Showing 213001 words to 216000 words out of 557259 words

Chapter 72 - 𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

469

Tabbas bata taba kula da wannan kyan ba,wanda inda tasan dashi tana da dukkan makaman da zata rusa tafiyar........a yanzu bayan komai yayi nisa ta yaya zata katse wannan wasan da bata taba ganin abinda maamah ta ciwa buri a kansa har haka ba.

"Yauwa sannu" Sabreen ta maida mata da salon yadda tace da ita. Haka kawai taji ba zata iya gaida matar ba,tun a waccar ranar duk wata kima martaba da kuma mutunci da ake ganin dan adam me girma da shekaru nasu duka su biyun suka kwaranye mata.

"Ya gida ya shirye shirye?" Hajjan ta sake dauriyar fada yadda sabreen din ke shan qamshi yana qara qona mata rai,amma duka wannan ba komai bane......tasan s nan kusa zata fahimci wace ita?kuma su waye su.

"Alhamdulillah" Ta sake amsa musu. Kai tsaye hajja ta gabatar da abinda ya kawosun,da dukkan alamu sun nuna ba'a maraba dasu ata nan din

"Saqone daga mamarki" Hajja ta fadi tana turawa zuwaira akwatin,ita kuma tana sadar dashi xuwa ga sabreen dake binsu da idanu.

𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐓𝐀 𝘭𝘪𝘵𝘵𝘢𝘧𝘪𝘯 𝘬𝘶𝘥𝘪 𝘯𝘦

08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

̶B̶O̶O̶K ̶2

ⱧɄ₲Ʉ₥₳

𝙋𝘼𝙂𝙀 8


Page 8

Duniya ta

Sai data qarewa akwatin me ruwan gold kallo,sannan a nutse ta aza kallonta akan hajja,don tayi yaqinin itace jagorar tafiyar kamar wancan karon.

Kallon kallo ne dake nufin ina buqatar qarin bayani. Da yake hajja din 'yar gari ce har ta fahimci ma'anar kallon,ta saki wani qaramin murmushi sannan tace

"Kusan duk inda akace ana arziqi tsiya guduwa takeyi.....lallai ba shakka kina cikin matan da sukazo duniya a sa'a da har tarihi zai baki daman kasancewa matar muhammad jadda.......wannan suturan ta lashe miliyoyin kudi.....kuma an tanadeta ne kawai saboda ki sanayata a ranar da za'a miqa ki zuwa gidan fuad,wannan shine burin uwar mijinki da kuma umarni na farko da takeso ki fara dauka cikin tafiyar ku......lallai ne muddin kika kasance me biyayya ina miki busharar keda sunan talauci kinyi adabo.... Aiki ne na qididdgaggun watanni,amma ribarsa zaki ci gaba da cin gajiyarta har qarshen rayuwarki data zuri'arki". Idanu ta lumshe a nutse sannan ta budesu. Tana jin wani murmushi yana taso mata daga qasan zuciyarta amma kuma batason bayyanarwa hajja dashi. Shin sun dauka ita din wawiya ce da har zata aminta da komai daya fito daga garesu?,sunyi tsammanin shirunta galaba ce a tare dasu?,ko sauraro da dakonta a kansu suna tsammanin alkhairi ne?.

Zamowa tayi a nutse daga saman kujerar ta zauna a gabansu gaba daya tana langwashe qafarta. Idanunta tsakiyar na hajja ta soma magana da nutsuwar nan tata dake qarawa maganarta kwarjini da fahimta a muryar me sauraro

"Ina zaton aikin data nema daga gareni zaya tsaya ne kawai iya kan danta.......aiki kawai tace zanyi mata na wata uku ko hudu......bata da hurumin komai cikin rayuwata.....kama daga cima ko sutura......" Ta tsaya iya haka tana maida numfashin bacin rai. Ranta ya fara dugunxuma na ganin yadda suke qoqarin maida rayuwarta tamkar gare gare tsakanin uwa da d'anta da suka zamo tsatso daya......abinda sam ba zata lamunta ba kenan,ita tayi mata......danta ma yayi mata?,shin ummeeenta su ta haifawa su?.

