Showing 249001 words to 252000 words out of 557259 words

Chapter 84 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

520

aka haifeshi sai dataji kowacce gaba ta jikinta ta saki. Wani irin abu da bata taba ji akan kowa ba ya soma bin sassan gudanar jini na jikinta yana aika saqo wa zuciyarta,wanda kafin ya kammala bayanansa ya sauka gaba daya ya wuce da nutsuwarta dama zuciyarta gaba daya.

Ta fahimci akwai ire irenta da yawa a wajen bayan tashin taron,saidai ba alamun samun fuska ko dama daga wajen kowacce diya mace,wannan dalilin ya sanya tabi ta hanyar mahaifinta.

Ta samu damar gaisawa dashi,saidai abu na farko daya sanyaya mata jiki hannu data bashi da nufin suyi hand shaking kamar yadda yake gaisawa da kowa,sai ya jefa mata wani irin kallo ya maida hankalinsa ga wani abu na daban.

Bata haqura ba sai data sanya mahaifinta ya nema ganawa dashi a masaukinsa dake banana island kafin yabar lagos kenan,a nan ta fito kanta tsaye ta gaya masa abinda ke dauke dashi,amma sai ya saki wani murmushi daya qarasa qona mata ruwan jiki gaba daya,ya kuma bata saqon daya kusa tashin kanta a aiki.

"Am so sorry kinji....ni bana soyayya.....infact ba time na ire iren wadannan shirmen,ina fata kema zaki maida hankalinki akan karatunki okay?" Gaba daya shirme ya dauki abun,yadda ya tsaya ya mata maganar ma ta tabbatar albarkacin mahaifinta taci. Still bata jin zata iya haqura dashi,ta samu daman ganinsa a karo na biyu ba tare da yasan ita bace. A nan ta gane ainihin wayeshi,ya fiddo mata true color dinsa,abinda ya birkitata kenan,batayi qasa a gwiwa ba ta bashi tabbacin bata taba neman abu ta rasa ba.....a kansa kuma ba zata fara ba,zatayi duk yadda zatayi don ganin ta mallaki soyayyarsa ta kuma mallakeshi.....ta kuma ci masa alwashin duk inda ya shiga tana biye dashi har sai randa ta samu abinda takeso.

Ko a yanzun zare rafkeken sunglasses din idanunta tayi tana qoqarin sakar masa murmushi,yayin da ransa ya motsu da zummar baci amma kuma mamaki ya mamaye wannan gurbin.

"May i ask who's let you in?" Yayi maganar yana qoqarin danne fushinsa. Murmushi ta kuma saki tana rolling idanunta cikin salon jan hankali

"As your guest,i think you should welcome me first" Ta furta tana narke murya. Baya ya sake ja kadan ganin tana qara takowa inda yake

"What brings you here?" Wannan karon ya fada adan tsaurare,alamun bacin ransa suna fitowa fili. Kallonsa tayi a kaikaice tana sake yadda da maganganun da aka gaya mata a kansa. He's not a womanizer,he's not into playing games with women......ta yaya kike tunanin zakiyi winning kansa?" . Ta tuna da maganar da daya daga cikin qawayenta suka mata. A lokacin ta dauki zancan nata ne a matsayin kishi,saboda samun cikakakkiyar dama da tayi da take ganin zata kawoshi cikin rayuwarta,damar da mata da yawa suke nema basu samu ba.

"Am here for you fu'ad.....please ka bani gurin zama tukunna mu tattauna a nutse"

*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 28


28


"Get out of my house" Ya fadi ba alamun fara'a ko walwala a tattare dashi. Wannan fuskar me cike da miskilanci,wadda zai wahala kaga wani abu me kama da murmushi a kanta ta sake dinkewa tsaf

"Please mana" Ta fada da wata irin shagwaba tana hade hannayenta waje daya

"Zaki fita ko sai na kira masu fiddamin dake?" Ya kuma fada yana ware mata idanunsa da suke da wani irin kyau me jan hankali wanda suka sake fusgar hankalinta.

