Showing 360001 words to 363000 words out of 557259 words
daha quruciyarsa har kwanan gobe bai fasa ba. Tsaf ya gama karantar farouq din,sanin da yayi masa sani ne ba na yau ko na jiya ba,ya gama karantar abinda ya shirya,don haka har ya gotashi ya sanya hannu ya fincikoshi baya gami da zaunar dashi a gefansa.
"Zauna kayi dariyarka yadda kakeso" Ya fada yana shan mur gami da dage girarsa dukka biyun sama tare da qoqarin danne abinda ya taso masa game da saqon fareeda. Maganar fu'ad din sai ta zama kaman tsokana ga farouq din,take kuwa kowacce dariya dake cinsa ta fashe,ya soma qyaqyatata,harda sauka daga kan concrete chair din ya zame yayi Zaman dirshan cikin grass carpet din yana dariyarsa abunsa.
"Kayi me isarka,don wallahi muka shiga ciki kayimin a gaban yaran nan saina faffasa maka baki" Ya sake fada yana hade ranshi
"Aah...me yayi zafi?,bani na kar zomon bafa,wallahi ko ratayar ma ba'a bani ba" Ya fadi yana qoqarin danne dariyarsa. Wani kallo ya watsawa farouq din yanata qoqarin maintaining girmansa.
"Farouq?"
"Allah ya taimakeka" Farouq ya fada yana daga masa hannu da shigen gaisuwar sarakai
"Kada ka batamin mode dina" Ya fada yana ware masa idanunsa duka a kansa.
"Ango ai baka laifi koka kashe dan masu gida......girmanka ne,Allah ya taimakeka tuba nake....." Naushi ya kawo masa Allah ya rufa masa asiri ya kauce ya samu iska,farouq din ya sake komawa da baya yana sassauta dariyar tasa,don magana yakeso suyi me muhimmanci.
β
*FAREEDA*
Da qyar ta tattara kanta tana laluben hanyar fita daga dakin. Tunda take a rayuwarta bata taba jin ta muzanta irin na wannan ranar ba,don ko data koma daki kasa hada idanu tayi da lubna qawarta.
"Ke da zaki bude wuta kuyi spending night din gaba daya kya dawo haka da wuri?" Ta tsareta da tambaya sanda ta hautsina kayanta tana laluben inda take ajiye kayan mayenta ko zata samu wani abu da zai dauke mata baqincikin da takeji. Bata samu komai ba,abinda ya sake hautsinata kenan,ta kama gashin kanta ya damqe da qarfi sannan ta sake tana dakawa lubna tsawa
"Get out of my sight.....idiot" Tabe baki lubna tayi tana matsawa gefe. Ta sani indai muhammad jadda ne ta qwallafa rai a kansa yanzun ma ta fara wahala da sonshi,bata taba jin wadda a tarihi ta taba samun koda alamu alamun nasara ba a kansa. Da qyar ta iya hada abinda ya bugar da ita ta zube tana bacci ruhinta cike da cin alwashin cikin mutuncin maamah idan ta farka,tare da shaida mata ta dawo mata da kudadenta da dukka taci muddin ba zata iya mallaka mata d'anta ba. Ta dauka duniya ba wadda take da iko dashi sama da ita....ta kuma dauka mallaka mata shi shine abu mafi sauqi da zata iyayi mata.
*MAAMAH*
Tun saukarta a qasar ba zata ce ga wata cikikakkiyar ibada data iya samu ta aiwatar ba,dukka hankalinta da tunaninta yana a kansu. Me dame yake kashewa ameenatu?,me dame sabreen ki shiryawa a kanshi?,ta bayyana masa sirrinta ne kaman yadda taci alwashi ko.kuwa?. Babban a binda yafi damunta da tsaya mata a rai batun fareeda,gashi har yau din ba taji komai daga gareta ba,bata kirata ba ita kuma bata da number wayarta bare ta fara nemanta. Abu daya ta sani shine.......tabbas.....kofa zatayi yawo tsirarara.....koda malami ko babu.....koda boka ko babu saita nunawa SABREEN DA AMEENATU girman isarta akan danta. Idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba ba shakka ita din ba diyas halas bace.
