Showing 402001 words to 405000 words out of 557259 words

Chapter 135 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

479

ga fuskarta data futo sosai ta madubin. Wani kallo yake mata ko qiftawa baya yi,yana fatan tayi kuskure ko sau daya ta daga kai ta kalleshi,yana son karantarta ta cikin idanunta sosai,ya sake matsawa sosai jikinta yana sansana kanta dake fidda wani irin sassanyan qamshi.

Ta gama nata brush din amma tanata juyashi a hannunta,ta rasa yadda zata gaya masa.....ta kasa daga kai ta kalleshi ma bare ta samu qwarin gwiwar gaya masa. Ya karanci hakan,murmushi ya qwace masa.

"Wannan kunyar daga ina?" Ya tambayi kansa da kansa daga can qasan zuciyarsa.

Yana sane yaci gaba da cinye musu lokaci,yanason tayi magana amma kuma ta gaza,har zuwa sanda taji ta soma tuqewa,saita ajiye brush din,ta kuma juyo da hanzari tana fadin.

"Ni na gama" Qurjinsa ta fada kai tsaye,don babu wani space da zai bata daman wucewa. Kan qirjinsa idanunta suka fada,ni'imtaccen gargasar qirjin tayi maraba,ta daga idonta a hankali tana kallon tazarar nisan tsahon dake tsakaninsu. Ya fita tsaho sosai,duk da cewa ita din ba gajeriya bace,idanunta suka sauka kan Adam's apple dinsa daya fito sosai ta maqogoronsa kaman zai fado.

Wani abu guda daya tal da yake burgeta ga halittan namiji kenan......batasan meyasa yake burgeta ba,amma dai tasan yana bata mamaki,ta jima kuma tanason taji abun ya yake,tauri ne dashi?,yana musu zafi ko kuwa?,ba tare da tunanin komai ba ta miqa yatsanta a hankali zuwa wajen ta tabashi.

Cikin kowanne jini dake harbawa a jikinsa yaji saukar yatsan nata,ya hadiye wani abu daya sanya Adam's apple din motsi yayi qasa ya sake dawowa saman. Kasa jurewa abinda yakeji din yayi,sai ya fincikota sosai zuwa jikinsa ya matseta a qirjinsa da kyau yana dora fuskarsa saman wuyanta.

"Wannan tsokana ne ai......yanzun kuma inda zan ritsaki kona nema fansa saiki isheni da kukan banza......har a kiramin anni ma da momma ko?". Kunya ce ta kamata me tsanani,akan jiya yake tsokanarta ta sani......sannan ita kanta batasan ma'anar abinda tayin ba yanzun,taji tana sha'awar tabawa ne kawai.

"Nifa wannan gaisuwar baiyimin ba......ina buqatar zuzzurfan alaqa tsakanin da iyalina......inason ki zama qawata.....aminiyata......mamana.....yayata.....qanwata....oh" Sai kuma ya tsaya yana dagota daga jikinsa gami da dan dukan goshinsa.

"Ashe fa ance sai anyi shawarar za'a soni ko aah ko?" Ya fada yana ware mata idanunsa. Kauda kanta tayi gefe daya zuciyarta na bugawa,wani murmushi yana son kubce mata amma tana hana hakan,bata ankara ba taji ya dagata cak ya azata gefan sink din bandakin,hakan ya bawa santala santalan cinyoyinta daman bayyana don bathrobe din ta dage kadan.

"Kinsan me?" Ya fada yana tsayawa tsakanin cinyoyinta,hucin numfashinsa dana daddadan turarensa yana sauka a fuskarta.

"Karki wahalar da kanki DUNIYATA kice saikin koyawa kanki sona......" Daga kai tayi ta kalleshi abinda yakeson gani kenan dama tun dazu,saidai ita din tayi hakanne saboda mamakin maganarsa. Girarsa ya dage mata dukka biyun yana jin dadin ganin qwayar idanunta. Oily eyes daya jima yana kokwanto shin akwaisu?,sai gasu a jikin abinda yake mallakinsa gaba daya.

"Yes.....iya soyayyar da nake miki ma ta ishemu mu rayu ni dake.....bake kadai bama.....har babies din da zamu haifa nan gaba" Ya fada yana dora hannunsa saman plate tummy dinta,abinda ya sanyata jan wani irin numfashi saboda tafin hannunsa guda daya daya dora saman budaddun cinyoyinta.

