Showing 441001 words to 444000 words out of 557259 words
ko mutuwa nayi za'a binne ni a tsakiyarta".
Wani gigitaccen yanayi maamah ta shiga,idanunta bibbiyu duka a warwaje take kallon sabreen din. Kalaman yarinyar na yau sun girmi hankalinta,saidai duk da haka zuciyarta tana tuna mata ita din MARIYA CE FA.....giwa kuma kota fadi tafi qarfin wawa.
"Kinyi kuskuren fara son abinda nice silar zuwansa duniya......"
"Amma ina me farincikin bake kika halicceshi ba ko?" Ta maida mata idanunta tsaye a kanta.
"Ba wani doguwar sa'insa bane tsakanina dake kodon albarkacin wannan dake kwance a marata...." Ta fada tana nuna cikinta da yatsa.
"Sassauqan umarni ne na ki fiddomin mijina ko ina ya shiga.......awa ashirin da hudu kacal kike dashi.....sannan......taron 'yan jarida karki fasa.......hakan shi zai sauqaqewa muhammad sanin asalin launin kalar mahaifiyarsa" Ta qarashe maganar tana daga mata wayar hannunta.
"Maimakon zazzafan labarin uwar riqo me kidnapping dan riqonta.....wataqila sai labarin ya canza akala zuwa labarin BAQAR UWA" Ta qarasa fada da wani mugun confidence daya nuna har cikin idanunta.
Wani gigitaccen kallo maamah ke yiwa sabreen din,wannan wacce irin BAQAR JARABA ta hadu da ita?,sam sam ta mance da batun video da yake cikin wayar,lallai kuwa da ta nemi hanyar da zata salwantar dashi,saidai a yanzun ba salwantar da video din kawai take nema ba......tana neman sassauqar hanyar da zata shafe babin sabreen......ta kuma shafe labarin rayuwarta gaba daya daga duniya.
Ko sau daya itama bata daga qafa daga kallon maamah din ba,a wannan karon tanajin takai maqura.......itama takai qarshe,kuma ko meye zai faru saidai ya faru. Ko kadan bata yi mata kallon bil'adama cikakkiya a yanzun. Tanajin ta shirya tunkarar kowanne yaqi,ta shirya tunkarar kowanne qalubale akan muhammad fu'ad dinta......tana jin ta shirya ta sadaukar da komai a kansa koda hakan yana nufin salwantar numfashinta.
Tsaiwar maamah a wajen yayi mata,don tana jin akwai sauran maganganu daya kamata ta gaya mata,idanunta suna lumshewa da wani irin bacin rai,mararta tana murda mata da wani irin ciwo ta kalli maamah
"Ina kyautata zaton har yanzu bakisan asalin wace sabreen ba......amma lokaci ya kusanto da zata shaida miki ainihin kalarta.......har yanzu baki tunzura sabreen ta nuna miki wace ita ba......to amma yanzu anzo wannan gabar.....duk inda za'a juya duk inda zakiyi ki tsaya tsakaninki da ita,huda nadra haneefa anni farouq musaddiq da saddiq.......uban gayya DUNIYATA fu'ad......wadannan din ahalina ne.....jinina ne,iyaye kawunnai kuma kakannin abinda yake yake cikina ne,uwa uba me gayya DUNIYATA jadda.......taba daya daga cikinsu?" Saita girgiza kanta tana sake tsareta da idanu.
"Bazai taba zame miki abu me sauqi ba.....jeki gwada idan zaki iya.....zabi ya rage naki.....nima wayewar garin goben nake jira.....ki tara 'yan jarida.....idan kinso kiqi nemomin mijina kiga yadda DUNIYARKI zata tarwatse a karo daya" Takai qarshen maganar rashin tsoronta qarara yana bayyana.
"Idan kin fita ki rufen qofan" Sabreen da amai ke tasowa ta fadi tana zamowa a nutse daga saman gadon ta doshi bandaki da 'yar sassarfa gudun kada ta zube aman a wajen.
