Showing 399001 words to 402000 words out of 557259 words

Chapter 134 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

460

tsiya yaci kuka ya qoshi,da wani irin zafin nama ya juyata fuskarta ta daina facing dinsa,saidai can dinma ba sauqi,hips dinta ke tsokane masa idanu,sai kawai ya rabata da jikinsa waiko hakan zai sanya ya rage ganin abubuwan da yake gani din.

Baisan shima nasa hannuwan rawa sukeyi ba sai bayan ya zura mata rigar ya dagata daga jikinsa yana zazzarga mata igiyoyin dake riqe da bayan rigar. Sosai hannuwansa suka kama rawa,daure igiyoyin suka gagareshi. Ya runtse idanunsa da matuqar qarfi yana fatan daidaituwar mode dinsa,saidai ko daya bude ba abinda ya canza saima numfashinsa daya fara fuzga kaman me ciwon asthma.

Hannuwansa ya dora saman kafadunta gaba daya ya juyo da ita da wani irin hanzari,yadda red din gown din ta sake haskata sai yaso.tafiya da ragowar numfashinsa da yake kokawa dashi. Gaba daya labbansa rawa suke kaman me rawar sanyi ya soma lalubo kalmominsa......

"DUNIYA TA.... please,kiyimin alfarma na sake kasancewa dake karo na biyu......please na roqeki karkice zaki hanani" Firgicin data shiga ya kusa fin nasa,take itama jikinta ya kama rawa,ta zare idanunta duka a kansa tana jin kaman zasu zazzago tsabar tsoro. Ta motsa labbanta zatayi masa magana a tsorace amma ya rigata

"Am so sorry.....naso na barki har sai sanda kika fara sona.....naso na barki har sai sanda kika gamsu da kanki kikayi accepting muhammad fu'ad......but.....kece DUNIYATA bani da wani gurin zuwa sai wajenki din dai" Sake rudata kalamansa sukeyi,batasan yadda zata masa bayani bama,neman gurin tsira kawai takeyi,saita saka hannunta tana neman zame hannuwansa daga kafadarta. Sarai ta fahimci a rude yake kaman yadda take a rude,idanma tace zata tsaya masa bayani bazai fahimta ba. Damqe kafadun nata yayi idanunsa suna sake juyewa hadi da canza launi.

"Please mana.....na miki alqawari wannan karon......I'll be gentle with you.....i will never harm you again" Ya fada yana jin kaman ana qara izashi zuwa gareta.....kaman yana qara loosing tunaninsa gaba daya. Sake buda baki tayi still bata sare ba,duk da tsoron dake sake dabaibayeta da nufin masa bayani ko kadanne,amma sai.ya kama hannuwanta duka ya sanya tsakiyar tafin hannunsa kaman me begging dinta

"Please....please.......na yadda da kowacce kalan tuhuma zakiyimin......na yadda da kowanne zarginki a kaina......kome kikace nayi ina neman gafara akai......kinqi bani dama tun a baya nayi bayanin kaina......I'm pleading with you.......grant me this favor" Ya qarasa maganar yana zubewa a gabanta......

Ji yake ya shirya rasa komai.....ya shirya kuma sadaukar mata da komai,yayi qasa da kansa yana jiran cewarta jikinsa naci gaba da rawa.

Wani abu ya tsarga mata jin digar wani abu me dumi saman tafin qafafunta,wata irin faduwar gaba ta ziyarceta saboda abinda zuciyarta ta raya mata.

"Muhammad fu'ad jadda ne kuka a gabanta?,muhammad fu'ad fa?,wanda gidan jaridu da mujallu kowacce fitowar rana zuwa faduwarta suke rububin buga labari akan kamfaninsa......suke rububin fidda labari akan kalan jarumtarsa tun kan ya balaga har zuwa girmansa......jaddan da qasashen duniya keyi dashi?,jaddan da maganarsa manyan kamfanonin qasashen qetare dake sarrafa diamond sukeji?,yau shine under her feet?.

Daidai inda zaren tunaninta ya tsaya kenan,sai dauko mata sunkutarta da fu'ad din yayi zuwa lafiyayyar shimfidar da muraaka suit suka zubeta musamman saboda masoya masu yawon watan zuma wato honeymoon irinsu fu'ad din.

