Showing 21001 words to 24000 words out of 557259 words
Saidai dai dai sanda ta saki labulayen da zummar shiga ciki din taji sallamarsa ta karade tsakar gidan. Qaramin tsaki taja,tabbas tunda aka jishi da sassafen nan kamar haka to ba a shakka wata tijarar yazo yi,ko kuma akwai abinda ya hadoshi da wani. Idan da sabo zata iya cewa sun saba da halayyarsa,macce daya ce cikin gidan suke dasawa har baka iya jin kansu. Har gwara ita tasan maganinsa,ta kuma san ta yadda take bulloma tsiyarsa,duk da bata taba tsaiwa ta kulashi ba anji muryarta a matsayinsa na qanin mahaifi a gareta.
Sakaya qofar kawai tayi ta sake zuge labulen sosai sannan ta wuce uwar dakin ta yadda ba zata tsaya bata lokacin jin meke faruwa a tsakiyar gidan nasu ba,domin ita din tana cikin jerin sahun irin mutanen nan ne dai basa shiga abinda bai shafesu ba,wanda ya shafesun ma sai tura takai bango,bata da magana sam sam bare hayaniya. Wannan hali nata da siffarta ta sanyi da sauqin hali da kuma yauqinta ya sanya da yawa suke mamakin WANNAN DABI'A TATA......Dabi'ar da har yanzu su kansu basu da cikakken yaqinin a kanta,duk da cewa suna kallon gamsassun hujjoji ai sun gama bayyana a fili a game da ita.
Babban bedroom ne qwarai wanda iya dauke gado da wardrobe guda bibbiyu,sai dressing mirror guda daya. Duk da cewa wai daga bacci aka tashi amma dakin neat yake,komansa akan tsari,ga kuma wani sassanyan qamshi da yake fita kaman dai yadda falon yake.
Daya gadon da yake shine qarami ta nufa,wanda ke lullube da lallausar shimfida da tattausan blanket peach color. Tun batakai ga zama ba rurin da wayarta keyi ya cika mata kunnuwa,sai ta haye saman gadon ta lalubo wayar ta cirota daga gefan pillow dinta.
Iphone 15 ce dake dauke da wata irin cover me kyau data dace da wayar da kuma me wayar gaba daya,ta zubawa sunan dake yawo saman screen din idanu
*_ibraheem_* ya nuna mata. Wani gajeran murmushin gefan baki ta saki dake cakude da wani emotion. Siririn tsaki taja saman harshenta,ta fara qoqarin rejecting kiran
"Done and dusted.......an gama da shafinka tun a jiya" Ta fada qasan ranta tana tuna yadda al'amura suka tafi mata successful kaman yadda aka saba.
Sai data tabbatar tayo blocking ta kuma shafe duk wani abu daya shafeshi cikin wayar,bata bar hujja ko qarama ba da zata nuna tsohuwa ko sabuwar alaqa ko kuma mu'amala tsakaninta dashi ba. Ta sake bin wayar ta tabbatar komai ya koma kaman da,sannan ta duba wata ma'ajiya ta daban ta lalubi wata number ta kira ta kara wayar a kunnenta.
Bugu biyu aka daga ana sallama cikin zaquwa da zumudi
"Ina fatan saqon ya riskeki?" Tayi tambaya zuwa ga daya sashen
"Ya riskeni qwarai kuwa tun a daren jiya.......ina godiya......na gode sosai,ina me baki haquri kuma akan sabanin Fahintar da nayi miki a farko.....gashi kuma ko sunanki ma ban sani ba"
"Ba buqatar hakan......infact ma daga yau ba zaki sake samu na ko jin muryata ba......abinda na baki kiyi qoqarin tattalashi,ki kuma boyeshi daga sanin mijinki.......abu na qarshe saiki tayashi jiyya.....kinsan yadda zaki sanya masa tawakkali cikin zuciyarsa,don nayi imani ya zuwa yanzu zaiyi wahala bai zauce ba,na barki lafiya" Ta yanke kiran ba tare data barta tace komai ba,duk da tarin abubuwan fada masu yawa da take dasu take kuma son gaya matan.
Itama goge number dinta tayi ta kuma sakata a sahun sauran tarin lambobin dake akwatin katangewa dake cikin wayarta. Layinta layi ne dake da wani irin tsaro na musamman,wanda ba kowacce number da bata yarjewa bace take iya samunta. Tana da ire irensa sunfi guda ashirin,duk kuma sanda take da muradi ra'ayi ko kuma buqatar hakan ya taso tana iya sauke wanda taga dama ta dora wani.
