Showing 348001 words to 351000 words out of 557259 words

Chapter 117 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

537

musaddiq......kukan musaddiq a duk dare sanda maamah ta tafi ta barsu.....kukan abbansa sai ya zama abu mafi tsanani da azaba daya taba gani.....wadannan abubuwan suka sanya ya tsani kuka ainun.....duk da yana da tsananin dakiyar nuna bai dameshin ba.

Hannunsa ya dora saman goshinta don cire mata gashin daya sake lullube mata goshin,yana jin kowacce kalma ya debo saita qwace daga bakinsa.......yanajin duk duniya ba wata kalma harshe yare ko lafazi da zaiyi daidai da kunnuwanta idan ya fadesu......shi a karan kansa yakejin kamar ba'a qirqiri wata kalma ta ban haquri da ta dace ko zata dace da girman laifinsa ba. Da sauri ya janye hannunsa yana jin yadda fatar jikinta ke fidda wani irin huci kaman yadda jikinsa ke fitarwa

"Ya salam.......ya salam......am sorry,i hurt you sabrrr......Am sorry.....i hurt you,I'll do everything possible to make you feel better" Ya fada yana neman yadda zai gyara mata zamanta a jikinsa. Jinginarta a jikinsa jinta take kaman wani nau'in azaba na daban,batasan yadda wata rai zata fahimci yadda takeji ba.....tana jin kamar zata sake suma ne,don numfashinta sam baya kaiwa hunhunta yadda ya kamata. Tanaso ta gaya masa ya janye jikinsa daga nata amma ba wannan bakin,sai kawai kukanta ya qaru akan nada,abinda ya sake hargitsashi kenan.

A zahirin gaskiya baisan yadda zaiyi mata ba don baisan yadda akeyi ba,hasalima shi bai taba zama yayi tunanin zuwan rana irin wanna ba a nan gaba a rayuwarsa bare ya nemi ilimin yadda akeyi ba.

Jikinsa ya zame yana jin yadda zazzabi ke dafa qasusuwansa......amma tashin hankalin jinin da yake gani daga jikinsa ya dame wannan. Wayarsa ya dauka,sai ya samu kansa da rasa wanda zai kira.....wazai kira?,wa zai gayawa?,yace masa me?.

"Farouq" Kawai shine sunan daya fado masa. Bai damu ba da yadda farouq din zai kalli abun.....abinda kawai ya dameshi yadda zai ceci ranta daga ta'addancin daya tabbatar yayi mata. Idan ya daga kai ya kalli inda jinin ke kwance sai yaji ya aikata baqin fasadi ne kawai yau a daren nan,qaramin kisan kai kawai yakeji ya aikata.

"Hello......zamu kwana ne....wajen nan fa yayimin,ina tunanin dawowa nida fannah....."

"Am at home" Kawai ya fada da wani irin sound da yaja hankalin farouq din. Aje yanayinsa yayi gefe da wasan dake cikin muryarsa ya bawa fuad hankalinsa

"Is something wrong?" Ya fada da tsananin kulawa a muryarsa. Sai daya runtse idanunsa sannan ya budesu yana maidasu inda take kwance sannan yace

"Yes farouq......a rude nake.....please help.....i don't know what to do"

"You are not alone......am here to help,take your time and tell me what's happening?" Farouq ya sake fadi cikin yanayin kwantar da murya.

"We had our first night farouq......i caused her serious injury" Ya fada da tsananin nauyin abinda yake fita daga bakin nasa,saidai kuma ya zama dole yayi hakan,don gani yake kaman tana dab da komawa sumanta.

Wutace ta daukewa farouq din. Shima maganan ya masa dan nauyi kadan,duk da ya jima da sanin duk wadda zatayi irin wannan karon da fuad din abun bazai zama da sauqi ba. Don ya bashi relief sai yace.