"Am sorry DUNIYATA.....am sorry my world" Shine abinda ke fita daga bakinsa cikin wani irin gigitaccen yanayi. Tsoro ne fal qirjinta da zuciyarta,tuni ta fara sakin nata kukan tana hango kanta gaban Dr fadwa ana sake dinketa. Tana sake rewinding azabar da tasha wancan ranar.....ta kasa mantawa da yanayin daren da kuma lokaci. Hatta da wucewar kowacce daqiqa a lissafe take a wajenta....abune da ya kasa barin kanta da mafarkanta.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 101


101


_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_

_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_

_Bukhari da muslim_




"Kar ka cutar dani" Ta fada a galabaice tana jin yanayinta yana canzawa.

"Bazan iya cutar dake ba.......sonki ne yayimin yawa.....ki taimakamin na koyi controlling nasa" Ya fada ba tare daya saurara mata ba.

"In ka cutar dani ko ka zalunceni......"

"Ki daga hannu ki roqi Allah ya hukunta miki ni.....ki roqi Allah yayi miki sakayya......ya jarabceni da wani son da yafi wannan yawa da fadi" Ya fadi yana tallafo kanta gami da sanya jirkitattun qwayar idanunsa cikin nata dake cike fal da hawaye......dukka hannayensa suna rawa kaman wanda aka tsamo daga ruwan sanyi. Idanunsa kawai firgitata suke,ta saka hannu zata riqeshi saidai ko kadan bayason sakejin wata magiya tata,don haka ya rufe bakinta ruf da nasa.

A hankali ya shiga aike mata wasu irin zafafan saqonni.......wasu irin abubuwa da tun tana turewa har suka fara kama mata kwanya.....suka jefa ta a duniyar tunani.....suka dauki duk wani tsoro nata da fargabarta sukayi cilli dasu can bayan gadon.....suka gusar da duk wani hankalinta tunaninta taurin kanta tsiwa dama tsoronta. A hankali saiga me jadda yana komawa fagen,fagen da bai taba zaton zai sake ziyarta ba karo na biyu cikin rayuwarsa.......yayi musu ragama da jagora zuwa wata sabuwar duniyar da shi da ita basusan akwaita daban bace.....tasha banban da duniyarsu ta wancan karon nasu.

β˜…Tun yana dakon jiran fu'ad har ya soma lalubarsa cikin gidan,don dakinsu ya shiga zaman jiransa. Ko ina ya duba bai ganshi ba,bai wani zurafafa tunani ba ya dauki wata motar ya fita ya zauna da baqin nasu,suka kammala meeting din ya sallamesu,ya kuma hada duka documents din a take ya aika masa ta email. Kaman yadda suka tsara daga wajen sai ya wuce dauko anni data tafi wani herbal center a traditional market dinsu. Suna mota take tambayarsa fu'ad din

"Mun fito tare so uzuri ya maidamu,sai nace bari nazo na daukeki" Daga haka suka rufr chapter din suka dauko wata har suka isa gida.

Komai anni ta gama har tayi shirin kanwaciya amma bataga sabreen ba. Tana saman abun sallah tana shafa addu'ar shafai da wutirinta tace da amna.

"Ina ameenatu ta shiga ne?" Kai ta girgiza,itama tun dazu take nazari

"Ban sani ba wallahi anni,maamah dai tayi kiranta,tunda ta fita kuma bata dawo ba". Shuru anni tayi haka kawai taji gabanta yana faduwa.

" Maamah ce ta kirata?,tunda ta fita kuma bata dawo ba?" Ta sake maimaita statement din tana duban idanun amna. Kai ta gyada mata.

"Turqashi" Anni ta fada tana miqewa hankalinta yana tashi,zuciya ta fara fasalta mata abubuwa kala daban daban da zasu iya faruwa.

"Indai wani abune ya faru kaman yadda zuciyata ke gayamin......indai wani abu mariya ta aikata na cutarwa ga ameenatu.......tabbas saita gane bata da wayo......a wannan karon saina nuna mata ainihin kalata" Anni tayi maganar a zuciyarta tana zare hijabin jikinta,ta dauki dankwali ta daura tana duban amna

"Ki zauna ina zuwa" Abinda kawai tace da ita kenan ta murda qofar tana ficewa.