Tana shirin shigewa duvet ta kwanta wani kiran ya sake shigo mata. Batason takura sam,sai taja tsaki tana kallon fuskar wayar.
Shine din dai,batasan me yasa ya matsa da yawa ba,bataso a yanzun akwak enough kudi a hannunta,tanaso taje hutu koda na taqaitaccen lokaci ne kafin ta fada zuwa wani agenda din.
"Tsautsayi da alama keta kiranka" Ta furta qasa qasa ta jawo wayar tana rejecting kiran shima sannan ta kashe kiran gaba daya ta jefar da wayar. Kanta ta mayar ta qudundune sosai cikin blanket din,saidai ko minti biyar bata yi ba cikakke ta miqe zumbur kamar wadda aka tsikara,ta sauko daga saman gadon tana qoqarin daure gashinta me santsi dake rufe gefan fuskarta.
Kyakkyawar drawer dinta ta bude banqaran hijabs,ta fidda wani qaramin farin hijab cikin jerin hijban da take amfani dasu a lokaci irin haka idan zata shiga wanka. Sama kanta ta zurashi,wanda wannan ya fidda kyakkyawar fuskarta tsakanin hijab din,ya kuma fidda wata sihirtacciyar kama akan fuskar tata. Towels dinta ta nufa ta zari guda daya,sannan ta matsa gefan daya drawer dinta ta jawo ta can qarshe ta fidda set na kayan wankanta dake cikin wani dan kyakkyawan kwando kaman kwandon kaba,ta rataye toweldon saman kafadarta ta fara takawa a hankali tana fita a dakin tare da sake gauke fuskarta da kyau wanda kusan haka dabi'arta take duk sanda zata fita zuwa ainihin tsakar gidan nasu,duk da dama ita din ba matum bace data cika fara'a.
Duka duka mutanen dake sabgarsu a safiyar ranar cikin sararin tsakar gidan ba zasu wuce mutum biyar ba. Dukkaninsu kuma mata ne da a shekaru suke qasa da nata shekarun idan ka dauke mutum daya dake ta bakin kitchen dinsu,zaune saman kujera 'yar tsuguno tana ta kokawa da wutar ice da take qoqarin kunnawa hayaqinta yana dawo mata cikin idanu yana sake tunzurata da hasalata.
Duk wanda suka hada ido dashi sai ya janye dubanshi daga kanta kamar yadda itama kusan haka take musu,duk kuwa da cewa wasunsu suna son tankawa a gareta kaman yadda a wasu lokutan yake kasancewa,saidai wanzuwar ta bakin kitchen din ya sanya ba wanda yayi gigin aikata hakan a cikinsu.
Bata dakata ba har ta isa bakin makewayensu da ko yaushe yake cike da tsafta da kulawa,ta xare towel din wuyanta ta azashi saman qofar bandakin idanunta nakan shaheed,yaron da aka kawoshi yaye daga gidan mahaifansa zuwa gidan kakanninsa. Yaron yayarta ne,yayarta ta kusan biyar,d'iya a wajen gwaggo mace ta biyu a wajen mahaifinsu.
Ido suka hada da yaron,sai ya sakar mata murmushi,a hankali itama ta motsa bakinta tana maida masa martani. Tana da wani boyayyen soyayya ta yara a zuciyarta,saidai zuwan yaron sai ya zame mata kamar wani mabudi ko kuma wanzuwar sabon abu da bata saba gani ba cikin gidan wato murmushi kowacce safiya a tsakar gidan mahaifinta wanda ya jima da shudewa tun bayan gushewar mahaifiyarta.
Tanason yiwa yaron magana,amma tayi imani rayuka zasu iya baci daga qarshe,dole ta kauda kai,ta sirka ruwan zafin data fito dashi ta fada wankan.
Kafin ta kammala taji masu buqatar shiga bandakin da yawa,masu qananun mitoci da qorafi duka sunayi,wasu su juya wasu su zauna suna dakonta gami da ci gaba da yasar da maganganun da tayi imanin da biyu suke yinsu kamar yadda suka saba.
Zuwa yanzu ta fara tunanin yadda zata maida qaramin dakin dake kusa da dakinsu toilet. Daya daga cikin dabi'a daya ta gidansu data tsana kenan,sharing toilet.