Bayan sallar la'asar kawai saita kasa sukuni,tsakanin jiya da yau kawai saita dinga jin kaman wani abu zai faru ko ya faru,wannan ya sanya ta lalubi number wayarsa ta soma kiransa cikin jin isar mallakinta ne shi ya kamata ya zamanto sai yadda tace ko ta lamunce sannan ayi.
Qarar wayar fu'ad din ta sanya hankalinsa ya koma kan wayar daga kan farouq da ya fahimci iya shege kawai yakeson samun dam yayi masa......baisan yadda zuciyarsa ta tumbatsa da wani irin yanayi akan yarinyar ba?. Komai bai dameshi ba irin yadda zai maidata mallakinsa fiye da yadda ya maidata a yanzun......yanaso ita kanta a jikinta ta sallama cewa ita din mallakarsa ce har abada,sai ya kalli farouq ya daga masa yatsa alamun zai amsa wayar. Kai ya jinjina masa,saidai kafin yakai ga dagawar wayar ta yanke. Qoqarin lalubota yakeyi ya kira sai tex ya fado masa
_"Duk wanda kayi gangancin kamawa ko hukuntawa cikin mutanenmu dake hannunka.......ba shakka labarin matarka zai zama labari na farko da zai zama fitaccen labari kowacce safiya saman jaridun qasar mu da qasashen dake huldar kasuwanci dakai,suke kuma ganin kima da daraja a tare da kai_
Wani irin fusgar hankalinsa saqon yayi,saidai kuma kafin ya sarrafa kwanyarsa ya fahimci komai kiran maamah ya danne saqon,dole ya kauda abinda ke taso masa ya daga kiran yana sawa a kunnensa,bakinsa dauke da addu'ar
"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta taj'alal hazna iza shi'ita sahla". cike da fatan ba wani abu bane na daban zata baro dashi ba bayan abubuwan dake dabaibaye dashi ba.
*_Da sauran masu bibiye da rayuwarsa kenan_*
*_Ya zafafa da gaske wajen yin campaign na samun soyayyar ta,xaiyi nasara ko kuma zata zille masa?_*
*_shin fareeda zatayi nasara ta hannun maamah kuwa?,kaman yadda tayi nasarar sanyashi auren sabreen a wancan lokacin?_*
*_munata gangarowa da MAFARIN warwarar kowanne qulli da tonuwar binnannun asirai_*
*_sai ince muje zuwa dai_*
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 83
_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_
_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_
_Bukhari da muslim_
83
Cikin cikikakkiyar nutsuwarsa yayi sallama,zuciyarsa bata fasa neman dauki da ambaton sunan Allah ba.
"Wa'alaikumussalam" Ta amsa masa a dake,tanaso ya fahimci cewa lallai shi din me laifi ne a wajenta.....wannan fahimtar tata da zaiyi ya zama sila kuma jagora zuwa ga wanzuwa da amsar babban burinta a yanxu na auren fareeda.
A nutse ya fara gaidata,ta amsa masa a dake kaman dazun. Shuru ya ratsa na wasu sakanni kafin tace.
"Baku hadu da fareeda bane?" Mamaki kadan ya kamashi,mamakin yadda akayi maamah din tasan da zuwan fareeda Maldives.
"Mun hadu" Ya amsa mata kai tsaye,kasancewar mutum ne shi da wahala ko tsanani basa sakashi yayi qarya.
"Amma me ya hanaka zama me masaukinta?......tunda kana da tabbacin ba don kowa tazo ba sai don kai". Mamaki ya sake kamashi,ya lumshe idanunsa yana jin takaicinsa yana sake daduwa. Gaba daya maamah din kowacce rana sake jirkita takeyi tamkar wahainiya,wasu abubuwan nata da takeyi sai ya dinga ganin tamkar ba cikin hayyacinta take ba. Maamah ke magana,uwar data kawoshi duniya,inda wani ne ya masa magana makamanciyar wannan yana da amsoshi masu yawa da zai bata.
