Showing 63001 words to 66000 words out of 557259 words
wani abu dake shirin tunkarowa. Ya gaza fahimtar tsakanin ita da ANNI WACE MAHAIFIYAR?,WACE KUMA UWAR?.
Cikin nutsatstsen takunsa ya miqe daga zaman da yayi saman sofa bed yana sanya rufaffun takalmansa na fata berluti brand da suka dace da suit da lafiyayyen suit dinsa *hugo Boss* brand da sukayi fice wajen fidda luxury suit daga zare da yaduka gami da auduga mafi daraja a duniya.
Tsaye yayi gaban mirror yana cirar madaidaicin comb da yake amfani dashi wajen taje kwantacciyar sumar dake fuskarsa qasan habarsa da kuma kansa. Sumar da ko yaushe cikin sheqi take da asalin santsinta da wani irin darkness da gashin yake dashi nuturally. Sosai fuskarsa ta sake fresh,cikakkiyar eyebrows dinsa da eyelashes dinsa masu baqin gashi sun sake fidda ainihin kyawun fuskarsa,sun kuma sake taimakawa kyakkyawar qasumbarshi wajen sake qawata fuskarsa da wani irin ajiyayyen kwarjini.
Sai daya feshe jikinsa da sassanyan turarensan nan na din din din sannna ya kalli lafiyayyen agogon fatar dake kwance luf saman fatarsa. Lokaci ya cika daidai kamar kullum da zaici wani abu,ya taka a nutse yana isa inda dan kyakkyawan silver tray din ke ajiye wanda komai ke ajiye samanshi bisa tsarin da akasan wanda zai mu'amala da tray din yake dashi.
Har ya miqa hannu zai dauki glass mug din dake da murfi sai ya dakata saboda qarar wayarshi dake side pockets na suit nasa.
Hannu ya zura ya zarota yana duba me kiran. Sunan nan dai na dazu ya sake bayyana
"Amna....amna" Ya fadi sau biyu a hankali yana motsa jajayen labbansa da sukayi wani fresh suka sake fidda red color nasu kamar me amfani da wani kebantaccen abun shafawa labba
Sai daya koma a nutse ya zauna saman sofa sannan ya daga kiran
"Hamma......"
"Amna......i will be busy today fa"
"I know fa yaaya......anni ce kawai tace na gaya maka ka kirata"
"Lafiya dai ko?" Ya tambaya yana dan motsa fuskarshi
"Hamma......waye yasan tsakaninka da anni kuma?" Wani qaramin qasaitaccen murmushi ne ya subuce saman labbansa,wanda ya fidda kyawun fuskarsa sosai
"Jealous girl" Ya furta a hankali. Siririyar dariya ta kufcewa amna din,ya latse wayar yana laluban number annin. Tunda ya tashi da sassafe kafin ya fita yayi kiran layin nata har sau biyu saidai ba'a daga ba,sai ya bada uzurin banbancin tazarar lokuta dake tsakanin nigeria da South Korea din wala'alla tana nata baccin ko don yanayin jikin nata ma.
Tana gaban mirror tana fama da tazar doguwar sumarta. Wani abu guda daya da taqi jini shine duk abinda zai taba mata kai. Tun tana qarama daya daga cikin dabi'unta bata qaunar kitso kwata kwata,wannan ya sanya har sai da ummunta ta taba aske gashinta,saidai kowanne bawa da irin halittar gashinsa,don babu jimawa wata sumar ta fara taruwa ta kuma sake cika kan da yalwarta da santsinta har taso tafi ta baya da aka aske.
Sake runtse idanunta tayi sanda ta sanya comb din a tsakanin gashinta,daidai sanda ta sake jin daddadan sautin nan irin na dazu. Ta wurga fararen idanunta saman purse din dake ajjiye saman madubin.
Idanu ta zuba mata,kaman zata dauka sai kuma ta share taci gaba da abinda takeyi,wannan ya bawa wayar daman ci gaba da kadawa har ta gaji ta tsinke.