Gini ne irin na da wanda duk yawan jama'ar gida suna hadaka ne a bandaki qwaya daya tal!. Zata iya cewa da sauqi nasu tunda akwai wadatar tsafta.
Ko data fito babu wanda tabi takai,sai data kammala uzurinta na daura alwala a nan bakin famfo sannan ta tattaro kayanta tana barin wajen. Sai a sannan ta kallo mata biyun dake zaune daga bakin bishiyar.
Daya ta girmi daya a shekaru,saidai dayar ta dara dayan jiki. Sun kalleta sun kuma dauke idanu kamar basu ganta din ba. Ba abinda ya dameta da hakan
"Ina kwananku?" Ta furta da muryarta me laushin nan tana yin gaba ba tare da tayi koda yunqurin tsaiwa ba da salon gaisuwar da duk safiyar duniya bata daukewa kowacce cikin su ukun ba muddin zasu hadu a farfajiyar gidan.
Amsa mata sukayi kaman yadda suka saba din,can qasa suna kuma binta da wannan kallon dake dauke da tarin ma'anoni can qasan ransu,wasu.
sun furta su sun kuma bayyana,wasunsu kuwa an barwa zuciya AKWATIN SIRRI.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*π³πͺπ³πͺ
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*π₯°π₯°
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
PAGE 15
A nutse take ratsa falon harta cimma uwar dakin nasu. Duk takunta guda daya sauke qafarta da dauketa zuciyarta cike take da kewa. Wata qatuwar kewa data zamewa kowanne motsi na rayuwarta lazim. Kewa ce da zaiyi wuya ita iya barin gangar jiki. Kewar mahadin rayuwa jigon rayuwa mahadin numfashi wato MAHAIFIYA.
Duk yadda lokaci yakai ga wulwula gudu,duk yadda zamani yakai ga fara yin tsaho da nesanta bawa daga dukkan tunani radadi da damuwoyin abubuwan da suka shude amma ya gaza yin nasara a kanta ta wannan fannin. Mahaifiya daban take cikin rayuwar 'ya'yanta,babu ma ya mahaifiya irin tata......jajirtacciyar uwa data zamewa maraicinsu sutura,ta zame musu bango abun dafawa,ta hana musu kuka akan rashin mahaifinsu.....sai gashi a yanzun suna kuka.....irin kukan da kunnuwa ba zasu iya ji ba,idanuwa ba zasu iya gani ba.......ta saka dukkan wani qarfi da iyawarta ta tare wannan shingen maraicin......tozarta da wulaqantar rayuwa dake shirin danne musu numfashi har ya zuwa lahirar duniyarsu.......tallafewar data sabbaba mata tarin ciwuka.......nauyi me yawa a qirjinta da rayuwarta......ya kuma bude mata qofofi masu fadin gaske cikin rayuwarta......ya maida JARUMA a mafi yawan lokuta.....wani lokacin kuma MAFARAUCIYA dake bude dukkan qarfin qwanji dana zuciyarta don cimma burikanta.
Ya dasa mata abubuwa masu yawa cikin ZUCIYARTA ya kuma sanya dolen dolen ta sauya akalar rayuwarta ta fanni da dama. Ta koma tamkar tarwada me wahalar kamawa cikin ruwan da take ninqaya. Ta kuma koma tamkar hawainiya dake canza kala a duk sanda taso hakan,ta bace ta kuma saje da duk yanayi ko launin da takeso ko kuma taga dama.
Tana da tarin sunaye masu yawa da a duniya a yanzun bayan ainihin sunanta na yanka SABREEN. Sunayen da ba'a yiwa yanka ba don tabbatuwar samuwarsu a kanta.
Akwai idanuwa bakuna da hankula masu zafi da batasan adadinsu ba a kanta. Kowanne kuma da irin nashi kallon.....hasashen da furucinsa dangane da ita.
Karon farko ta sakarwa fuskar nan tata murmurshi data fito tawai bisa fuskar madubin dame gabanta duk kuwa sa siririyar qwallar dake kwance cikin qwayoyin idanunta masu sheqi kaman an diga ruwan zaiba. Karaya da kuma qwarin gwiwa na karakaina tsakanin qirjin nata,saidai ko sau daya bata aminta ta dauki FADUWA TSORO ko kuma ja da baya ba.
