Showing 108001 words to 111000 words out of 557259 words

Chapter 37 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

539

da kunnuwanta.

Tayi mugun tsoratar data dinga ja da baya da baya tana girgiza kai. Yana tsaye ya kafeta da idanu,abun yana masa sugar sosai. Irin hakan yafi buqata don ta haka ne sabreen din zata fuskanci girman nasa aikin. Ya samu sabon ruhi sabon gangar jiki da baisan komai ba game da rayuwa......zai hurewa zuciyar kunne,sannan ya mori gangar jikin yadda yaso ya kuma watsar da ita tamkar wani yasashen abu maras amfani. Yana tsaye harta gudu a layin ta bacewa ganinsa,sai ya bushe da dariya.

Hakan da tayi ya tabbatar masa qwaila ce,ya kuma bashi tabbacin baa taba gaya mata kalmar so ba sai a kansa

"Allah sarki......gashi baki fara da jin kalmar ba a sa'a......anyway......ko mene ya faru dake 'yar uwarki ce taja miki" Ya fada yana juyawa don barin layin ya qarasa inda yaransa ke cikin mota suna jiransa.

Hannunta har rawa yake sanda take warware takardar. Tsakanin alhamis jumaa asabar da kuma yau lahadi ba wasu mintuna biyar kyawawa da suka wuce ba tare da tunanin abinda ya faru tsakaninsu ya dawo kanta ba. Duk juyin da zatayi sai kalamansa sun dawo mata,kallonsa murmushinsa da kambamawarsa. Fuskarta kam ta kalleta yafi sau adadi tana sake duba kyawun surarta da yake yawan jaddadawa. A yadda take gani ba mace me kyan yaa sabreen dinsu......ashe itama to tana da kyau dinne da gaske?,ko kuma yana fada ne kawai?.

*_Hello me kyau,fadin azabtuwar da idanuna da zuciyata sukayi saboda rashin tozali dake ba abu bane me sauqi......ina fata zaki daure a gobe ki barni naga wannan kyawawan idanun da zuciyata ta mutu a kansu.....idan ba haka ba.....zan iya rasa numfashina_*

Da sauri ta duqunqune takardar ta kuma jefa a toilet ta bita da flushing zuciyarta na bugawa sosai. Tsoro zumudi fargaba da mamaki dukka suka hade mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi.

Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja qofar ta bude ta fito ba tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura alwala tayo dakin nasu.

Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe abinci tayi zaune saman kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi kitchen.

Yanzunma da kallo sabreen ta bita har ta shige kitchen din. To wai me yake samun huda take wasu wasi haka?. Bata sani ba,sai ta girgiza kai ta taka hannun kujerar tana dauko babbar dardumar da sukan shimfida suyi magariba da ishai akai suyi bitar karatun makaranta ta taimaka musu da wanda zata iya.

Da ruwan zafi sosai tayi wanka bayan wucewar hajja saboda ciwo da jikinta yake mata sakamakon zaman mota data jima batayishi kaman haka ba. Ta shirya kanta cikin fafi indian abaya me laushi,ta yane kanta da mayafin abayar daya kasance medium cotton kaman yadda jikin dogon rigar yake.

Cikin falon tayi zaune bayan ta kirayi me aikinta ta canza mata channel. Qafafunta a miqe saman side glass table din,hannunta dauke da glass cup dake cike da lemon raspberry tatacce me asalin tsadar. Babu wani abu da zata ci ko tayi amfani dashi cikin gidan da yake da qaramin kudi. Komai nata me tsada take zaba,hatta da ruwan da zata sha kuwa ballantana akai ga sutura ko wayar hannunta.

Ko a yanzun haka ta gaya masa tana buqatar ya sauya mata iPhones din hannunta guda biyu. Iphone 15 da wata tsaddadiyar waya sabuwar qira da kamfanin Samsung's. Duka duka wayoyin ba wadda tayi wata uku,to amma garin gane ganenta ta hangi wasu sabbin fitar,su kuma takeso ta riqe.

