Showing 183001 words to 186000 words out of 557259 words

Chapter 62 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

475

yarinyar zamu binciki waye mahaifinta......idan har ta cancanta.....zai auri mata biyu a rana guda.....zabinsa da zabinki.....komai bazai wuce kwanaki hudu ba,don haka ki sanar da iyayensa bangaren danginki don a fita haqqin kowa dake kansa". Daga haka ya juya yana takawa a nutse yana fita a falon.

Miqewa tayi tsaye tana bin bayan nasa da kallo,Zuciyarta na wata irin tafasa,ta yaya kansa tsaye da wannan confidence din yakeson nuna mata qarfi da iyakarta akan abinda duk duniya tafi kowa iko dashi?.

"Ba zata sabu ba" Ta dauki wayarta da sauri tana kiran hajja.

"Daga hankalin na meye?,koma wace muna da boka,fiddata bazai zama wani abu me wahala ba.....ki bashi kwatance gidan da sunan mahaifinta na ainihi.. ..kibi a hankali ki zuba masa idanu......wannan karon harshi sai munyi maganinsa"

"Na gode aminiyata......duk duniya bani da masoyi kamarki"

"Yiwa kaine ai" Ta fada da binnanniyar ma'anar da ita daya ta barwa kanta saninta.

*****A mamakance yake riqe da takardu biyun a hannunsa yana dubansu. Gyara zamansa ya sakeyi sosai sannan ya daga kansa ya kalli anni dake zaune a gabansa

"Abunne yaketa bani mamaki aminatu.....yarinya daya ce shi da mahaifiyarsa duka ke fatutuka fa". Dan muskutawa kadan anni tayi tana daidaita zamanta.

"Ina cikin damuwa abba tun randa kace maamah ta zabawa fuad matar aure......bamusan ya zata kasance ba yarinyar.....to amma yanzu kuma na shiga rudani ne,ya akayi dukansu suke neman yarinya daya cikin rayuwarsa?". Shuru abban ya danyi,sannan ya ninke takardar ya ajiye a gefansa yana sake dubanta

"Ina aminatu?" Dan murmusawa kadan tayi saboda shi kansa yasan wannan sarar tasa tana bata dariya

"Gani abba"

"Yauwa.....abu na farko da nakeso ba gaya miki shine......ki dinga tunawa mariya itace mahaifiyar Muhammadu na ainihi,ita ta dauki cikinsa tahaifeshi ta kuma reneshi na wasu shekaru kafin ya dawo hannunki.....dole haqqin dake wuyansa nata yafi naki.....sannan so na uwa daban yake,duk yadda kikeso ki kawar masa da abu me cutarwa akwai guraren da ba huruminki bane shiga cikinsa"

"Abba nafi mariya qaunar me babban suna....." Wani murmushi ya saki yana girgiza kai

"Kin fita sanin ya kamata ne,kin fita kuma tausayin dan adam da qaunar yara koda ba naki 'ya'yan bane.......mu ajiye wannan.....abinda nakeso dake......a baya kafin bincike ya zamaya ya fito daga gida daya nima ina da wannan shakkar da kokwanton,saidai kuma ba hurumina bane na hana.....bugu da qari na samu relief da naji shima itace yarinyar da yake nema din,koda mariya da tata manufar na hadashi da yarinyar.....to shi ba yadda za'a yi ya cutar ai da kansa da kuma tasa rayuwar......abun tambayar qwaya daya ne kawai dana gaza banbancewa........ya akayi dukkaninsu sukasan yarinyar?,kuma dukkansu suka afu a kanta?,wanda samun amsar shima na huruminmu bane.....don muhammad yakai munzalin baligi kuma aqili da bazai dauko abinda zai cutatar dashi ba".

Kai kawai anni ke kadawa,maganganun abba suna gamsar da ita,daga bisani da saki nannauyar ajiyar zuciya

"Haka dukka maganganunka suke abba....daga yau in sha Allah bazan gushe ba ina adduar idan akwai sharri cikin lamarin.....ubangiji al'arshi ubangijin sammai ya juyar dashi ya koma alkhairi,ya kuma tsare dukkan wani sharri"

"Yau aminatu na......yanzu kikayi magana me kyau" Sai ta saki murmushi tana jin kunya tana dan kamata,don har yanzu girma tsufa ko shekaru basu sanya wannan kunyar dake a tsakaninsu ta gushe ba.

