Showing 465001 words to 468000 words out of 557259 words

Chapter 156 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

491

as possible.....ta iya yiwuwa ya rage zargina.....ta iya yuwuwa kuma ya daina katsemin muhimman lokuta na da DUNIYATA". fuskewa farouq din yayi yana sosa kanshi

"Eh to.....kaman tafiyanma zaifi mana Alkhairi gaba daya.....don bana tunanin idan ka zauna a nan dinma warkewar arziqi zakayi,gadon ya muku kadan gwara a koma gadon gida". Toshe bakinta sabreen tayi,salin alin ta debi kayan kunyarta taja jikinta tana barin gurin tun wani a cikinsu bai ganta ba.

β˜…Salati drivern ya saki,hannuwansa bisa saman kansa yana sake sakin salatin gami da cewa.

"Ku kawo dauki bayin Allah......hajiya ta zube". Dukka hankalin ma'aikatan gidan ya tattaru a kanta,saidai har matan ciki tsoro da shayin dagata suke,basusan haqiqanin abinda zai biyo baya ba idan suka dagata bayan ta farka.

"Dole haka za'a ceci ranta,kome zai biyo baya ai ba za'a barta ta mutu ba ko?". Malam sa'adu me gadi ya fada.

"Matso ke raliya ki kama musu ita" Ya fadi yana matsawa baya.

"Gashi ba kowa gidan Alhaji hamza ballantana muji ina ake kaita" Malam sa'ad ya fada yana duban driver din.

"Kowanne asibiti ma kaita za'a yi tunda abune na gaggawa.....ki shigo mu tafi" Yace da raliya yana shigewa cikin motar.

Tuqi yake a gaggauce yana tsoron kada ta mace a hannunsa,babar babban mutum irin me jadda ta mutu a hannunsa tabbas ba qaramin tashin hankali bane.

Tafiyar minti shabiyar suka samu wani private suka tsaya a nan,aka dauko wheelchair aka dauketa akai,har a sannan bata dawo daidai ba.

Sai da suka kashe minti kusan sha biyar a kanta sannna ta farfado,suka cire mata oxygen suka daura mata ruwa da suke saka ran minti talatin ya qare sannan likitan yace zaije ya dawo kafin ruwan ya qare.

Kanta kawai take mirginawa tana jin qirjinta yana mata wani ciwo,duk inda ta juya fuskar raliya data drivernta kadai take gani,har bacci ya saceta.

Still data farka din ba wasu sabbin fuskokin saisu din dai. Wani abu ya tsaye mata a wuya,wasa wasa tana shirin kamanceceniya da tsintacciyar magen da bata da wani gata. A hankali ta sauke dubanta kan wata mata dake kusa da gadonta,wanda su biyu ne kacal dama a dakin. Yara hudu ne tsaye a kanta,tana zaune saman gadon,daya a hannun damanta.....daya a hagunta,dayan yana tsaye saman kanta yana bare mata ayaba yana bata tana ci,dayar tana saman kujera gaban gadon nata riqe da robar yoghurt tana jira ya gama bata ta miqa mata.

Hira suke a tsakaninsu,kowanne fuskarsa dauke da walwala duk da cewa jinyar mahaifiyarsu sukeyi. Tana gama ci ya karbi bawon ya jefa a Dutsbin,zai karba yogurt din daga hannun ta zaunen ta hanashi.

"Saika kwashe ladan duk kai kadai,nima inaso" Ta fada tana kai roban bakin mahaifiyartasu.

Idanu maamah ta dauke tana runtse idonta,wani irin bacin rai yana ratsata. Tasan koda kwatar kwatar kwatar kudin fu'ad duka yaran matar basu kai ba.....amma yadda suke tattalinta da nuna mata qauna da kulawa kadai abun kallo ne.....ita gata ta qare da zama 'yar kallo,cikin rayuwar kadaici da rashin wani sashe da zai tallafeka.