Dif tayi tana sauraren sautin yunqurin aman da takeyi daga bandaki.....wasu irin taurari suna zagaya kwanyarta tun daga gaba zuwa baya
"Wacce irin lalacewa ce ta sameki MARIYA?" Ta tuhumi kanta da kanta tana jin wani zazzafan gumi yana karyo mata.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 121
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
121
Daga nan inda take tana iya jin kakarin aman sabreen da take kwarashi da wani irin wahala da kuma galabaita. Aman tana yinsa ne da dukka zuciyarta da wani irin karyewa da sarewa,wani irin rauni ne yake cikata a duk sanda ta tuna
"Ba fu'ad a gefanta.....qarfinta.....rayuwarta......kuma duniyarta gaba daya,hasalima ba wanda yasan yana ina......yana raye ko ya mutu,me gobensu zata haifar musu su duka?".
A maimakon tausayi dake sauka zuciyar kowacce 'ya mace a sanda taga 'yar uwarta mace cikin hali na ciwon laulayi saboda sanin ciwonsa da tsananin da yake dashi......a bangaren maamah fitar aman sabreen sai takejin kamar wani sauti ne na barazana a gareta......kamar wani sauti ne dake gaya mata dukkan komai naki ya kusa zuwa qarshe.....asirinki zai tarwatse muddin haduwa da tabbatuwar alaqa yaci gaba da wanzuwa tsakanin sabreen da fu'ad.
"Ya zanyi na cire cikinnan?,ya zanyi na rabata dashi?" Abinda zuciyarta ta dinga gaya mata kenan da wani irin qunci da tsananin takura.
Yunqurin aman shi ya sanya anni qarasowa cikin dakin da wani irin mutuwar jiki da sarewa,zallar mamaki da kuma tsananin tsoron hali da kuma dabi'ar maamah din.
Da baya da baya ta dinga tafiya har takai bakin qofar dakin,idanun maaman akan anni,haka idanun anni din itama akan maamah,saita juya tana fuskantar qofa ta murdata ta fice.
Asalin gigicewa takeji gaba daya har cikin kwanyarta,me yasa duk wani motsi da zatayi sai yarinyar ta zame mata cikas?.....me yasa take zamewa rayuwarta da duk wani motsinta matsala ne?,yaya akayi ta gayyato matsala cikin rayuwarta?. Idan ta duba ta sasanni da dama sai taga takunta na baya yafi kyau......takunta na baya yafi fita akan wanda take fafatawa bayan shigowar sabreen rayuwarta. Batasan me ya dauki hankalinta ba tun a wancan lokacin da har tabar yarinyar da video din bata salwantar dashi ba,ko a sannan tana ganin bata da wani power.....ba kuma abinda zata iyayi?,ko wannan shine sila?.
Cikin tausasawa da tausayawa anni ke riqe da ita,tun tana iya fitar da dan abinda ta samu kurba har ya zamana ba komai cikin aman sai yawu kawai,abinda ya qara adadin galabaitarta kenan,don tanata yunqurin aman kuma babu wani sauran abinda yayi saura a cikinta. Wani hawaye na taru idanun anni sanda take kwance ana qara mata ruwa gudun kada galabaitar ya taba lafiyar yaran da suke cikinta,tausayin sabreen din yana ratsa anni sosai. Ta sani ba abu bane me sauqi wajen mace ta shiga irin wannan yanayin.....ko ita a baya data taba rasa abba,bawai rashi na mutuwa ba,aah saidai rashi na rabuwar aure na dan lokaci,ita kadai tasan me taji,ita kadai tasan ya taji.....ita kadai tasan abinda ta fuskanta,to ballantana wannan,wani yanayi ne da babu tabbas ko sahihancin zance akanshi.....wani yanayi ne da ba wanda yake da tsayayyen abun fada akai. Gefe daya lalurar ciki.....ga qananun shekaru,ga kuma uwa uba me kankat wato MARAICI.