A komai tafison ta zama cikin sahun mutane na farko da ake ganin komai sabo a wajensu. Inda tana da iko komai zai zamana ana ganinsa ne ta wajenta,sanda zai soma zagayawa hannun masu kudi irinta ita ta dade da cin zamaninta. Ta sani,a dukiyar da d'anta yake dashi yana da qarfin kudi da mulkin da zai iya sanyawa a qera mata duk abinda take buqatar ya kasance nata ita kadai daga kowanne kamfani a fadin duniya,to amma ta fahimci rayuwarsa baya daidaitata dai dai data sauran masu kudin irinsa. Ba kuma haka takeso ba.....ba haka take muradi ba......tanaso ta gansu suna rayuwa daidai da matakin arziqinsa. Ta fahimci yana cikin sawun mutanen da ba kasafai suke bayyana arziqinsu ba,sai abinda ya riga ya bayyana ba yadda zasuyi dashi.

Aka idar da magariba akayi ishai shuru. Tun tana tattalin maganganun da zatayi dashi har wasu suka fara bace mata. Ta daga kai ta kalli agogon dake shirye saman tv din falon takwas da rabi na dare,to shin sai yaushe zai shigo?,sai yaushe wannan abun zaizo qarshe?.

Sannu a sannu sanda taga an doshi tara na dare babu alamunsa,wayoyinsa dukka a kashe shida musaddiq din da zata sanya ya kira mata shi a duk inda yake.

A ranta ta dinga jin cewa hadin baki ne......a ranta kuma ta dinga ji aminatu ce ta hanasu.....a yanxun haka qila suna can gabanta......ta zaunar dasu sai abinda tace musu.

Wannan tunanin ya dugunxuma mata zuciya,har taji bata da wani sauran zama cikin gidan. Dakinta ta wuce kawai bayan ta ajiye kofin lemon,ta shiga zaro takalmi cikin jerin takalman alfarma dake adane a shoe rack dinta. Cikin zuciyarta takeji yau din Alhaji hamzan zata tunkara......tanaso taji shine yayi mata cikin yaran ko ubansu?,tana so taji da ita dasu wai waye ahaqqu dasu?.

"Nazo muje ne?" Zuwaira ta tambayeta sanda taga tana dosar qofar fita daga falon

"Zauna basai kinje ba" Ta amsa mata a gaggauce tana fita a gidan.

Mugun bugun da takewa tafekeken gate din gidan ya fusata securities din gidan,saidai kuma lokacin da suka duba wadda ke bugun ta na'uarar tsaro dole kowannensu fusatarsa tayi nata guri.

Basusan ainihih matsayinta ko ita wacece ba......amma yadda suka fahimci girmamawar da take samu daga mazauna gidan ya basu alamar cewa tana da nata matsayin na daban.

Ko kallo security din daya bude mata qofar bai isheta ba ballantana tabi takan welcoming nata da yakeyi tare da bude mata qofa ta biyu da zata sadaka da farfajiyar gidan. Daga nan wasu security din su sake marabtarka kashi na uku kenan kafin kakai ga ainihin cikin gidan ka zarge qofar da zata sadaka da babban falon anni na farko.

Bata taba tunanin zata sake takowa cikin gidan ba karo na biyu.......don duk lokacin data tako din alatun gidan yakan zame ma idanu da zuciyarta barazana. Tana jin kamar kowanne abu idan ta kalla a gidan yana mata izgili ne tare da gaya mata da dukiyar danki aka samar dani......baki kuma da wata izza ko power ta mallakata.

Kowanne taku daya idan tayi cikin gidan ranta quna yake......sak fasalin yadda takeso gidan da zata rayu ya kasance sai gashi kacokam a yau din irin wannan dream house din nata mallakin aminatu ne.. Wasu mutane da basu da masaniyar sanda ta dauki cikin fuad har ta haifeshi.

Qofa ta qarshe da zata bata daman shiga falon annin nanma sai data jinkirtawa na'ura sannan ta bata izinin shiga,ta dauke kanta ranta yana suya da wani irin fushi. Tafi qarfin ta tako gidan alhaji hamza har abada.....inda sun bata girma da martabarta da a yanzun ba shakka ita ake zuwarma haka neman gindin zama.

Tana sane da yadda mabuqata ke yawan ziyartar gidan karbar taimako a duk sati......taimakon da ta tabbatar daga fuad ake rabashi.......sai gashi ita duk yadda taso ta dinga cina farfajiyar nata gidan da mabuqata,tana raba musu kudi a envelope yadda taso abun bai samu yadda takeso ba. Bai hana taimako,amma saidai ta rubuta list na mabuqatan ya hadasu dana gidan alhaji hamza a raba musu taimakon tare.