"Relax....ina zuwa". Yana sauke wayar daga kunnensa. Murmushi kadan ga qwace masa duk da qasan ransa tausayin adda sabreen ne fal. Yasan za'a fuskanci hakan daga fuad din,duk da tsananin wayewarsa da sanin lunguna da saqo na qasan duniya.....gogewarsa da mmu'amalarsa da kalar mutane daban daban jinsi daban daban......amma yau saboda tsananin kamewarsa da zame kansa daga dukkan wani batu ko sabga data shafi wannan fannin ya rasa yadda zai taimakawa matarsa. A ransa yaji tabbas ciwon ba qarami bane tunda yaji damuwa sosai a muryarsa.

Ya jima yana kallon number wayar anni ta qasar yana kwatanta yadda zai kirata ya gaya mata. Wannan din wani training ne nata data musu. Ko.meye nasu idan ya samesu komai nauyinsa bata yarda wani ya fara jibantar matsalarsu ba kafin ita bare a nan din baisan waye zai kira ba,dole ya koma ya shiga sms ya tura mata saqo kaman haka.

_"Muhammad yana dakinsa......he needs your assistance"_ yana tura mata ya aje wayar,don bayason ta kira neman qarin bayani don wabillahi baisan ya zai mata shi ba.

Tsaiwa cak yayi kuma wani abu yana dawo.masa da baya.

"Ya akayi first night yazu musu da hakan if ba virgin bace?" Ya raya maganar a ransa,sai kuma yayi saurin kawar da ita don shi ya jima da qaryata duk wani hasashe na fuad tun ba yau ba.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 76


76


Sanda saqon ya iski anni dawowarta gidan kenan,tazo ta samu gidan ba kowa basu dawo ba. Daki ta wuce ta sauya kaya ta dauki wayar tana fitowa parlor da zummar kiransu taji me ya kaisu yin dare bayan tayi warning dinsu kan hakan kafin su tafi?. Jiya sam bataga sukuni ko walwala saman fuskar fuad ba,kuma tana ankare dashi,yadda ya kasa ya tsare a falon,bai koma daki ba sai bayan dawowarsu. Tasan yana da zurfin ciki sosai,ba kasafai ka fiya sani ko gane abinda yake damunsa ba,amma ita din uwace,koda wanne yare sukayi magana su dukkaninsu tana iya fahimtarsu.

Shigowar saqon ya dakatar da ita daga qoqarin kiran nasu da takeyi

"Wani sabon sakarcin ne kuma haka?" Ta fada tana zama saman kujera da gorar ruwan dake hannunta ganin me saqon farouq ne.

Sau biyu tana maimaita saqon,tasan tunda ya fada da gaske fuad na cikin gidan,duk da bataji alamun akwai kowa ba a ciki,amma sai kuma saqon yaja hankalinta. Cikin fargabar kada wani mummunan abu ne ya faru dashi ta ajiye gorar ruwan tana maida hijab din jikinta,ta miqe idanunta kan qofar dakin,ta taka a hankali ta isa qofar.

Knocking ta fara yi,knocking din farko ya sauka kunnuwan fuad dake tsugunne gaban gadon yana monitoring numfashinta,gani yakeyi ko yaya ya matsa zai iya sauke idanunsa a kanta ya tarar ba numfashi tattare da ita.

"Waye?" Yayi namijin qoqarin tambaya

"Anninku ce" Ta fada a nutse. Idonsa ya lumshe ya kuma bude duka lokaci daya yana furta

"Rabbi yassir wala'ta'asir.....ya salam sallim" Yana jin kaf rayuwanshi idan ka debe rayuwar da maamah ta jefasu y taba shiga tashin hankali irin na yau ba. Baisan ta yaya zai bari anni ta shigo ta gansu a haka ba duk da zuwa yanzun ya saka Moroccan jallabiyya a jikinsa tun sanda ya kira farouq. Ita dince sam jikinta yaqi tabuwa masa,da yakai hannu kusa da ita sai maga ruwan hawayen dake idanunta yana qaruwa,ba bakin magana sam sam a tare da ita,amma duban data masa guda biyu tal ya karanto wani irin fushi da kyara a tattare da ita.

