Showing 240001 words to 243000 words out of 557259 words
bin maza.
Ko a motar kamar ba wanda yasan da zaman juna. Kusan nasa tunanin ma na tafiyar dake gabansa ne daga yanzu zuwa kowanne lokaci,yayin da nata tunanin ya.lula duniyar yadda zata fidda 'yan uwanta daga wannan wasan da bata shirya shigarsu ciki ba.
Sanda suka isa gidan sam bata wani jira guard sun bude mata qofa ba,gurds din da take mutuwar jin haushinsu tun daga sanda suka hanata rawar gaban hantsi a gidansu. A yanzu kuma a wannan gidan ta fahimci dasu ake kowanne motsi,wannan wacce irin masifa ce kamar raqibu da atidu da buwayin sarki ya saukar maka da suka zama lallai ka rayu dasu don su dauki dukkan ayyukanka,masu kyau ko akasin haka.
A gaggauce ta wuce duka falukan ta zarce hallway zuwa bedroom din,burinta kawai ta isa ga gallababbiyar wayar ta hadu da maamah.
Da zafin nama ta birkita inda ta aje wayar kafin su fita,saidai kuma sama ko qasa ba wayar ba dalilinta. Cak ta tsaya tana gwama numfashi,sai kawai ta bude jakar data dawo da ita ta fidda asalin wayarta da take kiran kowa da kowa da ita.
Asalin layin maamah din ta kira,wanda bugu biyu ta daga,saidai bata jiyo komai ba sai muryar haneefa daga gefe da alama hira take mata ita kuma tana fadin
"Allah auta?" Idanu ta runtse,ta lura da gaske ta shiryawa wasan...... Ta ruwan sanyi takeso ta cutar da rayukan da basuji ba basu gani ba.
"Me kikeso?,me kike buqata?" Ta tambayeta kai tsaye ba tare data damu ta amsa sallamar data mata ba. Wani shu'umin murmushi ta aje,sannan ta jita tana cewa
"Haneefa jeki kwanta kema,idan na gama zanzo na daukeki mu wuce daki tare"
"Tom" Ta amsa mata kamar yadda yawanci haka maganarta take,abun kuma daya sake sokar zuciyar sabreen kenan.
"Mallakamin d'ana nakeso kiyi.....ni kuma zan mallaka miki 'yan uwanki ta ruwan sanyi,dama naki ne". Tayi mata bayanin hankali kwance. Suya sosai taji zuciyarta tanayi,tanason fadin maganganu da dama......tanason tayi abubuwa da dama amma kaman an danne harshensa sai zallar bacin ran dake mata zullo
"Why ni?,me yasa saini ne?" Ta fusgi kalmar daga harshenta ta watsawa maamah ita.
"Saboda ni a wajenki kawai na hango irin zarrar da nake buqata......a aikinki na gano abinda zaisa aikina ya cimma gaci.....uwa uba kina da wani irin kyau da zai iya saurin rusunar da zuciya ya kuma narka zuciyar kowanne d'a namiji". Qit kawai ta kashe wayar tana jifa da ita gami da cusa dukka yatsunta goma cikin sumarta.
Maganganun maman sun isheta haka,a yanzu basu take da buqatar ji ba. Kowacce tsiga ta jikinta ta miqe,taji wani irin matsuwa da fatan isowar kayan aikin maamah din hannunta. Inama ace zai yuwu ta danneshi tayita dura.masa abincin?,daga safe zuwa yamma ya zame mata mallakakke kaman yadda takeso ita kuma ta samu yancin 'yan uwanta. Tabbas! Inda babu 'yan uwanta da maamah din tayi garkuwa dasu,babu abinda zai hanata nuna mata ainihin kalarta da kuma ainihin yadda wasan zai gudana.