A mamakance hajja ke binta da kallo,bata taba zaton haka daga gareta ba,kallon hajjan ya isheta hakanan,dom haka ta miqe cikin rashin damuwa tana gyara lullubin kanta tace da ita

"Ki gaya mata damuwarta ta tsaya iya kan aikinta kawai......indai tace zata hada da shigar da rayuwar sabreen......komai bazai tafi yadda take tunani ba.....ni din tamkar wahainiya nake a wasu lokutan.....sawun keke da gane gabansa yake da wahala koda a wajen gwanaye".

*MAAMAH*

Idanunta ta runtse bayan hajja ta jera mata dukkan wadannan bayanan da sabreen ta aiko mata dasu ba tare data rage komai a ciki ba.....koda ta manta wani abun zuwaira dake gefe tana taso mata dashi. Ta bude idanunta cikin bacin rai tana duban akwatin da iya shi daya kawai kudi ta zuba masu yawa,banda kayan banda kuma aikin da akayi akan kayan.

"Yarinya ce qarama tabbas.....amma na yarda da gaske tana da hadari........tana kuma da wasu boyayyun abubuwan da bamusan dasu ba......iya kalmominta na yau sun sake zaburar dani akan dole na ninka shirina a kanta......amma ba wannan ba.......asarar data sani nayi tun a matakin farko yafi damu na....."

"Kada ki damu.......akwai mataki na biyu da nayi imanin ba zata tsallakeshi ba......saidai shi na biyun bangare daya ya qunsa.......bangaren cusa soyayyarta a zuciyar fuad ya saraya,saidai a samo masa wata hanyar ta daban". Ajiyar zuciya maamah ta saki tana jin sassaucin tashin hankalin dake sauko mata

"Wannan dinma wahalar da nayi a kansa bazai tafi a banza ba.....koda bataso sai tayi amfani dasu,ta hanyar da takeso ko ta hanyar da bataso bata kuma shirya mata ba". Daga haka ta jawo akwatin ta cusashi qasan lafiyayyen gadonta.


𝙈𝘼𝙁𝘼𝙍𝙄𝙉 𝙏𝘼𝙁𝙄𝙔𝘼𝙍......

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀


Tamkar jira akeyi su kammala sauka daga jirgin,wayarsa dake riqe hannun daya daga cikin guard dinsa da tun tafiyar zuwa yanzu shike da alhakin riqe masa ire iren wadannan kayan nasa.

"Sir.....oga farouq" Ya sake matsowa kadan bayan fuad yana fadi cikin rusunawa. Baice komai ba ya miqa masa hannun shi kuma ya dora masa wayar,ya dawo da wayar fuskarsa yana duban kiran farouq din yana ci gaba da takawa yana fita a wajen.

Boyayyen murmushi ya saki,tun jiya ya kashe wayarsa dama duk wani hanya da farouq din zai sameshi,yasan tabbas idan ba haka ya masa ba bazai shafa masa lafiya ba,zai birkita masa lissafi ne kawai.

"Idan baka da niyyar dawowa ne malam ka yiwa mutane magana.......awa uku kadai suka rage awannin daurin aurenka su cika......amma still ace baka iso ba?".

"Who told you dude?.....mu hade a Bristol,banason hayaniya" Daga haka ya kashe wayar ya miqa masa yana magana dashi ya tura masa number dakin da yayi booking already. Yana da gidajen da zai iya sauka a cikin su,saidai sam sam baya shaawar ya sauka a can din gudun kada a cimmasa a dameshi da damuwa.

Abinda bai sani ba yayi gudun gara ne,don kusan mafi yawan abokansu da sunzo ne don farouq a Bristol din sukayi masauki.

Sanda saqon yakai wayar farouq shafa kansa kawai.yayi,yaci alwashin sai ya rama wasa da hankalin da fuad din yayita yi masa. Ya ajiye wayar yana kiran musaddiq kan ya fiddo mota yanason kai yakai ga fitowa su ruskeshi a can.

