Showing 264001 words to 267000 words out of 557259 words
kuma fallasashi.
"Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye ba wani wasa ko sassauci a muryarsa,abinda ya sanya zuwaira ta ida rudewa,ga turancin daya jefeta dashi wanda ya saka a duhu
"Eh....na'ammmm.....eh"
"Wacece ke?" Ya maida mata tambayar da hausa. Caraf ta kama maganar tasa
"Nice zuwaira.....zuwaira ce,me aikin da hajiya maamah ta aiko don taya uwargida sabgogi da hidimomin gida". Ta qarashe fada tana daddafe hannuwanta a qasa,saboda ji tayi kamar zata fadi daga tsugunnen.
Hannayensa kawai ya zube a aljihun wandonsa yana ci gaba da kallonta,yana kuma son ganin fuskarta sosai. Duk wani daya rabi maamah yana da nashi question mark din a wajensa.....duk wani wanda maamah zatayi qoqarin hada connection tsakaninsa dashi baida aminci ko nutsuwa kwata kwata dashi,don haka yake sake shawarwarin qarawa musaddiq kwanakin zamansa a qasar da ya aikeshi ba tare da wani qwaqwaran dalili ko kuma buqatar hakan ba.
Hannayensa nasa ya sauke ya soma takawa yana sauka daga wajen,zuwa sannan qiris ya ragewa zuwaira ta saki fitsari a wando.
"Kada na sake ganin gilmawarki cikin gidan nan indai ina nan......duk ranar kuma da kikayi sake hakan ya faru.....ki fara hada kayanki na barin gidan nan....basai nace ba"
"In sha Allahu ranka ya dade,tuba nake" Ta fada dukka jikinta yana rawa.
Daga ita har sabreen ba wanda yacewa da dan uwansa komai. Kusan minti biyar da fitarsa sannan ta tattara qarfinta ta miqe tana sake hawa steps din dining da sabreen ke zaune akai. Fuskarta qunshe da munafukin murmushin nan ta soma gaidata
"Barka da asuba ranki ya dade.....ashe har kin gama aikin?,ba zaki jira nazo ba?,hidimar ai sai tayi miki yawa,da sai na rage miki ai.....iyaka idan na gama abincin ki bada kalar maganin da za'a zuba a ciki......kedin abar tausayi ce ranki ya dade,kullum addu'ata da fatana ki kubuta daga hannun hajiya mariya lafiya" Zuwaira tayi maganar cikin matuqar sanyin muryar.....tsantsar alhini da kuma nuna damuwa.
Tunda zuwaira ke maganganun nan a jejjere sabreen bata daga kai ta kalleta ba sai da tazo gabar qarshen maganar tata. Kalmar tausayi data furta a maganar nata yaja hankalin sabreen ya kuma tsaye mata a rai. Sosai ta zubawa zuwaira idanu tana son tantance gaskiyar abinda ta fada,saidai kuma abun mamaki haka kawai sai taji ta kasa gamsuwa da ita.
Boyayyen numfashi ta sauke,sannan ta tattara hankalinta a kanta tana hade ranta tsaf
"Wannan duka ba huruminki bane.....kiyi abinda ya cancanci kiyi kawai" Sai ta miqe daga saman kujerar tana niyyar tafiya. Da sauri zuwairan ba tare da ta ji ciwon tsaidata a wata iyaka da tayi ba tace
"To ranki ya dade abincin fa?,yauma saidai a zubda?"
"Idan kina da buqatar ci kya iya ci ai" Ta amsa mata da gatse tana sauka daga step din idanunta yana sauka kan laila dake shigowa parlor din.
Sanye take da robber gown wadda tabi kowanne shape na jikinta ta lafe mata. Fuskar nan fes da kwalliya zaka rantse ba safiya bane ba. Ba komai a kanta sai wani qaramin bandana da bai rufe komai a gashin kanta ba. Wani mahaukacin tashin qamshi jikinta keyi,wanda turaren turare ne na musamman da aka tanada saboda wani mutum na daban.
Duk da fuska ko kuma jikinta ba wata kwalliya.....amma haka kawai ta fusgi hankalinta. Sassanyan kyan nan nata da baya buqatar kwalliya ko wani abu makamancin haka yana nan shimgide saman fuskarta. Haka kawai taji ta muzanta duk da kwalliyar dake jikinta,amma duk da haka sai taji ta raina kanta. Tashin farko wasu kalmomi na hajja suka dawo mata fes cikin kwanya suka qara mata azama da qwarin gwiwa. Muhammad jadda kawai take da buqatar gani,don haka taci gaba da shigowa falon tana jin izza tare da fatan ko yaya ta gwadawa sabreen wani abu da zai sosa ranta.