*DUNIYATA LITTAFI KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 23
23
Har wani nauyi idanunshi ke masa saboda tsohuwar gajiya da sabuwar gajiya dake a jikinsa,ga kuma wadda ke jiransa a gaba. Wanka ya fara yi,sai kawai ya sauya pyjamas dinsa ba tare da yabi takan abinci ba don baijin gajiya zata barshi yayi hakan yabi lafiyar lallausan gadon nashi dake gewaye da kyawawan pillows daa luxury bedsheet din dake qarawa bed din zama wani na musamman me cike da alfarma da wata nutsuwar samun lafiyayyen bacci.
Numfashi biyu kacal ya sauke wani lallausan ringtone ya katse masa relaxing din da yayi. Duk kiran da zai shigo wayar yasan na wani makusancinsa ne,hakanan a baya so din ya miqa hannu ya dauko shafaffiyar wayar me wani irin kyan daukan hankali.
Sunanta da ya gani ya sanyashi miqewa daga kwanciya zuwa kashingida zuciyarsa tana bugawa,ya lumshe idonsa yana budewa lokaci daya,can qasan ransa yana fatan Allah yasa ba wani jagwal dinne ya taso ba ko zai sameshi.
Cikakkiyar sallama yayi mata,ta amsa da wani irin yanayi na karsashi da kulawa.
"Akwai baqi a qofar gida,sun gaya min securities na gidan sun hanasu shigowa" Har ya sauke qafafunsa qasan gadon da zummar yaje ya duba ta na'urar tsaronsa,sai ya tuna ashe ba'a gida yake ba nan wani sabon muhalli ne,baida tabbacin an gama installing nasu,dole ya koma ya zauna gefan gadon a nutse yace
"Baqi kuma maamah?....at these late hours?"
"Eh......ba wasu baqi bane......me aiki ce nace tazo don ta tayata zama,da kuma yanayin gidan naku dole saida mataimaki daban". Numfashi sosai ya zuqa yana fesarwa,kowanne taqi kuma kowanne taku da motsi na maamah magana ce me zaman kanta.....wanzuwar aiki ne da sai ka saka hasashenka da kyau zaka iya cimmasa.
"Amma maamah ina tunanin tafiya zamuyi.....dani da itan gaba daya jibi idan Allah ya kaimu....so koda tazo dinma zata zauna a gidan ne ita kadai.....nace if possible ta bari idan mun dawo....i will call you saiki turota" Har tsakiyar kanta taji wani abu ya tsarta mata,hakan kuma ya bayyana har cikin sautinta daya canza nan da nan,abinda ya sake bashi wani haske.
"Har zuwa yaushe zaku dawo?".
"2to 3days ne.....just bude kamfani kawai zanyi na dawo" Ya bata amsa bawai yana nufin dukkan maganganun daya fada haka suke ba. Duk da bai iya qarya ba......amma a wannan muhallin ya samu fatawar qarya a kansa a yanzu halastacciya ce.
Adadin kwanakin da taji basu da yawa sai taji damuwarta taqaitacciya ce........ta cika da fatan tafiyar ta sake basu kusancin da zai damqa mata dukka amanarsa a hannunta,yadda suna dawowa komai zai fara cikin sauqi aminci da kuma nasara
"To yayi baida damuwa.....ammmm amma ba....kace su barta ta shigo na bada saqo ta bawa d'iyata". Kai ya jinjina yana cewa
"Alright" Sai ya gintse kiran. Wadanda suke on duty ya duba sannan kai tsaye ya kira daya daga cikinsu. Saidai kafin basu damar bata damar shigowa sai daya basu dan qaramin aikin da tun kafin zuwaira ta qarasa ciki suka gama aiwatarwa suka tura masa.
Bawai bayan ta shigo cikin gidan ba......tun daga farkon layin daya amsa sunan MUHAMMAD JADDA STREET ta gama raina kanta dama komai nata,bata sake tsinkewa ba sai da suka iso qofar gate gate guda biyu da fuskar gidan ke dashi daban daban......ta gama kuma narkewa gaba daya tun daga harabar gidan har zuwa falon farko da suka zauna suna dakon sabreen.