Ta wani bangaren kuma abinda ke daga mata hankali shine.....irin maganganun da taji ana musaya tsakanin maamah da sabreen,wanne irin makami yarinyar ke dashi har haka da ya girgiza mariya farat daya?.
Batasan adadin lokutan data share a zaune gaban sabreen ba,tana riqe da carbinta wanda har yatsunta sun fara zafi saboda riqonsa. Dare yayi nisa sosai,ita kadai ce kawai,don ta hana kowa zama tare da sabreen din sai ita,gani takeyi babu wanda zai iya kula da ita irin yadda takeso,gani takeyi dole ita kadai ce zata iya bata wannan kulawar.
Yadda taga rana haka taga dare,sau daya tak sabreen ta farka tsahon daren zuwa safiya,ta bada tea dan kadan,bacci ya sake kwasheta ta koma.
Sai anni take ganin baccin yafi zama alkhairi akan ta zauna idanun ta biyu tana kuka,ko don saboda lafiyar yaran da take dauke dasu.
*_WASHEGARI_*
K'arfe tara na safe a nan ta yiwa alhj hamza kibiya.....musaddiq da saddiq da sauran guards na fu'ad wadanda suke gida da wadanda suke kan hanya sanda abun ya faru. Iya su uku suka shigo,don ko amna ya hanata zuwa asibitin gudun kada su hadu suyita yiwa mutane kuka.
A sannan anni na gaban gadon sabreen din,tana ta neman yadda zata sanyata taci wani abun komai qanqantarsa.
Karon farko da magana me zurfi ta hada alhaji hamza da sabreen. Shi ya tsaya kan saita saka wani abu a cikinta. Tana kuka hawaye daya bayan daya haka ta dinga karbar tea din daga hannun momma bahijja wadda ta shigo daya baya.
Sai data soma yunqurin dawo dashi sannan ta barta,ta wuce da mug din ta daurayeshi sannan ta dawo dashi ta ajiye.
Shuru ya ratsa dakin na wani lokaci,kowa ka kalli fuskarsa cikin nazari da kuma alhini yake. Alhj hamza ne ya fara magana.
"Toh.....bamu da abinda zamu cewa ubangijinmu sai godiya.....kafin ya jarabcemu da wannan ya mana tarin baiwa da ni'imomin da ba zasu irgu ba....cikar iko da adalcinsa ne ya jarrabi bawa akan dukkan abinda yaga dama a sanda yaso.....to mu ba zamu butulce masa ba,alhamdulillah da duk yadda yayi damu......mun tattauna da masu ruwa da tsaki cikin sha'anin tsaro na qasar nan dama maqwaftanta,kuma suna bamu tabbacin lalubo inda suke ko wani abu daya shafesu cikin qasa da awanni ashirin da hudu in sha Allah......su kansu guard da suke aiki qarqashinsa dukkaninsu basuyi bacci ba,ba wanda ya zauna ko ya kwanta,aiki suke akan batun ba qaqqautawa....kuma ana samun haske sosai,su kansu na yadda da qwarewarsu in sha Allahu komai zaizo cikin sauqi" Ya qarasa maganar yana basu tabbaci a maganarsa dama fuskarsa.
"Ubangiji ya amince....Allah ya bayyana gaskiya a duk inda take" Momma ta fada cikin sanyi jiki da tashin hankali. Sunan sabreen ya kira,ta amsa masa ba tare data iya dubansa ba,don kuwa ita kadai tasan abinda takeji.
Nasiha sosai yayi mata me ratsa jiki da hankali akan imani da qaddara da daukarta.
"Zan dauka abba in sha Allah.....zan dauka" Ta fadi kawai tana sauke idanunta saman tafin hannunta daya wani qara dashewa yayi haske kaman ba cikakken jini a jikinta.
Da daya da daya suka fara juyawa suna fita.
"Saddiq" Ta kirashi abinda ya dawo da hankalin anni kanta don wNi abune da bata taba yi ba. Shima a mamakance ya juyo yana kallonta,sai ta sanya hannu ta yafitoshi.
Dawowa yayi a nutse,y jawo kujerar da momma ta tashi akai ya ajiye daura da ita.