Yayi mamakin ganin motocin jadda har guda biyar a wajen suna jiran isowarsa. Bai gama wannan mamakin ba farouq ya fito cikin daya daga cikinsu yana qoqarin rufe wayarsa ya jefata a aljihu.

Wani kallo me kama da harara ya watsama fuad din wanda ya jingina kawai jikin daya daga cikin motocin yana kallon qarewar fushin farou a kanshi. Ya sani shi ko farouq din babu me iya fushi da dan uwansa.....duk wani abu da daya daga cikinsu zai fadi burga ce kawai da cika baki,da zarar sunyi face to face yake wucewa tamkar bai faru ba.

Koda ya iso duka yakai masa ya goce yana wannan tsadajjen murmushin nasa

"Haka kawai ka nakasani bayan banyi komai ba?" Ya furta murmushin yana shimfide a fuskarsa

"Sa'arka daya wallahi......yau babbar rana ce" Farouq ya fadi yana buda masa murfin motar da kansa. Sai daya shiga sannan yabi bayansa,yana zama wayarsa kuma ta dauki tsuwwa ya ciro yana amsata.

Tunda suka taho a hanya farouq ke amsa wayoyin mutane iri iri. Yana ankare dashi amma baice komai ba,ko a iya haka ya samu alama da shaidar lallai gayyar jama'a farouq din yayo.

"Kada kacemin tsayawa kayi ka batawa kanka lokaci kayita kiran mutane?" Yayi maganar yana tabe baki cikin rashin bawa abun muhimmanci. Wani kallo ya watsa masa

"An gaya maka kowa irinka me wai?,kai abinda ka dauka daban.....yadda mu muka dauka......aure komai lalacewarsa sunansa aure.....barema ba lalataccen koda na bariki ne".

"K'nnnnn" Kawai ya fada yana zamewa gami da yin relaxing sosai jikin motar

"Nidai muyi mu qarasa,bacci ne a ido na,kwanakin duk da nayi acan ba wani bacci na samu ba".

" Mutuwa zakayi ba bacci ba" Farouq ya fada cikin harzuqa. Kallo daya ya yiwa farouq din ya lumshe idonsa yana cewa

"Allah ya baka haquri" Daga haka bai sake cewa komai ba kaman yadda bai kuma bude idonsa ba har sukaje.

Da lallausan farin towel ya fito daga toilet din dakin daya zame masa masauki daure a qugunsa. Ya qarasa gaban madubin dakin yana duban yadda farouq ya zube masa duk wani kayan shafawarsa. Duddubasu yayi kawai ya ajiye yana mamakin yadda farouq ya dauki auren nan serious. Sai ya jawo stool ya zauna akai yana kallon kyakkyawar fuskarsa ta cikin madubi gami da sanya qaramin towel yana tsane ruwan kansa. Koda ya gama sai ya aje towel din,ya soma lalubar wayoyinsa. Sunyi da larab zai kirashi don ya tabbatar an gama design na hall din dake cikin kamfanin inda za'a gabatar da taron budeshi a jibi kaman yadda ya tsara.

Gajiya yayi da dube dubensa,sai ranshi ya bashi farouq ya kwashesu. Qaramin murmushi ya saki,yasan zai aikata,kuma duk zaiyi hakanne don ya tilastashi shiryawa. Duk da abun ba wani muhimmanci gareshi ba a wajensa.....amma farouq ya tattara duka lokacinsa akan komai dason ganin komai ya tafi daidai din,ya qarasa gaban madubin ya sake zama yana bude lotion dinsa na dindindin ya fara shafawa. Yana tsaka da taje sumarsa me tsananin daukan hankali aka murda handle din aka turo,bai motsa ba don yasan mutum daya ne zai masa haka.

Ta cikin madubi ya hangoshi ya shigo. Sai ya samu kansa da dan qare masa kallo. Yayi kyau cikin wata irin danyar shadda dake nuna nauyin kudaden da aka narkar domin siyenta,aka kuma keta alfarmar nera tare da nuna mata iyakarta wajen tsara mata dinkin jikinta.