"DUNIYATA....Kinsan yara nawa nakeso ki haifamin?" Kasa amsa masa tayi,tafi buqatar ya matsa baya kadan kada ya dagula mata lissafi,abinda ta fahimta kaman yana son sake mata wayo ne kawai yake saka kusanta kanshi da ita.

"Karka zaqe da yawa.....har yanzu ban gama yanke hukunci ba" Ta fada cikin tsanani dakiya. Dariya yakeso yayi sosai amma ya dake,ya fahimci qarfin hali irin nata da zallar qi fadi dake dawainiya da ita.

"Don't worry.....kedai ki tayani ji ma kawai ya wadatar dani" Yana kaiwa nan ya sunkuceta gaba daya tamkar ya dauki 'yar jaririya yana takowa zuwa bedroom din.

"Ka saukeni" Ta fada a narke,saboda ta lura gaba daya ya raina dagata,ya maidata kamar wata 'yar bebin roba.

"Ta yaya zakiyi nauyi kina wasa da abinci?,indai kinason mu shirya saikin koyi cin abinci irin na muhammad fu'ad" Yakai qarshen maganar yana direta saman sofa bed,sannan ya fara takawa a hankali zuwa saman dressing table yana kwaso kayan shafanshi data tabbatar yafi qarfin talaka irinta.

Gabanta ya zubesu gaba daya sannan shima yabisu ya zauna a gabanta yana tankwashe qafa tamkar bawa da uban gidansa. Ya soma bude cream cream din da wasu irin abubuwa da batace ga sunansu ba ya fara tatsawa a hannunsa sannan ya kamo hannunta yana juye mata su a ciki.

"Zaki iya haifamin yara dozen biyu?" Yayi maganar murya a sanyaye da wani zuzzurfan sauti yana riqe da hannunta da yake maida cream din daga hannunsa zuwa nata.

Idanu tadan wara tana dubansa da kyau.

"Please am serious.....ko through IVF ne.....a dinga saka miki biyar biyar.....nayi alqawari ba zaki sha wahala ba.....zan biya ko nawa ne a ciresu cikin aminci.....zan kashe miki ko nawa ne DUNIYATA.....nayi alqawari" Mamaki sake kasheta yayi ganin yadda yake maganan da dukka gaskiyarsa,hakan ya bayyana itama a idanunta,sai ya saki wani murmushi yanayin fuskarsa yana canzawa.

"Kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana sakar mata hannu don ta samu daman shafa man daya tatso mata.

"Naso mu da yawa abbanmu ya haifa.....nayi wannan burin saboda gidan masu yara da yawa yana burgeni,saidai kuma mu biyu aka haifa.....inaso na tarawa abbana zuria me yawan gaske.....zuri'ar da zasu dawwama suna masa addu'a da sadaqa jariya.....bani da sha'awa ko burin auren mata biyu.....dake kadai nakeso na rayu DUNIYATA shi yasa nakeso ke din daya ki zama uwar dukka yarana" Ya qarasa fada yana dubanta.

"Baga fareeda ba?" Tayi zancan da wani yanayi da ya sanya murmushi kubce masa,yadan dafa goshinsa yana cewa.

"Maganan fareedan bai wuce ba?..... apologize din da nayi jiya baiyi ba?.....okay am ready to repeat it" Ya fada yana jinjina yadda abun yafi tsaya mata a rai fiye da komai. Kafadunta duka biyun ta daga tana kauda kai

"Ina ruwana nikam.....am temporary......"

"Temporary?" Ya katseta cikin maimaitawa yana dubanta da kyau ba tare da ya barta ta qarasa fada ba,sai ya ajiye boyayyen numfashi

"You're my world.....kece DUNIYATA sabrrrrr....na rantse da Allah.....banda ubangijin daya haliccemu ba wanda ya isa ya qwaceki a hannuna.....ke kanki baki isa ki raba kanki dani ba.......ko mutuwa ina kai qararta wajen Allah.....muddin tana da nufin rabani dake ubangiji ya hukuntamin ita". Sosai maganarsa ta ratsata,taci gaba da shafa wa hannayenta man cikin wani irin kasala ba tare data dago idanunta ta kalleshi ba.

"Ya kamata muje kiyi break" Ya fada yana katse shirun hadi da miqewa. Batasan me ya matsa yayi ba sai daya miqo mata rigar saman cinyarta.