"Allah ya isa ameenatu.....Allah ya isa" Ta fada a sarari tana ji har zuciyarta anni ta mata cutar da bazata taba iya wankuwa daga ranta ba.....hakanan kowacce kalar fansa data shirya dauka ba zata iya ramawa daidai da abinda tayi mata ba.

Daga raliya har driver din da kallo suka bita,saidai babu bakin magana,daidai nan likitan ya shigo.

"Ta farka ko?" Ya fada cikin kulawa yana dauko file din gami da sake duba abinda ya rubuta,ya qara wasu rubuce rubucen sannan ya ajiyeshi yana dubanta.

"Hajiya ki rage saka bacin rai a zuciyarki.....ki rage saka damuwa a ranki,kina da hawan jini bai kamata ki dinga zama cikin damuwa ba.......irin wannan gaskiya yana iya haifar da matsala kala kala,ba'ason abinda zai dinga sanyawa jinin yana hawa haka ta farat daya....kuyi qoqarin ganin ta kiyaye" Ya qarasa maganar yana dubansu raliya ganin maamah din taja idanunta abinta ta kulle.

"Tom.....in sha Allah" Raliya ta fada a sanyaye a ranta tana cewa mu asuwa?,indai taji da kunnenta ai shikenan mun kubuta.

"Kuna iya tafiya gida.....amma da zarar taji wani abu daban ayi hanzarin dawowa,saboda yanzun takai matakin da dole a dinga yawa checking up nata".

"Mun gode likita" Driver ya fada bayan ya karbi takardar magungunan daya rubuta mata.

Yana shirin tada motar ya dan waiwayo

"Ya za'a yi da magungunan nan hajjaju?,zamu siya ne a hanya ko za'a kawo?".

"Kai sagiru" Maamah dake a qufule da yadda suke jaddada mata cutar hawan jini ta kira sunansa.

"Naam hajiya".

"Ka fita daga ido na......hawan jinin banza hawan jinin wofi?,maqaryatan banza wanda mutum baya ciwon Allah da annabi?,shekarata nawa a duniya hawan jinin bai sameni ba sai yanxu ina fafutukar cika burikana?,Allah ya tsinewa wanda ya fasa cewa ina da hawan jini.......hawan ruwa ne dani.....bani takardar nan nan" Ta fada cikin fada tana miqa masa hannunta.

"Hajiya......ki tsaya ki duba maganarnan,don bakiga yadda kike bane dazu.....bai kamata ki wasa da magani ba....." Kai ta jijjiga.

"Lallai sagiru wuyanka ya isa yanka.....ashe kana dab da rasa aikinka" Ta fada cikin mamakin tsaiwa.musu da yayi da ita.

"Ka bata mana sagiru" Raliya tayi saurin tunasar dashi,salin alin ya miqa mata yana cewa.

"Tuba nake,Allah ya baki haquri".

" Idanma hada baki kukayi dasu saboda ku manna min ciwo ku kasheni to ta Allah ba taku ba.......rayuwa a duniya yanzu na farata,maqi gani ya kauda idonsa" Ta fadi tana yayyaga takardar ta watsar ta window tana cewa

"Muje gida" Tana jin lallai tana buqatar tayi magana da fu'ad da gaske.

Ya gama shirin kwanciya tsaf sanye da pyjamas masu taushi farare qal,yana zaune saman yalwatacciyar sofa yana binta da kallo sanda take qoqarin gyara masa gadon don yaji dadin kwanciya.


"Sabrrrr" Ya kirata da sautin da ya sanya taji tsigar jikinta ta zuba. A nutse ta waiwayo tana kallon lumsassun idanunsa.

"Yau bazan kwanta kan gadon nan ba". Da dan mamaki take kallonsa,kafin takai ga tambayarsa dalili sai musaddiq yayi knocking. Sabreen ta sauka a nutse tana nufan qofan da dan mamaki,don yanzun sukayi sallama dasu zasu wuce gida. Kanshi yadan rusunar yanajin nauyinta da tsoron kada hamman ya fatattakoshi.