Farar hula ce saman kanta da aka yiwa nadin farin rawani,wanda aka saki jelar rawanin ya zubo ta qirjinsa daga gefan kafadarsa ta dama. Iya abinda ya iya gani kenan,amma fadin yadda shigar ta qarawa farouq din kwarjini ma ba'a magana.

"Kayi kyau ango" Ya fada da sigar zolaya yana maida idanunsa saman mirror table din yana aje comb din hannunsa tare da lalubar hair spray.

"Kaima yanzu zakayi naka kyan.....don komai namu iri daya zai kasance". Da sauri ya daga kai ya kuma juyo gaba daya yana dubansa hadi da fiddo sexy eyes dinsa sosai zuwa waje,abinda ba kasafai ya fiya yi ba

"Wanne irin rigima ne wannan farouq?,kafi kowa sanin banason manyan kaya basu dameni ba......for god sake zakace babban riga zan saka harda wani qarin rawani kamar nine zan jagoranci sallar juma'a na yau din?".

Watsa hannuwansa farouq yayi

"Kai ka sani" Ya fada a gajarce yana nufar inda kayan suke ya soma ware masa.


𝐃𝐮𝐧𝐢𝐲𝐚𝐭𝐚 𝐧𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐧𝐞
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
𝘡𝘢𝘧𝘢𝘧𝘢𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳

̶B̶O̶O̶K ̶2

ⱧɄ₲Ʉ₥₳

𝙋𝘼𝙂𝙀 9


Page 9

Duniya ta


Tsaye yayi ganin da gaske farouq din yake,daga qarshe baida wani zabi illar amsar kayan daya dinga yi da daya da daya yana sanyawa.

Komai nashi fari ne qal yayi amfani dasu,tun daga undies har zuwa complete suturar jikinsa. Qerarren handmade half shoe din me ainihin tsada da kyau gami da daukan idanu dan asalin qasar italy,da agogon rolex me asalin daraja da ya samu ado daga wani yanki na gold din da kamfaninsa ke sarrafawa.

Gurin saka rawanin akaso asha daru,amma shigowar ahsan cousin din farouq ya raba gardaman. Shi ya karba ya nada masa shi tsaf saman kansa

"Ya subhanallah......ya Allah,na taba ganin wanda rawani ya yima kyau kaf tsayin rayuwata kuwa irinka?.....amma ban taba ganinsa dashi ba farouq" Ya maida tambayar kan farouq sanda fuad ke tsaye gaban madubin yana kallon yadda fuskarsa ta fita fes kamar an sauya masa ita. Wani annuri shi kansa yaga tana futarwa wanda bai taba gani ba,da gaske manyan sutura suna qarawa mutum kwarjini,karon farko yaji manyan kaya suna sake burgeshi.

"Lokaci yayi" Yaji farouq yana fada ba tare da yaji amsar da ya bawa ahsan ba.

"Ya salam" Ya fada sanda suke yo tattaki shi da farouq da ahsan zuwa ma'ajiyar motoci na Bristol din. Yawan matasan masu jini a jika daya gani kowa cikin shigar fararen kaya da babbar riga ya bashi mamaki. Abokan da da yawa ya manta dasu,wasu kuma haduwa tayi wahala,saidai kowa a cikin su yana cikin jerin sahun matasan da suke wasa da kudi som ransu saboda samun cikakken sukuni da arziqin rayuwa. Parking lot din ya cika gaba daya da motocinsu,ta wannan tana wane wannan,a haka ya qaraso gurinsu da natsattsen takun nan nasa kamar namijin talo talo.

Daya bayan daya yake basu hannu suna gaisawa,wasu su zolayeshi wasu suyi masa qorafi. Da yawansu bashi da abun cewa,musamman yadda yaji gabbansa sunyi sanyi da ganin mutanen da farouq din ya tara masa duk kawai dondai su shaida daurin auren da bai gama gamsuwa da yiwuwarsa ba. Ba wanda shigar fuad din bata dada da qasa ba,don ya dace da shigar ainun,harma tafi karbarsa sama da farouq din.