Bai ankara ba bai kuma taba kawo haka zata kasance ba ya tsinceta ta fada cikin faffadan qirjinsa tana neman kai masa kyakkyawar runguma. Baiyi wata wata ba bai kuma sake bata koda minti biyar a jikinsa ya yakiceta ya watsar gefe. Wani irin tafasa zuciyarsa keyi,wanna shine karo na farko da wata mace ta rungumeshi irin haka.

"Tashi ki fita thn ranki bai qarasa baci ba,stupid!" Ya fadi a tsawace yana nuna mata qofa. Miqewa tayi tana kade jikinta,duk da ba wani baci tayi ko datti ba saboda gurin fes yake da wata irin tsafta da take ta'ammali da ita a komai nasa,cikin borin kunya tace

"Yakice ni daga jikinka baya nufin fidda soyayyarka daga zuciyata......zan tafi,amma kuma zan dawo,zan kuma ci gaba da kasancewa dakai,zan zama cikin kowanne motsi naka har sai na cimma nasara na samu abinda nakeso". Daga wannan ta dauki jakarta tana nufar qofa da dan sauri,qasan zuciyarta da tsoron yadda mode dinsa ya koma,amma abinda takeji a kansa ya danne komai.

Iska me zafi ya furzar yana shafa sumarsa da tafin hannunsa. Kwata kwata yaqi jinin mace maras jan aji........yana matuqar son mace me aji.....mace me dan wani tasiri kadan na girman kai,wanda girman kai a wajen mace yana alamta alamu na kamun kai,girman kai yana cikin siffar da akeson mace dashi.....amma a mu'amalarta da maza kamar haka. Komawa yayi saman kujera ya zauna yana fidda numfashi me huci. Yana daya daga cikin abinda yasa ya rasa interest akan mata,yana daya daga cikin abinda ya sanya har yanzu ya kasa gano macen da zata sace zuciyarsa kwata kwata.......saboda yanzun mata yana hangen sun rasa dabi'un nan guda biyu zuwa uku masu tsananin tsada fiye da diamond...... Masu tsananin zame musu ado fiye da adon gold a jikinsu,wato KUNYA da kuma KAMUN KAI.

Wayarsa ya dauka ya kira abdus_samad yana qoqarin danne fushinsa,bugu daya tak ya daga

"Who gave her permission to enter?" Tambayar da yayi kenan a taqaice.

"Am sir......" Ya fada adan daburce don jikinsa yana bashi laifi yayi

"Did someone invite her in?" Tambayar ta qarasa daburtashi gaba daya,ya kuma fahimci laifi yayi.

"Am sorry sir......am sorry,naga diyan ambassador....."

"Keep quite......are you out of your sense?,don diyar ambassador ce?,meye alaqana da ita?,dama akwai wannan tsarin na ku barmin mutane suna shigomin guri anyhow?,meye amfaninku idan haka zata ci gaba da kasancewa?" Ya kasa magana kawai sai haquri da yake faman jera bashi,don tunda yake dashi irin fada irin haka bai taba hadasu dashi ba. Bai jira cewarsa ba ya yanke wayar yana ajiye wani tsaki. Ji yayi sam zaman parlor din ya isheshi,bama parlor din bama,abujan gaba daya,ya miqe yana wucewa bedroom dinsa,cikin jikinsa gaba daya yana jin kamar ya yanke inda nata jikin ya tabashi. Bacin rai sosai yakeji a qirjinsa,duk wani nau'i na sabo ya tsaneshi,sai yau gashi ta sakashi abinda yake matuqar gudu da kaucewa. Yasha shiga harkoki da abubuwan dake cakude da mata,amma yanayin kamewarsa da kuma miskilancinsa yasa suke tsoronsa matuqa,ba wadda take zuwa masa da zancan banza,tun daga secondary school university da tafiyansa service,duka Allah ya tsareshi ya kuma tsare imaninsa,duk da irin farkamakin da yake samu.