Rigar jiya ce dai da bata saka ba,saita daga ido tana masa kallon Why?. Kafada ya daga yana watsa hannuwansa.

"Zan iya saka miki if ba zaki iya sawa ba" Kai ta girgiza masa da sauri,don ta tuna jiyan,daga saka rigar labari yasha banban.

"To ka fita sai na shirya" Ta fada a shagwabe still

"Inje ina?,bayan ko na fita dinma saina dawo na taimaka miki na daure miki rigar kin manta?" Ya fada hannuwansa na goye a qirjinsa yana qare mata kallo,don hatta cikin bathrobe din ba qaramin kyau tayi masa ba.

"Na rufe idona.....inkin gama sakawa ki gayamin" Ya fada yana juya mata baya gami da maida kallonsa qofa yana ganin gilmawar ruwa ta tsakanin labulayen da basu gama rufuwa ba.

A gurguje ta saka rigar,tanayi tana waiwaye wai kada ya juyo ya ganta bata sani ba. Dariya yakeyi abinsa can qasan ransa,don yana ganinta tarwai ta wani glass dake gabansa ba tare da ta sani ba.

"Zan iya juyowa?" Ya tambaya yana danne dariyarsa.

"Eh" Ta fada tana turo baki gaba,abinda yayi matuqar burgeshi har yaji kaman ya kama lips din ya shanye.

A nutse ya dinga bin igiyoyin yana daure mata,kowacce daya saiya tambaya

"Tayi haka?" Kai take daga masa mafi yawa,ta koma kaman kurman qarfi da yaki,ta tabbatar kaf halittun bayanta ya gama qare musu kallo,tana jin yadda yake sakin ajiyar zuciya time to time. Yadda maroon din rigar ta zauna daga bayanta kadai ya qawatar dashi gami da tafiya da hankalinsa. Ya dora yatsunsa a hankali saman fatar wuyanta,inda wajen ya danyi jajaja. Hannunta ta dora saman nasa tana dan danne wajen,guri kusan uku duka haka sukayi,yasan kuma shine sila,zare hannun nasa yayi yana juyo da ita tana fuskantarsa.

Idanunsa ya lumshe yana kuma budesu duka samanta.

"You look so gorgeous" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin sassanyan yanayi yana duban qirjinta da yayi redness shima guri uku. Yatsantsa yakai wajen yadan taba sannan yace

"Does it hurt?" Fuska ta kwabe masa cike da shagwaba kaman zata sake masa kuka,sai ya yarfar da hannunsa yana fadin.

"Ayyah.....sorry,bari na fanshi wannan ciwon" Ya fada yana ja da baya fuskarsa da murmushi. Luggage dinsa ya kwantar ya bude,ya ciro wani dan mitsitsin box ya tako gabanta.

"Qaramim gift ne....for you duniyata" Ya fada yana ciro wani siririn agogo dake zuba qyalli. Koda bakasan meye ba kasan abune me matuqar daraja,kallo daya zakayi masa kasan abune me tsadar gaske,bashi da girma ko fadi amma yana daukan ido sosai. Matsowa yayi kusa da ita sosai,ya miqa mata hannunsa yana kallonta da ido. Ta fahimci me yake nufi amma saita noqe,bai wani tsaya jiranta ba yasa hannunsa ya kamo hannun nata sannan ya fara saka mata agogon.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 103


103


"Ya subhanallah" Ya fada yana juya hannun cikin tafin hannunsa. Ya mata wani irin kyau kaman saboda ita aka qirqireshi,ya zuba idon hannu yana jujjuyashi kafin a hankali yace.

"Our latest wrist watch...2025,kin masa kyau duniyata.....nayi accepting wannan design din saboda ke,koda baiyi daidai da ra'ayin dealers dinmu ba,i love it for the sake of you" Ya qarasa maganar a tausashe yana kai hannunsa yayi kissing hannun nata,still idanunsa a kanshi,ya zura hannunsa a aljihunsa ya fiddo wayarsa ya laluba wata number ya kira. Bugu daya aka dauka,da hausa taji yana magana.