_tofa.....πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚,me anni zatayi?,masu karatu ku tarota,ku gaya mata ba ruwan maamah a nan......dan annin ne yayi kidnapping takwararta da kansa_πŸƒπŸ½β€β™€οΈπŸƒπŸ½β€β™€οΈπŸƒπŸ½β€β™€οΈπŸƒπŸ½β€β™€οΈπŸ˜†πŸ˜‚πŸ˜‚


Daidai lokacin da maamah ke dakinta,abun duniya yana sake ta'azzarar mata da wani irin zafi qunci da tashin hankali. Kaf tunaninta ya karkata akan yadda zata raba sabreen da wannan copy din video din da yake hannunta.....rabata dashi din shine tamkar mabudin iya wurgar da ita daga rayuwarsu cikin qasqanci da tozarcin data tanadar mata.

Ta duba agogo ta duba agogo har sau babu adadi......ta duba agogo duk bayan kowanne wucewar daqiqa.....cikin saka ran fuad zai dawo ya lallasheta......fu'ad zai dawo yaji meye damuwarta kaman kowanne d'a yakewa iyayensa,saidai tun tana dubawa tana kuma lissafawa har ta bacewa lissafin.

Kowacce alama da shaida ta nuna mata bazai dawo ba.....ya fita abinsa ne,bashi kuma da niyyar bata wannan lallashi da kulawar da take yunwarsa. Ranta yakai qarshen baci,da gaske dai bai dauketa uwa ba mahaifiya.....kunnuwanta na tuna mata wata hira da taji musaddiq da saddiq nayi,suna gulmar fu'ad din. Ya fita aiki ranar sai gashi ya dawo da Rana,suka dinga dariya suna gulmarsa,wai da zai fita ne yaga ran anni kaman a bace....da yaje office ya kasa sukuni,dawowar da yayi yazo zagayata ne ya tabbatar ta warware,ba kuma wani a cikinsu bane ya bata mata rai ba.

Tuna wannan kawai ya sake hura wutar zuciyarta,sai kuma ta tsinci knocking da fushi yasa ta kasa tambayar waye,ta miqe kawai ta bude qofar a fusace.

Anni ta gani a tsaye tana duban ta,wani irin kallon kallo dake dauke da ma'anoni da yawa a zukatan kowannensu.

"Zuwa nayi duba sabreen.....ta shiga dakinki kuma har yanzu bata dawo ba?,ina kika kaita?". Me neman kuka ne wanda aka jefa da kashin awaki,wanda yake jiran kadan ya fashe,saita fito daga dakin gaba daya tana duban anni tana huci.

"Dama dab nake da zuwa wajenki na tambayeki wanne irin baqin sihiri kika yiwa 'ya'yana?,wacce irin shirka kika ta'ammali da ita ameena?,da yake bani da haqqinki sai gashi kin kawo kanki da kanki kina tambaya akan abinda ni yafi cancanta na tambayeshi". Mamakin maamah din ya kasheta,ta zuba mata idanu sosai tana ganin yadda take haqilo kaman zata fidda maqogoronta.

"Mariya......tambaya daya ce nayi ina kika kai sabreen?,don bata dawo dakinta ba". Wani banzan kallo ta watsawa anni tana dubanta.

" Au.....bacewar karuwa dama abun mamaki ne?,har akwai mamaki don an wayi gari an tarar karuwa ta gudu daga dakinta?"

"Subhanallah" Anni ta fada tana ware idanunta akan maamah mamaki yana ratsata. Surukarta?,matar d'anta take kira karuwa saboda wani son zuciya nata?.

"Ameena.....ina me baki shawarar warware duk wani qulli da kikasan kin yiwa yarana tun daga zamanin quruciya zuwa yanzu.....idan kuma kinqi wallahi wallahi ni mariya bazan qyale ba......na dauki cikin yaran wata tara na haifesu.....naci kashinsu da fitsarinsu amma rana daya azomin da bariki da salon mallaka?,ubanme kike basu wanda ni bazan iya basu ba?,uban me kike musu?". Sosai zagin ya sosa zuciyar anni,sai ta koma ta zauna tana qare mata kallo hannayenta harde a qirjinta.

