Showing 228001 words to 231000 words out of 557259 words

Chapter 77 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

422

abinda yayi niyyar fada din,sai kawai ya zame wayar daga kunnensa,qasan ransa yana fassara maganar farouq da kuma sakata a inda farouq din ke nufi

"God forbid" Ya fada qasa qasa. Hasashen gaba days banbarakwai yayi masa sanda ya dora tunanin a muhallin da farouq ke nufi,tattara tunanin yayi ya azashi a mizanin shirme gaba daya,ya fara lalubar number amna.

Sai data kusa yankewa sannan ta daga

"Hamma" Ta fada a shagwabe.

"Hamma ka manta dani.....adda tayi taking dinka away.....as far as yadda zata iya" Ta qarasa fadi da qaramar dariya a muryarta da ba sosai ta bayyana ba

"You amna.....lovey dovey will never be forgotten........hayaniya yayi yawa amna.......bansan haka ake abun ba"

"Hamma yafi haka fa.....don kaqi bada hadin kai ayi komai" Hannunsa ya dora a goshinsa yana furzar da qaramar iska. Shikam ko zancan bayaso,abinda yake gabansa kawai yanzun shine damuwarsa.

"Ya gidan?" Ya tambayeta.

"Full with 'yan biki dake jiran walimar anni......ina yini hamma" Ta hade amsa tambayar tasa da gaisuwa.

"Alhamdulillah.....how about anni da abba?"

"Abba dai ya fita tun dazun.....kuma ina jin sai dare zai dawo........anni tana daga baya da mutane"

"Okay.....bata wayar"

"Okay hamma" Ta amsa shi tana miqewa gami da ficewa.

Bai yanke kiran ba saita maida kunnenta,tana tafiya wajen annin tana ta bashi labarai kala kala. Bai yanketa ba yayi shuru yana saurarenta. Yasan halin amna sarai,bata gajiya sam sam da hira.

"Kice ameh ya kirani....."

"Okay hamma.....ga anni" Saita miqawa anni wayar,ta samu plastic chair daya daga cikin kujerun dake wajen ta zauna tana kallon yadda aka qawata wajen walimar da wani irin tsari me kyau,tamkar wani hamshaqin event center.

"Barka da warhaka anni......ya hidima ya rana?" Murmushi ta sauke,har cikin ranta farinciki yana mamayarta idan ta tuna a yau muhammad dinta ya zama cikakken magidanci

"Barka kade me babban suna.....mun tashi lafiya zance ko mun yammata lafiya?". Tambayar tata tadan sakashi yaji nauyi,kada itama fa ta dauka wani abune ya boyeshi,kada ta fassara wani abu na daban akan yarinyar ma da bai samu daman ganinta ba

"Lafiya anni alhamdulillah"

"Haka akeson ji.....na aika baraka takai muku breakfast da lunch.......nayita so nace idan ta isa ta hadani da d'iyata mu gaisa saina sha'afa......in tana kusa bani ita" Rasa abinda zaice yayi,yadan diririce kadan har hakan yaso ya nun alamu a muryarsa,yayin da annin ta dauka wani abunne na daban ya kawo hakan,kodai baiso aji muryarta a fahimci wani abu,don haka ta katseshi

"Kaga rabu da ita.....anjima idan kun iso wajen walima ma gaisa.....za'a fara immediately after asr prayer"

"Allah ya kaimu anni.....Allah ya qara girma da lafiya"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ta fada tana jin dadin yadda sam baya gajiya da mata addu'a.