"Mun siya design dinnan......sannan madam ta ninka price din da wasu dollars din akai ainihin price din". Ya fada a nutse da alama yana magana da wasu ne

" Alright " Taji ya sake fadi yana katse kiran,yana maida wayar aljihunsa tana dubansa idanunta a warwaje,sai daya daga kai sannan suka hada ido,fuska ta narke

"Wacce madam din?" Ta tambaya da siririyar muryarta dinnan,miskilin murmushi ya sake mata

"Akwai wata bayan ke?" Saita sake fidda idanun

"Ban da kudin siya fa....thought dai bansan nawa bane"

"Amma kina da muhammad jadda ko?" Ya furta yana ja baya kadan idanunsa a kanta. Yana jin dadin kallonta sosai,sai yakejin duk wata tsohuwar kewa ta rayuwarshi tana sulalewa,yana jinsa wani sabon mutum na daban.

Duban hannun nata tayi,haka kawai taji kaman ya saka mata wani abu me daraja da yawa,sai takejin hannun ya mata nauyi.

"Na gode.....na gode sosai" Ta samu kanta da furtawa a sanyaye. Wani tsadajjen qaramin murmushi ya saki yana girgiza kansa.

"No.....no need duniyata.......ba irin wannan godiyar nakeso ba.....the only one i want........" Sai bai qarasa ba ya mata nuni da shimfidadden gadon. Da sauri ta juya masa bayanta tana kasa hada ido dashi,ta fahimci yana bawa abunnan muhimmanci tamkar baisan kayan kunya bane?.

A nutse taji ana yafa mata abu ta baya,ta daga kanta sai taga wata baqar sassalkar abaya ce,manal alhammadi shine tambarin da yake maqale a hannun rigar,ta fidda idanunta tana jin wani abu yana girmamarta,ta taba jin company din,wanda dukka abayas da yake fitarwa luxury ne masu tsada da aji sosai,ta sansu ne saboda ita din masoyiyar abayar ce.

"Ba wani kunya tsakanin muhammad fu'ad da duniyarsa......ba kunya tsakanin muhammad fu'ad da matarsa......abinda kawai yake buqata......madawwamiyar soyayya da zata mamaye rayuwarsa.....ta bashi wani farinciki da nutsuwa daya rasa a rayuwarsa.....duk da cewa ina zaqewa da yawa.......amma wannan abun nake bara" Ya rigata fada kafin ita ta fada. Boyayyen murmushi ya subuce mata,wato daga jiya zuwa yau ya fara haddace irin kalmominta kenan da take yawan maimaita masa?.

Juyo da ita yayi yana zura mata hannayen rigar ya furta

"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.....komai saikin masa kyau?" Yayi maganar yana dage girarsa.

"Komai saina masa kyau?.....ko komai sai yamin kyau?" Ta tambayeshi tana mamakin yadda yake juya maganar daga qarshe ta koma farko.

"Kece kike musu kyau basu keyi miki ba.....don dama kedin me kyau ce.....you're not ordinary duniyata" Yayi maganar sanda ya dago daga tsugunnan balle mata button din da yayi har qasa. Mayafin ya warware yayi mata lafiyayyen rolling tana tsaye tana kallon ikon Allah,ya kama hannunta zuwa gaban mirror yayi tsaye a bayanta.

"Duk wani abu me daraja rufeshi akeyi a killaceshi" Ya furta a nutse yana duban kyakkyawar fuskarta ta cikin madubin,yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa saboda ita,kishinta yana sake ratsashi da kyau,yana sake jin tabbas......lallai ba wanda zaisha ba kuma wanda zaici bulus daga cikin mutanen dake hannunsa a yanxu.......tun daga kansu mashkur har zuwa kan zuwaira da bibo.

"Ga aro nan na baki.....idan munci abinci mun dawo zaki bani kayata" Ya fadi wannan karon yana dan sanya seriousness saman fuskarsa. Dan dubansa tayi kadan,sai ya gyada mata kai alamun tabbatarwa. Yanaso ne yayita kallonta,yanason wucewar kowacce daqiqa tayishi bisa idanunsa,yanaso yaci gaba da kallon baiwa da ni'imar da Allah yayi masa,yanaso su kasance a haka shi da ita......da zaiyiwu su qare rayuwarsu cikin irin wannan yanayin na dagashi sai ita.

