Showing 366001 words to 369000 words out of 557259 words
yayi knocking,sai kawai ya dunqule hannunsa ya daki kujerar da yake kai,kafin yaja jikinsa yana miqewa.
Hannunsa yasa ya birkitota a tausashe,ta saka hannuwanta tana kare jikinta....saidai batasan sanda ta saki hannayen nata ta damqo hannunsa dake shirin yaye skirt dinta duka zuwa cikinta ba,wanda dama tuni ya tattare ya bayyana santala santalan cinyoyinta.
Birkitattun idanunsa ya zuba mata,kai take girgiza masa da guntun hawayenta. Bayani yakeson mata amma ya kasa,koda ya bude bakinsa ba kalmar data iya fita,har sai da yaja gyaran murya sannna ya samu maqogaronsa ya washe.
"Inason na gani ne ko dinkin ya warke......ba wani abu zanyi miki ba" Ya fada a tausashe. Kuka ta kuma saki tana jin wani rikitaccen yanayi yana mamayarta,duk yadda yayi mata bai isheshi ba har sai ya bankada sirrinta?.
Wani knocking da farouq din ya qara saki shi ya ratsa har kwanyarsa ya kuma dakatar dashi,ya kalli farouq din ta camera din yaji kaman yakai masa naushi ta ciki. A hankali ya saki skirt din,ya kuma zame hannunsa daga nata ya miqa hannu yana dagota,sannan ya taimaka mata ta maida kayanta gaba daya. Yana daga zaune a wajen ya dannan lock ya bude mata,ta sauri ta soma sauka ta fice tana kauda kanta ba tare data yarda sun hada ido da farouq ba.
Sai daya tabbatar ta fita ya sanyo kai ciki. Idanunsa yakai kan kujerar data koma qaramin gado,sai ya maida dubansa kan fuad dake zaune dafe da kansa da dukka hannayensa duka biyu farouq din zaiyi magana ya saka hannu ya bude daya side din motar ya fice da sauri,sai ya bishi da kallo sannna daga bisani ya sheqe da dariya,ya saka hannu ya dauke masa agogonsa da da alama baisan ya fice a hannunsa ba.
"Allah yasa ta haukataka" Farouq ya fada yana mimmiqewa abinsa saman kujerar abun yana masa dadi. Ba yaro bane shi,yana kallon wajen yasan da magana.
Kai tsaye ya wuce cikin gidan,Allah ya taimakeshi bai samu kowa a parlor ba,sai ya zarce zuwa dakinsa yana sauke numfashi cikin tsananin kasala. Tun a motar ya tabbatar wanka ya kamashi,ya fidda kayan jikinsa gaba daya ya wuce toilet ya sakarwa kansa ruwa me dumi. Gilmawarta kawai idanunsa suke ganin cikin toilet din,kowannw motsi nata......fitar hawaye cikin kyawawan idanunta da bai taba lura da wani irin tsaga da zubi da Allah ya basu ba sai yau......tausasan lips da tafukan hannayenta.....wani irin cikakken hips da bai taba ganin irinsu ba duk da cewa kallon mata ba dabi'arsa bace daman.
Sai da yaji nutsuwa tazo masa sannan yayi wankan ya fito,ya sake shirya kansa cikin wasu qananun kayan ya kuma ficewa.
Koda ya koma motar baiko kalli farouq ba,ya rufe murfin ya bawa Jordan umarnin ya tayar su tafi.
Bata iya komawa cikin gidan ba,saita zagaya ta baya can tana tattara nutsuwarta. Ta kusa mintuna talatin kafin ta samo kanta,ta sake gyara hijab dinta sannan ta wuce cikin gidan gabanta yana faduwa,tana fatan Allah yasa kada anni ta gane komai.
Kaman wata mara gaskiya haka ta tura qofar dakin tana saka kanta. Duban farko anni tayi mata ta tabbatar kuka tayi,sai ta dauke kanta kawai tana tattare kayanta ta fita ta basu dakin. Fitar annin yadan bata nutsuwa kadan,ta taka a hankali ta zauna saman sofa inda amna ke zaune tana buga game.