Wayar ya sauke daga kunnensa yana duban fuskar wayar. Sai ya sake gwada kira yana mamaki kadan cikin ransa,don tunda yake da annin bai taba kiran wayarta sau biyu ba ba tare data daga ko ta biyo kiran ba,sai gashi yau kira na biyar kenan zaiyi mata,duk da annin da kanta tace ya kiratan zasuyi magana. Kodai akwai laifin da yayi mata?,ya tambayi kansa duk kuwa da yasan ba haka bane. Abune mawuyaci ka batawa annin rai,musamman su din sanyin idaniyarta guda hudu.
Sake leqa fuskar wayar tayi a karo na uku kenan da ake kiran wayar. Suna daya ne dai MUHAMMADU. Siririn tsaki taja tana jawo wayar gabanta,cikin tarin abubuwan data tsana harda maimaita kiranta a waya koda kuwa kiran me muhimmanci ne. Ba wayarta bace amma ranta taji ya baci data duba taga miscal shida kenan harda na dazu,don haka dab da wayar zata katse ta daga adan zafafe ta karata a kunne.
Karamar ajiyar zuciya ya saki Lokacin daya fuskanci an daga wayar,a hankali ya maida hankalinsa ga daukan kiran da akayi,cikin jikinsa sai ya dinga ji kaman ba anni bace. Koda cikin bacci anni ta daga kiransa zaya fahimta ballantana idanushi biyu.
Kamfanin wayar ya fara irga sakannin da akayi ana riqe da duka layukan biyu,mamaki yaji yadan fara kamashi,yayin da a nata bangaren kuma ranta ya ninka baci akan na dazu. Ansan ba'a da abun fada aka addabi mutane da kira ba qaqqautawa?,an daga kuma zaa bar mutane da riqon waya a hannu?.
"Idan ba wani abun fadin zaa ajjiye wayar" Ta fada tana cije lips dinta na qasa saboda haushin da takeji cikin ranta.
Daga wayar yayi daga kunnensa yana duba number still duk da yasan number anni ce ba kuskure a ciki. Amma baquwar muryar me kama da muryar babies itace ta daure masa kai. Sai ya dakata daga takun da yakeyi don dauko mug dinsa,ya soke hannunsa a aljihun trouser na suit dinsa tamkar me jin sanyi
"Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye
"Ina me wayar?" Ya sake jifanta da tambayar
"Bansan me wayar ba.....koma wace me wayar wayan baya hannunta......ka jira idan ya koma hannunta ka sake kira" Ta amsa masa a taqaice tana gintse kiran.
Sautin Din din din na yankewar kiran ya sakashi janye wayar a kunnensa mamaki yana kashesa
"Who's she?" Ya furta a fili yana trying na sake kiran layin,saidai ya taras da na'ura tana gaya masa wayar a kashe take.
Sosai ransa yayi qololuwar baci,wacce irin yarinya ce haka mara kunya wadda bata iya magana dana gaba da ita ba?. Maida akalar kiran nasa yayi ga musaddiq zuciyarsa na masa wani irin zafi. Bayan magana da take fadi kanta tsaye harda katse masa kira?,wayan nata ne?,ko itace tayi kiransa da zata katse masa waya?.
Daidai sanda yake zaune a falon tun bayan wucewar maama da zuwaira kiran muhammad fu'ad ya shigo masa. A kasalance ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa,yana tsammanin driver manu ne ya gaji da jiran fitowarsa yayi kiransa. Sunan da ya gani a rubuce jikin wayar ya sanyashi sauke ajiyar zuciya gami da daidaita zamansa. Ya jingina bayansa da kujerar yana kara wayar a kunnensa. A ladabce yayi masa sallama
"Wa'alaikumussalam.....wace mara kunyar kuka bari wayar anni taje hannunta.....har tana katsema mutane kira?"