Yana maqale da hannunta suke sauka zuwa bangaren cin abinci,private ne wanda ya dauko musu cook dinne musamman saboda iya su biyun. Sun samu dining room din cike da cima kala kala,abincin Africa da wasu na Nigeria. Macace da batace ga daga qasar da take ba,ta tarbesu cikin haba haba sannan ta fara serving nasu cikin kulawa,lokaci lokaci tana magana da fu'ad da hankalinsa ke waya cikin yaren Dhivehi,har ta kammala ta juya ta fita tana basu guri.

Juya spoon din take kawai a plate din tana hadiye wani abu a qirjinta. Batasan meye ba amma ya tsaye mata a wuya. Bai ankara ba,sai daya gama uzurinsa da waya sannan. A mamakance yake dubanta.

"Start mana madam....banason wasa da abinci fa?".

"Itama fareedan ce?" Ta tambayeshi da wani salo daya sanyashi karantar zallar kishin dake kwance a idanunta,saidai kuma a sarari qwalla ce kwance saman oily eyes dinsa,sai suka qara wani sheqi.

Dariya yakeson mata saboda wani irin farinciki yaji yana lullubeshi,tun daga saman zuciyarsa yana sauka ta kowanne sashe na gangar jikinsa. Har ya fara winning haka da wuri? Ya tambayi kansa yana taya kanshi murna,amma a bayyane sai ya lanqwasa fuskarsa alamun tausayi.

"Me kuma nayi?". Muryarta na rawa kadan tace.

"Kunata magana da yaren da banaji.....tanata maka hira kana amsawa?". Wannan karon kam kasa boyuwa dariyarsa tayi,abinda ya tunzurata kenan.

" Karki wuce gona da iri sabreen,karki rudu ki fada soyayyar abinda ba yafi qarfin ajinki.....abinda yafi qarfinki,abinda baki da tabbas a kansa.....shin kin Manta maamah tana nan?". Tambayar data tarwatsa duk wani qwarin gwiwa da take qoqarin tattarawa kanta,taji kuma komai ya tsaya mata cak.

Dab da ita ya dawo ya zauna,ya kama hannayenta ya saka cikin nasa yana matsawa a hankali.

"Kin taba ganin mutum ya canza DUNIYARSA?" ya mata tambayar kai tsaye,qasa tayi da kanta don sai takejin tana son jefa rayuwarta cikin hadari ne kawai,muddin ta sakewa zuciyarta ta fada sonshi to ba shakka ta fada babban tarko......babban tarkon da zai bawa maamah daman walagigi da rayuwarta yadda taga dama.

"Amsar itace aah......ke duniyata ce,babu daman na sauyaki ko na hadaki da wata ko wani abun......ni muhammad jadda naki ne ke kadai,don ke kadai aka halicceni.....ki rubuta wannan ki ajiye"

_to zamu gani,anya hajiya maamah zata qyale kuwa???_


*ANNI*


Tun a jam'in sallar asuba da sukazo yi taga bata ga fu'ad ba.....still da tace farouq ya turo mata shi komin dare baizo ba,har suka gama waya da abba Alhaji hamza kibiya dake tashi umrar ta kwanta amma ba fu'ad din ba dalilinsa.

Sanda suka kammala sallar sai tayi zaune kawai tana lazimi,tunaninta yana rarrabuwa,bataga fu'ad ba......bataga sabreen ba,duka ina suka shiga?. Ta wata fuskar sai takejin relief na rashin ganinsu su duka biyun,don zuciyarta na qissima mata wani abu,ta wani bangaren kuma bataso ta sake jikinta akan hakan,saboda tasan wace mariya din.

Takwas saura farouq ya shigo gaidata. Yana daga zaune gabanta ya dan dubi amna dake kwance tana shirin komawa bacci

"Ta duba qur'aninta kuwa?". Kai anni ta daga masa

" Ta duba" Sai ya jinjina kai. Wani sabo ne da raino data musu dukkansu,dole kowacce safiya....komai uzurinka ko meye kakeyi ka fara duba qur'ani kafin komai.

"Kiramin fu'ad.....ka gwadamin dukka layukansa" Anni ta fadi tana gyara zamanta.

"Na gwada wani tun jiya a kashe,amma bari na gwada sauran" Farouq ya fada hankalinsa kwance,don shi kam ya gama hasashen inda aka haihu a ragaya ma. Baya tunanin ko maamah ta yiwa fu'ad farin sanin da shi yayi masa.

Daya bayan daya yabi layukansa yana kira amma kowanne gaya masa ake a kashe yake,sai ya daga ido kawai yana duban anni

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login