"Bansan da zuwanta.....batayi shawara dani ba kafin ta taho.....and a yanzun ina da iyali maamah,bani da wata alaqa da ita ta kusa ko ta nesa,banda dangantaka da ita" Ya amsa mata da kwantacciyar murya duk da tarin quna da bacin ran da yake ji na cin zuciyarsa.
Idanunta ta qanqance cikin jin tashin hankali yana ratsata a hankali a hankali. Meye yake shurin faruwa?,meye yake faruwa da har yau din fuad da bakinsa ke ambaton INA DA IYALI?. Yaushe ne ta samu wannan matsayin a wajensa?,wata kalma da bata taba jin ta fito daga bakinsa ba?.
Tarin masifa da wani irin tsanar sabreen tana ratsata,batasan wanne kalar abu ya kamata ta yiwa yarinyar ba......a yanzun a dukka illar da aka mata a rayuwa bayan ameenatu sabreen din itace ta biyu,koda ta raba sabreen da fu'ad bata jin taci riba idan tabar yarinyar haka siddan taci gaba da rayuwarta,tana jin ya kamata ta ajewa rayuwarta wani babban tabo ko miki da zai sanya koda a gaba zata zamewa wasu izina a kanta. To amma babban qalubale da barazanarta a yanzu shine TA WACCE HANYA ZATA RABASU?. Haka kawai take jin matsanancin faduwar gaba da fargaba idan ta tuna kalaman sabreen akan auren fu'ad,bawai ta fara son fu'ad bane matsalarta,idan hakan zata kasance ma zai zame mata daidai,tsoron shine shi fu'ad din......yana da wata irin zuciya da bata iya soyayya ba kaman yadda bata iya qiyayya ba......yana da wata irin zuciya me riqe abinda takeso da gasken gaske..... Wata irin zuciya da idan tana so tana so.....idan bataso bataso,zuciyar da zata iya sadaukarwa da abinda takeso komai data mallaka.....ta zamewa abinda take qauna kariya daga dukkan wata iska ko kuma guguwa.
"Wanne iyalin kake magana akai fu'ad?,iyalin da nice silar wanzuwarsu a rayuwarka?.....ko kuma iyalin da babu wata kima ko martaba a tattare dasu?.....ko kuma ni da aka tsinceni daga ayarin tafiya aka wofantar dani saboda kun nunawa duniya bani da wata daraja a wajenku?,ni din ba kowa bace a wajenku?". Wani ciwon kai dukka maganganunta sukaso tasar masa lokaci daya,ya sanya tafin hannunsa ya dafe goshinsa yana murzashi a hankali tare da lalubo me ya kamata yace mata?,gefe guda kalmar IYALIN DA BASU DA WATA KIMA KO MARTABA tana masa zillo cikin kwanya.
"AKWAI WANI ABU A LULLUBE" yaji wani saqo na zuciyarsa yana gaya masa. Idan har maamah ta aura masa sabreen ne saboda ta yarda da tarbiyyarta kaman yadda tace da farko......me ya kawo wannan maganar a kanta a yanzu?. Bayajin akwai wani abu qwaya daya da zai iya tunawa wanda ya taba hadasu koda cikakkiyar magana bare yayi tunanin akwai abinda ta taba yi mata.
"Fareeda ta taso qafa da qafa.......ta sameni har muhallina......ta girmamani matarka ta tabamin haka?,fareeda tabar qasarta ta biyoka har inda kake,bata da kowa batasan kowa ba saboda tana sonka.......me matarka ta taba yi me kama da wannan?". Kanshi yaji ya sake qullewa......a yau din duka me ya kawo maganganu akan sabreen?,me yahau kan maamah duka akan sabreen din?.
"Ina me baka umarni a matsayina na uwar data haifeka.......nan da kwanaki goma zan bar qasar nan......ba wani jirgi da zanbi,ba wanda zaizo ya daukeni....kai da kanka nakeso kazo ka daukeni ka kuma kawoni Maldives......ka kuma soke barinku qasar ka daidaitashi da nawa barin har sai na kammala uzurina sannan mu tafi......daga qarshe ina me baka umarni kaje kaga fareeda......ka kuma marabceta kaman yadda kowanne baqo yake marabtar baqonsa......wannan umarni na ne indai nice na haifeka" Daga haka ta yanke kiran ba tare data jira cewarsa ba.