****Shudewar awanni uku kenan da wata murya tayi kiranta,ta kuma shaida mata cewa kirane nakai tsaye daga gurin hajiya mariya akan batun neman aurenta,ta aminta ko aje zuwa mataki na gaba?.

Duk da batasan meye ainihin abinda suke nufi da mataki na gaba ba,amma hakan bai hanata sauke saqo da kakkausar murya ba.

"Idan tana saurare shikenan.....idan kuma saqo zaki isar mata ki tsaya ki saurari komai dakyau don kada kiyi batan koda harafi daya wajen isar mata da saqona......ni aminatu sabreen ba haja bace a kasuwa da kowa zai iya tayata da farashin da yaga dama ya kuma siya,'yantacciyar diya nake ba baiwa ba wadda keda daman zabawa kanta komai da kuma kowanne yanayi na rayuwa......da ita da d'anta dama dukkan dukiyar da suka mallaka basa gabana koda kuwa zasu mallakamin dukkan abinda suka mallaka din.......ki gaya mata kada ta sanya ran wataran akwai abinda zai canza ni......ba wani abu da zai sauya tunani na akan maza......ba d'anta bama kawai.......har yau ba'a samu nasarar Haifa min wanda zai janye ra'ayina naji ina da niyya ko sha'awar ya zama mijina".

Sosai kalaman suka daki maamah wadda ke zaune a gefe tana sauraron komai. Ba zata iya jurar jin wadannan nauyayan kalaman ba,don haka ta miqa hannu ta gintse kiran cikin wani matsanancin fushi,sannan ta dauki wayarta tana laluben wata number tana cewa

"Zaki fahimci cewa komai yana da nasa iyakar".

Numfashi ta zuqa tana duban agogo,sai tayi zumbur ta tashi ta zauna. Batasan yaushe lokaci yaja har haka ba,batayi sallar azahar ba don haka ta miqe tana sanya slipper ta nufi tsakar gidan nasu.

Yadda taga kusan kowa da kowa cikin yara da jikokin gidan sun dawo sai ya dauki hankalinta. Su huda kusan sune sahun farko da sukafi kowa dawowa gida akan lokaci,ya akayi yau suka zama na qarshe?. Tun tana daura alwala take sanya ran shigowarsu amma shuru,ta kammala ta wuce daki,ta tayar da sallah ta kammala,sai tayi zaune a wajen tana zuba kunnuwa.

Shuru maqatau,abinda ya sanyata miqewa kenan gabanta yana faduwa. Basu taba kai warhaka a makaranta ba,har gashi masu zuwa islamiyya cikin gidan sun fara wucewa,sai kawai ta dauki wayarta da key din dakin ta fito.

Layukan nasu ta duba amma babu su,abinda ya tsananta faduwar gabanta kenan. Ta dauki wayarta zummat nemo busari yazo ya dauketa suje makarantar sai gabanta yayi wani mummunar faduwa sanda idanunta suka sauka kan number wayar da aka kirata dazu. Tunanin ya sake bnagazar Zuciyarta abinda ya sanya qafafunta yin sanyi qalau,ta sulale tana zama saman dakalin dake daura da ita hannunta yana yin sanyi qalau.

Wayarta taci gaba da kalla tana kuma taya agogon dake fuskar wayar irga wucewar kowanne second,har zuwa sanda ya nuna mata qarfe biyar daidai harda rabi na yammaci sai kawai ta danna kan number ta kira.

Kira ta dinga yi ba qaqqautawa amma ba'a daga ba,yayin da duhun dare yake sake kusantowa,yan islamiyya da wadanda na sukaje kasuwa sunata dawowa suna giftata kowa idanunshi a kanta don bash saba ganinta haka zaune a waje ba,wanda ita sam bata damu da hakan ba,har zuwa sanda kallon da yawan kiran suka soma quntata rayuwarta,saita miqe tana komawa cikin gida afujajan cikin matsanancin tashin hankali.