"Turqashi!.....anzo wajen" Musaddiq ya fada qasan zuciyarsa. Ya sani kowanne bayani zaiyi masa ma ba lallai ya fahimta ba. Ya tsani ya kiraka ka katse masa waya har sai idan shi ya buqaci hakan. Bashi da abun ce masa don haka muryarsa a raunane wadda tayi laushi saboda tarin tunane tunanen dake kanshi yace
"Kuskure aka samu hamma......kayi haquri....bari na hadaka da annin" Ya fadi yana miqewa tsaye.
Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,ya koma saman sofa bed din ya zauna yana jawo mug din yana duban dafaffiyar tumeric fresh milk din ciki kamar yau ya saba ganinta.
Da sassarfa ya soma kowawa ciki,dab da zai isa stairs din yaja ya tsaya saboda annin dake saukowa a nutse zuwa qasa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
Page 36
"Dama baka tafi ba?" Anni ta jefa masa tambayar a nutse tana jifansa da kallon tuhuma. Kalar tausayi ya koma yana karya wuya
"Bazan iya tafiya bane anni na barki"
"Saboda kana tsoron kada ta cinye nama na?" Ta sake tambayarshi cikin salo na gatse.
Ya gama fahimtar gatsen take masa amma sai ya basar yana binta da wayar lokacin data wuceshi tana zarcewa saman kajurun falon ta zabi daya ta zauna
"Anni......hamma ne yakeson magana dake" Ya furta yana rusunawa a gabanta
"Kiraminshi......wataqila yayita kiran layina bai sameni ba" Ta fada tana daukan remote hadi da sauya tashar dake aiki cikin tvn.
Sipping yakeyi na madarar yana irga yadda agogon dake facing dinsa yake bugawa. Ranshi a bace yake amma yana qoqarin danne hakan. Qarar wayar ya sanyashi waiwayawa inda ya gangarar da wayar yana kallon kiran musaddiq. Yasan ba kiran qashin kansa bane.....na anni ne,don haka bai barta tana burari ba ya jawota ya daga yana sakata a kunne.
Da wannan calmness din nashi yayi sallamawa anni. Itama ta amsa masa har cikin zuciyarta tana jin wani farinciki yana saukar mata da jin tasa muryar dake bayyanar mata lafiya qalau yake.
"Barka da warhaka anni" Ya fada yana dan rusunar da kanshi tamkar yana a gabanta. Yana jin wannan respect din har cikin zuciyarsa
"Barkanka me babban suna....."
"Kin tashi lafiya?,ya jikin naki anni?.....ina fatan ba wani matsala ko damuwa?" Ya tambaya cikin kulawa. Ajiyar zuciya ta sauke hade da furzar da numfashi
"Ba ciwo,sai damuwa da kukeson sakani kai da musaddiq". Maganar ta dukesu duka su biyun,har musaddiq dake zaune a gefe ta sanyashi daga kai cikin hanzari yana dubanta.
" Subhanallah......subhanallah anni kiyi haquri.....me mukayi?" Ya furta yana jin damuwa sosai cikin ranshi tare da tuhumar kansa akan sanya damuwa ga ruhin da kullun burinsa ya kyautata musu?.
"Fuad.....yau ka gaida maama daga safen nan zuwa yanzu?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi dauke wuta,sannan a hankali ya hade labbansa guri daya ya kuma amsa mata a hankali da
"A'ah".
"Me yasa?"
"Ba komai" Ya amsa mata kai tsaye,saboda shi din mutum ne da bai iya qarya ba sam komai girman laifinsa kuwa
"Me ya hanaka daga wayarta sanda ta kiraka?"