Ita ta fara katse wayar,sai shima ya sauke yana kallon fuskar wayar. Inda anni ta sani data qyale walimar nan,duk da ita walima duk inda take albarka ce. Agogo ya kalla har daya na rana yayi,sai ya aje wayar yana jin zuwa yanzu ya kamata ya laluba kitchen ya samu koda tea ne ya sanyawa cikinsa. Duka wani abu daya saba sha da safe irinsu goji berries water da turmeric tea,cinnamon tea da sauransu,wannan ya sanya yake da wani irin cikakkiyar lafiya da kuzarin da idan ya shiga cikin maza kuzarinsa yake fita daban,kaman yadda yake da cikakkiyar lafiya irin ta d'a namiji,wanda yayi imanin banda busy da business daya saka a gabansa suka fatali da komai da yakeji......tabbas da bai isa yakai har wannan lokacin haka ba,dalilin da yasa ya janyewa amfani da wasu abubuwan irinsu ginseng tea,sai time to time idan yana da buqatar hakan,ko ya kwana biyu bai sha ba.

Fararen loopers slipper ya sakawa qafafunshi,wadanda suke mahadi ne na fararen pyjamas din jikinsa da suka fidda siga da surarsa. Yanayin fatarsa kadai ya isa ya fadi maka irin wadata da nutsuwa da yake ciki,skin dinsa so fresh da ba lallai ta wata macen ta samu irin wannan kyan da glowing din ba.

Sai daya shiga toilet ya daura alwala,ya dauki qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida takalmin ya nufi qofa yana gyara hannun pyjamas dinsa daya tattare.

A nutse ta idar da sallara azahar tana maida idanunta wajen sujjadarta. Tana jin idanun a jikinta sunyi mata nauyi,nauyin da bata raba dayan biyu yunwa ce da kuma bacci. Baccin kam tana da tsananin buqatarsa,ita kanta ta sani,saboda ita kanta tasan cewa taci bashin baccin yadda ya kamata,abincinne bata jin akwai muhallin da zata sakashi a cikinta,saidai jikinta na sake gaya mata ya zama dole ta nemeshi.

Dole ce ta sanyata miqewa,a nutse ta nade abun sallar,ta gyara yafen dan madaidaicin hijab din data dauko daga closet din nata ta daure igiyar sannan ta juya tana lalubar qofa bayan shawarar da zuciyarta ta bata nata duba cikin kayan da aka kawo ko zata samu abinda zata saka a cikinta.

A nutse ya sauko daga saman yana sake jin nutsuwa da gidan da tsarin gidan. Ya dauke idanunsa daga hallway din da yake kyautata zaton shiyyarta ne. Qofan dake damansa ya karya zai bude sai kuma ya fasa,ya koma ya kama handle din wooden door din ya bude yana isa ga falon.

Ko ina da komai yana nan kamar yadda ya barshi a jiya,da alamu ba'ayi amfani da parlor din ba kwata kwata. Zarcewa yayi parlor din farko wanda keda kitchen din,ya sauka daga kan step din a nutse sannan ya zarce zuwa dining da hake hango basket akai,da alama saqon da anni tace ta aiko ne.

Yana daga tsaye ya miqa hannu a mamakance ya jawo basket din,yadda aka kawoshi haka aka ajiyeshi,da alama ba'a ko budeshi ba ballantana a taba komai a ciki.

Waye to ya karba saqon ya shigo dashi?. Ba kowa sai ita wannan shine amsar daya bawa kansa,don ya sani ba wanda zaiyi gigin shigowa cikin gidan saboda sunsan doka da kuma tsarinsa. Duk wani ma'aikaci dake aiki a qarqashinsa,daga cikin company har zuwa cikin gida kowa yana tsayawa iya limit dinsa ne,ba wanda yake wuce qa'idar aikinsa ko kuma limit dinsa.

Komai anni ta zuba na duka irin abinda tasan yafiso yaci da safe ya kuma ci da rana,ya sauke qaramar ajiyar zuciya yana sake jin qaunar matar da martabarta suna hauhawa a zuciyarsa. Baiga wani abu da zai taba annin ya bari ba ko wayeshi,take sai yaji ransa yadan baci,ganin kamar ta wofantar da kayan da aka kawo din. Daidai abinda cikinsa yake buqata ya zuba,kafin ya gama duka ya bata wajen saboda rashin sabo,ya manta when last yayi serving kanshi,duk wani motsinsa akwai masi hidimta masa.

