Showing 231001 words to 234000 words out of 557259 words
kamar yadda musulunci ya tanada......zaki kuma zaman gyara halinki yadda zaiyi daidai da halin mataye na gari,ta yadda wataqila a gaba idan kin hadu da wanda kika dace da ra'ayinsa,zai dauki mace ta gari ba makwadaiciya me qarancin duka wata siffa me kyau ba.......".
Banda sunansu huda,da zabin maamah dake mata amsa kuwwa cikin kwanya batajin zai fadi dukka wadannan kalmomin bata zazzage masa fiye da abinda ya gaya mata ba. Ba zata iya tuna cin mutuncinta da akayi a duniya da yakai wannan muni ba......cin fuska irin wannan a gaban idanunta,cikin salo na gadara da ganin isa.
A nutse ta daga idanunta da wani irin coolness ta watsasu saman fuskarsa. Kallon kallo suka yiwa junansu na wasu sakanni,kowa da abinda ke gudana cikin zuciyarsa game da dan uwansa. Fuska ya sake tsukewa sosai ya dage dukka girarsa biyun
"I told you.....your attitude needs a serious adjustment.......bazanyi tolerating any nonsense ba.....just obey all of my rules" Yana kaiwa nan ya miqe a nutse yana ajiye mug din sannan ya sake zuba hannunsa a aljihun wandonsa still yana kallonta.
"If you have any plans i beg you kada ki fasa......if you collect some money or something else.....kiyi duk abinda kike ganin kin tsara" Yayi maganar wani abu yana taba zuciyarsa,zarginsa kuma yana sake qarfi a kanta da ganin sunan maamah kawai cikin wayarta. Wani mahaukacin bugun zuciya ya haifar mata,ba shiri ta sake daga kanta zuwa gareshi sanda yake barin wajen. Wannan karon kam duk qwarewarta wajen iya boye hawayenta abin ya faskara,fara tsiyaya sukayi kafin ta sake jin muryarsa yana fadin
"Qarfe hudu akwai walima wajen anni......bana african time don ban sanshi bama.....i hope you get it" Ya sake fada ba tare daya waiwayeta ba.
Kasa tashi tayi a wajen wani irin baqinciki yana nuqurqusarta. Tsantsar tsana da haushin maamah yana sukar zuciyarta. Bata qyale ire iren wadannan abubuwan.......ba abinda yake sakata sarewa ko fargaba,amma ta mata mugun qulli da dabaibayi da 'yan uwanta?,why?.....me su huda sukayi da zata sakasu a wannan wasan?,me yasa ba zata bari suyi tsakaninsu ba a nan zata fahimci wacece sabreen din....muhammad jadda......yana buqatar ta karanta masa karatun d'iya mace,if gana expecting taka kowacce mace don yana da dukiya da kuma kyau......zata so ta zama macen farko da zata banbance masa tsakanin aya da tsakuwa,amma a yanzun hakan kuwa zai yuwu?.....she needs to be very humble don ta kubutar da 'yan uwanta......but ba zata dauki raini wulaqanci da kuma cin fuska daga wajensa ba,wannan shine lokaci na qarshe da zata bari ya jera mata maganganu masu zafi irin wannan,zata saka dukkan effort dinta donta gamawa maamah aikinta cikin sati biyu ta kauce ta barsu da rayuwarsu su qarata,idanma gasashi zatayi ta cinye dukka damuwarsu ce.....itama nata familyn ta sani,zaman lafiyarsu da kwanciyar hankalinsu shine first priority dinta.
A nutse ta miqe ta ta soma kauda komai badon maganganunsa ba....sai don da gaske bai kamata abar komai a wajen ya lalace ba. Neman abinci da samunsa abune me matuqar wahala wanda itace shaida akan hakan. Ta killace komai sannan ta tattara ta wuce zuwa dakinta,saidai qasan ranta cunkushe yake da wani irin bacin rai tare da lissafe lissafe masu yawan gaske game da yadda zata tunkari rayuwar.
"Don't be sad.....kada ki takura kanki da yawa.....just live your life normally yadda ba zaki cutu ba" Abinda zuciyarta ta dinga nanata mata kenan.