Bata cewa amnan komai ba don batasan me zata fada ba,gani take yarinyar itama ta karanci komai,kawai saita zame ta kwanta ta maida idanunta ta kulle. Ga mamakinta sai komai ya dinga dawo mata,zuciyarta ta dinga wani irin bugu sanda ta motsa taji jikinta yana fidda sassanyan qamshin nan nasa.
"Qamshin turaren hamma adda sabreen.....ko ya sammiki ne ki sanmin nima?" Amna data tsaida game dinta ta fada tana duban sabreen. Gabanta ya fadi,tadan ware idanunta kadan tana duban amna,saita rasa ma abinda zata ce mata,don haka ta juya kwanciyarta tana bawa amna baya sannan ta amsa mata da
"Bacci nakeji amna please". Qaramin murmushi ya subucewa amnan
"Ni na sani.....hamma na bazai qyaleki ba.....hamma na ba gama garin maza bane,saikinso hamma kamar ba gobe.....sai kinso hamma sama da komai da kike dashi" Amma a fili sai tace
"Ayi bacci me dadi tare da mafarkin hamma na" Tana jinta amma bata ce komai ba,tsoro takeyi kada ta fadi abinda zai sanya a gane komai tattare da ita.
Har suka soma daukan hanya ba wanda yace da kowa komai,sai daga bisani fuad din ya gyara zamansa yana tambayar farouq ba tare daya kalleshi ba
"Ina zaka ne ka shigo mana mota?" Yayi maganan a dake,wanda duka farouq yasan yayi ne don borin kunya kada ya sake masa magana kan abinda ya shigo ya tarar.
"Kai ina zaka?"
"Vaadhoo" Ya amsa masa kai tsaye.
"Me zakayi ne a Vaadhoo?" Farouq ya tambayeshi yana duban.
"Gurin fareeda.....but don't ask too much" Ya amsa masa a gajarce. Bai iya qarya ba.....shi yasa ya masa kandagarki. Motsawa kadan farouq yayi,yaga fareeda a ranar kafin su baro vaadhoo din,kuma jikinsa haka kawai ya bashi akwai abinda ya faru. Ba kasafai ya fiya son barin fuad idan yana fushi ya dauki.mataki akan mutum ba,shi yasa fitowar da yayi ya zargi wani abu ya kasa zama ya biyoshi,ya Tabbatar indai wani abu ne ya hadashi da fareedan bazai barta tasha da kyau ba koda waye ubanta,to amma sai yakama bakinsa,baiso yace wani abun farouq din ya sauya shima.
_uhmmmm.....fareeda?.....ga maza nan gareki....malam farouqu ko muhammad jadda zai barka ka shiga har inda zaije din?,bari mu gani_
_maza maganin maza....da d'aya da d'aya komai zai fallasa_
_ina muku barka da litinin da cikakken yaqinin mun dawo sai munga abinda ya turewa buzu nadi,na gode_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 86
86
Idanu sosai farouq ya zuba masa,kaman zaiyi magana sai ya fasa ya maida kansa kan wayarsa sukaci gaba da chart da fanna. Abu daya ya sani shine,bazai bar fuad ya qarasa wajen fareeda shi kadai haka kai tsaye ba,don yasan halinsa sarai.....bai iya daukan abubuwa serous ba.
Jifa jifa suke maganganu da suka shafi kasuwanci,wanda saisun samu dama irin haka sukeyi,duk da kusan shirun fu'ad yafi yawa. Har yanzu tsigar jikinsa zubawa takeyi idan ya tuna abinda idanunsa suka gani tattare da ita karo biyu kenan,har yanzu yana jin kowanne sassa nata cikin hannunsa da jikinsa kaman suna tare.
"Anya zan iya barinta for 2months kuwa?" Ya tambayi kansa cikin shakka da kokwanto.