K'aramin towel da yafi kama da handkerchief ta sanya ta tsane qwalla don kada ta bata daman fitowa,ta miqa hannu ta jawo stool ta zauna a kai tana saka hannunta tana kokawar daure sassalkan gashinta dake qoqarin kwancewa daga daurin farko datayi masa.
A nutse ta jawo set na kayan shafarta da take amfani dasu. Skin care product ne da suke mahadi da shower gel cream da sauran tarkace,wanda kudinsu duka zai tasamma dubu arba'in.
Kudi ne me nauyi da ciwo a wajen me qaramin qarfi,to saidai ta wajenta amfani dasu sun zame mata jiki kaman yadda suka zame mata wajibi. Tana son ado,tana qaunar tsafta da qamshi,wanda da a baya bata basu muhimmanci ba,saidai daga bisani ta gama karantunta tsaf......ta fahimci kowanne taku a rayuwa akwai abokin yinsa.....akwai sauyawar yanayi da ta zamewa jiki da rayuwa dole......dole sai an aiwatar da wasu abubuwa ake samun wasu abubuwan,dole sai an gusa koda da taki daya ne sannan ake samun wasu sabbin damarmakin suke shigowa rayuwar dan adam.
Gayunta na daya daga cikin abinda ya sake sama mata MUMMUNAR SHAIDA da kuma mummunan zato daga bakunan mutane da dama. Zaton daya kamata ya qona mata rai.....ya sanyata fidda qwalla masu zafi.....a maimakon hakan saidai kawai ta murmusa,ta kuma motsa ta barka a wajen da salon abun nan dake nuni da BANI DA LOKACINKI/KA.
Tsaf ta duk wani shafe shafe nata,ta kuma gyars gashinnan me tsanani yauqi sheqi da tsaho,ta dameshi cikin ribbon me dan girma,abinda ya sake bawa ainihin kamanninta fita ras kenan.
Koda ta bude ma'ajiyar kayanta tsaiwa tayi tana tunanin suturar da zata dace da jikinta a wannan lokaci. Shaqe take tafff da tarin suturu na alfarma,masu tsadar da koda ba'a gaya maka ba kai kanka ka sani. Suturun da a tashin farko xakasan sunfi qarfin wanzuwa cikin wannan wardrobe din.....kaman sunfi qarfin ma ace akwai wani cikin gidan daya mallaki masu darajarsu.
Juya zagayyayun idanunta tayi tana dan lumshesu kadan zuwa bangaren abaya. Sai data gama nazarinta sannan ta jawo daya daga ciki. Egyptian abaya ce me asalin daraja da kuma kyau wadda kudinta ya tasamman dubu arba'in da 'ya'ya. Sam sutura me tsada ba damuwarta bace,tana iya mallakarta a duk sanda tayi marmari ko kuma muradin hakan.
Da sanyinta dinnan da yake cikin halittarta take daura belt din da abayan yazo dashi bayan ta saka ta farko ta kuma dora alkyabbar da abayar tazo da ita. Siririn mayafi ta zaba daya dace da rigar tayi rolling me kyau da ma'ana,take zagayyar fuskarta ta fito cif tsakiyar veil din,sai ta kuma duba handbags dinta dake rataye sama da goma sha biyar kowacce da takalminta mahadi a qasanta.
'Yar qarama ta dauko qirar kamfanin D&G da takalminsa,ta natsa gaban madubi ta dauki turarenta ta bintike kan ta feshe jikinta dashi,sannan ta zari wayarta ta jefa a jaka tana duba agogon dake daure a tsintsar hannunta ta doso falon.
Jakar ta ajjiye tana jawo tea flask dinsu tana qoqarin budewa. Bata fiya son cin abinci da wurwuri da safe ba,to amma kuma tana tunanin zaiyi wahala idan ta fita din ta iya tsaiwa taci komai tasan halin kanta da kanta sarai.
A tsaitsaye take kurba kyawawan idanunta zube fes saman qaramar waya me keypad data dora saman cinyarta tanata qoqarin kiran wata number.
Bugu biyu aka dauka,muryarsa ta bayyana cikin wayar da wani irin shauqi da doki
"Da wacce irin saa yay na wayi gari ne?,ya Allah" Ya fadi yana zama gefan gadon bedroom dinsa.
Taqaitaccen murmushi me qaramin sauti ta sake tana kai cup din