Kallo daya ta yiwa lailan ta watsar da ganinta a wajen,taci gaba da wucewa ciki ba tare data damu da kallon qurillar da laila ke mata ba. Ita sam bata ma dauketa a sunan damuwarta ba,damuwarta ta tsaya ne kan yadda yake neman maidata boyi boyin qarfi da yaji. Ta share masa sassa ta hada da wankin bandakinsa dama underwears dinsa,tana jin koda sama da qasa zasu hade ba zatayi wannan aikin ba. Lumshe idanunta tayi tana qara jin takaici yana cikata. Bashi da masaniyar hatta da girkin da take masa dole ce ta sanya take masa ba?,har wani qyashi da baqinciki ke rufeta gami da kasalar bacin rai duk sanda ta tsinci kanta dumu dumu a kitchen tana hidimar dafa masa abinci.
Dakinta kawai ta wuce bayan ta saqale masa key dinsa jikin qofarsa,tana fatan ya dawo ya samu sassansa da muqullansa a inda ya barsu.
Dining din laila ta wuce kai tsaye tana wani taku kai kace itace matar gidan,ranta ya cika maqil da kishi da hassadar sabreen din. Ko daga nesa ka hangosu sabreen din ta fita quruciya.......amma miskilancin yarinyar da shegen girman kanta mamaki yake bata. Bata taba mata kallo biyu ba....kai zata ma iya rantsewa sau daya ta mata nutsasten kallon cikin idanu Randa taso blocking mata hanya. So take ko yaya taga wutar kishinta a idanunta,to amma kullum suka hadu tana yin kamar babu aka kawo gidan aka ajiye ba dan adam ba.
"Ma aka dafa?" Ta tambayi zuwaira Kai tsaye tana latsa wayarta sanda zuwaira ta kusa gama kwashe warmers din.
"Sai yanzu Allah yayimin tashi,don haka saiki jira na gama da aikin matar gidan tukunna" Zuwaira ta gaya mata gatse gatse gami da satar idanunta ta gasa mata harara. Kullum ta tuna warning da kuma jan kunnenta akan ta yiwa yarinyar biyayya da hajiya mariya da hajja uwar yarinyar suka mata akan tabi yarinyar sau da qafa bama matar gidan ba.....sai taji kamar ta zabge yarinyar da mari.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 36
_An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace,manzon Allah S A W yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta har gari ya waye_
*_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan qin da tayi kuma ta samu ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna ganin bata samu wannan shahadar da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_*
36
"Ki gaggauta da Allah.... Am starving,ko ki bani wannan da kike debewa in fara dashi"
"Sannu akuya......" Zuwaira ta fada a ranta,amma a fili saita ajiye mata warmer din tana cewa
"Zaki iya ci mana.....amma kafin kicin ki fara sanarwa tsohuwarki gudun maida laifi a kaina" Ta fada dadan zafin rai. Haka kawai sai laila tasha jinin jikinta,don haka ta miqe tana sauka daga wajen
"Fresh nakeso.....kada ki wuce minti talatin" Bata ma iya amsa mata ba ta dauke ragowar warmer din tana wucewa kitchen din gami da jan tsaki qasa qasa.
Tafiyar minti arba'in da shida ta sadashi da mansion House din alhaji hamza kibiya. A qofar tafkeken gate din dake qara nuna alfarmar dake cikin gidan motocin suka tsaya bisa umarninsa,don yanaso ne ya gaida anni ya fito......ya kuma haida maamah din sannan ya wuce office din. Akwai cushewar ayyuka sosai yau din bisa schedule din da saddiq dinsa na yau da saddiq ya tura masa tun jiya da dare,wannan ya sanyashi fita da wuri. Wani irin qarin investors suketa samu a dukka kamfanoninsu,duk da yana yin komai bisa kula don ya tabbatar akwai mutanen dake bibiye dashi,kuma nasararsa a wancan lokacin yayi imanin ta tarwatsa musu dukka shirinsu..... Faduwarsu kuwa da shurunsu yayi amannar bawai suna nufin komai ya wuce bane.
Gidane dake cike da tsari,da kuma kusan duk wanda yake gidan bisa tsari da sanin ya kamata yake zaune. Kowa yasan aikinsa,tun daga kan security guards da sauran masu aiki na cikin gida dama farfajiyar gidan,hakanan bayin Allah da suke daukan nauyi dake wani sashe daban na cikin gidan me kama da qaramin estate kowa bisa tsari da sanin ya kamata yake.
