Showing 336001 words to 339000 words out of 557259 words

Chapter 113 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

496

Fitowarta daga toilet shi ya sanya ya ware rinannun idanunsa a kanta. Duk da bata iya ganinsa sosai amma taga alamun ya farka daga baccin. Dama ya kamata ace ya farka din,tunda agogo ya nuna mata lokacin magariba yayi,amma kuma batasan yadda zata tayar dashi ba,to ya samawa kansa lafiya daya farka din. Dakin ya mata duhu saboda yadda duhu ya soma mamaye garin,saita laluba har ta dace da makunnin ta kunna qwan dakin,take haske ya gauraye ko ina tarwai. Idanunsa ya lumshe yana cusa shi cikin pillow

"Oh shit" Ya fada qasa qasa. Qoqarin tashi yake kafin hakan takai ga faruwa sai gashi ta rigashi kunna hasken dakin. Ta yaya zai iya tashi ya miqe ya wuce zuwa bandaki a yanayin da yake ciki?,tambayar dashi kansa baisan amsarta ba.

A nata bangaren ta gama gajiya da zaman dakin,burinta kawai ya budeta ta fita,bataga wani alfanun zamansu suna musayar numfashi ba idan ba tsabar muguntar nashi bane ya motsa. Ta duba luggage dinta ma sam bata ga hijab ba,sai mayafai ta hada kusan uku dasu zatayi sallar. Ba ita ta hada kayan ba,zata iya cewa batasan ma meye a ciki ba,anni ce ta musu siyayyar duk da uban lodin kayan da suke da wanda ita kanta batasan adadi ba,amna kuma ta shirya mata tace basai ta buda ba ta saka mata komai,ta kuma biye matan bata duba ba.

Bashi da wani sauran abinda ya rage illa dole ya tashi din,don haka ya tattara uban duvet din ya nadeshi a jikinsa ya sauka yana wucewa toilet din a gurguje. Ta danyi mamakin shigarsa toilet fa duvet,amma sai kuma sai ta kauda abun daga ranta ta shimfida abun sallah tana jiran lokaci ya qarasa cika.

Ya jima a toilet din yana qoqarin ganin yanayinsa ya daidaita,yasha azaba qwarai har ya dinga tunanin anya yau zai tsallake kuwa?. Kowanne jijiya ta jikinsa aikawa take da saqo,sai bayan kusan minti talatin ya samu yanayinsa ya dawo daidai,amma abinda yakeji a jikinsa bai sauya ba tunda jikin bai samu abinda yakeso ba. Dukka jikinsa ya wani mutu qwarai da wata irin kasala data sakar masa da nauyin jiki,haka yayi wanka ya daura alwala ya fito. Sauqinta daya data samu tana sallah sanda ya fito din,don da alama a yanzun ma gaba gadi ya fito abinsa,ya buda kayansa ya shirya cikin Moroccan jallabiyya black me adon golden din zare,ya saka qaramae gold din hula ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki key ya bude qofan ya fice don zuwa su hada jam'i dasu saddiq kaman yadda suka saba duk sanda sukayi tafiya a qasashen daba masallaci a kusa da masaukinsu.

Fitarsa sai taji kaman ta samu 'yanci ne,ta kammala sallarta ta fada wanka. Koda ta fito lokacin isha'i yayi,tasan qwarai tana da nauyin wanka,amma na yau ya haura na kullum saboda ba qaramar wahala tasha wajen gane yadda zatayi amfani da kayan bandakin ba.

Da karsashinta ta isa ga luggage dinta,saidai kaf ta cajeshi babu wata suturar arziqi da zata iya sakata ta fita,sai uban lingerie data zuba mata kaman karuwar dake neman customer.

Takaici ya sanyata komawa ta zauna ta rafka tagumi,kusan mintina ashirin ta kashe a haka kafin ta jawo akwatin ta sake birkiceshi ko zata dace. Baqinciki ya sanyata daga lingerie din daya bayan daya tana qare musu kallo. Kaya ne na rashin kunyar da ita kanta kunyar wasu a ciki takeji idan ta daga

"Amna kin kwafsamin.....kin kasheni......shi yasa kikace kada na duba kayan" Ta fada a fili daidai sanda ta daga wata lingerie din da aka yiwa wani yanka na wulaqanci,aka fidda gidan mama daga qasa kuma aka mata wata huda.

Shigowarsa da sallamarsa duka lokacin guda ne,ta saki rigar da sauri ya bita da kallo,ta miqa hannu da gaggawa ta tattareta ita da sauran tana zubawa a akwatin sannan ta miqe.