Akan idanunta biyu ta buga uku tazo ta shude aka doshi hudu. Bata dako niyyar shirin komai bare akai ga batun zuwa walima. Komai nasu baya burgeta......bata da buqatar kuma ta cudanya dasu sam sam.
Daidai lokacin da yake samanshi bayan dawowarsa daga sallar la'asar. Yaga kira daga security din dake waje sun shaida masa yana da baqi gasu zasu shigo ciki. Tunda yaji haka yasan 'yan gida ne.....inda baqin fuska ne lallai saisun nema izini an basu kafin su barsu su shigo,sai ya qarasa shiryawa cikin shaddar daya dauko,don already wandon yana jikinsa kafin yayi receiving call din.
Wagambari ce a jikinsa,asalin tsadajjiyar wagambari sky blue da aka yiwa wani irin dinki na alfarma dake nuna zallar zamani da kuma sanin darajar ado da dinki. Ba wani mutum da zaiga sutura a jikinsa ya sake ganinta ya maimaitata,kusan sakawa daya yakewa kaya ya gama dasu,shi yasa duk sati cikin fidda suturunsa ake.
Gaban madubi ya tsaya yana karya hular da zai sanya,shi gaba daya a takure yake,ire iren wadannan sabgogin bai saba dasu ba kwata kwata,wani harkar taro na biki,idan kanason ganin karsashinsa kazo sashen maganar kasuwanci. Kayan jikinsa kansu nauyi sukeyi masa,baisan ma me yasa a kayansa na wannan watan aka hada masa da dinkin manyan riguna ba,amna daya tuna farouq sai ya tabbatar shirinsa ne kawai.
Halfcover ya sakawa qafarsa dan qasar italy da akayi cinikinsa da dollars masu yawa. Ya sanya hular saman kansa take wani irin mutum.....lafiyayyen half cast ya fito me matuqar daukan hankali da kwantaccen kwarjini daka iya wucewa da zuciyar kowacce d'iya mace.
Waya daya ya dauka kawai sannan ya soma barin dakin. Yana sauka ne cikin takunsa dake bayyanar da nutsuwarsa jin kansa da kuma kamun kansa irin na cikakken namijin daya hada abubuwa da dama.
"Wow summa wow.....hammana" Muryar amna ta fara sauka a kunnensa sanda yake fitowa zuwa parlor din.
Yadda tayi maganar ya sanya murmushi subuce masa,ta kuma tuna masa da lokutan baya da yake very free ba kaman yanzu ba. Kullum ita ke bawa kwalliyarsa mark,anni na zaune a gefe tana musu dariya,saddiq na tsokanarta wani lokaci harsu sanyata kuka,shike tare mata shine ke hanasu.
"Hamma ka sake zama ango sak......don Allah BB farouq,kalli ta nan gefen" Sai datayi maganar ya lura da farouq dake zaune kujerar qarshe riqe da wayarsa yana dannawa. Kadan ya daga kai ya kalleshi ya maida ga wayarsa
"Yayi kyau mana amna.....amma kubarni nima soyayyata nake qoqarin gyarawa......Allah bazan qara wata uku a qasa ba.....guy dinnan daga jiya zuwa yau kalleshi ya sake canzawa?".
"Stop it farouq......" Fuad yayi saurin fadi yana duban amna kafin ya maida kallonsa ga farouq din. Ya fahimci sarai abinda yake nufi,akwai amna a wajen
"Hamma........am eager to see my aunty wallahi.....where's she?" Ta furta alamunta na nuna da gaske sabreen takeson gani,tana jin qaunarta sosai har cikin zuciyarta saboda hammanta.
"Jeki fito da ita" Ya fada yana yiwa amna nuni da hanyar. Bata ko tsaya sauraren komai ba ta wuce wajen da sauri saurinta.
Qarasa takowa yayi wajen da farouq ke zaune bayan wucewar amna din,aje wayar farouq din yayi yana dubansa.