Yana gaban wardrobe yana sauya kayan jikinsa yaji ana masa knocking,muryarsa can qasa da sauran tasirin bacin rai a ciki ya tambaya

"Waye?"

"Saddiq ne hamma".

"Come in" Ya bashi dama lokacin da yake sanya rigar jikinsa.

Yanayin yadda yaji sadiq din ya shigo ya tilasta juyawa yana duban fuskarsa. Sai yabi hannunsa da kallo wanda yake dauke da system

"What's wrong with you?" Ya tambayeshi yana tsareshi da idanu. Kasa amsa masa yayi,sai daya samu waje ya zauna daga saman carpet ya ajjiye system din sannan yace

"We got the announcement........ana zargin an samu muggan qwayoyi cikin jewelry company dinmu". Ya qarasa fada yana buda masa saqonnin da suka samu daga dukkan kafofin dake da alaqa dasu daya nabin daya.

Hannuwansa kawai ya zube cikin aljihunsa yana kallon system din. Yanajin wani yanayi yana zagayashi,hankalinsa nason tashi amma yana gayawa kansa da kansa

"All is well" A irin wannan lokutan na tsanani,lokutan da jarabawa irin wannan ke tunkararsa rauni yakan rugo da gudu ya mamayeshi.....a irin wannan lokacin yakanji yana da buqatar wata halittar a gefe da zata same masa qwarin gwiwa......banda qannensa banda farouq da yawan daukan mas'alolinsa yake ganin suna masa yawa,ya kamata ya rage masa daukan matsalolinsa haka.....tun daga quruciya kunnuwan farouq zuciyarsa dama gangar jikinsa suke fama da matsalolinsa.....zuwa yanzu ya kamata ace ya huta.....anni,wata irin rumfa ce sha shirgi ita da abban gaba daya,ya kamata kunnuwansu su samu sassaucin jin damuwoyinsu a yanzu haka da girma yazowa kowannensu.......akwai personal mutum da yake buqata daga gefe da zai zauna a wannan matsayin.

"Hamma wannan saqonnin barazanar basa da alaqa da faruwar wannan abun kuwa?". Kai yake jinjinawa sanda yake takawa a hankali yana matsawa daga wajen

"Definitely......but I'll make it clear im not Intimidated" Ya fada da wani irin qwarin gwiwa yana dora top saman rigar t.shirt din jikinsa.

"Let's go.....ka kira William kace ya samemu a can....."

"Amma hamma.....flight isn't ready"

"We'll take the road" Ya furta yana riga saddiq yin gaba.

Kafin sukai ga isa lagos ya gama shirya dukkan abinda ya kamata ace ya tsara din. Suna dab da shiga garin har a sannan idanunshi biyu,ko daya baiji wani buqatar bacci ko kuma ya huta ba. Yaja qaramin tsaki sanda suka dauki hanyar kamfanonin. Ya fahimci ita kalmar SO ko a meye ta shiga wahala ce kawai da walagigi da ruhi,wannan ya sanya banda soyayyar family dinsa bai taba saka soyayyar komai cikin ranshi ba,sai yanzu gashi kwatsam......kamfanin ya shiga ransa har baisan adadi ba......gashi kuma ya zama abu na farko da son nasa keson zame masa wahala,da wannan ya qara ji a zuciyarsa lallai tabbas ya kamata ya nisanci soyayya iyakar iyawarsa.

Duk da sun nuna matsayinsa yafi ya taso da kansa amma ya kauda wannan. Ya karbi duk wani bincike nasu ya dora da nashi. Da gaske an samu wani dan qaramin store cikin kamfaninsa cike da qwayoyin da inda wani me qaramin matsayinne ba shakka sai ya tafi dauri gidan gyaran hali,amma da yake a nigeria muke.....kuma kura ma tasan gidan me babban sanda sai ya zamana dakatar da kamfanin kawai akayi sai bincike ya kammala.