"Gani adda" Ya fada yana mata duban mamaki.
"Akwai labari da nakeso na fitar kashi uku......kashi daya gidan tv radio dana jaridu......kashi biyun da yayi saura tv radio ne kawai zaiyiwu su haskashi" Ta fada tana dubansa.
Magananta taja hankalin anni,ta kuma tuna mata da duk tattaunawarsu da maamah ta jiya. Sakin kayansu da take kwashewa tayi wanda za'a koma dasu gida,ta tako a hankali har inda suke.
Duban saddiq anni tayi fuskarta ba walwala
"Tashi kaje parlor.....idan na gama hada kayan zan kiraka" Fuskarsa da mamaki da kuma wani zumudi nason jin qarashen maganarsa da sabreen ya miqe,saidai babu yadda zaiyi anni ta katsi hanzarinsa.
Inda ya tashi ta koma ta zauna tana duban sabreen.
"Wanne labari zaki fitar sabreen?"
"Yadda akayi uwa ta zama me dillancin yaronta don kawai ta mallakeshi......yadda wata uwa ta zama azzaluma wadda batasan ciwon 'ya'yan cikinta bama bare na wasu....yadda wata uwa ke burin murqushe 'ya'yanta ta gaji abinda suka bari......yadda akayi sabreena ta zama matar muhammad jadda ta hannun mahaifiyarsa" Sabreen ta fadi muryarta nason karyewa amma tana bawa kanta da kanta qwarin gwiwa,tana jin babu wani abu da zai hanata aiwatar da wannan abun,daga nan zuwa dare muddin bataji komai dangane da muhammad dinta ba. Koda sabreen bata fayyacewa anni komai ba.....annin da kanta ta gama fahimta.....wani tsohon zargi da shakkunta kan maamah lokacin aurensa shine yakeso ya tabbata bayan wani lokaci.
"Akwai kuskure cikin aikata haka sabreen......kinsan wanne kuskure?" Anni ta tambayi sabreen tana son qwato hankalinta da nutsuwarta,domin kuwa ta hangi abubuwa masu tarin yawa cikin idanun sabreen din masu kaifin gaske suna kai kawo.
"Mariya bata da asara.....domin kuwa tata rayuwar tazo qarshe idan aka dangantata da taku......mariya bata da wata asara me yawa,kece kike da jini a jika.....kace kike tara zuri'a yanzu.....domme zaki yiwa kanki wannan barnar?" Anni ta fada tana kallon idanun sabreen tanason taga iya dadin yadda maganar ta shigeta. Kai sabreen ta mirgina gefe....kamar anni ba zata fahimci nata shimfidadden takun ba.....wannan abun wani taku ne kuma tarko ne me kyau idan anyi amfani dashi ta hanyar daya dace......tarko ne da zata kama kowacce kurwa ta maamah din.
"Kinsan wace mariya ta gaske?,kinsan yadda me babban suna suka rayu?" Haka kawai taji tanason ta sakeji daga bakin anni,ta tabbatar koda shi ya gaya mata.....koda shi ya labarta mata bazai gaya mata yadda anni zata sanar mata ba,don haka ta kadawa anni kai a hankali tana dubanta.
A nutse anni ta warewa sabreen komai.....rayuwar fu'ad tun kafin tafiyar mariya da kuma tafiyartata,yadda ta samesu da irin wahala da tasha kafin ta maidashi kalar mutumin da yake a yau,duk wani qalubale da kuma gwagwarmayar rayuwa tasa.
Hannu kawai sabreen ta saka ta lullube fuskarta da tafin hannuwan nata,sai takejin a wancan ranar a Maldives tamkar bai gaya mata komai nasa bama.....kaman ba wani abu daya gaya mata daya shafi rayuwarsa. Ta yaya zata iya controlling hawayenta a fuskarta?,ta yaya zara iya.hana kanta zubar hawaye?,wacce irin asararriyar uwa suka samu?,wacce irin uwace wannan wadda da ita gwara babu?. Lallai ba shakka zatayi komai.....har fiye da abinda take hasashe a baya ma zatayi.