"Mutumina......akwai labari kenan" Ya qarashe zancan yana kashe masa ido. Harara ya gasa masa
"Gidan jarida na bude daga jiya zuwa yau baka sani ba?" Dariya sosai farouq ya tuntsire da ita.
"Idanma hakanne Allah an maka uzuri.....da gaske ba wani abu sabo?,baka kawo kusanci tsakaninku ba?"
"Kaga don Allah malam dakata" Ya fada da husky voice dinsa
"Na gama gane inda ka dosa gaba daya fa.....na gaya maka ne abinda yasa na kawo ta cikin gidan nan kenan ko kuwa?,ko bunsuru ne ka aje?...." Dariya sosai ta qwacewa farouq fiye da dazu,yayi qasa qasa da muryarsa yana dubansa
"Maganar gaskiya ban yarda dakai ba.....i know you kaima ka san da wannan......a hadaka da halal dinka gidan da ba kowa saikai da ita.....kuma kacemin bakayi filling distance din dake tsakaninku ba.....anya wannan kyan da naga kanayi zakacemin duka a banza yake?". Rasa me zaiyi masa ya huce yayi,sai kawai hannunsa ya fada kan remote din dake gefansa,ya shammaceshi ya wurga masa ya sauka a kafadarsa. Duk duniya farouq kadai ke masa irin haka,yana sake hararasa yana zura hannunsa a aljihu ya fiddo wayaraa
Idanunta kawai ta ware daga kashingiden da take sanda taji ana knocking na qofar. Kashingidar da ta yita ne kawai tana tunanin abubuwa masu yawa tare da qoqarin cudanya abubuwan dake mata kai kawo cikin kwanya. Tunani kala kala ta dinga yi sanda taji ana knocking din.....shine ya biyota ya sake cin zarafinta ko kuwa?.....wasu ne suka sake zuwa gidan ko ko yaya?. Daga qarshe da taga bata da zabi dole ta motsa labbanta tana fadin
"Waye?"
"Nice adda....na shigo please?" Amna tayi tambayar cikin zaquwa. Kiran adda din da akayi sai ya sosa mata wani miki,mikin kewar 'yan uwanta wadanda su kadai ke kiranta da wannan sunan. Ambatar sunan ya sakata miqewa ta zauna sosai tana zuro da qafafunta qasa.
"Shigo" Ta amsa kawai kai tsaye ba tare da tasan waye ba.
"Assalamu alaikummm" Amna ta furta duka tare da shigowarta cikin dakin cikin murmushi tana riqe da handle din qofar idanunta akan fuskar sabreen yayin da fuskarta ke qunshe da wadataccen murmushi
"Wa'alaikumussalam" Sabreen ta amsa mata tana mata duban rashin sani.
"Ma sha Allah" Amna ta furta a sarari tana kasa dauke idanunta daga kan sabreen,murmushin saman fuskarta kuma ya kasa bacewa. Dama ta sani......ta sani tabbas hammanta ya iya zabe......tasan hammanta lallai zai zabo matar da ba irin ta kowa ba,amma bata taba tsammanin iya zabinsa yakai har kaman haka ba.
"I know.....kece adda sabreen dinmu ko?" Tayi tambayar da murmushi sosai tana nunata da yatsa idanunta a kanta. Dan shuru sabreen tayi tana kallonta ba tare data iya amsa mata ba,kwanyarta na mata lissafin wacece wannan din?. Tana da surutu sosai da alama,amma kuma yanayinta kadai ya gaya mata me kirki ce.
"Sunana amna hamza kibiya.....nice autarsu hamma fu'ad". Tayi mata bayani a taqaice saboda ganin yadda take mata kallon rashin sani. Ta fahimci sarai bayaninta......qanwarsa takeson cewa,kamar ta basar sai kuma wata zuciyar ta tambayeta
"Meye laifinta ita?" Don bataga wani hali na daban tattare da ita ba duk da a yanzun ta fara ganinta,amma bahaushe yace alamar qarfi tana game qiba.
