Showing 552001 words to 555000 words out of 557259 words

Chapter 185 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

478

ba.

Haduwarmu uku da jib magana ta hadamu. Shima maraya ne,banda wanda nake gayawa damuwata amma ganin kirkinsa da yadda da nayi da nutsuwarsa a ranar mukayi dogon hira dashi.

"Basa taimako Don Allah,ni shaida ne.....amma idan basu taimakemu don Allah ba,zamu diba ta qarfi da yaji" Da taimakonsa muka soma gudanar da plan dinmu,ranar farko na fadi,aka biyo sawunmu,Allah ya hadamu da busari ya daukoni kyauta,wanda tun daga ranar ya zama dan adaidaita sahuna,daga baya bayan uban gidansa ya qwace abun hawansa,na hada dukka kudina na siya masa wata,sanadin haka kwananmu biyu ha abinci,saboda shi dinma marayanne,kuma shike daukan nauyin tsohuwar mamarsa wadda shi kadai Allah ya bata a duniya"

"Sannu a hankai aikinmu ya dinga tafiya daidai,indai zan fita sai nayi nasara,ina yin nasara ina gane cewa maza babu Allahba ransu,wasu mazan sukan daukaki matan bariki su wulaqabta iyalinsu,wasu mazan kuma saidai ki bada jikinki su baki kudi,don haka mukayi tsare tsaren da duk wayonka bani zuwa gurin da kakeso,saidai na sameka a guri public mu qarqareta a nan,na zare kudin ta hanyar taimakon jib dake sarrafa na'uarar,daga ranar kuma ba zaka sake jina ko ganina ba,bazan sake kuma zuwa duk wani guri da muka taba haduwa dakai ba. Nasha samun barazana amma Allah ya kiyeyeni,ban taba yarda ko farcena wani namiji ya tabamin ba duk kuwa iya wayonka,wanda ni nasan hatsari na saka kaina me girma,ba wayona ko dabarata bane kuma ya qwaceni ba,zuciyata akwai Allah ya duba.

Duk namijin da zan hadu dashi ina fara karantarsa,adadin son matanka da fasiqancinka.....adadin barnar da zaka gani a dukiyarka......akwai nutsasun maza daidaiku dakeson aurena da tun tafiyar farko nake zamesu daga gareni saboda basu cancanci na cutar dasu ba,amma kuma bani da wani nufin aure kai ko sha'awa ma baya bani.....mazanma dukkaninsu haushi suke ban,saina sallamesu salin alin duk iya nacinsu kuwa.

Yadda nake shiga me kyau nake fita da yadda duk wata buqata nake sauke mana ita ba tare da anga ina sana'ar komai ba sai bacin suna yahau kaina......yayin da shaidar zur dasu bibo ke qarawa 'yan waje ya sake basu qwarin gwiwar yadda da komai a kaina,ban damu sosai ba sai dana qara hankali,amma damuwata ta dadu qwarai sanda naga suna qoqarin brainwashing ma su hud akan qazafin karuwanci da zina.

Kudi suka fara shigowa har suka fara fin qarfin buqatuna,sai a sannan na lura akwai tarin marayu a unguwanni daban daban,mabuqata marayu da iyayensun harma da marasa qarfi......saina saka marayu guda hamsin nauyin su saman kaina,duk wani abu da zan samu kuma kasonsu yafi nawa yawa,a haka na dinga kula dasu da nawa qannen......har xuwa sanda na hadu da mika'il komai kuma ya faru" Ta qarasa maganar tana sanya gefan mayafinta tana share qwallar data jiqa mata fuska.

"Ki yafemin......ki yafemin sabreen don girman Allah......ku tayani roqar anni ta yafemin" Muryar maamah data sauka musu a baza wadda ta saka sabreen sake sakin kuka.

Ashe dama akwai rana irin wannan da zatazo?. Sautin kukan ya taso anni tana dubawa ko cikin yaranne suke rigima,saidai sanda ta kawo qarshen motar taga sabreen ce saita zauna a wata kujerar tana shirin tambaya,amma yadda maamah ta riqe hannunta gam cikin nata ya tsoratata ya kuma bata mamaki.

