Showing 387001 words to 390000 words out of 557259 words
kulawa.
"Ku debi abincin ku bita dashi" Anni ta fada. A gareta sai taji kaman chance anni ta bata na matsawa daga wajen,don haka ta motsa da nufin miqewa amma ya maidata ya zaunar da hanyar danne mata qafa. Idanunta ta daga ta kalleshi,sai ya dage mata dukka girarsa biyun yana tsare gida.
Dole taja bakinta tayi shuru gudun tashin tashina gaban anni
"Amna diba kikai mata" Fuad din ya bawa amna umarni kai tsaye,tana kallo amna ta shirya abincin musaddiq ya dauka mata wasu suka gangara zuwa dakin annin.
Koda ta shiga dakinma still numfashinta tana jin kaman baya isarta,sai ta kunna a.c ta dauki remote din ac din tana qure number qarshe,kafin ta qarasa gaban gado tana wurgi da dan kwalinta. Me yasa duk wani kafi da ta sanya aka mata baya aiki a kanta?. Ta tambayi kanta da kanta. Duk mutumin da zata daukeshi aiki cikin tafiyarta.....duk mutumin da zai ratso da kansa tsakiyar harqallarta sai ta tabbatar ta mallaki bakinsa da tunaninsa.....to amma ita me yasa ta kasa samuwa cikin tafin hannunta?.
"KINYI KUSKUREN ZABOTA......AKWAI NADAMA ME YAWA......TAURARINTA BASA TABUWA" Duka maganganun bokan suka dawo mata kamar sannan yake furta mata su.
Juyawa tayi tana neman zama daidai nan musaddiq dake gaba ya shigo amna na biye dashi.
"Anni ce tace a kawo miki daki,idan kin huta sai kici" Cewar musaddiq.
"Saboda ga mayunwaciya?.....shi zaki a jejinsa har sai an masa tayin abinci?,aisaidai abinda ya farauto yaci ya bawa sauran namun daji su qarasa abinda ya rage din" Ta fada tana makawa amna harara. Amna din bata ko daga kai ta kalleta ba,tadai qarasa ta ajiye tray din kusa da inda musaddiq ya ajiye nasa ta juya tana ficewa,sai shima ya soma bin bayanta ba tare da kowa yace komai ba.
"Kai musaddiqu zo nan" Ta kirashi a fusace ganin yabi sahun amna. Qofar ya saka zai dawo ciki ta watsa masa harara
"Rufen qofata shashasha mara kishin uwarsa,kaima ka soma hawa turbar dan uwanka ko?,an zagi uwarku shine zungui zungui zakabi bayanta?" Ta fada a matuqar hasale,a yau tana jin shi kansa musaddiq din ya zama silar faruwar wasu abubuwan. Yau inda ace ya bata goyon baya da nasarorin da zata samu zuwa yanzu sun haura haka.
Baice komai ba ya rufe qofar ya dawo ya zauna yana dubanta.
"Uban waye ya siyawa waccar karyar 'yan barikin waya me tsada har haka?" Ta fara jifansa da tambayar da tafi damunta. Fuska yadan yamutsa kadan yana maimaita sunan,hankalinsa ma gaza cafko ainihin wa take nufi.
"Kai maida hankalinka.....sabreena nake nufi" Cak tunaninsa ya dakata na wucin gadi cike da mamaki. Dama addan take kira da wannan mummunan sunan?.
"Hamma ne....amma ai ta cancanci abinda yafi waya ma maamah,tunda ita din matarsa ce,kuma yana da halin siya mata,uwa uba ma kuma tana da hankali da nutsuwa,ta cancanci fin haka ma"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.....kasan me kake cewa musaddiq?" Maamah ta fada cikin tsananin tashin hankali,idan har abinda kunnuwanta suke jiye mata lallai shima ya shiga tarkonta......sai taji gaba daya hankalinta yana qoqarin kubce mata. Amma da yake bariki iyawa ce,sai tayi qoqarin maida hankalinta gangar jikinta sannan ta zauna a gefansa.