Shima wayar ya sauke daga kunnensa yana kallonta,kafin ya sakata a tafin hannunsa yana dan dokata kadan kadan. Kallonsa farouq yayi kafin ya aje dubansa ga wayar hannunsa. Ya fahimci wadda tayi kiran ya kuma ji wani abun da take cewa saboda magana take da qarfi da kuma fushi.
A abinda yake lisssfawa zaiwa fareeda kowanne ya debo sai yaga yayi masa kadan. A hankali maganganun maamah din sai yaji kamar suna tafiya da farincikinsa suna son rushe duk wata walwala daya samu.
Idanunsa ya bude kan farouq yana hadiye kowanne bacin rai da maamah ta sanya masa da rudanin saqon daya shigo wayarsa a dazun.
"Ina jinka......kaman magana kakeso muyi ko?" Yace da farouq. Idanu yadan zubawa fu'ad din,sai yaji tausayinsa yana kamashi. Kowacce ni'ima da baiwa ta rayuwa Allah yayi masa......amma ya rasa UWA TA GARI. Ya sake yarda tabbas rayuwa jarabawa ce,hakanan kowanne dan adam akwai inda tashi jarabawar take,ba wanda yake samun jin dadin duniya dari bisa dari.
Murmushi farouq ya sakar masa,sai yaji bazai iya kowacce magana dashi a irin wannan yanayin ba,don haka ya sauya akalar zancan yana yin murya qasa qasa
"Wai yaya akayi wannan gingimarin ta iya hawa saman keke?,karaya nawa keken ya samu?,duk da ni shaida ne akan yadda keken ya kusa komawa akwala sabod......" Naushi yakai masa cikin sa'a ya daki iska. Ya fahimci lallai da gaske farouq so yake ya maidashi birin wasanshi. Gefe farouq ya koma yana dariya,can qasan ransa yana jin dadin hararar da fu'ad yake watsa masa,yasan tabbas ko bai nasarar gusar da baqincikinsa ba zai rage masa wani abu.
"Wallahi ka iya bakinka akan iyali na......kada ka yarda mu saka qafar wando daya dakai" Yayi maganar yana nunashi da yatsansa.
Ido farouq ya zaro yana daga hannuwansa sama
"Ya salam.....kace me?,iyalinka?,unbelievable.....wazai tayani jin wannan kalmar.......sabreen won the battle" Qaramin dutse ya dauka zai jefeshi ya kwasa da sassarfa ya wuce cikin gida yana cewa
"Wallahi ta haukatashi......ya zama madoki" Tilas dariya ta subuce saman labbansa. Sai da farouq ya bacewa ganinsa sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa. Kai tsaye ya kira jordan sukayi magana ta wasu mintuna sannan ya kashe,ya kalli agogonsa yana lissafin awannin da suka rage su kaishi gurin target dinsa.
β
K'arfe takwas na dare agogon Maldives ya gama shiryawa cikin wasu lafiyayyun trouser da t.shirt. ta fidda sigarsa sosai da wani sassanyan kyau ke tsayawa a zuciyar dukkanin 'ya macen data Kalleshi. Wani irin mutum ne da zai wahala ka kalleshi ka kauda kai,koda baka furta komai a kanshi ba amma zai tsaye maka a zuciyarka da idanuwanka. Jikinsa yabi ya feshe da turarukansa,sannan ya sanya sau ciki a qafarsa,ya dauki wayarsa da maqulli ya nufi qofar fita daga dakin.
Dukkaninsu suna dining area suna cin dinner. Kusan tunda suka iso garin tare suke cin abincin safe dana dare,na rana ne kowa da tsarin cin abincinsa bai yuwu suci lokaci guda. Ire iren wadannan abubuwan sune suke qarawa iyalan anni hadin kai qaunar juna shaquwa tare da fahimtar juna.