"Ameenatu ki yafemin........ki yafemin,iya abinda zan iya cewa daku kenan....kunyimin halaccin da bazan iya biyanku ba amma baqar zuciya da shaidan gaba daya sun sanya idanuna rufewa,kin yafemin don girman zatin Allah ta yadda idan na tashi mutuwa zan mutu cikin salama". Sosai qirjin fu'ad yayi nauyi saidai wani farinciki kebantacce yana dawainiya dashi. Har yanzu ya daina jin sautin kukanta na daren jiya,sanda ta sanyasu a gaba shida musaddiq akan su yafe mata. Wani irin kuka dake dauke da zallar nadama cikin ido murya da kuma lafazinta. Daga shi har musaddiq ba wanda baiyi kuka ba......wani hukuncin Allah da lamari na uwa kuma.......cikin awanni biyu kacal da sukayi zaune da ita tana qoqarin basu labarin komai da hardaddiyar muryar ta,saiga zukatansu dukka sunyi wani irin sawai. Basu bar dakinba saida tayi bacci tsakanin qafafunsa shida musaddiq,wanda ko bayan sun fito a dakin shi da musaddiq din ganin komai suke kaman mafarki,sai suka samu kansu da rungume junansu. Fu'ad ke lallashin musaddiq

"Ba abinda yafi qarfin addu'a......ba wani lamari da yafi qarfin Allah,alhamdulillah da Allah ya qaddara mata shiriya tunda sauran damarta" Wadannan kalaman su suka tsagaita kukan musaddiq.

"Anni ki roqamin hamza ma......na cutar da mutane da yawa ta fuskoki da dama......amma yanzu kune nake gani kune tare dani ku kuka rage.....ku yafemin naji dana sauran mutane.....hajja da laila dukkaninsu babu su bare na nema yafiya a garesu........fareeda ta haukace bata da cikakken hankalin da zamu yafewa juna nida ita".

"Allah ya yafe mana gaba daya" Cewar sabreen qwallar farinciki na fita a idanunta.

"Allah ya tabbatar damu kan hanya madaidaiciya.....Allah ya kyautata qarshemu" Anni ta qara da wannan tana goge Qwallar farinciki da Allah ya qaddarawa maamah shiriya bata mutu da haqquna ba saina wadanda suka rigata gidan gaskiya.𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 176


*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1




176



Zuwa yammaci sun daura niyyarsu suka kuma fara gabatar da umarar wanda cikin awa biyu suka sauketa.

Itakam sabreen kusan duk sanda sukazo tana yin nesa ne da ayarin familyn jadda,don tana jin kamar tafi kowa yawan buqata a cikinsu.

Sau tari bata sake haduwa dasu sai a masauki. Abinda ya gudana kenan yau dinma,don bata tashi komawa hotel dinsu dake daura da harami ba sai tsakiyar dare.

A gajiye ta bude dakinsu wanda yake cikin jerin dakuna mafiya tsada dake hotel din da BB farouq ya kama musu. Kowa da iyalinshi,sai kuma babban daki dake dauke da bedroons guda biyu,anni ta dauki daya maamah ma ta dauki daya da jikokinsu da masu aikinsu.

Da sallama ta shiga dakin,muryarta can qasan maqoshinta da wata irin gajiya a jikinta.

Yana zaune da farin soft and cotton shirt me zagayayyen wuya,sai boxer da bai qarasa idon sawunsa ba.

Littafine a hannunsa wanda yake bayani akan hajji da umra da kuma falalar madeena yana dubawa,ya daga kai a nutse yana amsa mata gami da zuba mata narkakkun idanuwansan nan. Qafafuwansa ya janye yana gyara mata pillow din dake wajen,da idanu ya mata nuni tazo ta zauna,saita qaraso tana zubewa saman kujerar.