Duk wasu sarari da filaye na yiwa maamah kara zuwa yanzu sun fara cika,bata kuma da saura wanda zata bude mata taci gaba da zuba jujinta. Kai tsaye kuma hankalinta kwance ta kirata

"Mariya......abinda na basu baki dashi.......kin kuma rasashi har abada......yadda kika kasa rungumarsu kiji qansu a sanda suke da rauni......to kema kin rasa wannan cikakken tausasawar sai wadda zasuyi miki donsu fita haqqinki da haqqin addininsu......shima wannan din xasuyi miki shine saboda sun mori iyayen goyo da sukasan hagunsu da damansu.....daidansu daba daidai ba......banda haka ke dasu dama dukkan abinda suka mallaka sai gani sai hange daga nesa. Inda ce hankalinki a daidai yake......inda ace hankalinki cikin jikinki yake.....ba cikin dimuwa kike ta neman duniya idanu rufe ita da abinda yake cikin ta ba......da baki buqatar bayani kan me yasa kika rasa kike kuma rasa kowacce dama,take kuma kufce miki.......bari na gaya miki wani abu.....ni ameenatu na tsere miki.....ni ameenatu ba zaki taba kamoni a zukatan naki 'ya'yan ba bare nawa 'ya'yan.....sauran dukkanin abinda zaki zata ko ki tuhuma wannan ke kika sani.....kuma keda zuciyarki......zuciyar bawa birninsa,abu daya zance miki shine......kada ki yarda kada kuma ki kuskura wani abu ya samu sabreen,idan kikayi wannan gangancin to tabbas zan saka a binneki a cikin qasar Maldives me tarin farin rairayi" Ta qarashe maganar tana nuna maamah da yatsa,sannan ta miqe tsaye sosai.

"Daga yau gobe zuwa jibi naga dawowar diyata cikin gidan nan.....ko da fu'ad ne yace zaiyi ganganci da rayuwarta shi dake aurenta saina hukuntashi.....ballantana ke da nake kyautata zaton kwangilarta kika dauko". Anni na kaiwa nan ta juya tana barin wajen,tanata qoqarin controlling fushinta kada maamah din ta ganshi.

"Aikin banza kenan qafafa da mallakin wani.....ke me ya hanaki haifar kamarsa?,kinga sai kiji dadin yin mulkin mallakar da kyau ba tare da kowa yaga wallenki ko ya qalubalanceki ba" Tayi maganar da nufin fusata zuciyar anni.

Da wani lafiyayyen murmushi ta waiwayo tana kallonta.

"Banda abinki tunda kin haifomin ai kin hutasshe dani......don yadda nake hutawa ko asalin wadda ta kotseshi bata rabauta da wannan ba....idan kinajin tsuntsu daga sama gasashe to fu'ad ne a hannun ameenatu" Ta qarashe maganar tana bude mata tafukan hannayenta sannan ta juya taci gaba da tafiya abinta.

Kamar hauka zai kamata haka taji maganganun anni saman kanta. Kasa shuru tayi ta soma zuba ruwan masifa da zagi.

"Ameenatu.....nafi qarfinki....nafi qarfinki wallahi,bakisan wacece mariya ba....kibar ganin zamani ya cimmata......to ki giwa ta fadi tafi qarfin wawa,tafi qarfin kiyashi ya jata.....zan nuna miki asalin wasan indai na haifu cikin uwata da ubana".

Bataji komai cikin abinda take fada ba,don already ta wuce daki ta kuma maida qofar ta kulle.

"Bari yazo shima zai sameni.....bazan sake kwana gida daya da wannan annamimiyar makirar ba.....dole yazo ya zaba,koni ko ita" Ta fada kaman zararriya tana jawo luggage dinta tana watsa kayanta ciki,sai kuma ta tsaya cak.

"Ina yarinyar ta shiga?" Ta tambayi kanta gargadin anni da fuskar daba wasa tana dawo mata,saita saki kayan hannunta ta koma gefen gadon ta zauna.