Tsaki kadan yaja ganin bacin da wajen yayi,ya soma wassafa yadda zai aje masu masa hidima cikin gidan kaman yadda ya saba,don bayajin zai bari ya takura har haka,ya dauko komai cikin qaramin serving tray ya dawo ainihin parlor din,sai ya azashi saman side table. Har zai zauna sai ya fasa,ya dauko remote yana lalubar channel din dake haska rate na dollar pounds da rate na diamond da sauran harkokin kasuwanci. Har yanzu yana cike da mamakin yadda abun ya kasance,duk da iya bincikensa har yanzu ba wanda yasan daga ina faduwar gold din haka rugu rugu ya samo asali.

Ya soma sipping pomegranate juice kenan idanunshi suka sauka akan basket din. Tun basket din jiya da farouq ya hadoshi dashi,wanda shi kansa baisan anihin meye da meye a ciki ba. Bacin ran da yaketa qoqarin boyeshi dole a wannan karon ya bayyana kanshi.

"What's all these nonsense?" Ya fada can qasa labbansa suna motsawa.

Kamar jira akeyi yayi tambayar yaji alamun motsin mutum. Fararen idanunshi ya daga still cup din yana saitin bakinsa,baikai bakinsa ba bai kuma dire ba,ya zube manyan idanunshi a kanta. Karon farko da ya fara mata kallon kai tsaye a rayuwarsa,karon farko da yayi mata kallon da zai iya gane face dinta.....don kuwa a baya zai wahala ya iya cireta cikin mata goma ko biyar idan aka zube masa su.

Kwata kwata bata lura da mutum ba sanda take sauka daga steps din zuwa qasa don nufar kitchen,amma da yake cikin dabi'arta akwai sanya idanu da kula da motsin komai da komai dake kewaye da ita,da kuma sanya hankalinta bisa yanayin kowanne abu saita dinga ji a jikinta kamar akwai wani baqon abu da babu shi dazu a parlor din. Juyi biyu ana uku idanunta suka sauka akan nasa........itama karon farko kuma lokaci na farko a rayuwarta datayi masa duba nakai tsaye.....duban dake rataye da abubuwa masu yawan da suka faru.

Wani nannauyan abu taji yana fita daga idanunshi zuwa nata yana neman kwarjanta mata shi da wani irin madaukakin kwarjini da bata taba siffantashi a dukka hasashenta dashi ba,sai ta janye idanunta daka kaf sashen da yake tana jin wani bala'e'en haushinsa yana sauka mata a hankali a hankali da wani yanayi me kama da tsanar mutum. Shine silar komai da komai,shine kuma maja ragamar kowacce kalar qaddara data sameta da kuma zata iya samunta a nan gaba.

Tashi zuciyar kuwa ta cika da mamaki a yanzun da idanunsa ke sake haska mata qarancin shekaru qarara dake tattare da ita. Wani irin qyanqyaminta da wasarta suna nasar zuciyarsa. A wannan age din nata da duka duka idan tayi wuta bai wuce ace tana level one ba......amma s irin shekarun har take da fikirar SATA SANE FASHI DA MAKAMI TA YANAR GIZO.....abu mafi muni kuma shine KARUWANCI BIN MAZA.

Wannan abu na qarshe daya tuna kadai ya sanyashi yaji zuciyarsa ta sake matsewa. Koda aboki ne dashi yake da dabi'ar neman mata......ba aboki ba,koda abokin kasuwancinsa ne kai muddin wannan din dabi'arka ce.....muddin kuma ta bayyana ya sani to yana haqura da huldar kasuwanci dakai.

"Zunubinsa daban dude......haka mu'amalarku ma daban.....shi da Allah wannan halin nasa,baka da ikon canzashi" Kadan daga cikin abinda Farooq ke yawan gaya masa. Harara yake balla masa wani lokacin

"Bani da sha'awar karbar kudi daga hannun ma'abocin sabon ubangijinsa,wattaqu fitnatalla tusibannal lazina zalamu minkum kaaassah(kuji tsoron fitinar da idan tazo bata shafar iya wadanda sukayi zalinci kadai a cikinku).idan kana neman albarka ubangiji cikin samunka....kayi qoqarin kaucewa masu saba masa,sai taka dukiyar tayi albarka". Irin maganganun nan sun jima suna fafatawa a kansu shida farouq.