"Anni......fargaba kiranta yake sanyamin,anni banason ganinta tana kirana.....anni bana buqatar mu'amala da ita......nafiso taci gaba da nisantarmu anni kaman yadda tayi a baya......bama buqatarta......duk sanda zan ganta anni sai naji wani abu a kanta.....inama zaku fahimci laifi mafi girma data aikata mana wanda yafi tafiya ta barmu girma muni ciwo da kuma girman zunubi?" Wadannan sune abinda so samu ya kamata ya cewa annin,amma kuma bakinsa ya gaza furta hakan,sai shi kadai daketa jujjuya maganganun cikin zuciyarsa. Ya rasa waye zai zayyanawa su,ANNI dince,to amma bayaso yabar mata wani abu da zaya yi mata tsaye a zuciyarta ko kuma a rayuwarta. Damuwa itace abu na qarshe da yayi alqawarin tarewa anni shigarta,kamar yadda ta sanya duk wani qarfin iko na jiki dana aljihunta ta tare ma rayuwarsu kasancewa da wanzuwa cikin damuwa har kawo bigiren da suke kai haka a yanzu. Wannan tunanin ya sanya ya zabi bawa anni amsa ta hanyar cewa
"Ba komai".
" Ban tsammaci haka daga gareka ba Muhammadu,kanaso abbanku yaji ba dadi a ransa shima kamar yadda naji?" Ta fadi cikin tausa murya tamkar tana magana da qaramin yaro.
"Ko kadan anni.....kema da muka sanya kikaji ba dadin yanzu haka kiyi haquri ki yafe mana......za'aci gaba da kokawa da zuciya,kuma zaa gyara in sha Allah". Murmushi ta saki tausayinsu yana narka mata zuciya. Lallai duk dan da baiyi sa'a da dacen uwa ba abun tausayi ne shi.
"Bakuyimin laifi ba muhammad.....illa dai lahirarku da kuma fagen rayuwarku da nakeson na sake share muku ita tas". Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa ta karaya......inama ana canjen uwa?.......inama ace anni ita ta haifesu kamar yadda ta haifi Sadiq da farouq?.
" In sha Allah anni bazai sake faruwa ba"
"To Allah ya yiwa rayuwarku albarka,ya tsaremin ku daga dukkan sharrin me sharri"
"Kinyi addu'a me kyau anni" Ya furta qasan ransa,don sai yaji kaman ta nemawa kanta tsari ne daga dukkan wani matakin da maama keson kutsawa dashi cikin rayuwarsu.
Ya jima yana juya wayar a hannunsa,tunani da dama suna kutsawa kwanyarsa. Sai yaji gaba daya madarar da duka breakfast din da aka kawo din ya fita a ransa,don haka ya maida mug din ya ajiye,ya miqe ya jawo bedside drawer ya zari dukka abinda yake da buqata ya taka a hankali yana fita a dakin jiki da zuciyarsa duka babu walwala da karsashi.
Sannu a hankali motar dake dauke dashi zuwa companyn ke tafiya busa qa'idoji da dokokin qasar,yayin da shi kuma yake kwance jingine sosai da back seat din na motar. Wayarsa ya sake cirowa cikin rashin walwala ya budeta,bangaren kira ya shiga yana duba adadin miscals na wayar nashi. Miscall dinta shine na qarshe a jerin kiraye kirayen daya rasa cikin wayarsa. Ya bude numbers din yana kalla tamkar me qoqarin haddace numbers din. Tsahon wasu sakanni sai ya dauke duban nasa ya mayar ga titi da yake ita hangowa tarwai ta glass. Haka kawai yake jin bayason kiran,gaba daya bashi da wani hope ko marmari akan dukka wani abu da ya shafeta,ta kashe komai ta kuma qonashi murqus tun a shekarun baya da suka shude,ME YAYI SAURA?. Amsar da kullum take biyowa baya shine BABU.
Da wani dan qaramin hanzari ya danne zuciyar tasa ya danna maballin kira,kiran kuwa ya tafi direct kai tsaye,wanda cikin qasa da sakan goma kiran ya isa ga wayartata.