Wani gumi ne ya tsargo mata tana jin hankalinta ya fara kadawa. Anni tana da power din da bata da ita.....tabbas ne wannan,don idan akace ana buqatar ganin fuskar maman muhammad jadda ta anni ce za'a fara nunowa.....daukakar fu'ad ta sanyashi alaqa da manyan mutane da hankali baya zato,da yawansu kuma suna alaqa da anni a matsayin itace mahaifiyarsa......KENAN UMARNI DAYA ZATAYI A KANTA AYI MATA YADDA TAKESO?.

Tambayar data sanya 'ya'yan hanjinta curewa waje daya kenan,saita jawo wayarta da sauri tana nemam number fu'ad.

Kiran duniya wayarsa a kashe,ta kira tun tana irgawa harta bacewa lissafi,sai ta aje wayar kawai gefe tana tunanin meye abunyi?.

_πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚,maganin dan banza karen maguzawa ko inji hausawa.....shin a wannan lokacin hajiya maamah xata shiga hannu ko kuwa?_

_meye hasashenku?_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 102



102


Tsaye take gaban qawataccen madubin bandakin me tsananin haske da hasken rana daya soma mamaye sararin samaniya ta bullo ta wasu sassan glasses na bandakin ya kutso ciki.

Daure take da bathrobe me tsananin taushi,fara qal data zauna a jikinta bisa taimakon igiyoyin dake maqale a jikinta,saman kanta daure da towel data nade gashinta me tsaho da santsi,wanda ruwan da ya jiqashi ya sanyashi kwanciya ta gaban goshinta dama wasu sassa na wuyanta. Brush ne riqe a hannunta.....amma sai ta kasa matsa toothpaste a jiki,saita buge da kallon fuskarta ta jikin madubi data fito tarwai kaman ka saka hannu ka ciro.

Daren jiya ke faman mata yawo cikin kwanya......tanata tuna shudewar kowacce daqiqa a tsakaninta dashi. Iya yawan abun kunyar data tafka bazai barta hada idanu dashi ba,ba zata iya ba sam koda daidai da minti daya.

Duk yadda take tunanin abun zaizo kaman na farko sai komai yazo mata da ba zata,saida komai ya kammala sannan ta tsinciki kanta tsakanin hannuwansa,bata da wani zabi illa fashe masa da kukan kunya. Ya sani sarai......yasan abinda takema kukan,amma sai yayi kaman bai fahimta,ya lalace sosai wajen rarrashinta......daga qarshe ya juye mata tashi kalar shagwabar data sake tsumata,ta sanyata tayi luf ba shiri tana jin kunya da nauyinsa suna kamata.

Zare brush din daga hannunta da taji anyi ya sanyata firgita

"Good morning sleepy head" Ya fada yana tsaye daga gefanta ya kashe mata idanu yana qoqarin saka mata toothpaste din.

"Morning" Ta fada tana sadda kanta qasa tana jin wani irin nauyinsa da bata taba ji ba. Tunda taji ya tashi ita taqi koda motsawa,har yayi wanka ya fito yayi sallah yadan fita a dakin,fitar nasa tayi amfani dashi tayi wuf ta shiga wankan da xummar ta shirya kafin ya fito tayi sallah ta sake boyewa cikin duvet.

"Feel free......brush kawai zanyi na fita" Ya fada yana matsowa bayanta. Dab da ita ya tsaya,har jikinsa yana gugar nata,fuskarsa ta fito bayan tata ta cikin madubin,ya zube idanunsa fes da suka qara wani irin haske saman tata fuskar ta cikin madubin. Wani irin murmushi ne kwance a fuskarsa.....wata irin shimfidaddiyar walwala da makamanciyarta bata taba wanzuwa saman fuskar tasa ba da annuri suke fita daga fuskar tasa. Qwayar idanunta yaketa laluba yana son ya kalla amma ta hana mishi kallo,ta zura brush din kawai a bakinta tana wankewa tana kuma jin yadda yake sake shigewa jikinta da sunan brush zaiyi.

Ta gefe da gefen cikinta ya zura hannuwansa ya zari brush dun,ya saka toothpaste duk a hakan yana sake shige mata,ya tura brush din bakinsa ya soma wankewa shima a hankali yana sake maida idonsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login