Kowanne motsi da yadda laila ta gaza sukuni,ta kasa danne zallar zalamarta da kuma dimuwa da yadda gidan yake duka kan idanun zuwaira take yinsu,zuwairan da tayi banza da ranta tamkar ma batasan tanayi ba. Mummunar qullaci ta samu zuciyarta dayi akan hajja harira.....ko maamah bata fuskanci manufar harira na hadota da ita ba ta gama karantar komai.....baqinciki qyashi da hassadar ta zauna ita daya a gidan take mata......to itama ta lashi takobin zata gara nata wasan akan laila da hajja,zata kuma murza musu kalar nata zaren.
Karo na biyu kiran daya shigo mata yadan darsa mamaki a ranta,saidai a yanzun da 'yan uwanta ke tare da ita,bata jin zata iya tsallakewa kowanne kira da zatayi mata.....don tana cike da tsoro da fargabar shudewar kowanne minti a sanda suke tare da ita.
"Ki sauka zuwa falonki kina da baqi.....saqon farko kawai naci su baki.....kiyi qoqarin fara amfani dashi daga gobe zuwa jibi". Bata jira cewarta ba ta katse kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana binta da kallo kamar bata gane yaren da maamah tayi magana dashi ba.
𝐌𝐢𝐧𝐭𝐮𝐧𝐚 𝐭𝐚𝐥𝐚𝐭𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐲𝐚 𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐚 𝐬𝐡𝐮𝐝𝐞
Daidai sanda jerin motocinsa ke fita daga gidan don komawa nasu gidan,tana zaune daga gefe zuciyarta tayi wani irin nauyi dauke da tarin kalamai da al'amura da tayo tsarabarsu cikin gidan.
Tasan tayi qasa d window din motar sanda amna tayo mata rakiya tana mata bangajiya,amma batasanma bata maidashi ta rufe ba saboda yadda zuciyarta tayi nisa a wani bigire na daban.
Daidai lokacin da yake zaune bayan motarsa yana danna wayarsa yana qoqarin neman location na gidan da yazo din. Nishin motocin yaja hankalinsa ya cire kansa daga wayar yana maidawa kansu.
Motocin muhammad fuad jadda daban suke,kaman yadda komai daya shafi jadda diamond chore resources ya fita daban. Cikin qirjinsa yake jin buri da fatan inama ya kasance tamkar wannan matashin me matuqar sa'a?.....wanda ya fado duniyarsa da wani irin sa'a da yayi Imani ba kowanne dan adam ke samun koda shigenta ba. A lokaci na quruciya......da qananun shekaru sanda jini ke zagayawa da kyau a jikinsa......ace ya mallaki d'anyun kudade irin wadannan?.....ya mallaki kyau da sura irin wannan?.....yayi wani irin tambari da kuma suna,sunan daya watsu sassan duniya dama kuma ba'a batun tambarar sunansa a qasarsa ta haihuwa.
Kamar cikin majigin film.....kamar wulqawar walqiya cikin sararin samaniya ya hangi wani Kyakkyawar fuskar......fuskar daya aza dukkanin burinsa a kanta......fuskar daya sha kwana ya tashi da cikakkiyar sha'awarta tare da tunanin yadda zai maidata ta zama tasa har abada......fuskar da daga qarshe ta jefashi cikin bala'i masifa da barazanar faduwar kowacce daraja arziqi da wadatarsa a yanzu da yaketa fafutukar maidawa......fuskar da a yanzun ba fuskar da yake yunwar nema ya d'aid'aita rayuwarta irinta.
Bazai iya cewa ga sanda ya zamo ya kuma diro daga saman motar ba sai da ya fara takawa da zafin nama da zummar ya kamosu,ingarman motocin suka masa wani irin fit suka barshi da kama iska ba tare ma da sunsan meye shirinsa ba.