"Amma meye amfaninka a gurinsa musaddiq?,dan uwanka yana irin wannan almubazzaranci da dukiya amma kana ganinsa?,ba zaka saitashi ba?,ba zaka hanashi ba?,ba zaka sanarmin ba don in daidaita al'amuransa ba?,wayar million saba'in wa matarsa uwarsa bata da ta ko million talatin?". Shuru kawai yayi maganganun maamah suna masa banbarakwai. Kai tsaye zai iya cewa ta jahilci rayuwarsu da gasken gaske,kuma kome zai gaya mata ba fahimtarsu zatayi ba,don haka ya zuba mata idanu kawai yana dubanta har takai qarshen maganarta. Da kanta ta sallameshi ta koma tana zama cikin matuqar firgici da bacin rai,zuwa yanzu tana kyautata zaton BOKAnta tabbas ya gaza.....yaqin nan da bakinta zata yishi,da dukka wata power irin ta uwa da Allah ya bata.
Wuni guda gaba daya bata bawa kwanyarta wani sukuni ba ko kadan,gaba daya tunaninta ta tattarashi akan yadda zata yanke wanzuwar sabreen cikin rayuwar d'anta. Zuwa sannan jikinta yana bata ci gaba da wanzuwar sabreen din bazai haifar mata da d'a me ido ba. A dukka shawarwarinta zuciyarta tafi rinjayarta ta bangare guda......ta raba auren ko da tsiya koda tsiya tsiya......da qarfi da yaji koda kowa hakan bai masa ba.....zata gwada qarfin qwanjinta da kuma adadin girma izza da nata ikon na uwa.
Wannan saqar data gama yi ita ta sanya ta fita cin abincin daren ranar da wani irin izza da cikakkiyar qwarin gwiwar samun mafita.
Ta samesu duka saman dining din,ta bisu da kallo daya bayan daya tana jin ciwon yadda annin ta samu daman hade kansu duka,yaran da suke nata da wadanda suke ba nata ba. Ta saki qaramin shu'umin murmushi qasan ranta tana bawa kanta tabbacin komai dab yake da qarewa.....muddin ta samu nasarar yage KASKA wato sabreen daga jikinta,sauran zata qarasashi ne da dukka qarfinta.
Kujera taja ta zauna tana shaqar iska d'ai d'ai,ta sake ware idanunta tana nan sashen da fu'ad yake saidai bata ganshi ba,ta buda baki zatayi tambaya ya shigo parlor din da nutsatsen takunsa.
Sanye yake da suspender da Fedora hat datayi matuqar masa kyau,tamkar wani baturen England,kunnensa maqale da earpiece amma dukka hankalinsa yana kan sabreen dake zaune gefe idanunta akan amna da wunin yau duka take more wayar sabreen din. Wani abu ya sosa masa zuciya,baisan wanne irin taurin kai gareta ba......koda wasa bai taba tunanin zata sanya qafa ta shure maganarsa ba,saidai nan kusa yayi imanin zai ladabatar da ita don duka cikin halinta shine hali guda daya da bazai iya jurarsa ba.
Kaman dai dazun anni ta sanyata tayi serving nashi,ta miqe a hankali daga gefansa tana qoqarin zuba mishi soyayyar shinkafar. Hannu ya sanya ya jawo cucumber a gefansa ya tura gabanta yana fadin
"Slice it" Ya fada da wani irin shanqamshi daya dan bata mamaki. Hannu ta saka ta jawota,ta dora saman plate ta soma yankawa. Sosai zuciyarta tayi zurfi a tunani,abinda ya janye hankalinta kenan har wuqar da take yanka cocumber din ta taba hannunta.
"Wayyo Allah na" Ta fada tana yarfar da hannu tana jin zafi da radadin wuqar yana shigarta.
"Yankewa kikayi adda?" Amna ta fada da sauri tana matsowa,abinda yaja hankalinsa kenan zuwa gareta daga kan wayar da yake latsawa.