Tanason masa maganan ya turo mata amna amma batason halinsan nan,ya kammala abinda yakeyi ya doshi hanyar fita

"Idan kin gama abinda kikeyi din ki fito za'ayi dinner"

"Don Allah ka turomin amna" Ta katsi numfashi tana fadi da sauri har sai daya waiwayo ya kalleta,karon farko da magana ta nutsuwa da respect harma da begging a ciki ya taba hadasu,sai baice komai ba ya fice abinsa.

Harara ta ballawa qofan tana jin baiken kanta,me yasa ma ta roqeshi?,gashinan ya yarfata a banza,dama me hali ai baya fasa halinsa,ta tsugunna tana hade kayan cikin takaici. Saidai ko gamawa batayi ba amna tayi sallama,ta tsaya daga qofa tana leqowa a darare.

"Ki shigo malama" Ta furta tana jifanta da harara.

"Shigowa makwancin hamma din kai tsaye haka hadari ne" Ta fada tana shigowa kaman yadda ta buqata. Tana mamakin irin tsoronsa da sukeyi da yadda suke kiyayarsa qwarai.

"Yau fada zamuyi dake har anni saita shigo sasanci"

"Me nayi adda?" Ta tambaya tana waro idanunta gami da dafe qirjinta

"Kayan da kika zubamin dama kenan amna?" Ta tambayeta tana dan kama kunnenta. Dafe kunnen tayi dariya tana kamata,duk da riqon babu zafi amma tace

"Wayyo kunnen autar anni......aradu anni ce tace duka na zuba miki su,ni kuma da naji tace haka saina kwashe wadancan......bansan mix ya kamata ayi ba" . Kunya ta saukarwa sabreen,sai kawai ta saki kunnen amna din

"Saikije ki daukomin hijab dinki,kayan fice ficen ma duk na fasa sakasu tunda baki sakamin kayan zaman gida na arziqi ba,da hijab zanta zama"

"Kaina bisa wuya na" Ta furta tana dariya gami da ficewa. Gudun jira sai kawai ta shirya kanta cikin riga da wandon,rigar ta sauko mata har saman mazaunanta,wandon kuma cif jikinta,don ya fidda sigar santala santalan cinyoyinta da faffadan qugunta.

Murda qofan ya sanyata juyowa da sauri tana zaton amna ce ta dawo,saidai a maimakon amna din sai taga hammanta. Fuad ne tsaye fuskarsa babu walwala,kai tsaye ya soma kallonta tun daga qasan qafafunta,idanunsa kuma suka cake akan qirjinta,abinda ya sanya yaji wani yarrr tsigar jikinsa ta zuba. Fes abinda yaji da dumi da qamshin da wajen kiyi ya dawo masa fes a qwalqwalrsa,sosai jini ya harba ko ina a jikinsa,yayi gaggawar damqe numfashinsa gami da hana faruwar abinda yake shirin faruwar dashi.

Kallon qurillar da a yau yayi mata karon farko a tarayyarsu ya ratsa kowanne jini dake gudu a sassan jikinta. Idan tace zata juya masa baya nan ma tasan bata tsira ba,komai na jikinta ita kaΓ±ta tayi imanin a bayyane yake.

"Karki fara gangancin fitowa a haka......ki nema kinomo ko hijab ki saka a jikinki". Sai ya saki qofar yana juyawa yana jin numfashinsa kaman zai tsaya da aiki.

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 71

71

Tun kafin ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na daidaituwar al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun muhimmanci.

Ba jiya ko yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata tun basu mallaki hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu guda ne tattare dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling irin na kowanne lafiyayyen namiji.

"Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa sanda fu'ad ke zama a dining din kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana cewa

"Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya kamata ba"

"I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa yasan farouq din bai aminta ba.

Tare suka jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan wayarsa yana duban sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya umarta ba,saboda yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi ganin karon farko tayi abinda yace da ita.

Gaida anni ta sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq da yake da sauqin kai.

Amna ce ta soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring anan qasar wato hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da dama. Yawa yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa wajen iya sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni ko kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki bane babba.

"Sabreen" Anni ta fada tana dubanta

"Na'am anni"

"Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza mata,amma hakanan ta miqe ta dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana kallonsa wai ko zaice ya isa haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan wayarsa

"Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta raya mata. Wato fareedan ce mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida lokacinta?.