Bayajin zai iya bari maqiyansa su kalli faduwarsa da wurwuri haka,wannan ya qara masa qaimin shiga binciken da kansa gadan gadan.

Ya fuskanci tarin abubuwa masu yawa cikin case din,wannna ya qara masa qaimi,bai kuma yarda yayi handling case din ma kowa ba.

Duka da bacci da cin abincinsa qalilan ne. Amintattun experts investigators din daya aminta dasu kawai suke aiki ka'in da na'in,ba dare ba rana. Bai gayawa kowa abinda ake ciki ba banda anni da yace ta tayashi da addu'a,akwai matsala amma qarama ce ba wata babba ba,haka ya gayawa abba da farouq. Saidai sam hankalin farouq ya gaza kwanciya,don yana dawowa daga seminar dinsa ya biyo bayasa a washegari.

Yadda ya ganshi ya tabbatar abun ba qarami bane,don ya nuna har a jikinsa don kuwa ya dan rame kadan saboda rashin bawa abinci muhimmanci. Ya sake sallamawa da miqa wuya kan muhamnadun yaci sunan muhammad din,namijin gaske ne da gaske......daga yadda ya tunkari komai yake gabatar dashi da dukka qarfin gwiwarsa da jarumtarsa kadai ya qara tabbatarwa NAMIJIN DUNIYA NE.

Yanata qoqarin dodging komai farouq ya dubeshi.

"4weeks without me dude.......have you noticed your appearance?.....check your reflection" Ya fada yana kama hannunsa zuwa gaban concealed mirror din dake wajen.

Ya kalli fuskar tasa kaman yadda farouq ya buqata,sai ya saki murmushi ya miqa hannu yana shafa fuskarsa.

"Chill out mana dude,nayi settling komai,It's come to an end......My evidence supports my claim....and it speaks for itself,all the fact are on my side,na gama komai gobe zasu saki kamfanin.....abu daya ya rage na gano shine,who's pulling the string" Hannunsa farouq ya riqo yana girmama qarfin jarumtarsa,yana jin inama ya samu irin wannan jarumtar tasa

"We'll leave no stone unturned,we'll find him together" Rungume kafadar farouq yayi,yana sake jin qaunarsa cikin ransa.

A gaba ya sakashi ranar,yasa ya ajiye komai tunda bincike ya kammala. Da kansa ya zauna ya masa gyaran fuska da sauran wasu abubuwa,yana masa suna hira yana bashi labarin nasa progress din da aka samu bayan seminar din. Duk duniya da farouq kadai yake irin wannan sakewar. Ranar duka tare suka qarar da ita,sai dare sannan kowa ya wuce makwancinsa,da zummar gobe da kamfani yaci gaba da aiki jibi tabbas dole su wuce gida,wanda sam bai fahimci meye ma'anar matsawar da farouq din yayi bama.

Ya dauki wayar da zummar kashewa ya tarar da tarin miscalls da kuma saqonni,guda daya ya duba ya fahimci wacece. Fareeda ce....saqo bayan saqo kamar bata da wani sauran aikinyi sai tura masa da saqon.

"How did she get ahold of my number?" Ya tambayi kansa da kansa. Tunawa da yayi da mahaifinta ya sauqaqe masa wahala,yasan samun numbersa zai zame mata wani abu kenan me sauqi. Tsaki yaja ba tare da yabi takai ba,ya kashe wayar ya kwanta.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 29


29


β˜…Cikin kwanakin har ruwan jikinta takeji kaman ya qare saboda tsabar wani irin kadaici da dumbin tunani da yake cike a kanta. Sati hudu cur tana a cikin gidan......ba motsin kowa ba gilmawar kowa,ba hira da kowa,ba waya,daga ita sai tv sai karen gidan dake haushi nesa da muhallinta. Ada ko parlor din bata fitowa tana qunshe a daki,daga bisani ta fahimci depression na loneliness zai iya kamata,don haka da kadan da kadan ta fara fitowa tana zama.