Ba jimawa suka isa Vaadhoo suka kuma wuce glowing beach. Wayarsa ya ciro a nutse,ya rubuta gajeran saqo ya turawa mutum biyu sannan ya maida wayar aljihunsa yana gyara zamanshi. Yasan manufar farouq.....yasan meya sanya ya biyoshi,shi kuma baya fatan abinda zai rageshi ko ya hanashi cin uban fareeda la'ada waje. Zarginta yake dari bisa dari akan wasu abubuwa da dama,yana da tabbacin zaiji abubuwa da dama daga bakinta akam sabreen. Ya shirya kare mutuncinta da martabarta,ya shirya tsaya mata a duk inda ake buqatar wanda zai tsaya maka......ya kuma shirya nunawa duniya ita din matarsa ce kuma iyalinsa ce dake da kima mutunci da martaba kaman kowacce mace.
A hankali motar ta dinga ratsa farin yashin da bame yawa ba,kasancewar sasannin tsibirin ruwa yafi yawa,ba kasafai kake doguwar tafiya bisa mota ba saidai boat boat.
Kyakkyawan parking jordan yayi,fu'ad ya sanya hannunsa ya bude motar yana sanya qafafunsa waje. Budewa farouq yayi shima ya fita,ya zagayo gefan fu'ad din sannan suka fara takawa zuwa muhallin da aka tanada saboda zaman shan iska. Da idanu ya yiwa jordan alama,sai yaja baya ya barsu su biyun har suka isa saman kujerun. Suna zama wasu Maldivians guda uku suka qaraso. Cikin harshen dhivehi daya kasance yaren qasar,biyu daga cikinsu suka zauna dayan ya juya zuwa sashen da aka tanadi abubuwan sha saboda baqi. Ba jimawa ya dawo ya zube musu halal drinks da ruwa da gasashen kifin da aka wadata da vegetables da da lemon. Agogon hannunsa fu'ad ya kalla,yaja baya yana miqewa.
"Ina zuwa" Ya fada yana basarwa,hankalin farouq yakai kanshi,amma maganan da daya daga cikinsu ya masa cikin harshen turanci ya dauki hankalinsa,ganin fu'ad din gaba kadan ya matsa yana waya bawai gurin ya bari ba gaba daya sai ya maida hankalinsa kan mutumin,saboda ya masa magana akan abinda ya shafeshi ne wato harkar noma da Samar da iri da taki na zamani. Sannu sannu ya bashi hankalinsa sosai saboda hirar tayi masa,da wannan fu'ad ya samu ya zille abunsa ba tare da farouq ya ankara ba.
Yana takawa zuwa dakin shida Jordan ranshi na sake baci. Ya tabbatar a ranar akwai abinda yasha......akwai abinda ta bashi. Yaya akayi ma tasan dakin daya sauka?,har ta samu access da dakin cikin sauqi?,bayan wajen ya sani wajene me tsaro da matuqar sirri.
A lokacin tana zaine d'ai d'ai saman gadon tana busa shisharta. A kwanakin shisha kawai take bugawa cikinta ta hada da syrup. Tuni ta kori lubna daga dakin,saboda tana jin bata buqatar kowa a kusa da ita. Tana buqatar abinda zatayi refreshing damuwarta kafin tasan abinyi next. Bata taba tunanin zata hadu da asara da faduwa ba irin wannan,ta dauka komai zai tafi daidai,musamman data san cewa ba qaramin dosage ta sanya a zuba masa ba. Sai gashi cikin mintuna qalilan komai ya wargaje,tsananin taurin kansa da kafiyarsa ya hana komai yayi tasiri.
Tun bai murda qofan ba qamshin flavors din ya soma masa maraba,ya yatsine fuska rai bace yana isa qofan. Duk da wajen mutane da yawa flavour na shisha qamshi yake musu.....amma tsananin yadda ya tsani shaye shaye ya sanya shi a wajensa baida maraba da warin wiwi. Daga ranar kuma da bincike ya tabbatar da zuqa daya na shisha daidai yake da ka shanye sigari kara dara biyu ya sake mata muguwar tsana,inda Allah ya rufa musu asiri kaf dinsu Allah ya duba addu'ar anni a kansu,babu me shan komai koda shishan da wasu suke mata kallon ba abar shaye shaye bace.