"Ya salam" Ya fadi yana jin tsigar jikinsa na tashi da jinin dake biyo hannunta,har baisan sanda wayar hannunsa ta sulale ba maamah tabi wayar da kallo.
Tuni ya miqe ya kama yatsan da jinin ke fita yana kallo,har cikin jikinsa yakejin kamar shi ya yanke din.
"Me yasa bakiyi a hankali ba?" Ya fada yana zube mata fararen idanunsa. Kanta ta kawar gefe tana jin kallon nasa ya aza mata nauyi da yawa,uwa uba ga maamah a wajen da batason komai ya sake hadasu.
"Musaddiq......duba dakin anni ka samo mana abun wanke ciwo" Ya fadi yana janyeta daga tsakanin dining din zuwa kujerun falon ya samu waje ya zaunar da ita yanayin tsaye a kanta.
Da qyar maamah ta iya lalubar numfashinta,ya zama dole a yau ta datse wannan igiyar......ya zama dole ta bata ta kuma tarwatsa koma meye yarinyar ta qulla.....kowanne irin shu'umin malami ta samu ita mariya saita nuna musu qarya suke duka ita dashi din.
"Idan ya gama qaramar haukar......ka gaya masa ni uwarsa mariya ina kiransa zuwa dakina" Ta bawa musaddiq saqon don tana jin kota gefansu ba zata iya rabawa ba bare ta tsaya tayi magana da dayansu shi ko sabreen din. Kai tsaye hanyar dakinta ta nufa tana harhada hanya.....a yau koda sakin sabreen shine abu na qarshe da zata aiwatar a rayuwarta saita tabbatar ya afku kafin ranta ya fice daga gangar jikinta.
*_dan dan dan dan dan dan.........masu karatu.....uhmmmmm......bakina da goro.....zamu gani kuma......shin xai tabbata ko kuwa?,sai nace ku tara dani ranar litinin in sha Allah,na gode_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 96
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_*
*_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_*
*_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya qaruwa dasu?_*
*_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_*
*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*
*lace*
*kowanne nau'in shaddodi*
*yadika na maza da mata*
*mayafai*
*lafaya*
*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana*
*sarqoqi da agoguna*
*under wears*
*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*
*_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA YI KINA DORA RIBARKI?_*
*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_*
*Sassauqan farashi me ban mamaki*
*_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine muradinmu_*
____________________________
96
_An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A W,sai tace: dabi'unsa alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin kalolin kyawawan dabi'u dukka haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_
A nutse ya zaunar da ita saman kujerun yana riqe da yatsar tata tamkar wadda taji wani gagarumin ciwo. Sosai idanusa suka bayyana tsananin damuwa,ya tsugunna a gabanta a hankali idanunsa na saman fuskarta. Bata yarda ta kalleshi ba,tana ji kusancin dake tsakaninsu kaman yana sake yin yawa,tana ankare da yadda maamah tabar wajen cikin wani irin yanayi da yafi kama da zallar fushi da kuma fusata,a haka musaddiq din ya dawo ya aje masa qaramin akwatin yana komawa da baya don barin wajen kaman yadda sauran suka bari da d'aya da d'aya. Dukkaninsu wata kalar soyayya suke gani a shimfide saman fuskarsa,kaman yadda idanunsa basu boye komai ba.
Murmushi ya subucewa farouq din yana jin fu'ad yana sake tafiya dashi,duk da komai yasan yana yinsa ne ba cikin hayyacinsa ba saboda bugar dashi da giyar soyayya tayi.......ya sanya P_cap dinsa yana daukar key din motarsu ya saka a aljihunsa don fita dama ke garesu da daren ya soma sauka ta bayan kujerun yana barin parlor din,don shi kansa bazai iya zama yaga ya wannan love game din zai wakana ba. Wani sashe na zuciyarsa kuma cike taf da mamakin mode din maamah......fushin dake tattare da ita da saqon data barwa musaddiq. Ya jima yana wani tunani akan matar......ya dade yana wani hasashe a kanta,saidai a sanin da ya yiwa fu'ad ba zasu kasa hasaso abu guda ba.