Har amnan ta sare,sai kuma taga ta saki qaramin murmushi da yayi barazanar dauke hankalin amnan saboda yadda ya fidda kyawun innocent face dinta
"Qaraso mana" Ta furta tana miqewa tsaye tare da komawa saman sofa bed". Dukka energy dinta ya dawo,ta tura qofar a nutse tana ci gaba da murmushi ta tako ciki tana samun wajen zama saman wata sofa din ta daban
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862
π π π π π π π π
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 19
19
"Am sorry aunty.....hala nayi disturbing naki kina hutawa" Ta sake fadi tana murmushi. Maida mata martanin murmushin tayi,wanda har sai da amnan ta furta
"Ya salam,wanne irin kyau ne haka?". Kai ta girgiza
"Ko kadan....."
"Barka da rana,kin yini lafiya?,ya baqunta?,anni na miki ban gajiya,munzo mu wuce dake wajen walima......kowa yanaso ya ganki don jiya baku samu shigowa ba saboda dare ko?" Ta jero dukka abinda ke tafe da ita da wanda ke ranta kamar ba itace anni ta jawa kunne kada tazo ta cikata da surutu ba. A iya bayananta kawai ta gane wacece ita.....diyar matar nan da cikin kalamanta kawai zaka fahimci nutsuwa gami da tarin ilimi a ciki,wannan ya sanya sabreen sake sakar mata jiki kadan,saidai ta wani bangaren tana tunanin ta inda zata zamewa zuwa walimar,don sam bata shirya sake shiga kowanne taro ba. To na meye ma zata yita nuna fuskarta wa danginsu,bayan bawai tazo bane don ta zauna?.
"Amma walimar......" Sai maganar tata ta katse saboda daga mata hannu da amna tayi sakamakon shigowar kira,tayi blushing kadan sannan ta kalli sabreen
"Anni fa ba zama anyi suruka.....ungo nasan kirannan naki ne". Batason katsewa amna doki da farincikin da take ciki,don haka ta miqa hannu dole ta karbi wayar
"Idan ba zaki samu daman zuwa ba diyata kada kiji kin takura.....kiyi zamanki,dama taro ne na sanya albarka,sai a sallami mutanen". Ji tayi ba zata iya mata haka ba,ba zata iya watsa mata qasa a ido ba,don haka tace a hankali
"Muna hanya in sha Allah"
"To Allah yayi muku albarka,Allah ya kawoku lafiya"
"Ameen ameen" Ta amsa tana miqawa amna wayar idanunta nabin amnan da kallo. Ta fahimci wani farinciki takeji sosai,duk da batasan na meye ba,ganin amna din sai ya tuna mata da huda dinta,duk da ta girmi huda,saidai ita kuma ta girmi amna qila sa shekara uku ma ko hudu.
Dole ta miqe ta soma qoqarin rage yafen jikinta da dankwalin kanta don shiga wanka,ta lullube jikinta da qaton towel ta wuce tabar amna tana bata labarin sabreen din,abinda yaso badda bacin rai da takurar zuciyar da take ciki ta shige bayi da boyayyen murmushi a qasan fuskarta.
Komai na toilet din na kayan wankan ba irin nata bane,amna tunda ta karanta sunan products din da brand dinsu tasan harka ce kawai ta girma akayi. Daga yanayin sulbi da qamshin shower gel din kadai ta sake sallamawa,wannan ya dauketa minti kusan ashirin sannan ta gama. Towel biyu kawai ta shigo dashi,ta daura dayan,dayan kuwa dole ta nade kanta dashi saboda sumarta data jiqa da ruwa,ba wanda zata yafa don suturta jikinta,don haka ta sako shower slipper din zuwa bakin qofar toilet din ta cireshi saman water proof doormats din dake sashe na biyu na toilet din ta murda handle din ta bude qofar.
Daidai lokacin daya soma duba agogo ganin sun sakashi dabi'ar daba tasa ba.....dabi'ar daya tsana ya kuma ja mata kunne a dazu da kada ta soma aikatata kwata kwata. Tsaki yaja ya fara lalubar number wayar amna,saidai ya kirata kusan sau uku bata daga ba,wannan ya sakashi miqewa a fusace yayi ciki yana cewa farouq
"Ina zuwa".