Hannu ya miqa ya zare mata hijabin jikinta bayan ya karbi handbag dinta da carbinta ya ajiye,ya zare mata hular saman kanta,wanda hakan ya bawa gashinta me sulbi daman bajewa.

"Yanzun nan nake shawarwarin binki.......daren yayi yawa duniyata......me kiketa roqa hakane wanda Allah bai baki ba?" Ya qarasa tambaya da murmushi kan fuskarsa yana miqa mata ruwan daya tsiyaya mata a cup.

Sai data maida masa murmushin sannan ta karba ta shanye,ta ajiye cup din tana dubansa.

"Na godewa Allah......na gode duniyata......haqiqa Allah yayimin komai tunda ya bani kai......saidai 'ya'yanmu....uwa bata da wani sauran bacci a sanda ta tara zuria,kullum addu'arta shine yadda zasu samu rayuwa me kyau,ba irin rayuwar da iyayensu sukayi ba suka tsallake da qyar".

"In sha Allah.....tun basuzo duniya ba tun iyayensu ma basu hadu ba muke roqa musu rayuwa me kyau......ubangiji yaji kuma ya karba da yardarsa" Kai ta gyada cike da gamsuwa,yayin da shi kuma ya miqe ya wuce toilet.

Ruwa me dumi sosai ya hada mata,ya dauko mata towel ya fito.

"Oya zaki wanka ki dawo ki kwanta ki huta,kin gama hidimar biki kikazo kikayi tasu fauzan.......ga kuma zaman mana addu'a dana tabbatar idan ba nigeria muka koma ba bazai barki ki huta ba". Murmushi tayi idanunta suna lullumshewa saboda tsananin gajiya,ta miqe da qyar ya taimaka mata ta cire kayan jikinta ta karbi towel din tana wucewa bandakin.

Dumin ruwan ya hanata gama wankan da wuri,har sai da ta gasa jikinta sosai sannan ta fito,ta daura alwala ta tsane jikinta sosai,saita cire wata doguwar riga daya zaba mata me taushi dake jikin hanger ta zura sannan ta tako a nutse ta fito tana qoqarin daure gashinta da yayi mata damshi saboda ruwa daya taba.

"Hamma yau ko yatsana bazan iya dagawa ba......am really tired" Ta fada tana jin idanun suna mata nauyi sosai. Shuru taji bai amsa mata ba,bayan tana hango qafafunsa daga qasan idanunta yana daga tsaye.

"Hamma kaina ya jiqe,bazan iya busar dashi ba saida safe" Ta fada tana hayewa kan gadon,burinta kawai taji jikinta saman gadon.

"Meye wannan?" Tambayarsa ta ratsa kunnuwanta gami da saukar wani abu a jikinta sanda take shirin kwanciya.

Birkitacciyar fuskarsa ta kalla,yadda taga ya hautsine ya sanyata bin abinda ya jeho din da kallo da sauri.

Tablet ne na family planning wanda har ansha rabinsa. Saita saka hannu ta dauka gabanta yana wani irin bugawa,ta miqe da sauri da maganin a hannunta a rude ta sauka daga saman gadon.

"Magani ne hamma......"

"Na tsarin iyali ko?!" Ya fada da wata gigitacciyar murya dake nuna tsananin fushin dake sauka saman zuciyarsa.

"Eh hamma.....amma ka tsaya......"

"Na tsaya sabreen?,na tsaya kiyimin me?" Ya tambayeta qofofin hancinsa da jijiyoyin kansa suna budewa.

"Na tsaya ki gayamin ke kika tsaida haihuwa hakanan tun daga kan iffa?,na tsaya ki bani labarin yadda kika fara shan maganin planning?,ko na tsaya ki gayan kin gaji da haihuwa?"

"Duka ba haka bane hamma!" Ta fada itama da muryar data dagu fiye da dazu. Kalamansa gaba daya sun firgitata da wani irin tsoro,lafaxinsa gaba daya ya gama rudata.....ya zaiyi hukunci irin haka?.