A nan suka kashe wasu mintuna kusan sha biyar ana rudu irin na abokai,gaba daya wajen ya dumame da qamshin turaruka masu tsananin tsada,daga bisani suka fara shiga motocinsu suna tashi daga wajen. Convoy sosai suka hada da jerin gwanon motoci masu tsayi,kusan daurin auren sanannen labari ne daya karade kowa,don haka duk inda zasi gifta sai ya zamana kamar suna sake bada sanarwar afkuwar abun. Duk inda suka gifta saisun wafci hankula da kyawun motocin,kowanne traffic suka je ba jinkiri ake daga musu qafa motocinsu su wuce tas,don haka basu wani kashe lokaci sosai a hanyar ba suka isa inda suka nufa.

Bai sake ji a jikinsa komai da gaske bane sai sanda suka isa alu avenue dake nasarawa,masallacin alfurqan inda acan aka tsaida don shaida daurin auren. Jikinsa yayi wani irin sanyi sosai,yana ganin da gasken gaske komai yake wakana lallai.

"Ya salam.....ya subhanallah" Kawai yake fada a ranshi. Irin taron dafifin al'ummar daya gani bai taba zaton zai samu irinsu a gurin ba........manyan mutanen daya samu a wajen bai taba koda kawowa zai samesu a wajen ba.....duba da ba wani mutum daya daya gayyata da bakinsa. Manyan 'yan kasuwar duniya daga qasashen duniya daban daban......manyan 'yan siyasa da qusoshin gwamnati......shugaban qasa da attajirai gami da duk wani me fada aji,don kusan kowa qarin martaba ne a tare dashi halartar daurin auren.

Basu ma kai ga samun damar isa cikin masallacin ba saboda yawan al'ummar dakeson ganinsa tare dayi masa fatan alkhairi. Baisan iya dadin yawan manyan mutanen daya jima bai gani ba amma yau daurin auren ya tattarasu waje guda ba.....baisan kuma adadin su nawa ya gaisa dasu ba,har zuwa sanda kunnuwansa suka jiye masa ta lasifiqan cikin masallacin data fito waje tana fadin.

"Mun shaida daurin auren matashin attajirin dan kasuwar gold MUHAMMAD FUAD JADDA da amaryarsa AMEENATU AHMAD MU'AZZAM".

"AMEENATU?.....why?. Me yasa aka sanya mata wannan sunan?" Ya furta can qasan ransa. Ta yaya zai zamana tana da suna me matuqar martaba da mutunci a idonsa irin wannan?,why..... Full name din da aka kirata dashi bai tuna masa komai ba sai kawun nata rufa'i,ranar daya samu fill details nashi da wannan sunan ya sameshi. Ya saki siririn tsaki yana jin ranshi yana baci. Inda mutane sunsan ko su waye su da basu bata kudadensu ba wajen siyan ticket na jirginsu sun cika jingim wajen shaida daurin auren ba,ya sake jan qaramin tsaki yana juyawa tare da neman nesanta kansa da hayaniyar wajen,guard dinsa da duk hautsinewar wajen basu yarda sun matsa ba suka biyoshi a baya.

Can wajen motocinsu ya koma,sai daya shiga ya zauna sannan yace musu

"Don't.....karku gayama kowa ina ta nan idan ba farouq bane ya tambaya".

"Yes sir" Suka amsa a matuqar ladance suka maida murfin suka zuge masa.

Rawanin duka da babbar rigar ya cire ya ajiye gefe,sannan ya koma ya zauna sosai yana nazarin wajen ta cikin motar. Abinda ya lura dashi,bawai farouq kadai ba,hatta da abba ya dauki abun very serious,yaga mutanensa a wajen har baisan adadinsu ba......haka anni,yaga familynta sosai,tamkar tana auren farouq ne,sai ya maida idonsa ya kulle yana son tuno waye da waye ya gani daga bagaren maamah?.

Bai samu nasarar kaiwa qarshen tunaninsa ba knocking da aka yiwa glass din motar ta sakashi bude ido,ya ganshi farouq ne,yana daga kwancen ya danna remote ya bude mass murfin.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login