Takawa kawai yakeyi cikin hallway din ba tare da yasan wanne ne dakinta a ciki ba?. Haka ya dinga gota bedrooms din a hankali,sai daya isa na qarshe sannan yadan tsaya cak yana kasa kunne duk yasan bazaiji motsin komai ba saboda yanayin door din,a jikinsa kawai yaji da mutum a nan,sai ya juya yana fuskantar qofar ya murdata da dan zafin nama.
Opposite suke tsakanin qofar toilet din dana shigowa dakin,wannan ya sanya kai tsaye kowanne idanunsa ya fada kan dan uwansa sanda qofofin suka bude lokaci guda. Budewar da taja hankalin amna wadda take zaune tana jiran fitowar sabreen.
Sarqewa idanunsu sukayi lokaci guda......fuskarta tayi fresh sosai,glowing din nan da fatarta ta qara samu saboda gyaran data samu na musamman ya sake bayyana. Ruwan da tayi wankan dashi ya sabbaba tarwatsewar qwayoyin ruwan saman fuskarta,sai suma zame mata tamkar wani ado,musamman sumar gaban kanta data kwanta sosai ta kuma fito ta qasan towel din daya kimawa kanta don ta samu ya tsotse danshin da yake jiki. Ta sassannin dogon wuyanta duka wasu daga cikin sumar sun kwanta,sai suka zamewa wuyan nata kamar wani ado musamman kafadunya dake a tsaye da wani irin structure me daukan hankali da kuma tudu da zaunawar dukiyar fulaninta sosai a qirjin.
Duka cikin qasa da second goma idanunshi suka kai wadannan. Wanda baikai mintunan da hankali da zuciyarka zasuyi zaton duka wannan karatun za'a iya yinsa a wadannan taqaitattun mintunan ba. Haduwar idanunsu na farko yayi mata ba zata,don bata taba kawo bayyanarsa cikin dakin ba,don haka ta maida qofar da wani irin sauri ta koma baya ta tsaya zuciyarta na wani irin bugawa.
Idanunsa da yaji sunyi wani irin laushi ya janye daga bakin qofar yana tabe baki
"Kamar gaske" Ya furta qasan zuciyarsa,zuciyar tasa tana ayyana masa Allah ne kadai yasan adadin mazan da suka ganta a hakan,tunanin daya sanya wani abu me ciwo ya tsaye masa a wuya. Wai wanne ma tsautsayin ya kaishi ajiye kayan da suke tamkar na kasuwa cikin gidansa?,zai iya killaceshi da gaske ya canza masa rayuwar da ta zame masa jini da tsoka?.
"Ba damuta bane......damuwata na koya mata lesson ko saboda gaba......tasan ba kowanne kalar mutum kake tabawa ka kwana lafiya ba".
Duban daya maida kan amna sai yaga itama shi take kalla.......daure fuska yayi tamau saboda ya karanci abinda ke fuskarta harda wani qunshe dariya
"Karku kuskura ku wuce minti shida.....if not...." Sai ya nunata da yatsa kawai ba tare da yace komai ba ya juya ya fice yana tura musu qofar.
"Adda......wallahi hamma ya tsani jira.....nasan kema kin sani,hurry up adda anni ma jira take" Muryar amna data sanar da ita ya fita. Wani wawiyar ajiyar zuciya ta saki,a hankali ta saki qofar data qanqame,sannan tabi hannuwanta da suke rawa da kallo.
Da gaske ta tsorata,don tunda tazo duniya ba wani muharraminta daya taba ganinta a haka,wannan shine karon farko. Qoqari tayi ta hade hannayenta waje daya tana matsasu da kyau,sannan ta bude qofar sosai tana fitowa.
Miqewa taga amna tanayi
"Bari na baki guri adda ki shirya a nutse....."
"Yi zamanki.....zan shiga dressing room na shirya" Tace da amna din,don idan ta fita ta barta fitowarta zatayi mata wahala.....infact ma zata iya canza shawarar zuwan.
Tsaf ta shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa bayan ta gama bulayin neman kayanta na gida,saidai ko ire irensu bata