"Maamah keson magana da hamma" Ya fada yana miqa mata wayarsa. Bin wayar tayi da kallo kafin ta matsa tana baiwa musaddiq hanya. Dubanta yayi saita daga masa kai alamun ya shige,a sanyaye yake takawa ciki itama tabi bayansa da nufin gama gyara gadon ta fita ta bashi waje don ya samu amsa wayar sosai.

Wani yawu musaddiq ya hadiye yana duban hamman nasa daya tsareshi da ido.

"Maamah ce tace lallai na kawo......" Hannu ya daga masa yana amsar wayar,sai ya miqa masa yana fita daga dakin a gaggauce yana jin bazai iya jiran ma ya gama amsa wayar ba ya karba sa hadu gobe,don haka kai tsaye ya wuce inda cab ke jiransa.

Handsfree ya sanya wayar,ya kuma ajiyeta a gabansa kawai yana zuba mata idanu,irin yadda yakeyi idan ranshi yana bace kuma baya da buqatar amsa wani kiran amma tilas ta sakashi amsawa.

"Ina kyautata zaton kana jina?,ko yanzun ma 'yar mulkin taka ce ta daga kiran?" Tayi maganar da wata irin hasala da fusata.

"Muhammad fu'ad jadda ne" Ya amsa mata da wani irin nutsuwa yana zubawa sabreen ido wadda ka ta ke duqe tana gyara bedsheet din gadon da pillow case din.

"Naji dadin jin hakan......umarni ne daga uwa zuwa shashan danta wanda baisan inda yake masa ciwo ba.........ka kama dukiyar mahaifin yarinyar dake mutuwar sonka ka garqame.....ka masa sanadin aikinsa duka saboda kana hannuwan mutanen da suke riqe da ragamar rayuwarka......sai abinda suka ce.....ni mariya dana dauki cikinka daga gudan jini har zuwa tsoka.....harka zama mutum.....saboda lalurar rayuwa ta nesantani daku shikenan yanzun nice wulaqantatta a wajenka......to indai nice mahaifiyarka ina baka umarni cikin qasa da awa daya komai na ambassador khaled ya koma kan aiki daidai".

"Tom" Kawai yace da ita yana sanya dukkanin wani qarfi na qwanjinsa dana ruhinsa yana danne zuciyarsa. Wasu irin abubuwa ke taso masa......yana rantsuwa da ubangijin ka'aba......banda da gaske ya ratsa jikin maamah ya bullo zuwa cikin duniyar da yake rayuwa a yanzu a cikinta......babu wani halitta kaf duniya daya isa yayi masa quarter quarter abinda tayi masa a yanzun. Hannunsa yake mutstsukawa yatsunsa suna wani irin qara,yana jin wadannan mutanen guda biyu sun fara kai masa ko ina a rayuwarsa.

Kunnuwanta ne taji ba zasu iya dauke maganan maamah din ba,saita saki gyaran gadon ta soma nufar qofa tana takawa a gaggauce.

"Sabreen.....dawo" Ya fadi kansa tsaye ba tare daya damu maamah zata iya ji ba.

"Ina magana da kai kana kiramin sunan wannan yarinyar?,annamimiyar karu....." Ya riga ya shanshano abinda take da muradin fada,sai kawai ya sanya hannunsa da wani irin zafi ya datse kiran yana kashe wayar gaba daya.

Da gaske wani irin abu sabreen keji,wani yanayi taji yana tsarga mata,ba zata iya zama ba da gaske,ba zata iya jura ba.....don haka ta sake takawa zata fita,sai kawai ya sanya hannunsa me ciwon dake nade ya fusgota sai gata ta fado zuwa jikinsa yasa hannuwansa duka biyun ya lullubeta cikin qirjinsa kaman ya manta ko baisan ciwon dake hannunsa ba ko kuma wani sassauqan rauni ne da bashi da radadi ko zafi ko kadan.