Bata samu yin sallama ba,sai Allah ya sanya tana sanya qafafunta a falon idanun anni dake kashingide cikin lausasan sofa ya sauka a kanta.

"Ikon Allah" Anni ta furta tana miqewa daga kashingidar da tayin tana sauke qafafunta qasa idanunta akan maamah

"Da kinyi zamanki ma.....don ni ba wajenki nazo ba kaman yadda na alqawarta zuwa na na qarshe gidan nan......wajen hamza nazo" Maganar tata tazo qarshe dai dai sanda amna ke fitowa daga kitchen ta zuba abincin dare,don tace yau zaman cin abincin abban yayi dare da yawa,ba zata iya jiransa ba da wuri takeso ta kwanta.

Kallon kallo sukayi tsakanin maamah din da amna. A kallon farko ta fahimci wacece duk da wannan shine karon farko da ta fara ganin yarinyar ido da ido. Autar alhaji hamza kenan,yarinyar da ake gaya mata irin sabon dake tsakaninta da fuad......yadda take ji dashi da yadda shima yake ji da ita

"Idan har kikayi da wasa kina zaune zakiji ance 'yar gida akayi.....wannan matar zata aura masa autarta..... Kinga shikenan komai ya qarasa watsewa" Muryar hajja ta dawo mata akai cikin tattaunawar da sukayi da hajjan a dazu dazu kan hanyarsu ta dawowa gida.

"Ke amna......dubamin abbanku idan ya kammala,kice maza maza yayi baquwa"

"To" Ta fada tana ajiye plate din sannan ta miqe tana nufar qofar da zata sadata da sassan abban nasu ba tare da tabi ta ainihin farfajiyar gidan ba. Tana tafe tana waiwayen maamah,itama ta lura da hakan,sai taja wani tsaki me matuqar qarfi abinda ya sanya amna din maida kanta tana yin gaba.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 58
___________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy


Assalamualaikum

Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki.
Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode

https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
_________________________


Farfajiyar gidan ba kowa sai qofar dakin malam saidu da yake iya hangowa wanda yake a bude. Juyawa yayi zuwa sassan da spare din famfo dake bawa shukokin gidan ruwa yake,ya xame takalminsa,ya kuma xare agogon hannunsa ya jefa aljihu sannan ya matsa ya kunnashi. Dukkan hannayensa ya tara yana kallon saukar ruwan,sai yaji wasu kalamai suna dawo masa a ka

_"ka mutu mana......ai ba a kanka aka fara mutuwa ba,kuma ba'a kanka zaa daina ba......talauci da fatara tafi mutuwarka yimin barazana......ta kuma fi mutuwarka dagamin hankali"_

Wani abu yaji ya tsaye masa a tsakanin numfashinsa daya sanya ya cire hannayensa daga famfon. Wasu daga kalaman maamah kenan a can shekarun baya a bakin famfo tamkar irin haka,daidai sanda abban nasu yake daura alwalar sallar magariba. Takalmansa kawai ya mayar yana jin bazai iya ci gaba da xama a cikin gidan ba. Ire ire wadannan abubuwan da ba wanda ya sansu saishi,.....koda musaddiq kuwa......suna sanyashi yana jin kamar numfashinsa zai fita a wasu lokutan.

"Ko buta zaa baka ranka ya dade" Muryar malam saidu ta ratsa kunnensa sanda yake dab da qofa. Kansa kawai ya gyada masa yaja ya koma ya zauna,ba jimawa ya dawo da butar,ya karba ya fara dora alwalar a gaggauce,ya gama ya bashi ya karba ya maidata wajenta

"Zo muje malam said" Fu'ad ya fada yana ware hannun rigar sa.

Tare suka jera shida malam saidu din,duk da yadda yaso ya zuqe saboda girmamawa,me sunan malam kuma yana daga bayansu kadan ta yadda bazaiji wani abu da suke tattaunawa ba

"Magana zamuyi" Ya fada a nutsensa

"To....to" Ya fadi da hanzari

"Tambayoyi ne amma sai bayan mun idar da sallah zan saurari amsoshinsu"

"To ba laifi ai" Ya amsa masa,don ya saba lokaci lokaci dama yakan masa tambayoyi game da gidan ya kuma buqaci amsarsu.