"Ki taimaka please.....ki bari ko riga na saka miki" Wani fusataccem fushi ne ya sauko mata,ya saka mata riga bayan ya gama ketata ya kuma keta haddi da duk wani mutunci nata da take taqama dashi,ta kuma killaceshi tsahon lokaci?.

Yadda ta maida idanunta ta kulle ba tare data ko motsa ba ya tabbatar masa bata buqatar ganinsa ne gaba daya,ga anni na tsaye a qofa dole bazai yiwu ya barta tanata jira ba,haka ya doshi qofar can qasan ransa yana fadin

"Me yasa kayi haka farouq?" Yana qiyasta da wanne idanu zai daga ya kalli anni?.

Fuskarsa kawai ta kalla da yadda ya bude qofar cikin rashin karsashi tasha jinin jikinta.

"Kana lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da ido. A yau dai ko karen hauka ne ya cijeshi baya jin zai iya kallon idanun anni bare ya mata bayani. Ratsewa yayi gefe da alamun bata hanya. Itama batace komai ba,ta maida dubanta ne daga cikin dakin tana hango iya abinda zata iya gani din wanda carpet ne da dressing mirror kawai take iya gani,sai ta maida dubanta kan fuskarsa da a yau yakejin idanun anni tako ina a kansa da wani irin nauyi. Batace komai ba itama ta ratseshi ta soma takawa cikin dakin,wanda taku biyu kacal tayi shi kuma ya fice yana laluben inda zaije ya aje kayan kunyanshi nesa da annin,saidai a taku na hudu idanunta suka sauka akan Sabreen,jinin dake jajur yayi staining jikin duvet da comforter din ya marabceta,cikin qasa da second uku ta fahimci me ya faru.

"Subhanallah" Ta fadi tsigar jikinta yana tashi. Tasan ko meye ya faru a wajen artabu akasha ba kadan ba,ko tayi taurin kai yaje mata da dukka qarfinsa,qarfin da sam sam tsakanin nata da nashi baizo daya ba.

"Muhammadu......maida qofar nan ka rufe" Annin ta fada da madaukakin sauti sanda yake dab da bakin qofar parlor din. Cak ya dakata da abinda yakeyi din,ya maida qofar ya kulle kaman yadda anni ta buqata,ya dawo kuma a hankali cikin parlor din yana laluben wajen zama. Gangar jiki duka da zuciya sai yakejin kaman ba tasa ba,zafin zazzabi yana ci gaba da lullubeshi yana raunana jikinsa,saidai yadda kunyar anni ta rufeshi tafi masa nauyi akan zazzabin.

A mamakance take isa gaban gadon

"Ikon Allah" Tafada qasan ranta,wato ita dake lissafin ganin result ta hanyar dauka jika,ashe karatunma sai yanzu aka farashi?.

Sautin muryar anni cikin dakin sai tayi fatan inama qasa zata tsage ta wuce ciki?,yanzun yana da tsaurin idanun kiran ummansa taga barnar da yayi?,wanne irin terere ne wannna yaja musu?,anni fa.....anni,ya manta surukarta ce?,ya manta akwai kunya me girma tsakaninsu?.

"Subhanallah......ya salam" Anni ta.maimaita wannan karon a sarari saboda jinin data gani muraran daya wuce wanda ta hanga daba bakin qofa. Dukka jikinta yayi sanyi sosai,ta tabbata babban barna muhammad din yayi.

"Sannu......tashi a hankali ki qarasa bandaki" Anni ta fada tana kamata da tsananin takatsantsan ta yadda zafin ciwukan jikinta ba zasu dameta da yawa ba.

Wata siririyar qara sabreen din ta saki,qafafunta kuma suka lanqwashe tilas ta koma ta kwanta duk da anni riqe take da ita. Hawaye ne ke fita ta gefen fuskarta,tsananin tausayinta ya kama anni. Bata taba kawowa muhammad xai gwada rashin haquri irin haka ba,dole yarinyar tana buqatar motsawa ta gyara jikinta kafin ma a samu bakin zaren gane iya adadin barnar data afku.

Yana daga falon amma.yana iya hangensu saboda a bude anni tabar qofar,uwa uba yana zaune saitin wajen,saidai yayi kaman bashi a wajen.