Duk da jerin dinner abincin daren da me hidima da ita keta faman jere mata a gabanta amma ba wani abu daya daya burgeta ya ko ya bata sha'awa. Sai yanzu ta fahimci dawowa DUNIYARsu da kuma shiga DAULARSU ba shine kadai iya abinda take buqata ba. Ba shine kadai iya abinda ruhinta da zuciyarta suke da muradi ba. Lallai tana buqatar wani abu da yafi wannan muhimmanci a tattare da ita.
Ta juya a hankali tana duban zuwaira data cika plate da pepper chicken tana ci hankali kwance. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta
"Zuwaira....."
"Asama'u" Zuwairan ta amsa mata da bakinta daya cika da zallar tsokar kazar gwamnati(broiler).
"Me yake faruwa dani ne?......wa kaman ba nice ma'u ba?,kamar ba nice asama'u ba?,koda karin maganar nan da hausawa keyi ne yakeson tabbata a kaina?,lokaci shekaru da zamani suna son maidani wata lusara?......indai hakan ta kasance bazan taba yafewa kaina ba......bana ma fata hakan ta kasance,dole yarana su dawo qarqashin iko na kamar kowacce uwa.....dole su kasance qarqashin shimfidaddun dokokina.....suyi abinda nakeso na sakasu....su kuma bar abinda na hanasu......suso wanda nakeso.....suqi wanda bana so.....su kyautatawa wanda naso su rabu da wanda bana so.........dole na rabasu da aminatu.......dole Alhaji hamza ya zame musu babban abokin gabar da babu irinsa......zuwaira.....wannan karon burina da muradina me girma ne.....inaji kuma ina ganin kamar girman buqatata a wannan karon ya shallakewa aikin MADUGU.....Ina buqatar wanda yafi madugu zafi.....ina buqatar aiki da zafi zafinsa" Idanun zuwaira suna kanta har ta kammala,sai zuwairan ta nisa ta ajiye plate din naman hannunta ba don ya isheta ba,sai don gano damarmarki masu girma da yawa a gabanta.....da wata siririyar qofa da take hangota da fadin gaske daga can ciki.
"Akwai BAHAGO bayan madugu din......bani da kokwanto ko tantama a kansa.....tun ba yau ba......tun kina kogi na miki sha'awar zuwa wajensa amma kika qi bada hankali.....na tabbatar inda kin aminta da hakan da yanzu ba wannan matsalar a gabanki.....da tuntuni kin jima da tsallake wannan babin.....saidai kina da buqatar kudade..... Kudade masu kauri.....kaman yadda aikinsa yake da zafi haka yake da karbar kudi,saidai ribar da zaki samu yafi abinda duka zai amsa daga gareki".
Zamanta ta gyara sosai tana duban zuwaira. Ta sani ita din gaba take da zuwaira ta fannin abubuwa masu tarin yawa.....zuwaira bata isa ta hada kanta da ita ba indai ta wannan bangarenne......amma kuma komai qasqancin bawa akwai ta inda yake iya wuce maka
"Tunanin da ya fara zuwa kaina kenan.....abun nan yana min ciwo.....kamar ni zuwaira?" Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta
"D'ana......mamallakin jadda diamondchore resources amma bazan iya kallon mutum nayi masa kyautar million biyu zuwa sama ba?,zaman me nakeyi a duniya zuwaira?" Ta qarashe fada da wani irin zafi da take jin ya ishe mata har qasan zuciyarta
"Komai ya qare idan kinbi a sannu.......idanma baki da wannan jumurin zirga zirgar ai kina dani,driver kawai zaki yiwa umarni......fu'ad kuwa danki ne.....muddin kuma yana neman albarka.....dole ya biki" Ta fadi tana tallafar farantin namanta da nufin ci gaba da kaiwa cikinta. Daidai Lokacin kiran ya iske wayar dake yashe a gefe guda.
Tare suka kalli wayar,sai zuwaira da tafi kusa da ita ta miqa hannu ta jawota tana dubawa.