"Damn it!!" Ya fada a kausashe yana kaiwa iska naushi da hannunsa. Da gaske itace matar da muhammad fu'ad ya aura?,da gaske itace amaryar da akace masa ana yiwa walima yanzu haka cikin gidan Alhaji hamza kibiya?. Wani irin shu'umin murmushi ya subuce masa ya mamaye fushin da yake kwance akan fuskarsa,ya koma ya daki bayan motarsa da hannunsa daya dunqule
"Good......komai yayi daidai" Ya kuma fada a fili yana buga wani tsalle ya koma saman motar yana ci gaba da sakin murmushi,a hankali a hankali murmushin nasa yake qaruwa kafin daga bisani kuma ya kece da wata iriyar dariya yana sake bugun bayan motar gami da furta
"MUHSEENA" ainihin sunan da yake shine STAMP dinshi. Da sauri ya kuma saukowa,ya bude backseat din motarsa ya finciko wata magazine. Magazine ne da suka fidda sanarwar daurin auren da komai da komai,a sama an rubuta da manyan baqin
_THE BILLIONAIRE'S WEDDING FATIHA_ Kusan babbban abinda suka yita jaddadawa shine......bikin babban mutum me arziqi kaman muhammad jadda din,yazo ba tare da wasu shagulgula da aka dade ana hasashen za'ayi ba,luxury events da kowa ke mafarkin zaiyi a matakin arziqi irin nasa,shin meye sirrin?. Murmushi ya kuma saki sanda ya karanta tambayar qarshe,sai yaji kaman shi ya cancanci ya amsa tambayar.
"How i wish ina wajen da aka buga labarin nan?,tabbas dana basu full details na wacece wadda ya aura,ta yaya zaiyi shagulgula bayan BARAUNIYA ya aura?,TSOHUWAR KILAKI?" Ya fada a bayyane
"Ameenatu!" Ya kira sunanta na ainihi dake rubuce jikin katin.
"You will pay it......dole zaki biya ninkin farashinki" Ya sake fadi still a bayyane,boyayyen fushin nan dake kwance qasan ransa yana wani tasowa yana bashi tururin bacin rai har saman fuskarsa.
A gaggauce ya koma cikin motar tasa ya wurga magazine din,shima ya shige ya kunnata gami da bata wuta ya finciketa yana barin layin don sam yama mance maqasudin abinda ya kawoshi layin.
*_S A B R E E N_*
Tun bayan sallar asuba take a zaune saman abun sallarta a qoqarinta na hana kanta komawa baccin daya zame mata al'ada duk safiyar duniya. Bata da matsalar shirya su haneefa breakfast da sauransu,duka wannan huda zatayi kafin su wuce,sai yau abun ya zame mata banbarakwai.
Zuwa qarfe bakwai idanunta duka sun daddaure mata sunyi mata wani iri,ta miqe a hankali ta ninke abun sallar sannan ta taka tana nufar wata drawer ta zauna gefan gadon tana jawota.
Ledar jiya ce da zuwaira ta kawo mata,ta fiddota tana qarewa ledar kallo. Abubuwa biyu suna karakaina cikin ranta,kokwanto da kuma qwarin gwiwa,saidai kuma qwarin gwiwarta a wannan safiyar tamkar yana son korar kokwanton da takeji,don haka ta riqe ledar da kyau ta fara takawa tana fita a dakin. Can qasan zuciyarta ta birkita da tunanin me ya samu wayar momma?,me yasa ta kasa samunta?. Daga daren jiya zuwa asubar yau ta kirayeta har batasan adadi ba,tanaso taji daga bakinta.......tanason taji me yasa tabar su huda a hannun waccar matar?.