"Muhammadu" Anni ta kirashi kai tsaye,ya amsa yana tasowa. Idanunshi a kanta yana sauraren bayanin anni.

"Akwai ruwa me dumi a toilet.......ka kaita ta gyara jikinta tukunna.....ina zuwa" Anni ta fada tana nufar qofa don itama zuwa yanzun kunyar ke neman kayar da ita.

Hakan yayi masa,yabi bayan annin ya maida qofar ya murza key,sannna ya tako zuwa ciki yana nade hannun rigarsa. Sai yanxu kwanyarsa ta fara dawowa aiki,bazai kuma saurareta ba zaiyi kaman yadda anni tace,zaiyi yadda ya dace,dom haka yana qarasawa gabanta ya sanya hannu ya dauketa cak kaman jaririya haihuwar yau,ya lullubeta cikin qirjinsa yana wuce toilet din da ita.

Yana jin yadda ta damqe hannuwansa da kyau,da alama haushin dake cikin zuciyarta ne takejin kamar riqon tsaurinta a garesa zai sassauta abinda labbanta da bakinta ba zasu iya fada a yanzu ba.

Sake yaye mata dukka suturar jikinta yayi,ta sake runtse ido abun yana mata zafi. Cikin wasu mintuna jikinta ya zama bayyananne a wajensa?,yana qare mata kallo haka kanshi tsaye da kaifafan idanunsa da takejinsu a kanta?.

"Bazan kalleki ba indai har bakison hakan.....zan kulle idanuna har saikin bani izinin na budesu" Haushi da takaici suka lullubeta,harara takeson jefa masa zazzafa amma bataji idanunta suna a daidai din da zai ga harara tata yadda ya kamata. Banda ya raina mata wayo yana tsare yana qare mata kallo da wani irin yanayi dake qara kashe masa gangar jiki.....amma kuma yana gaya mata zai kulle idanunsa?, daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa ta furta a ranta.

Sake dagata yayi cak ba kuma bata lokaci ya sakata cikin bathtub din da anni ta hada ruwa me dumi qwarai. Wahalalliyar qara ta saki da muryarta dake nuna duka qarfinta ya qare.

"Ka sakeni....ka cireni a ciki" Ta fada hawaye na layi bibbiyu akan fuskarta. Wani irin narkewa zuciyarsa tayi da tsananin tausayinta da bai taba jin irinsa akan kowacce diya mace ba idan ka cire anni da amna. Saidai ko kafin ma yayi mata yadda tace ta sake masa wani zazzafan cizo a hannunsa dake dafe da tub din.

"Ouch!" Ya fada yana runtse idanunsa saboda tsananin cizon data sakar masa. Ware manyan idanunsa dinnan yayi a kanta bayan ya budesu,idanun da bataji komai tsahon xamani zata iya mance memory din daya aje mata a yau. Labbansa ya motsa yana jin zafin zazzabin har cikin idanunsa,to amma yanayin daya sakata a ciki yafi komai da yakeji ciwo. Ya sani ya shigeta ne da duk wani qarfinsa,yana tsammanin samunta budaddiyar hanya ga kowa......sai abun yazo masa a wata irin bazata a sanda bazai iya controlling din kansa ba kuma

"I'm truly sorry for the pain I've caused" Ya fada da wani irin calmness cikin muryarsa,sai ya sanya hannu yana cirota daga bathtub din,yana jin bazai juri barinta tana jin abinda takeji din ba......baisan girman pain din ba bare ya kwatantashi,saidai koma meye ya tabbatar radadinsa ya wuce wasa.

Bedside drawer ta isa tsigar jikinta na sake tashi gana girgiza kai da jinjina barnar data tabbatar ba qarama yayi ba,wayarta ta dauka ta duba last call dinta. Qawarta da suka rabu dazu hajja saudat ta kira.

"Kuna da wata gynecologist ne mace da zata iya home service kuwa?" Anni ta tambayeta kai tsaye.