"Duka ba haka bane to yaya ne?,kin taba samun tazarar haihuwa irinta iffa?,ko kin taba kaiwa haka?,shi yasa nayita tambaya ba bayani gamsashe?,ko shi yasa naketa magana ke sam ba damuwa a lamarinki!!!" Ya qarasa fada da wata tsawa data sanyata danne kunnuwanta tana fadin.

"Ya isa hamma!!" Ta fada da murya me qarfin gaske saboda tsoratar da tayi.

"Tsawa kikeso kiyimin?" Ya tambayeta yana nuna qirjinsa da yatsansa.

"Kiyi kome kikeso sabreen.......sonki da nakeyi ne ya jawomin......ki jani da duk kalar abinda kikaga dama.....kiyi duk yadda kikeso!" Ya fada yana wurgar da daya kwalin dake hannunsa a qasa.

"Karka qarayimin tsawa hamma" Ta fada tana jin fushi ya fara taso mata.

"Karka qara zargina akan abinda ba haka yake ba......idan ba haka ba..."

"Ba zaki yafe ba?".

"Basai na fada da bakina bama......na gaji hamma na gaji,wanne irin 'ya'yane ban haifa maka ba?,wanne irin baiwa ce Allah bai mana ba na 'ya'ya,samun tazara tsakanin haihuwa da wata haihuwar lallai sai ace sai ya zama daidai dana baya!......ana yiwa Allah dole ne?,idan kuma yace gaba daya ka gama haihuwa fa?!" Ta qarasa fada kuka yana qwace mata.

Wani malulun bacin rai ya taso ya saukar masa,donme zatace idan ya gama haihuwa fa?.

"Ban gama haihuwa ba sabreen.......saidai idan kece zakiyi silar faruwar hakan"

"Eh nice din.....nice hamma" Ta fada itama a fusace cikin gajiya da jin bayanansa.

"Okay.....okay.......yanzu kika fitomin a mutum.....kin tabbatar min da abinda nake zargi kenan".

" Ba zargi dama kakeyi ba.....kana cusamin laifin da bansan dashi ba......ko meye kake tunanin na aikata na aikata hamma!" Ta fada da wani irin kuka.

"Don kin aikata sai me?,saboda kinga na damu dake?,saboda ina sonki.......saboda kina ganin bazan iya rayuwa ba tare da ke ba?........idan na daina sonki shikenan?" Ya fada da salon tambaya yana dage mata girarsa dukka biyun gami da bude idanunsa da suka sauya launi.

Wani irin abu taji kaman an jibga mata a saman kanta.

"Kana zaton nima bazan iya rayuwa babu kai ba?,bazan iya rayuwa ba soyayyarka ba?......ka daina sona din fine......sai me?" Ta fada da qarajin kuka. A gaggauce ta juya ta fusgu hijabin data cire dazu ta maida,ta juya ko wayarta dake kuwwa bata dauka ba illa jakarta data ajiye ta fice a dakin a gaggauce.

"Kiyita tafiya.....zan iya rayuwa nima ko babu ke" Ya fada a birkice kaman wanda zai zauce.

Komawa yayi ya fada saman gadon yana jin wani irin bacin rai yana saukar masa. Tayi masa laifi kuma sannan ta fishi fushi?,ya samu yara alhamdulillah amma arziqin da Allah ya bashi yana jin yana buqatar qarin wasu......yanason ya gina family din da aka jima ba'aga irinsa ba......yanaso ya gogewa maamah gorin yawan haihuwar da tace asali dangin babanshi na dashi,haifarsu su biyu da tayi daga jikin ubansu ne.

Wani irin duhu da qunci dakin yaji yayi masa,tsahon awa guda da wani abu yana zaune guri daya batare daya ko motsa ba. Sake maida dubansa yayi ga sachet din maganin,ya saka hannu ya daga yana sake karantawa sai yayi jifa dashi wanda kai tsaye ya sauka a bakin qofa. Hannu bibbiyu ya saka ya dafe kansa yana jin yana wani sara masa,yaushe sabreen ta fara sha?,wanne lokaci ta dauka tana sha?,kada ya zamana ta illata mahaifarta fa?.