Amma da irin wannan abun nata har anni ke duban ta qyaleta?,me yasa anni ba zata fahimci cewa ita sabreen dama mutuncinta bararre ne a idanun mutane da yawa?......me yasa anni ba zata Fahimci zata iya saudar da komai wa fu'ad ba?,don don mutuncin nata da iyakarsa idanun fu'ad dasu anni?,duk da yafi qarfin D'A tunda wata yarda ce da sassanyan aminci ta samu a muhallin da yafi kowanne daraja.
"Ban gaya miki don kiyita kuka ba.....ban gaya miki don kiyita damuwa da sanya bacin rai ba.....na gaya miki ne saboda ki sani........ba kowanne mutum kake qarar da energy dinka a kansa ba". Kai sabreen ta jinjina tana sauke hannuwanta.
"Taso nayi tarayya da ita wajen raya zunibinta anni......ta kawoni da qarfi da yaji da'irar da ban shirya shigota ba.....saidai a yanzun ina kallon juyewar al'amarin daga sharri zuwa alkhairi...." A nutse itama ta gayawa anni yadda duka komai ya kasance tsakanin ta da maamah a wancan lokacin. Tayi shuru anni tana jin komai yana kwaranye mata,lallai duk inda xa'a qaunaci juna saboda Allah dole a dinga ji a jiki a duk lokacin da wani abu zai kasance da dayan biyun. Ashe ba'a banza ba ta dinga jin wani baqin abubuwa dangane da auren?,ba'a banza ba ta dinga jin rashin gamsuwa da komai?.
Al'amarin maamah sai taji yana sake girma a zuciyarta. Mamakinta tana jin kaman zai fasa ko ya kashe zuciyarta gaba daya.
*_WANI DARE!_*
Ranar ta kasance musu wani dare da dukkaninsu suka kwana suna juyayi da mutuwar mamaki kan halayyar mariya da komai nata.....daren ya zame musu wani dare da sabreen ta kwanta tana jin zata dan dagawa maamah qafa saboda anni data buqaci wurga lamarinta a kwandon shara abita da ruwan addu'a,saidai kuma wannan daren ya zama daren da yayi silar da sabreen ta soma sakin UPDATE akan maamah......wanda batayi tunanin akwai wani abu da zai dakatar da ita ba ko waye ko meye shi!.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 122
122
Har qarfe sha daya na dare anni tana zaune gaban sabreen,lokacinne kuma Dr mubeena ta gama daura mata wani ruwan daya zama shine abincinta yanzu saboda ba wani abu da yake iya shiga cikinta ya zauna,koda ya shiga dimma sai ya fito. Rubuce rubuce Dr mubeena ta kammala yi cikin file din sannan ta rufe,ta ajiye a gefe tana sanya idanunta kan sabreen dake kwance da shirin yin baccin da ta tabbatar qaryarsa ya shammaceta......saidai tasan zaizo ne kadai ta hanyar sinadaran da suka zubawa ruwan dake shiga jikinta,wannan ne kadai yake bata daman yin baccin daya kasance ba natural na qashin kanta ba.
Tausayi sabreen din take bawa Dr mubeena,tako wacce fuska ta kalleta tausayi take bata. Hannu ta miqa ta dauki abun gwajin BP din data gama gwada mata ta riqe a hannunta,tadan sakar mata murmushi wanda sabreen qarfin hali kawai tayi ta maida mata.
"Kiyi bacci sosai Mrs jadda......fi amanillah.....in sha Allah boss yana cikin aminci,Allah baya bari bayinsa na gari su wulaqanta kosu tozarta ko su wofanta" DR mubeena ta fada cikin kwantar mata da hankali. Murmushi ta tattaro da qyar ta samu ta maida mata martani,Dr mubeena ta kalli anni dake zaune gaban gadon kaman ko wanne dare tana riqe da tasbaharta.
"Yau ba checking din dare,BP