Zama yayi sosai gaban nata yana fida spirit ya tsiyaya cikin wani dan abu na silver,ya tsoma a auduga sannan ya dago yana kallonta. Still taqi bashi daman kallonta. Wani irin yanayi takeji yana bibiyar zuciyarta kaman zai narkar da ita. Yau ita sabreen yankewarta a hannu ya zama damuwar wani?,wani baqon lamari ne a wajenta da batasan ya zata fassarashi ba.
"Kin shirya?" Ya tambayeta da wani irin sauti,kasa ce masa komai tayi sai ya dora audugar saman yatsan nata.
"Wash" Ta fada tana qoqarin janye yatsanta gami da runtse idonta.
Hanata daman hakan yayi,sai ya zubawa fuskarta idanu yana ganin yau d'aya wannan tsiwar ta tafi sai alamun rauni da radadi.
"Am sorry" Ya fada can qasan maqoshinsa da wani kalan sauti daban ba irin na dazu ba,abun daya tilasta mata bude idonta ta zubesu cikin nasa. Abinda yakeso dama kenan,sosai yayi qoqarin riqe qwayar idanunta cikin nasa,ya matso da yatsar saitin bakinsa yana busa mata a hankali,abinda ya hadu da sanyin spirit din dana bakinsa ya bada wani abu daya sanya tsigar jikinta zubawa,tanaso ta janye hannun ya hanata,hakanan dole tabar masa hannun tana jin yadda jikinta duka ya mutu.
"Ya daina zafin?" Ya tambayana yana dorawa kansa alhakin yankewartata. Kai ta gyada masa a hankali,burinta kawai ya gama yabar mata hannunta ya matsa daga kusa da ita din.
Tsaf ya gyara,saida jinin ya tsaya da fita sannan ya kammale komai,ya qwalawa amna kira ta qaraso.
"Ki dauke kayan.....ki kula da ita zanje na dawo,zamu taho tare da anni" Kai ta gyada tana tsugunna tana hade kadan gami da yiwa sabreen sannu. Kai kawai ta daga,ita bataga wani ciwo da taji wanda yakai girman sannun da take mata ba.
Hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana kallonta,har sai da amna ta gaya hada komai suka wuce dakin annin.
Ajiyar zuciya ta subuce masa,yana saqa abubuwa da yawa a kanta,sai sannan ya duba inda yabar farouq a zaune,baya nan,yasan kuma ya fita qilan yana jiransa cikin mota,don haka sai ya fara takawa a nutse yana barin parlor din ba tare da musaddiq daya basu space ya isar da saqon maamah ba.
A mota ya samu farouq yayi d'ai d'ai suna shan hira da fanna dinsa. Kusan duka hirarsu yanzu tafi rinjaye ne akan shirye shiryen bikinsu. Baice masa komai ba ya miqa masa hannu ya karbi key din motar ya shiga ya tayar da kansa suka fara fita daga gidan gaba daya.
Basuyi nisa sosai ba farouq ya kammala wayarsa,ya ajiyeta gefe yana cewa.
"Sai yanzu hankalinka ya dawo kenan?" Ya fada yana kanne ido daya da sigar tsokana. Waiwayawa yayi ya balla masa harara sannan ya dauke kansa,kaman bazai tanka ba sai daga baya yace.
"Ina baka shawara kaqi ji ko?.....ina gaya maka ka dauke idanunka daga kan lamarina ni da iyali na amma kaqi ji ko?". Sosai dariya ta zowa farouq,ya kuma soma yin abarsa yana cewa.
"Allahu akhbar......dadin abun ma muma mun kusa aje iyalin nan muji abunda akeji......muji ya giyar soyayyar nan take bugar da mutum" Qaramun murmushi ya saki daya sake fidda kyan fuskarsa yana duban hanya.