Juyi kawai ya dingayi tsahon awa uku,sai daga bisani a hankali hankalinsa ya dawo gangar jikinsa,ya miqe ya shiga bandaki ya daura alwala. Saman abun sallah ya zauna yana karanta wasu addu'o'i hadi da sunayen Allah,A hankali sai yaji zuciyarsa tana saukowa tunaninsa yana daidaita.

Sannu sannu sai komai daya faru tsakaninsu ya dawo masa fes cikin kanshi,wani sashe na zuciyarsa ya dinga masa zafi.

Kwanciya yayi niyyar yi kafin ayi kiran sallar asuba,amma sanda ya isa gadon da zummar kwanciya sai maganarta ta fado masa.

"Hamma na gaji.....bacci nakeso nayi". A nutse ya sauka daga saman gadon,ya koma saman kujera da nufin kwanciya,nan ma sai yaji ya kasa.

Da daya da daya ya dinga sauya guraren kwanciya amma ko ina ya sanya kai sai yaji ya kasa,sannu a hankali ya fahimci zuciyarsa na neman 'yar uwarta ne.....zuciyarsa na neman mahadinta. Duk yadda yaso ga kafewa wajen fita nemanta amma sai zuciyar taqi bashi hadin kai,daga qarshe dai ya fahimci ba wata mafita da yake da ita illa ya fita ya nemo duniyarsa.

Yana miqewa ana kiran sallar farko,don haka sai kawai yayi alwala,ya zura riga ya sanya flipp flops dinsa ya murza qofar zai fita a dakin.

Farouq ya samu daga bakin qofar dakin

"Yauwa dude......dan yiwa adda magana please ta miqo maganin fannah,jiya ta manta maganinta a jakarta duka biyun.....kasan ba'ason fashin shansa" Farouq yayi maganar hankalinsa yana wani gurin bai bada hankali ga fuskar fu'ad ba.

Wani irin sanyi jikinsa yayi kaman an watsa masa ruwan qanqara,ya juya gwiwarsa a sabule ya koma dakin ya hada kan magungunan ya bawa farouq. Sanda farouq din ya wuce sai yaji kaman bazai iya sake taku ko guda daya ba,sai a sannan tunaninsa ya dawo,fannah tana shan maganin planning saboda matsala da take da ita a mahaifarta,dole take shan maganin sabida akwai buqatar ta huta sosai tsakanin kowanne ciki.

Sam bai kawo hakan a ransa ba,ta yaya ma zaiyi tunanin maganin fannah zai shigo jakar sabreen?.

Yana rangaji haka ya dinga takawa har yakai masallacin harami,daidai lokacin da ake dab da tada sallar,yayi raka'atanil fajr yabi jam'i aka tayar da sallar.

Koda aka idar zama yayi yayi addu'o'i sosai,yayi istigfari akan zato da kuma yanke hukunci ba tare da bincike ba. Ya jima sannan ya miqe ya fara zagayawa guraren da yasan tafi zama ko zai ganta,amma har ya gama zagayensa ya koma duba guraren da ba wajen zamanta ba baiga koda me kama da ita ba.

Zuwa sanda rana ta fito ya gaji sosai,dole ta sanya ya koma masauki. Ya samu yaran duka sun gama shiryawa,kowannensu kuma ummeensa yake da buqatar gani,musamman su fauzan dake jiran fitowarta su duba gifts da suka samu kafin su wuce harami.

Baisan amsar da zai basu ba,saidai kawai ya zauna cikinsu ya sadaukar musu da wannan lokacin,amma dai duk da haka hankalinsu yana kan uwarsu.

Har azahar shuru bata ba dalilinta,ga anni na nemanta,maamah ma da bata iya magana sosai sau uku tana tambayarsa.

Zuwa la'asar hankalinsa ya tashi,don masu neman nata suna qara yawa ne,iffa ma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login