A kanta idanunsa suka fara sauka,wani irin abu ya tsarga masa tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa. Tun jiya bai sake sanyata a idanunsa ba,suna dakin annin ita da amna. Bazaice ga abinda sukeyi ba,amma lokaci lokaci yana jin muryar amnan da motsinsu,ita kanta amnan bata sake fitowa ba. Ita da amna suna seat din kusa da juna,kaman magana suke qasa qasa,baka iya ji saboda musaddiq da saddiq da suka cika gurin da musunsu da bai gane ma akan meye suke musun ba.
Kaman wadda aka umarta,nata fararen idanun da a kwanakin yaga kaman sun qara girma ta daga ta watsa masa cikin rashin sanin shi dinne ya is wajen. Qwayoyin idanunsu suka gauraye da wani irin mabanbantan feeling. Da sauri ta janye qwayar idonta yayin da nata kallon a gareshi ya zame masa kamar wani irin dafi daya sabbabba mutuwar dukkan wasu gabbai a jikinsa. Tsigar jikinsa ta zuba sanda ta soma motsa wadannan siraran lips din nata tana tauna Chip's din dake gabanta. Bazai taba manta abinda yaji daga kowanne sashe na jikinsa ba a ranar farko daya soma tsotsar tausasan lips dinta ba......wani mahaukacin saqo da suka aike masa da baisan inda zai iya adana yawansu a kwanyarsa ba. Yanzun da take juyasu tana tauna sai ya zamana tamkar tsokanarsa takeyi haka yakeji tana aika saqo kowanne sassa na jikinsa.
Fitowarsa ya sassauta tashin muryar saddiq da musaddiq din,kowa ya maida hankalinsa jikinsa,kasancewar sunsanshi mutum ne da baison ire iren musunnan nasa. Yakance
"Shashanci ne wannan,kuna da abubuwan yi da yawa a gabanku cikin rayuwarku,shi ya kamata ku fuskata" Sau tari musaddiq yakanyi dariya idan bai wajen
"Shifa hamma ya dauka kowa irinsa ne.....ba baki nayi mana ba,amma ba zamu iya achieving abinda yayi achieving ba.....we are doing the best,amma ba zamuyi kaman nasa ba". Kujerar dake opposite dintata ya zauna,sam table din baida fadi sosai,wannan yana iya sawa idan ka zura jiki da yawa gwiwarka ta iya taba ta abokin zamanka.
Zamansa a wajen sai taji kaman gaba daya ya cika wajen.....kwarjininsa da qamshin sassanyan turarensa gaba daya ya gauraye wajen. Nauyin idanuwansa takeji har tsakiyar kanta,abinda bata taba ji ba a kansa tsahon tarayyarsu.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 84
_Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_
_Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_
84
"Barka da fitowa hamma" Amna ta fada wadda sun hadu yau kusan sau uku sun riga da sun gaisa already.
"Lovey dovey.....barka da dare" Ya fada cikin wani irin aji kaman me qididdige adadin kalamansa na ranar. Murmurshi amna ta saki qasa qasa.
"Hamma.....kada ka saka adda sabreen taji kishi fa.....sunan nan for now ya kamata ace nata ne". Daga shi har ita nauyi maganan ya musu musamman da anni ke a wajen,wadda tayi burus kaman bataji ba tana qarasa shan black tea dinta. Amnan ya kalla sannan a dabarance ya saci kallon sabreen din. Bayajin akwai wani suna daya cancanci ya kirata dashi......har yanzun duk sunan daya bata sai yaji tafi gaban wannan sunan. Daidai lokacin tana jefawa amna harara da fararen qwayar idanunta ne,wani irin kyau yaga ta sakeyi masa,tsigar jikinsa yaji ta zuba sosai har sai daya lumshe idonsa.
"Ka maida hankalinka fa.....aiki zaka fita kayi" Wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa ganin tana neman dagula dukkanin lissafinsa.
"Yi serving hammanku takwarata" Anni data kammala shan tea din ta yiwa sabreen magana. Hakan ya masifar