Duk girman gidan ko.ina fes yake da wani irin tsafta da qamshi. Ya zuqi qamshin har cikin hunhunsa sanda yake zama saman sofas na qaramin falon anni da mutanen da suke mafi kusanci da ita ne kadai ke iya haurowa har nan. Ba abinda ke saukar masa da nutsuwa kasala gami da tayar masa da wnai Tsunammen feelings irin qamshi. Duk sonshi da qamshin wannan ya sanyashi haqura dashi kan bedsheets da duvet nashi da pillow,wanda muddin ya kwanta akai da qamshi irin wannan to zai wahala bai kwana cikin wahala ba,ko kuma ya tashi da mafarkin da zai wajabta masa wanka kafin yakai ga sallar asuba.
Normally yanaso kowanne kusurwa na inda zaiyi mu'amala dashi ya zama kaman haka,sai ya lumshe idonsa kafin ya budesu sanda yaji sallamar anni.
Da dogon hijabin nan nata har qasa ta shigo wanda ke alamta masa sallar walaha take ya tasota. A wajenta ya koyi sallar walaha,tun yana yi yana fashi batabi jininsa ba har takai ya saba,ko a ina yake,kome kuma yake yi sai ya katseshi yayi,saidai idan abubuwan sunsha kansa ko sunfi qarfinsa ba yadda zaiyi.
Fuskarta shimfide da kararramammen murmushin nan nata ta qarasa shigowa,tayi bismillaha tana zama saman kujerar abinda ya sanyashi zamowa daga samanta yana gaidata.
"Tashi ka koma ka zauna" Tace dashi don ba kasafai yake iya zama saman kujerar ba idan suna kai ko ita ko abbansu,harma da maamah din kanta.
Kai ya girgiza yana tanqwashe qafafunsa saman carpet kamar qaramin yaro
"Nan ma ya isa anni.....akwai kunun tsamiya?" Kai tadan daga tana dubansa. Batayi tsammanin zai qara tambayar abinci ba sam sam daga wajenta,don kuwa a yanzun magidanci sunansa,saidai kuma ta masa uzuri,don tunda akayi auren bai taba neman komai ba,don haka tace dashi
"Akwai.....kasan dole ne kullum sai an yiwa abbanku.....har yanzu gargajiya taqi barinku,bari nasa a kawo maka" Ta fada da murmushi. Shima tsadajjen murmushin nan da kusan annin tafi kowa ganinsa a duniya ya sake
"Anni akwai abubuwa masu muhimmanci me tarin yawa a gero,inda mutane sunsan meye gero anni da kusan duka mun koma cinsa". Murmushi ta kuma yi tana miqewa gaba daya
"Gaskiya mana naga kun qulla kyakkyawar alaqa da fura.....nikam wannan traditional doctor din naka ya sake canzaka gaba daya" Murmushi kawai ya saki,shi kansa ya sani kalar cimarsa ba iri daya bace data kowa,sau tari a wani taro ko a sanda ya buqaci cin abinci da baqinsa na Africa ko nan Nigerian,sukan cika da mamaki idan sunga kalar abincin da yake ci.
Da kanta annin ta shiryo komai saman tray,harda qarin lafiyayyen qosai da kuma farfesun kan rago da yasha kayan qamshi tafarnuwa da wadatacciyar albasa. Akwai abinda takeson ta karanta a tattare dashi a fakaice a matsayinta na uwa bawai kai tsaye ba. Tun daga ranar da amna ta gaya mata zaunuwar zuwaira a gidan ko sau daya bata taba hutawa da tunani ba. Ta kasa aminta hakanan ta kasa gamsuwa. Fu'ad dan maamah ne halak malak,duniya ma ta shaida hakan,saidai tana jin bai kyautu tabar mata rayuwarsa ba,rayuwar da aka fafata aka sha fama kafin fara daidaituwar komai a cikinta. Allah shine ya raya muhammad fu'ad din,amma kuma itace sila,tasha fama qwarai da gaske,faman da har batason tunawa,faman da shine ya zama silar shaquwa tsakaninsu me yawan gaske. Har batason tuna wahalar da tasha dashi kafin cire shi daga depression daya samu kansa a ciki.
Tana shigowa ya miqe,bai barta ta qaraso ba ya isketa a hanya ya karba tray din ya qaraso dashi. Sanda yake shan kunun a nutse yana kuma cin qosan tana zaune a gabansa tana karantarsa,tana jin zuciyarta na matsewa,ta kuma damu tayi masa maganar dake qasan ranta,duk da haka tayi jarumtar sanda ya kammala sannan a tsanake tace dashi.
"Muhammadu...."
"Na'am anni" Ya amsa mata a nutse yana jin wata nutsuwa da qoshi na musamman yana ratsa cikinsa.
"Nace anya yarinyar nan basai an taimaka mata da qarin masu aiki ba?,gidan nan sai nakega ko masu aiki nawa aka zuba masa yana buqatarsu ko don sauqaqawa matar gidan,duk da yake kai baka fiya son mu'amalar masu aiki ba cikin sha'aninka". Murmushi kadan ya saki,baisan wanda a duniya ya sanshi sosai ya kuma karanceshi tas sama da anni ba.