"Indai tayi kuskuren sanya min 'yan uwa cikin harqallar da daga ni sai ita......tabbas sai na shayar da ita mamaki koda hakan shine abu na qarshe da zanyi a rayuwata" Ta furta a sarari ganin yadda duhu ke sake kutsowa ba'a daga wayar ba ba'a kuma biyo kiran ba.

Sanda ake haramar kiran sallar ishai,sanda take zaune kan abun sallah ta bada faralin magariba cikin rashin nutsuwa da tashin hankali tare da zurfafa tunanin inda zata kamo bakin zaren kiran ya shigo wayarta.

Duk da kirana ne da take ta dakon shigowarsa amma bata daga ba sai dab da zai tsinke.

"Ki sakesu.....don su din basusan komai akan rayuwata ba".

"Good......naji dadi nayi kuma farinciki,haka kwanyarki take ja da wuri?" Hajja harira ta fada cike da mamakin gaske kan yadda ta dauki haske da wuri. Lalle da gaske ne da akace musu tana da basira tana kuma da hadari.



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ΜΆH ΜΆU ΜΆΜΆG ΜΆU ΜΆM ΜΆA

β—¦β€’β—β—‰βœΏPAGE 99βœΏβ—‰β—β€’β—¦



Idanunta ta lumshe tana jan wani numfashi har cikin hunhunta,tana jin wani zafi baqinciki da radadi suna ratsa zuciyarta.

"Ina sake maimaitawa.....kada kuyi involving innocent lives a cikin wannan deal din......ku sakesu safely".

"Karki damu yarinya.....qannanki zasu dawo hannunki cikin aminci..... Munyi hakanne kawai don mu gwada miki banbancin tazarar dake tsakanin sama da qasa......don kuma mu nuna miki girman wutar da kikeson wasa da ita kike kuma tunkara ta hanyar bijirewa umarninmu"

Sake lumshe ido tayi,maganganun hajja suna ratsata ranta yana sake baci

"Ku sakesu" Ta sake maimaitawa muryarta cike fal da bacin rai. Ta nason fadin abubuwa masu yawan gaske,saidai kuma tana qoqarin tausar zuciyarta. Ta sani ta riga data shiga hannunsu,sun mata shigar sauri,sunyi mata kuma shigar ba zata,dole tabi komai a sannu,dole itama ta shammacesu kamar yadda sukayi mata suma.

"Zamu sakesu amma bisa sharadin kin amince da buqatarmu?......"

Wani yawu me tauri ta tattaro a bakinta ta hadiyeshi da qyar. Baya cikin tsarinta QARYA amma yanzu ya zama dole ta fara gwadata akan mutanen

"Na yarda" Ta fada kanta tsaye. Murmushi hajja ta saki sannan ta sake cewa

"Kada fa kiyi tunanin kin amince don ki yaudaremu mu sakar miki yan uwa haka siddan.....lalala.......kina iya karya alqawarin,amma ki sani daga wannan lolacin daga kuma rana irin ta yay rayuwarku tamu ce,ba wani motsi ko taku da zakiyi ba tare da munsan ina zaki ko ina kika nufa ba.....ko yaya muka sameki da laifin yunqurin karya wannan amincewa da kikayi daga yau har zuwa ranar da zaki kammala aikinki.....hukuncinki abune da bazai fadu ba,na barki lafiya" Daga haka kiran ya yanke.

A hankali wayar ta sulale daga hannunta,wanne irin abune kuma ke shirin tunkaro rayuwarsu bayan tarkuna data tsallake masu tsananin girman hatsari?,su waye ne wadannan mutanen?,me suke nema da rayuwarta?,me yasa basu hango kowa ba sai ita?. Take idanunta suka sake dawo mata da fuskokinsu.

Fuskar hajja a farko,ta tabbatar a yanzu haka ita uwar wasu ce......me yasa duniya ta cika da masu son zuciya da masu son rai?,a yadda take uwa tayi imanin ba zata taba bari wani aibu ko abu me cutarwa ya samu yaranta ba..... to amma me yasa su take qoqarin ingiza rayuwarsu zuwa ga wani bigire?,don ba itace ta haifesu ba?,kenan kowa dansa ya sani?,wai shin a duniya WAYE ZAI RUNGUMI MARAYA IRIN RUNGUMAR DA UWA KEWA DANTA NE?.