A zafafe yake kiran wata number,tsoronsa a karon farko ya kamata ganin yadda numfashinsa yake fita da sauri,zuciyarsa na wani irin bugawa.

"Haka fushinsa yake?" Ta tambayi kanta da kanta,daidai sanda kiran ya shiga aka daga. Ko muryar dake wancan bangaren bata jiba ya soma sauke musu umarni.

"Inaso a daren yau basai gobe ba.....fareeda khaleed mustapha ta kwana a a cell......ba ita kadai ba,da duk wanda ya kawo wargi ko yunqurin hana fita da ita" Abinda yace kawai kenan yayi wurgi da wayar.

Matseta yayi so sai a jikinsa,yana daga idanunsa da suka kada suka sauya launi yana zubesu cikin nata......


_tofa.....ran 'yan maza ya baci.....an manta da ciwon da ake jinya......ko sabreen zatayi aikinta?🫣,zamu gani_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 133


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



133


Sasai taji wani abu yana ratsa jinin jikinta game dashi......wani narkakken tausayinsa yana taso mata yana kuma mamaye ilahirin jikinta. Ta yarda dari har bisa dari cewa......da uwa irin maamah gwara ka rayu cikin maraici......da uwa irin maamah gwara ka zamana cikin layin yaran nan da ko dumin iyayensu basuji ba ubangiji ya karbi rayukansu......ta sake yarda da cewa.....komai ubangiji ya tsarawa bawa tabbas akwai manufa da alkhairi a ciki.

"Ya zakayi haka?" Ta fada tana sake saka idonta cikin nasa sosai tana kuma riqe da fuskarsa cikin tafukan hannayenta. Kaman wanda yasha wani abu ya maku yake magana

"Ya bazanyi haka ba.....ta yaya zanyi wasa da duniyata?.....ta yaya zan bari a taba duniyata?" Numfashi taja me zurfi wanda ya shige jikinta da wani irin mahaukacin sonsa da kowacce safiya yake qaruwa cikin ruhinta,ta sake bude idonta a kansa tana kallonsa.

Taga abubuwa da yawa cikin idanunsa......giyar soyayya da qauna.....da kuma wani irin fushi. Ji tayi kaman bata da wani sauran aiki daya rage mata a duniya a yanzun banda ta kwaranyar da wannan fushin da kuma damuwar daga wannan ruhin daya gama macewa a soyayyarta. Ba zato ba kuma tsammani yaji ta hade bakunansu guri guda.

Wani irin zazzafan kiss ta soma ajiye masa kafin ta tura harshensa cikin bakinsa ta soma sarrafashi kaman yadda yake mata. Cikin qasa da second biyu kowacce wuta dake jikinsa ta dauke,ya soma kokawar qwato numfashinsa,wanda bata daga masa qafa ba ta fara aike masa da qarin wasu saqonnin da suka birkitashi......suka sakashi ya soma mance wayeshi?,a wacce DUNIYAR yake?,meye matsalarsa a rayuwama gaba daya?.

Tayi masa ba zata ta qarshen qarshe......ta kuma tashi kansa da wasu irin zafafan salon da suka saka har ya manta meye ma yakeyi?. Wani irin saqo take aike masa me cike da jan rai......sai taji ya gaza jurewa ya juyeta ya maidata qasa.

Nutsuwarta taso maidawa jikinta,ta dafe qirjinsa a sanda yayi mata rumfa tana kallon narkakun idanunsa da suka sauya launi. Dubanta yayi shima yana neman qarin bayani,saita masa nuni da hannusa me ciwo da ya dafesu ya aza masa nauyi kaman ya manta yana da rauni.

"Kina tsoron jini ne?" Ya tambayeta ha tare daya kalli inda take nuna masa din ba. Fuska tadan bata daban,ta sani ba'a fiya son yayi wani aiki sosai da hannun ba,saboda a samu ya warke da wuri.....kuma wannan fitinar da yakeso yayin tabbas zata iya maida ciwon danye.