Ji tayi kaman jikinta na neman rasa duk wani confidence.....hakanan batason wanzuwa a muhallin da yake fesar da iska tana shaqa,sai taji kamar wadda ya fitar ita take zuqa,don haka ta juya a nutse da zummar komawa inda ta fito,tana ji har cikin ranta ta haqura da duk uzurin daya fiddota.

"Ke!" Ta tsinci husky voice dinsa da bata taba jinta kamar haka a kusa kusa ba sai yau......karon farko kenan,wannan ya hadu da saukar tsawar tasa ya sanya gabanta wani mummunar faduwa.....kafin ta samu tayi hanzarin daidaita nutsuwarta da tattara dukka qarfin ta.

Zuciyarta ke qarfafarta kada ta tsaya.....salon kiran da yayi mata din zallar raini ne.......yayin da ta nashi gefen ya fita hasala.

Ya za'ayi ya kirata yarinya qarama irin haka tace zatayi ignoring nasa?,yarinyar da yayi imanin tsakanin musaddiq da saddiq ma babu sa'anta......koda ta girmi amna ma kuwa yayi imanin ba zata bata sama da shekara uku ko hudu ba.

"Na rantse qafarki ta sake taku daya daga nan saina kakkaryaki na zubar" Ya fadi a hasale,saboda abinda tayi masan bazai tuna mutumin daya taba masa hakan ba tun sanda sunansa ya shiga duniya a matsayin muhammad fu'ad jadda.

Batasan me yayi mata birki ba,har ta daga qafar zata taka step na farko saita mayar ta ajiye. Zuciyarta na mata wani irin suya a qirji. Ita yau sabreen wani d'a namiji ke kwatsawa tsawa har haka?,saboda kawai yana tutiyar ya aureta?.

"Dawo ki zauna!" Ya sake fada a kausashe har sai da taji kaman yana daf da ita ne.

"Ki sake na maimaita miki kuma....wallahi yau a cikin dakin karnuka zaki yini" Ya furta muryarsa na bawa me sauraro tabbacin da gaske yake.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 17


18


Wasu maqalallun hawaye da bata tsammacesu ba taji suna tsatsafowa daga cikin qwayar idanunta,tayi hanzari da gaske ta dakatar dasu cikin bawa zuciyarta umarnin

"Ba faduwa.......ba bada damar ganin lago.....i want to win". Abinda ya saka hawayen komawa kenan,saidai har yanzu tana jin alamunsu.

Ta koma ko ta wuce abinta?,duk abinda zaiyi ma yayi?,ko kuwa ta zauna ya lissafa nasa qa'idojin itama ta sanya mishi nata iyakokin?. Bata tantance wanda zata dauka ba saiga kira ya shigo wayartata. Kallon wayar kawai sai taji tamkar wata sabuwar barazanar ce ta shigo cikin rayuwarta,sunan matar datayi saving dai still shi yake yawo. Abisa son ranta bata da Sha'awar sauraronta.....amma bisa tilastawar zuciyarta sai taji ba zata iya tsallakewa kiran ba,a sanyaye ta daga ta saka wayar a kunnenta.

"Tun dazun nake zuba idanun ganin kiranki ai.....na dauka zaki nema taimakon abu na farko da zaki fara girkawa a gidan" Muryar maamah kenan da kalamanta na farko data fara jerowa baya ga amsa sallamarta da tayi. Idanunta data lumshe ya tilastawa boyayyun hawayenta saukowa,amma sai tayi hanzarin daukesu tana sauraren muryar matar.