"Waccan matar da suka shigo da hajiya meye sunanta?,wace ita a wajenta?,yaushe ka fara ganinta a gidan?,sannan kamar sau nawa ta taba zuwa ko take zuwa?,ita kadai ce koda wasu?,tana dadewa cikin gidan?,suna yawan fita tare ko aah" Yakai qarshen dukkanin tambayoyin nasa sanda suka kai bakin masallacin,don haka yayi shuru yana adduar shiga masallaci a madadin tarin tambayoyin.


"Lallai na sake yarda da maganar bokan can.....lallai akwai aiki qwarai akan yaronkin nan" Hajja ta fada duk da nata yaron da matarsa data shanya a waje kowanne cikin motarshi yana jiran fitowarta.

Labba maamah ta cije kadan sannan ta saki sanda take maida riga maras nauyi a jikinta

"Ni kuma cewa nayi miki zan qyale wannan aikin ya cimmani?,na zuba idanu naga iya gudun ruwansa na yau kawai......amma duk abinda yakai gobe zakiji kirana......a gobe nakeso mu koma a fara aikinnan"

"Ai da zafi zafi akan bugi qarfe....." Hajjan ta fadi zuciyarta na saqa mata abubuwa masu yawa.

Har bakin gate din farko ta tako tana yiwa qawartata godiya da ban gajiya. A nan suka gaisa da yahaya da matarsa. Yadda ta samesu a jere kowanne da mota yana jiran dakon fitowar hajjan ba tare daya isa yabar wajen ba ba bisa umarninta ba ya sake ninka kwadayinta itama na kaiwa wannan bigiren,sai taji kamar ta jawo wadannan kwanakin da tayi imanin suna dab da zuwa......ranar ea zata nunawa aminatu da hamza cewa ruwa ba sa'an kwando bane.....hakanan koda giwa ta fadi tafi qarfin wawa.

Haka siddan?,daga maqotaka?,ba sidi ba sadada a kama mata yara a musu muguwar mallaka?,bayan ko sanda ta tafinma suna da wayon da zasu iya kula da kansu?. Da wannan qananun mitocin ta isa cikin gida.

Ya kusa minti ashirin yana fuskantar gate din gidan,harde da hannayensa kawai yana duban qofar kwanyarsa tana digesting maganganun da sukayi da malam saidu daga hanyar masallaci zuwa dawowarsu. Baisan a wanne matsayi zai ajjiye maamah din ba.....karo na uku da wani abu ya sanya yake tunanin ANYA ITA DINCE TA HAIFESU?,anya ita din UWACE?,akwai zuciya irin ta uwaye a qirjinta kuwa?. Me yasa kullum DUNIYA itace a gabanta sama da komai?,yayi tunanin shi da kowa ma zata canza ko kuma ta canza din.....amma sai kuma akasin tunaninsu ya biyo baya.....akasin tunanin da shi kadai gani na zuciya da lura da bin takunta sannu a hankali suke karanta masa komai a kanta....karatun da idanuwa kadai sunyi kadan su iya fahimta ko ganeshi.

Hannayensa ya sauke jikinsa a mugun mace,baya jin zai iya komawa cikin gidan nan,idanma yace zai koma din abinda zai wanzu tsakaninshi da ita bame dadi bane. Ko haduwarsu na 'yan mintuna kadai ya sake wani karatun. Ya dawo lafiya?,wacce nasara ko qalubale ya riska?,duka ba damuwarta bane......damuwarta shine KUDI.....me yasa bai turo ba?. Abu guda daya da bai taba faruwa tsakaninshi da anni ko abba ba......basu taba neman anini taro ko sisi daga hannunshi ba.....a hakan take neman kudin da zata rabashi da Alhaji hamza da aminatu?,mutanen da su suka bashi RUHI na rayuwa da yake yawo a jikinsa a yanzu?.

Kansa ne yaji ya sara,sai ya sake qara azamar barin qofar gidan ya juya zuwa nasu gidan. Gidan da a baya shine gidan maqota a wajensu amma a yanzun basu da gidan daya kaishi.

Tun a gate ya sallami kowa,ya gaya musu da wuri zai kwanta don gobe zasu fita da wuri,duk da baida yaqinin goben a yadda zai tashi saboda wani nannauyan ciwon kai daya saukar masa yanzu yanzu.

Tun bai qarasa sassansa ba ya kashe duka wayoyinsa,yabi ta qofar baya don bayason kowa yasan ya shigo din ya wuce sassansa.

Bai kunna kowanne fitila na sassansa da zai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login