Kallon farko da suka yiwa juna ita dashi,ita din saita dauka cikin gizanniya take ganinsa bawai me jadda bane real ain. Ta ajiye tiyo din shishan tana miqewa zumbur farinciki yana ratsata,wata mayaudariyar zuciya daga can cikin qirjinta tana gaya mata
"Ya rasa me kashe masa wutan sha'awarsa.....har yanzu abun na ruruwa a jikinsa shi yasa ya dawo miki......ya tabbatar ke zaki iya masa wannan aikin" Da wannan yaudararrun kalaman ta soma tafiya da sassarfa tana nufarsa fuskarta da shimfidaddiyar fara'a. Saidai kuma dab da zata isa gareshi ya qare yatsunsa biyar ya sauke mata wasu lafiyayyun maruka guda biyu qwarara hagu da dama,marukan da suka sanya kowanne connection na jikinta tsayawa na wucin gadi kafin komai ya dawo mata aiki.
Sai a sannan sashen dake gaya mata gaskiyar komai ya fara aiki,ta lura da wani lafiyayyen bala'i dake kwance saman kyakkyawar fuskar da a yau ta juye kaman ta mayunwaci kuma fusataccen zaki.
Nuni kawai ya mata da hannu na wajen zama,ta kalli gurin sannan ta maida dubanta kanshi zuciyarta na mata wani irin zafi. A yau ita fareeda Khalid mustapha wani d'a namiji ya sanya hannunsa saman fuska.....isashiyar macen da mata da dama suke buri gami da fatan hawa matsayinta?......macen da batasan adadin mazan da tayi rejecting ba da suke fatan mallaka mata komai nasu don ta kasance tare dasu?.
"Ni ka mara?" Tayi tambayar da yanayin dake nuna tsananin zafin da marin ya mata,bawai ga iya fuskarta kawai ba.....har cikin zuciyarta da ruhinta.
"Kina buqatar qari ne?" Ya tambayeta yana dage dukka girarsa guda biyu,hannayensa xube a aljihun wandonsa don ya tabbatar idan ba hakan yayi ba zai iya rufeta da mahaukacin duka. Shi kuma bai shirya aza hannunsa saman qazamin jikinta ba.....don bayajin ta samu wannan darajar. Marin da yayi mata dinma ya gaza shanyewa azo gabar ne,yana kuma son bata alamun cewa gagarumin bala'i ne ta daukowa kanta da bata da qarfin ikon tarewa kanta shi. Taku ukun da yayi yana jifanta da wani qasqantaccen kallo ya sake rage tazarar dake tsakaninsu sosai,wannan ya qara yawan kwarjininsa cikin idanunta,ya kuma sake qara mata tsoronsa. Abinda tafiso a rayuwarta shine ya kusantota,amma a yanzun da ya kusantota din sai take jin kamar wani baqin kumurcin maciji ne yake nufota.
Da hannu ya sake nuna mata seat yana zube mata idanun nan nasa dake da wani ajiyayyen kwarjini na musamman,wannan karon ba musu ta koma da baya ta zauna,saidai har qasan ranta tana rubuta abinda yayi matan a matsayin yaci bashi.
Gabanta ya iso yaja kujera dab da ita ya zauna,har tana jin fesowar qamshin sassanyan turaren nasa. Bata taba tunanun kwarjininsa yakai haka ba sai a yanzu daya sake kafeta da idanunsa da suka qara girma,ya zuba mata idanu kaman bazai daina kallonta ba. Ba abinda yake gani tattare da ita sai wata mummunar mace maras aji da kuma fasali idan ya dauko hoton fuskar sabreen dinsa ya kwatantata da tata. Wata ballagazar mace da babu wani abun burgewa qwaya daya tattare da ita.