"Na manta na gaya miki wannan ko zasu taimaka miki wajen cimma nasara........yana da zafin rai.....yana da kafiya,bayason raini bayason musu.......bayason qazanta........kiyi duk yadda zakiyi ki zama ke kike ci dashi......ki sadaukar da komai masa......ki qarar da tunaninki kan duk hanyar da zaki maido cin abincinsa hannunki.......wannan shine kadai abinda zai sama miki 'yanci....." Saita dakata kamar me shirin bata damar cewa wani abu kafin ta qara

"Idan kina da tambaya ko buqatar qarin bayani qofa a bude yake......zuwa anjima kina da baqi......saidai mutum daya ta qaru.....zan miki bayani a kanta.....af na manta na gaya miki.......dazu huda ta tsallaka shop din tsallaken titin gidanku fa". Mummunar faduwa gabanta yayi da ambatar sunan huda kawai a bakin maamah... Da gaske mutanen suke......sun mata tarko da 'yan uwanta,da gaske suke suna bibiye ne da rayuwar 'yan uwanta mahadin numfashinta?,da gaske kowanne motsi nasu a lissafe suke dashi?. Tabi maganar maamah ta tseratar da rayuwarsu?......a yanzu tana jin kamar shine babban haqqin daya zame mata dole ta sauke.

Batasan ya iso wajen ba,kawai abinda taji shine zare wayar daga kunnenta. Ba qaramin firgita tayi ba,saita waiwaya da hanzari tana fuskantarsa sanda ya zubawa fuskar wayar idanu lokacin da kiran yake yankewa da sunan mariya b'aro baro akai.

Ci gaba yayi da kallon fuskar wayar har sunan yayi disappearing yana sake maimaita full name din nata qasan zuciyarsa. Wani abu ya taso masa.......zarginsa yana daduwa daga kaso sittin cikin dari zuwa kasu casa'in da tara cikin d'ari.

A nutse ya maida qwayar idanunsa kan fuskarta,haka kawai taji qafafunta sunyi laushin da kafin ya sake cewa komai ta koma ta zauna saman kujerar dake daura da ita,tana mamakin yadda nature da colour na idanunsa suka sauya kadan.

Wayar ya cilla mata ta sauka daidai saman cinyarta,sai ya soke duka hannuwansa cikin aljihun wandonsa yana dubanta kai tsaye.

"Kada ki dauka zakiyi duka irin rayuwar da kikaga dama,kada ki dauka zakiyi kalar rayuwar da kikeso.....kada kuma mi rudu da cewa kinzo nan gidan don ki huta......ki debi adadin kudi da dukiyar da kikeso daga jikin muhammad jadda.....idan kin dauki duka wadannan abubuwan a ranki......" Sai kawai wani siririn murmushi ya kubce masa,ya cije redlips dinsa yana dage kafadunsa sama

".......kina ruwa" Ya qarasa fada yana jawo wata ottoman chair 'yar qarama zuwa gabanta yahau kai ya zauna

"Kisa a ranki nan kin shigo gidan tarbiyya da gyaran hali ne......gidan qare kukanka.......gidan bin daidai.......wadancan kayan duka da aka shigo dasu kin dauka a caca aka ciyosu?,ko kuma fashin yanar gizo da kutsewa account din al'umma akayi aka samosu da zaki bar komai cikin jakarshi?,salon idan ya lalace baki da asaran komai?" Wasu irin zafi sosai maganganunsa sukayi mata,irin zafin da bata taba kawowa ba. Ko mahaukaciya ce ita ta fuskanci inda batunsa ya dosa ballantana da hankalinta fes,zafin maganar ya tilastata daga oily eyes dinta masu sheqi dake shige da nasa ta kalleshi dasu.

Duka girarsa ya dage sama yana dubanta da fuskar da babu digon walwala ko sassauci a ciki

"Yes.......gidan nan dama komai da zai gilma a ciki zallar halak ce ta samar dashi.....so that bazan dauki almubazzaranci ba......dole ki kula da komai a daidai sanda ya dace da yanayin daya dace.....zaki zauna a cikinsa kiyi aiki irin na kowacce matar aure......zaki zauna a cikin gida

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login