Saidai daga zaman sai bacci,sai wanka sai wata kwanciyar. Gyaran gidan kansa bai wani dameta ba,don tana ganin ba wani muhalli bane da zata damu kanta a kansa,hasalima a nata ganin waje ne da lokaci kawai take jira ta barshi. Abu biyu take gyarawa,bedroom dinta sai kitchen din da ba wani abun arziqi take dafawa ba. Tun ranar da tayi abincin safen nan rabonta da tayi wani cikakken abinci ta sawa cikinta,iyakar yunwa idan ta ciyota ta soya qwai guda biyu... Kota dafa indomie guda daya kota soya potatoes taci shikenan.

A kwanakin tana jin yadda qirjinta yake riqewa amma taqi damuwa da wannan bare takai hankalinta kai,abu daya kawai take jira ya dawo,tayi duk yadda zatayi ta cika aikin maamah ta samu freedom. Ta sani tana da wata fitinanniyar ulcer data kusa sanyata tabi bayan mahaifi da mahaifiyarta bayan rasuwar ummensu. Ulcer data samo asali daga matsiyaciyar yunwar da tayi mugun horasu,takaita matakin da take xubda aman jini. Ta jima rabon data tashi,tunda ta samu sassaucin rayuwa suke iya ci su qoshi,amma a kwanakin nan da take bata alamu taqi maida hankalinta sam sam.

β˜…"Alhamdulillah" Shine abinda ya furta lokacin da ya fito daga toilet wanda ya barshi wata guda cur kenan.

Shirya kansa ya fara yi cikin butter milk color pyjamas yana tunanin kiran me sunan malam da ameh gobe kowa ya dora aikinsa a inda ya tsaya. Sam har ga Allah ya sha'afa da ita,abinda ya sameshi ya shafe abubuwa da yawa a kansa.

Gidan duka ya masa datti a yadda yake tsantseni da tsananin tsafta,ya kammala shirin nasa sai ya kasa saukowa saboda gajiya,ya bude freezer dinsa dake dining area dinsa na sama yana fatan samun wani abun.

Wuta ce 24/7 da kome zaka ajjiye a fridge din zaka sameshi fresh. Damammiyar fura ya ciro wadda ba komai cikinta daga nono din sai furar da aka markadasu suka hade jikinsu sosai. Furar daya samu ta masa daidai,don abace dame relaxing jiki da bada bacci me kyau da daddare saboda sinadaran da gero ke dauke dashi. Ta masa sanyi,baya kuma shan abu me sanyi sosai har haka,wannan ya sanya ya ajiyeta ya koma ya kunna tv don ya rage mintunan da zaiyi jiran furar.

Kadan kadan takejin kamar wani baqon sauti cikin gidan sanda take baro kitchen inda ta soya qwai guda biyu,tana taraddadin ci ma saboda maiqon dake jiki amma kuma batajin tana da wani abinciii bayan shi.

Fargaba taji tana cikata,wani irin matsanancin tsoro ya saukar mata. Sound ne tabbas wanda bata tantance na meye ba. To ko haurowa gidan akayi?,ko wani ne ya shigo ciki ya boye ba tare da sanin securities din ba?. Duka ba kalar tunanin da batayi ba,jikinta na rawa ta qarasa dakinta ta maida qofar ta rufe tana maida numfashi. Jin still da sound din sai tsoron yaqi barinta,ta taka da hanzari tabi duka windows din ta kulle sannan ta dawo tsakiyar dakin ta zauna tana raba ido tare da sauraron koma meye daga inda zai bullo.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login