"Tambayoyi ne zan miki su da bansan qwaya nawa bane,amsarsu kawai nake da buqata.......samun amsoshinsu sune kubutarki.......ki manta ubanki waye da farko.....sannan kema ki manta wacece ke......kiyi tunanin makomarki da abinda zai iya faruwa dake.......ki manta kin bawa mariya ahmad kudade don ta mallaka miki Muhammad fu'ad....." Ya fadi maganar yana jin wani d'aci yana tasowa daga qasan zuciyarsa,yana jin zuciyarsa kuma ta matse waje daya. Da wani irin zafin nama ta bude idanunta a kansa tana mamakin ta yaya yasan da wannan deal din?.
Sai daya hadiye abinda ya taso masan sannan yaci gaba da magana.
"Baki da wani ko wani abu da zai iya mallaka miki wannan muhammadun har abada" Ya sake fadi yana nuna qirjinsa da yatsarsa.
"Koda babu ameenatu sabreen a gefe na......ballanta tana cikin DUNIYATA tana cikin rayuwata....na tsere miki tserewa ta har abada.....bama keba,duk wasu mata ire irenki......WAYE YA BAKI DAMAN KIRAN MATATA DA KARUWA?.....WAYE YA BAKI WANNAN LASISIN?" ya mata tambayar farko da ita tafi tsaye masa a wuya fiye da kowanne abu.
Wata irin wutar kishi ta taso mata,ta kuma yaudareta da cewa ya zauna ne yaci fuskarta kawai......ta yaya tana cikin jerin masoyansa zai zauna yana mata tambaya akan wata mace da batajin ta fita komai?.
"Au bakasan karuwa kowa yake kiranta ba?,bakasan karuwa ka aura ba dama?". Ta fada tana danne tsoron dake taso.mata,saboda yadda zuciyarta ke qarfafa mata gwiwar idan yaga tsoro a idanunta to tabbas ta karya lagon kanta da kanta.
Labbansa na qasa ya cije yana kausa kansa daga fuskarta,kalamanta suna qonashi da wani irin zafi.
"Jordan" Akwai yace yana dunqule hannunsa waje daya,saboda bayason yakai hannunsa kan qazamin jikinta.
Taku daya jordan ya qaraso bayanta,wanda kwata kwata bata kawo komai a kiran nasa da yayi ba,ba zato ba tsammani taji an take yatsun qafarta an kuma murjesu da kyau har sai data fasa wata qara tana jin azaba tana ratsata,qarar yatsun kuma suka baqunci kunnenta da qas....qas.....qas...daya bayan daya,tabbacin qasusuwansu ne suke rarrabuwa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
EID MUBARAK TO YOU ALL
ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEN SUMMA AMEEN
SHUKRAN JAMEE'ANππ½ππ½ππ½π₯°π₯°π₯°
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 87
87
"Ka dagani......ka sakeni!qafata.....qafata" Ta fada a mugun rude kuka da fitsari dukka yana qwace mata lokaci guda,sake take dayar yayi sosai yadda itama yasan zataji a jikinta ba alamun tausayi sam a tare da jordan din. Sai daya kalli fu'ad sannan ya bada damar ya matsa baya,ya dauke qafarsa yana cewa.
"Kiyi magana dashi da manners.....kiyi magana dashi in a polite way......idan ba haka ba kafin bincike ya kammala duka sai na kusa dake sun kasa ganeki". Ko jordan bai fadi haka ba ta fahimci abinda ke shirin faruwa kenan.
" Shut up!" Fu'ad ya daka mata tsawa yana kallon yadda ta sauya launi tun karon farko.
"Wannan shine ya baki qwarin gwiwar buga sunana dana matata a jarida?.....bakisan ta fiki daraja ba?,ta fiki mutunci......ta fiki duk wani abu da mace ke jin tana taqama dashi ba......su wadanda suka baki shawarar aikata hakan basu gaya miki waye muhammad jadda ba?!" Ya jefeta da tambaya yana jin wani tururin bacin rai yana taso masa.
Tayi matuqar rudewa,ta kuma girgixa qwarai da gaske. An gaya mata....ma'aikatan ma sun gaya mata,da qyar ta samu suka yadda zasuyi aikin. Sun jaddada mata waye