A hankali kuma sai tunaninta ya hasko mata fuskar maamah. Har yanzu bata yarda ita din uwa bace ga yaron da take nemawa aurenta.......idan kuwa har hakan ya kasance da gaske ita uwarsa ce?tabbas tata lalacewar ta dara ta hajja. Me yasa take mata famfo akan danta ba zata tayata ta inganta masa rayuwa ba?,me yasa idanunta suke rufe akan cikar qazamin burin da batasan inda zai kaita ba. Wadannan tarin tunane tunanen su suka zaunar da ita adadin lokacin da bata sanshi ba.

******Dukkaninsu ta sanyasu cikin jikinta ta rungumesu tana sauke ajiyar zuciya a tare da hadiyar wani abu wani yanayi yana tsargawa a dukka sassan jikinta washegarin ranar da tayi zaune tana dakon ta inda zasu shigo. Dukkaninsu cikin abaya masu tsananin sulbi da tsada. Nadra da haneefa sun kasa daina bata labari tamkar wadanda sukayi balaguron alkhairi. Da alama zuciyarsu da hankulansu basu riski wani abu mara kyau ba a zahiri da zai ankarar dasu hadari suka fada ba.

"Suna da kirki adda.....wannan kayanma su suka siya mana fa bayan kowa ya zabi irin wanda yakeso" Nadra da kanta ke jikin Sabreen ta fada

"Munci kayan dadi sosai adda.......dakin da muka kwana me kyau sosai shima,harda Ac da komai da komai" Haneefa ta fada cikin zumudin gaske tana riqe box na chocolate dinta da kyau farinciki muraran cikin muryarta.

Idanunta ta mayar kan huda,ita daya ce kawai a zaune ta zubawa Sabreen idanu,tunda kuma suka shigo itace bata ce komai ba a cikinsu. Duban tsakiyar idanun hudan tayi ta karanci lallai nata feeling din akan mutanen yasha banban dana 'yan uwanta,zataso taji meye a zuciyarta?,meye nata hasashen. Zataso tayi magana da huda koda ba zata fahimceta gaba daya ba,aqalla ta rage wani nauyi daga zuciyarta dama qirjinta.

"Ku shiga ciki ku canza wasu kayan.....kema haneefa ki ajiye wannan chocolate din" . Tare suka miqe nadra tayi gaba haneefa tabi bayan ta suna maganganunsu.

Da hannu Sabreen ta yafito huda,sai hudan ta taso tsam ta dawo gabanta ta zauna. Dukka hannuwan huda Sabreen ta kama ta sanya cikin nata hannun,suka fara kallon kallo a tsakaninsu,kafin wani lokaci idanun Sabreen din suka cika taf da qwalla. Tana jin kamar ta gaza.......tana jin kamar ta kasa basu kariyar data dace dasu,tana jin tausayinsu matuqa da gaske,tanaso suyi amintacciyar rayuwa yantacciya kamar kowanne yaro. Tana qyamatar dukka abinda zaya tabasu,to amma da alama a dan tsakanin nan wata qaqqarfar guguwa ke shirin tasowa,wanda bata sani ba zasu kubuta daga azabarta da kuma qurarta ko kuma dukkaninsu zasu fuskanci wani sakamakon da ubangiji ne kawai yasan yanayin qarshensa.

"Inaji kamar na gaza huda.....kamar banyi aikin daya dace ba......" Tayi maganar qwalla cike a idanunta,muryarta kuma tana rawa sosai kamar zata saki kuka.

Damqe hannunta hudan tayi tana girgiza kai

"Kinyi dukkan qoqari adda.....kin bamu kowacce irin mafaka da kariya a rayuwarmu.....tundaga sanda suke daukemu jikina ya bani akwai matsala,duk kuwa da bamu fuskanci komai ba sai haba haba da maraba,sun bamu kowacce irin kulawa.....amma bamu sansu ba,bamusan su wayesu ba.....adda,abu daya suka gayan shine,dansu sukeso ki aura......me yasa ba zaki aureshi ba adda?,kaman alkhairi sukeson hadawa......me yasa bakison aure?". Kai Sabreen ke kadawa da sauri da sauri.