"Kiyi duk yadda ya dace anni......" Ya bata amsa cikin girmamawar data sake sanyata ta jishi a ranta sosai.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 37
_Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi neπ),yace:Manzan Allah S A W yace "da me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa na sabo,tabbas da ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara arba'in shine yafi masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_
_Bukhari da muslim ne suka rawaito_
37
"Da ina tunanin na tura mata ma'u da maigidanta malam ibrahim.......zataji dadin zama da ma'u sosai.....ina kyautata zaton haka,malam ibrahim kuwa koda kana da ma'aikata da sauransu zakaji dadin zama dashi in sha Allah".
"Anni ki zartar da komai da kike ganin ya kamata......ba buqatar sai kin gayamin anni" Ya sake fada har a zuciyarsa yana jin annin ta isa ta zartar da komai din.
Kai ta jinjina tana dan murmushi,har qasan ranta tana jin dadin yadda ya bata girma da kuma dama,duk da cewa tasan cewa abune me wahala ya musanta akan duk abinda tace din. Har bakin parlor na biyu tayi masa tattaki,bakin ta fal cike da addu'ar data zame mata dole,kowacce rana dukkaninsu su hudun basa kaucewa samun kyakkyawar addu'arta da bata gajiya da binsu da ita.
Qafarta daya saman daya take zaue cikin qawataccen parlor din nata da idan ka kirashi kai taaye da aljannar duniya bakayi kuskure ba,duk da ita a nata ganin sam har yanzu bai kai matsayin da take buri tsari da kuma mafarkin yakai ba.
Dukkan hankalinta ta baiwa zuwaira dake zayyane mata jawaban da muhimmancinsu a wajenta ya wuce kimar komai data mallaka a duniya. Jawabin dake da wani irin kima tamkar ta zinare a idanunta. Duk da bayanan ba abinda suke haifar mata sai wani irin tashin hankali. ba irin bayanan da take buqatar taji kenan ba.....amma duk da haka suna da muhimmanci a wajenta,don sune zasu zame mata tamkar tsani kuma fitilar da zata haska mata matakalar da zata taka zuwa matakin gaba.
"Amma fa tana qoqarin ganin ta aiwatar da aikinta......saidai ban hangi wata shaquwa soyayya ko kusanci da junansu ba ko kadan"
"Wannan kuma aikinta ne......ita kuma ya kamata ace ta fara samar da wannan dangantakar a tsakaninsu......a nan gazawar tata ta fito.....ta kowacce hanya ya kamata ta yaudari zuciyarsa har ya aminta da ita ya miqa mata wuya.......aikinki yana kyau zuwaira,ina buqatar magana da ita yanzun nan kafin na yiwa tufkar hanci tun daga tushiya"
"Yanzun zan sadaki da ita uwar dakina" Zuwaira ta fada cikin karsashi gami da jin dadin lambar yabon data samu.
Batasan adadin sau nawa ta duba agogo ba tana zaman jira da dakon kiran zuwaira. Qaguwar da tayi ya hanata jira zuwairan ta kirata ta maida kiran zuwa wayarta.
Ya shiga a daidai kuwa,sanda take rusune daga bakin bedroom din sabreen tana qoqarin fahimtar da ita amfanin kiran.
"Ina jinki kamar d'iyata ko jikata....ki daure ki saurareta,taqi kadan zai rage ku rabu in sha Allah". Duk bata gamsu da matar ba,duk da batajin nutsuwa da matar ko kalamanta,amma a ciki akwai abinda takejin gaskiya ne,a ciki akwai abinda takejin da gaske ya kusa tabbata din TAQI KADAN YA RAGE SU RABU.
Hannu ta saka ta karbi wayar,sai ta tura qofar bedroom din ta rufe ta koma ciki. Tana takawa cikin idanunta suna kan fuskar wayar,yau din a matuqar tunzure take,so batason wani magana da zata sake hasala hali da kuma yanayin da take ciki.
Gaban madubinta taja stool ta zauna,sannan ta kunna wayar ta sakata a hands free ta dorata saman madubin,sannan kuma a hankali ta maida idanunta saman fuskarta kamar me kallon maamah din zaune a gabanta.
"Ina jinki" Ta furta a nutse yana goye hannuwanta a qirjinta.
"Ina fata kina cikin lafiya da kuma aminci qarqashin kulawar d'ana?" Tayi maganar a nutse tana son kamo bakin zaren ainihin maganarsu. Kamar ba zata amsa mata ba,sai ta daga idanunta daga kallon dogayen yatsunta da gaba daya lallen da akayi mata na aure ya fice tas,tamkar ma ba'a taba digawa yatsunta lalle ba,ta maida oily eyes din nata cikin madubin daya bayyanar da