inda zai bullo mata.
Ambassador yana da kima da mutunci a idanunsa,musamman daya kasance babba harda furfura a fuskarshi,saidai fareeda tana crossing line da yawa da baya bari a crossing masa shi.
"What's bothering you?" Ya fadi adan fusace,yayin data narke marya Kamar qanqanuwar yarinya
"Kaineee" Labbansa duka ya cusa cikin bakinsa yana qoqarin hadiye takaicin data bashi. Sai ya sauke idonsa akan sabreen wadda baisan ta soma barin wajen ba sai a sannan.
"Where to?" Ya jefa mata tambayar data tabbata yanason jin inda zata ne. Ita ba zata tsaya tana jinsa yana hirarshi da matan banzanshi ba,ba damuwarta bane ya yanke dukan abinda yake ganin ya dace da rayuwarsa.....amma ita kuma ba wanda zai tilastata yin abinda batayi niyya ba......wannan din dabi'arta ne da ba canzawa. Sai data yi qaramin yaqi da zuciyarta sannan ta iya lanqwasa harshenta ta sarrafashi tana fadin
"Dare yayi inaso na kwanta"
"Idan kin gama you can go" Ya fada cikin halin ko in kula yana katse kiran fareeda itama gami da sanyata a DND mode sannan yaja coffee dinsa ya soma kurba.
Sassa ne na alfarma dake da yalwa wadatar kayan alatu dana qarau wadanda ke buqatar a gogesu,wannan shi ya sake bata mata lokaci ya kuma dauketa har kusan sha biyu na dare abinda ya bata mamaki samunsa sa tayi dungurgur ya sanya system a gaba ya zuba mata idanunsa yana sarrafata,wanda motsin takunta ya sanyashi rage mata haske sosai har baka ganin abinda ke allon.
Baki ta tabe ta qarasa,zuciyarta na ayyana nata waye ma yasan abinda yakeyi tsakiyar darennan.
"You are free" Ya amsa mata ba tare daya waiwayota ba,sai ta fara nufar qofar a ran ta tana fadin
"Shi mugun mutum ba kasafai bacci dama ya fiya damunsa ba".
Gyaran yayi masa sosai,don yafi qawatar dashi fiye da coffee din,don sam bai masa dadi ba irin yadda yakeso ya kasance ba. Jallab din jikinsa ya zare ya wuce toilet da zummar daura alwalar kwanciya bacci.
β
Duk a kasalance take kowanne aiki a yau,tun daga safiya zuwa daren da take kammala girkin daren. Sai takejin wani irin qosawa,gaba daya ta fara gajiya da komai. Tunda take wannan shine karon farko data aboci kitchen safe da dare da zummar dora sanwar girki.
Kamar ko yaushe bayan ta kammala abincin,ta taka a hankali tana nufar inda ta boye akwatin. Ta jawo ta miqa hannu ta fito dashi sannan ta bude. Kayan cikin ta fara fitowa dasu kaman yadda ta saba,daya bayan daya kuma ta soma zubasu saman abincin ta cakude dasu. Yau daya sai ta tsaya kawai tana kallon abincin,wani irin rashin dadi takejin zuciyarta tana mata a yau din,a