"Ban shirya aure ba huda.....ban shirya auren kowa ba,koda zanyi aure sai na aurar daku gaba dayanku a hannun nagartattun mazaje.....saina aurar daku a muhallin da nasan koda mutuwa nayi bani da haufi......bani kuma da kaico....amma ba yanzu ba,ba a irin wannan yanayin ba huda....idanma auren zanyi.....bazanyi auren cutatarwa ba,dansu baimin komai ba,ta yaya zan aureshi kawai don na zama silar da mallakarsa?" Maganganunta na qarshe ne hudan bata gane ba,sai ta zuba mata idanu tana kallonta.

Duk da tarin fargaba da yake ciki yake kuma kan fuskanta akan yadda zai tunkari Sabreen da maganar bada aurenta.....to qarshen tika tika tik inji bahaushe.........a yau shi rufai ahmad ya karbi komai na auren Sabreen din hatta da sadakinta bisa yanayin da bai taba zata ba.

Abinda yasha kwana yana mafarki shine......daga shi har Sabreen din sun cinye dukiyar aurenta da hannunsu,tun daga kudin aure kayan lefe sadakinta dama komai da komai na kudin baki. Sai gashi a yau ya wayi gari da baquncin wasu attajiran mutane dauke dakkan wata dukiyar aure. Kama daga sadakin aure daya tasamma naira miliyan biyar.......maqullin mota qirar Ferrari da baisan inda ma zasu ajeta ba........da tarin goro daya kusa huhu talatin,kwalayen alawa da suka kusa kaiwa kwali hamsin da tarin dabino da baisan ina zai ajiyeshi ba. Ga wasu uban kudaden da shi kansa baisan miliyan nawa bane na amarya kyauta ta daban,shi kansa ga wata dukiyar da aka mallaka masa a mazauninsa na uban amarya,abinda ya sanya jikinsa dukka ya dinga bari......Allah yasa komai ya tafi a tsari bisa taimakon kamilin amininsa.

Qarfe uku na yammaci motar da yasanya ta jido komai da komai ta tsaya a gaban gidan daya kasance gida ga d'an uwansa kuma uban riqonsa da yayi masa alkhairi masu tarin yawa a rayuwarsa.

Yara masu wucewa ne suka fara tsaiwa kallo ganin mota shaqe da kayan kwali kamar ana shirin bude provision. Wannan ya bashi damar kiran yaran,kafin wani lokaci sai gasu sun cika wajen harda wadanda ba'a kira ba,suka fara hidimar diban kayan suna shigewa cikin gidan dasu.

Hadiyya na daga bakin qofar famfo tana wanke uniform dinta na school of nursing,tazo gida ne weekend anjima kuma takeson komawa,yayin da bibo ke zaune saman kujera 'yar tsuguno daga qofar kitchen dinsu tana gyaran wake suna taba hira da shalelenta.

Daada ce ta fito a daki dauke da buta don kama ruwa gami da daura alwalar sallar la'asar. Daidai sannan yaran suka fara layin shigowa

"Kai.....kai daga ina?,ko.izzatu ce tazo?,izzatun alkhairi,don ita daya ce kaf gidan nan ke iya shigowa da kabakin arziqi haka" Bibo ta fada tana sakin murmushi

"Kawu ne yace mu shigo dasu,ku gyara waje don suna da yawa,a ina za'a ajjiye?" Wani yaro cikin yaran wanda shekarunsa suka dan dara na sauran ya fada yana sauke kwalayen hannunsa.

"Wai kana nufin rufai?" Bibo ta tambaya

"Indai shine aje masa inda yace,kada yazo ya yiwa jama'a tijara,bansan ma masifar data sakashi kawo mana kaya gidan nan ba,shi abinsa da baya tabuwa,tunda kudin cacar nan suka samu mu kuma bamu da kwanciyar hankali". Taja qaramin tsaki daada na gaban famfo tana tarar ruwa wanda suka kusa daukeshi don haka da qyar yake zuwa.

Tun tana irga adadin kwalin har suka fara yawa suka fara kuma shallake tunaninta. Tun daada na bandaki har ta fito tana daura alwalarta,sai bibo ta ajiya farantin waken tana cewa

"Wai rufai sai ya cika mana gida hankalinsa zai kwanta?,wanne irin kwalaye

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login