Duka anni na ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta

"It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka ko?". Kansa ya daga ya dubi anni yana gyada kai yana sakin qaramin murmushi. Karon farko data gayawa kanta da gaske yana da kyau kaman yadda takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu me kama da murmushi akan fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba wanda yake samun fu'ad din a asalin fu'ad dinsa sai anni.

"Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan abincin data zuba masan.

Abinci sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar bare a cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi.

Sai kunnuwa data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a goben. Amna keta lissafin abinda zasu kashe

"Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta girgiza kai

"Ko sisi amna.....me zan siya?"

"Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu fa,zakiga abubuwa da yawa da zasu burgeki.....kinji anni wai batason komai......adda komai sai tace bataso?".

"Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da dolla account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana murmushi,kunyarta tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke wayoyinsa.

"Zan kwanta anni"

"Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare ya fara" A nan ya barsu ya gangara ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa.

Wani mummunan horo kawai yakeji farouq yayi masa na hadashi kwana daki daya da ita. Gaba dayansa sai yake jinsa kaman a birkice yake,tun yana qaryata wanzuwarta daki daya dashi ne ya sanya yanayinsa komawa hakan,har yayi amanna cewa hakanne. A dare daya tak ya kasa samin isashen bacci har zuwa wayewar gari,wayewar garin da ya tashi da ninkin rashin kuzari da karsashi a tattare dashi,fiye ma da yadda ya kwana jiya.

Kowanne motsi farouq yana ankare dashi,dariya qasan ranshi kaman zata kasheshi.

"Duk dacin ranka.....duk miskilancinka halittar mace tafi qarfinka ko kai waye......qaton tuzuru dakai sai taurin kai da kafiyan da ba inda zasu kaika?,dama can sarari ka samu,nisan tazarar dake tsakaninku ya sanya kake ganin kamar baka da wata buqata ko sha'awa irin ta d'a namiji.....wallahi qarya kake fu'ad......a wannan fannin ni kaina na sallama maka.....zan gani idan tusa zata hura huta......daga yau zuwa gobe kawai na baka,if kaci gaba da taurin kai.....nasan matakin da zan dauka a kanka" Farouq yayi dukka wannan gulmar cikin zuciyarsa yana duban fu'ad dake zaune yana kurbar maca and ginseng tea. Kaman baiso yake daga cup din zuwa bakinsa,shi kansa,ranshi a jagule,baiso irin wannan yanayin ya tasammasa a irin wannan lokacin ba sam,saidai koma meye zaya faru bayajin zai yarda koda da wasa ya hada jikinsa da ita. Jikin da akullum ya kalla sai yayita lissafin adadin maza nawa ne suka rabeshi?,adadin maza nawa ne suka tabashi?,dame dame sukayi da ita?. Yana da bala'in qyanqyami na fitar hankali,wannan qyanqyamin ya sanya bayajin shikam ko mata biyu zai iya aura,gwara ya tattara mutuntakarsa a muhalli daya. Uwa uba wani irin kishi ne dashi,ba kuma wai yanzu ba,tun tale tale zai iya cewa da kishin ya tashi,dashi aka halicceshi. Baisan maruka nawa yasha daga hannun maamah ba sanda take kawo maza gidan abokan kasuwancinta da suke siyan shaddodin da ta soma business dinsu ba,baisan adadin yawan dukan da yasha a kansu ba......saboda muddin zaka sanya qafarka a gidansu,to shi kuwa zai kafe ya cake a qofa ya hanaka qarasawa ciki.

"Babanmu baya so......ya hana maza shigar masa gida,ka koma ka aiko qanwarka ko yayarka" Wadannan sune lafuzzansa a yayin da fuskarsa kan cika da wani irin fushi da zafin zuciya. Kusan baki suke sakewa,kusan duka duka shekarunsa a sannan ba zasu wuce goma sha daya ba,amma zuciyar manya gareshi,zuciyar data kubuta daga dukkanin tsoro saboda kare martaba da haqqin mahaifinsa. Wani lokacin idan ta jawoshi ta daka ta daka,abbansa dake daki kwance yana jiyya shi zaita kiransa,shi zai lallasheshi,yakan ce

"Komai na duniya me wucewa ne me babban suna.....komai kuma haquri ne yake zama silar cin nasararsa......ka daina bari ana tabamin lafiyarka me tsadar nan kaji?" Sau tari duk kalan dukan da zata masan ba kasafai ya fiya kuka ba,duk da cewa duka ne

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login