"Kota tashi bugar dakai farouq ba zaka ji abinda nakeji a kan sabrrr ba.....nata son daban yake a zuciyata......ban taba jin soyayyar abu a raina har haka ba.....bansan daga ina wannan qaqqarfar alaqar ke sake gina kanta ba duk wayewar gari zuwa faduwar rana" Yakai qarshen maganar yana furzar da numfashi a bakinsa.
Ido farouq ya zuba masa.......tabbas zuwa yanzu ya tabbatar da gaske MAHAUKACIN SO fu'ad din yakewa sabreen,irin soyayyar da bai zaci zata kamashi ba har ibada. Miskilancinsa da komai nasa na dabanne.......amma zuwa yanzu soyayya tana sauyashi zuwa wani mutum na daban,idan ya zauna yana masa magana akan yadda yakejin sabreen din cikin ranshi abun yana bashi mamaki sosai......yana jin kaman ba me babban sunansa ba,wanda komai da kowa basu dameshi ba idan ka cire su da anni.
"Inaji a raina da zuciyata......akwai wani abu cikin rayuwarta......akwai boyayyen abu.......i need to know farouq".
"Kabi a sannu........da sannu zakasan komai din". Kai ya gyada masa.
"Na sani......but am eager to know about everything about her......inaji kaman akwai sauran mutane daya kamata na hukunta bayan wadanda suke hannuna yanzu" Yayi maganar yana jin kalmar karuwa da kowannensu ya taba fada a kanta tana masa zafi har can qasan ransa.
"But naji maamah tana nemanka ma...." Farouq ya fadi yana tsoron kada fu'ad din yaji amma yaqi zuwa.
"Maamah kuma.......ba wanda ya fadamin" Ya furta haka kawai yaji gabansa yana faduwa. Ba kasafai kiranta ke zama alkhairi ba.....kai zaima iya generalizing cewa kiranta ba wani alkhairi ko abu me muhimmanci da d'a zai iya tsinta a cikinsa.
"Musaddiq ta fadiwa.....bansan me yasa bai gaya maka ba"
"Yabar parlor din ne......anyway koma meye zamu koma gidan.....saina qarasa" Ya fadi zuciyarta tana son lalubo dalilin kiran amma ya gaza.
Kai kawo ta dinga yi cikin dakin nata tana tattare kowanne tashin hankali da take ganin zata sauke masa har zuwa sanda zata tursasashi guntule igiyar jarababben auren data hada. Bata taba dana sanin aikata wani abu ba irin hada aurensa da sabreen......tabbas yarinyar tana neman zame mata qadangaren bakin tulu......itace cikakken ma'anar karin maganar nan da ake cewa DAN HAKKIN DAKA RAINA SHIKE TSONE MAKA IDANU. Inda qannenta suna hannunta kawo yanzu tayi imani da yaqinin da batasan ma wanne hukunci zata sakasu su karba ba a madadin 'yar uwarsu ba.
Minti daya zuwa goma sha biyar ta lissafa amma bataji shigowarsa ba,wannan ya sakata daukan wayarta ta kira musaddiq.
Ba'a daga ba amma taji an turo qofar dakin nata an shigo. Koda ta waiwaya musaddiq dinne,ajiye wayar tayi tana dubansa.
"Ina yayan naka?".
"Na shiga daki kafin ya kammala,ina fitowa na tarar sun fita shi da BB farouq". Wani irin kallo ta watsa masa cikin fushi tana qanqance idanu.
"Kasan me kayi musaddiq?!,kasan muhimmancin wannan kiran kuwa?....har yakai na baka saqo ka kasa zama ka jirayeshi ka isar masa?,kana hauka ne musaddiq!" Ta fada da wani yanayi daya bashi mamaki me kama da zata kai masa duka. A mamakance ya shanye mamakin yana yin qasa da kansa kafin yasake dubanta.
"Kiyi haquri,idan ya dawo saina sanar masa,ko ina sukaje nasan ba nisa sukayi ba".
" Baka da hankali.....bani da wannan lokacin,bani da Lokacin bata lokaci......wuce ka kiramin sabreen" Ta sake fada cikin daga murya tana nuna masa qofa.