Tsaiwa tayi cikin kitchen din tana tunanin me dame zata dafa ko ta soya da komai zai narke a ciki ba tare daya bada wata alama ba?. Aqalla ta kusa minti biyar kafin ta wuce store din.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_
̶B̶O̶O̶K ̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 24
24
Inda aka yiwa dankali Kyakkyawar ajiya ta duba,ta debi yadda take ganin zai isa,ta bude freezer shima ta debi nema ta rufe tana dawowa kitchen din.
Yau sai gata kace kace cikin hidimar hada breakfast,abinda ya zame mata sai lokaci lokaci idan huda bata da lafiya sannan ta karbeta.
Awa biyu ta share cikin kitchen din,sanda ta gama ta gama gajiya gaba daya,amma haka ta zaba warmer ta soma zuba komai a ciki.
Sanda ta bude ledar da zummar fara gudanar da aikinta cikin ruwan tea da dankalin data soya da kuma farfesun naman sai taji hannunta yana rawa. Hannuwan nata ta sanya da zummar qulle ledar ta maida ciki amma sai sunan HUDA NADRA HANEEFA ya fado mata......daga bisani maganganun maamah suka dawo.mata fes,sai takejin kamar umarni ne akeyi mata na KI AIWATAR.
Kai ta soma girgizawa,'yan uwanta sune haqqin farko da suka zame mata wajibi ta fara kubutarwa.......ba zata wofantar da rayuwarsu ba saboda mas'alar mutumin da ko qanqani baisan zafinta ko darajarta ba,don haka ta kunce komai......takuma aiwatar dashi kamar yadda zuwaira ta zana mata,ta debi kayan abincin ta jerasu saman dining.
Tsaiwa tayi tana kallonsu,kamar ba zata bar gurin ba,sai kuma taja da baya ta fara takawa tana sauka daga wajen.
▄A nutse yake saukowa daga saman stairs din,sanye da wata lafiyayyar suit ta kamfanin BRIONI da suka zama number daya wajen fidda suit na manyan mutane daga auduga da zararruka masu daraja. Yayi wani irin kyau sassanyan kyau kaman yadda yanayinsa yake nunawa kamar yau din bai tashi da wannan kuzarin nasa ba dake sake bada bayanin cikakkiyar lafiyar da yake da ita. Qafafunsa sanye cikin rufaffun takalman dake faman daukan idanu suna qara bayyanar darajar da yawan nauyin kudaden da aka sanya aka siyesu. Hannunsa daya cikin aljihun trouser dinsa,daya hannun kuma yana sarrafa wayarsa. Sassanyan turaren nan nasa da bai cika hayaniya da yawa ba ina busawa a hankali yana karade ko ina. Wani irin qamshi ne na musamman dake tashin kan mutane da dama,saidai idan ka debe farouq har yau ba wanda zai iya gaya maka exactly sunan perfume din da yake using. Musaddiq da saddiq sunsha zuwa su sata,amma sun kasa samunshi ako ina bare su siya.
A yadda yake saukowa daga shi sai wayarsa zaka rantse ba wata muhimmiyar tafiya bace a gabansa,kamar zaije qofar gidane ya dawo. Haka tsarin tafiyarsa yake,baya daukan komai sai documents dinsa da wasu mihimman abubuwa amma banda sutura. Kusan duk qasa ko garin da yake da huldar kasuwanci dasu yana da permanent gidan da ba abinda gidan ke buqata sai isowarsa.....idan ya sauka a wani gurin daban ba gidajensa ba to yayi hakanne saboda salon bad da hankali da wasa da hankulan abokan adawa na kasuwanci ko kuma dalili na ra'ayin qashin kanshi na haka kawai yaso.
Duba daya ya yiwa hallway din ya maida idanunsa ga qofar da zata sadashi da parlor din,sai ya maida wayarsa side pocket na rigarsa sannan ya maida daya hannun shima cikin trouser dinsa yana takawa a nutse cikin falon.
Sai daya zagaya falon