"Eh akwai.....'yar qasar syria ce.....tana da kirki sosai fadwa haleem".

"Na gode.....kimin magana da ita please,ki bata address na gidana.....if possible tunda bamu da nisa kada ta wuce one hour"

"In sha Allah kusa muke ai"

"Na gode" Anni ta fada tana katse kiran. Farouq ta koma kira,saidai kira har biyu bai daga ba,sai ana ukun sannan ya daga yana sosa kai.

"Ku kwana a can,ku biyasu kudin kwana daya.....but kakaimin amna gidan saudat acan nakeso ita din ta kwana"

"Okay.....in sha Allah" Farouq ya amsa shima yana jin dadin hakanma da tace,don shi kansa a yanzu ji yake ya zama surukinta,ina ga fuad din. Yadai tabbatar ba zasu qarke lafiya ba idan ya dawo hayyacinsa,to amma wa suke dashi sama da anni?,itace qawarsu abokiyarsu kuma.


_uhmmmm....tofa,sabreen naga kin dauki zafi da yawaπŸ˜„πŸ˜„.....amma dai muje zuwa_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 77


77


Da wani irin yanayi yake wanke mata kowanne sashe na jikinta da ruwan shower gel din. Wani kuka take saki kawai tana ji har a ranta ya gama da ita,bata da wani sauran qarfi da zata dakatar dashi ko guda daya,cizo kam ta masa shi har batasan adadi ba,amma ko a fuska baya nuna mata yaji zafinsa bare akai ga dakatawa da abinda yakeyi,tamkar ma ba jikinsa take ciza ba,idan ta saka bakinta ma tsaiwa yakeyi har sai ta cire don kanta. Shi kadai yasan me yake sake ji cikin jikinsa,ji yakeyi kaman baiyi komai bama,wani sabon feeling ke taso masa saboda santsin shower gel din dake sassan hannuwansa wanda da tafin hannu kawai yake dauraye mata jikin ba tare daya nema loofah ba. Kafin ya gama wanketa launin idanunshi sun sake canzawa sosai,numfashinsa yana masa nauyi tsakanin qirjinsa da hunhunsa,inda zai samu....inda zai yuwu yana buqatar sake kasancewa tare da ita ko yaya ne.....koda na mintuna kadanne,amma shi kansa yasan yadda take a yanzu dole tana buqatar medical care. Bai taba jin ya zama addicted to wani abu ba irin wannan abun,cikin qasa da wasu awanni qalilan yana jin kamar an halicci abunne sabodashi shi kadai.

Hannunsa ya sanya ya riqo qugunta bayan ya fiddota daga bathtub din. Idanunta yake kalla sosai wadanda suka rine saboda azabar kuka. Taqi kallonsa ta kuma sanya duka hannuwanta biyu tana turashi baya,amma ko motsi baiyi ba bare tasa ran zai matsa. Yadda takejin dumin fitar numfashinsa a rarrabe yana sake dasa mata matsanancin tsoronsa,shigen wannan yanayin taji daga gareshi dazu,a yanzun idan yace zai maimaita abinda yayi dazun ta tabbatar saidai ta taqaitawa kanta wahala kawai tayi sallama da duniya......ita kadai tasan abinda takeji,ita kadai tasan radadin da takeji yana ratsata a duk wani motsi da zatayi.

"Sabrrrrr....." Ya fada da sautin dake kama da rad'a,wani irin narkakken sauti dake da amo na can qasan maqoshi,idanunsa cike fal da wata irin mahaukaciyar soyayya da baiyi zaton cikin zuciyar tasa akwai wani space daya ragewa wata halitta ba.

Kanta ta dauke gefe,maganganu takeson gasa masa amma tana jin idan ta tsaya ta maida masa koda kalma daya ma yana da wannan darajar ashe?.

"Sabreeennn" Wannan karon ya kira sunanta full da wani irin sassanyan kuma kwantaccen sauti. Idonta ta lumshe tana mamakin jin sunan yau radam saman bakinsa,kiran sunansa a bakinsa daban yake da yadda kowa ke kiranta,kaman yadda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login