"Alright" Ya fadi da hanzari cikin qasa da second daya yana hautsinata ya koma qasan ita kuma ta koma sama ta maye gurbinsa.

"You're in charge now" Ya fadi yana dage mata girarsa. Wani kunya ya kamata,ta cusa fuskarta cikin ni'imtaccen qirjinsa da bata gajiya da wanzuwa akai.

"I give my self to you....i surrender to your will....play your role well" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi.

Duk yadda yake buri hakane ya kasance,duk yadda yake da buqata haka tayi masa. Abun ya gigitashi ya sanyashi fita a hayyacinsa,wasu maganganun daya dinga yi sai sukayi mata mugun nauyi,har ta dinga jin daga wannan ranar kaman ba zata iya sake hada ido dashi ba.

Wani sabon amarcin aka balle a asibitin tsakanin fu'ad da sabreen din,ba tare da kowa ya kula da lalurar da yake tare da shi ba.

Hankalinta ya tashi bayan komai ya lafa da taga bandages din hannunshi sunyi staining da jini.

"Ka gani ko?,dama bana gaya maka ba?" Ta fada a narke muryarta tana rawa tana shirin sakin kuka. Hannun nasa ya kalla ya saki murmushi yana jawota jikinsa sosai,duk qoqarin sauka da takeyi daga jikin nasa amma ya hanata.

"Please stay with me.....i could use some relaxation time......sai muyi wanka"

"Ciwonka fa?" Ta tambaya a mamakance tana kallon fuskarsa da tuni ya maida idanunsa ya lumshe yana fidda wani sassanyan murmushi.

"Forget about.....zasu gyara zuwa safe" Ta sake motsawa zatayi magana ya dora yatsansa akan labbansa.

"Shshshsh" Yace da ita,dole ta maida kanta ta kwantar,saidai hankalinta gaba daya yana kan ciwon.

Bayan sun idar da sallar asuba,tana kammala azkar dinta ta koma toilet don yin fitsari saiga jini. Ta razana sosai ta ware dukka idanunta tana duban jinin. Jikinta ta dauki rawa gaba daya,bata da wani qwarin daga murya ta kirashi,tana ma ganin kaman bata lokaci ne,sai kawai ta fito a toilet din da wani irin sauri.

Kansa ya daga yana kallonta sanda ta fito din,sai shima ya ware idonsa yana dubanta kafin ya miqe da sauri ganin yanayinta. Sosai ya riqeta yana tambayarta

"What's happening?.....relax.....gayamin" Pant dinta kawai ta daga masa,sai ya zare idanunsa waje kaman zasu fado.

"Oh shit......subhanallah" Ya fadi yana jin gaba daya ya gama firgicewa. Cikin kula da takatsantsan ya maidata gadonsa ya kwantar da ita.

"Lemme call a doctor" Ya fada yana fita a dakin da sauri don yana ganin tsaiwa kiransa ta landline ma bata lokaci ne.

Su biyu suka shigo,shi da wata likitan mace daban,yanata masa magana akan hannunsa amma bata wannan yake ba.

"Scan zamu fara yi mata don tabbatar da lafiyar babies din" Likitan ta fada tana qarasawa gaban gadon sabreen din.

Maida dubansa likitan yayi a kansa.

"Hannunka ya akayi yayi staining haka?" Ya tambayi fu'ad din wanda hankalinsa duka yake kan sabreen wadda dr din ta fara jawo na'urar scan wanda take a dakin permanently.

Kafin yace komai anyi knocking qofar an turo an kuma shigo. Farouq ne shida musaddiq dauke da breakfast da anni ke dafa musu.

Likitanne ya amsa sallaman,farouq ya qaraso dakin fuskarsa dauke da alamun tambayar abinda yake faruwa.

"Lafiya dude?" Farouq ya tambayi fu'ad yana qarasawa kusa dashi.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login