Showing 444001 words to 447000 words out of 557259 words
dinta ya kusa dawowa daidai da yadda nake buqata,kuyi baccinku,idan Allah ya kaimu qarfe shida ko biyar da rabi zan shigo". Ta fada cikin girmamawa itama tana jin alhini har cikin qasusuwanta na rashin labarin komai akan fu'ad din. Murmushi kadan anni tayi tana sauke qafafunta daga saman kujerar,yau momma ta dage lallai a bawa anni 'yar tayin kwana ko huda ko ma'u. Ta karbi ma'u saboda ta matsanta dole gobe su wuce mali huda taje tayi ton print dinta duk da a goben zasu rufe.
"Sannunku da qoqari kuma,Allah yayi muku albarka"
"Ameen,Allah ya qara lafiya saida safe" Tayi musu sallama tana fita daga dakin.
Idanunta a lumshe suke kawai,ita kadai tasan me yake yawo tsakanin qirjinta da zuciyarta,a duk sanda kwanyarta zata harba da lafazin.
"Sun harbeshi.....ba'asan inda suke ba!" Sai taji kaman zata mutu......sai taji kaman ba wata tazara tsakaninta da tashin alqiyamarta. Takanji faruwar komai kamar a mafarki.....daddadan farinciki da wata iriyar tsaftatacciyar kulawa tana shirin rikida zuwa tashin hankali da firgici.....wannan kusancin tashin farko ya juye ya koma kewa da tsananin buqatar makusanci izuwa zuciyarta.
Duk dare kafin alluranta su dauketa zuwa duniyar bacci.....duniyar dasu Dr mubeena suka matsanta mata zuwanta badon son ranta ba.....sai rayuwarsu tsakanin Maldives da madeena tayita dawo mata tamkar a faifan CD,takanji inda ana maida hannun agogo baya tabbas data maida.......tabbas data hanasu dawowa nigeri da tana da masaniyar ibtila'in da zai fada musu kenan.
Tun tana iya jin muryar anni da ma'u sama sama har ta daina ji,ganinta da ruhinta suka koma zuwa ga wanda ya yisu nadan wucin gadi.
Shuru da anni taji ma'u tayi shi ya bata tabbacin bacci yayi awon gaba da ita,saita gyara zamanta saman kujerar tana ci gaba da jan tasbaharta,tunanuka kala daban daban suna hana idanunta tafiya duniyar barawo wato bacci da itadinma duk dare satarta yakeyi,bata kuma fiya dogon zango ba yake sakinta,takan farka da mafarki ki razani duk dare,saidai ko sau daya bata taba farkawa ba ba tare da ambaton hasbunallanu wani'imal wakeel a bakinta ba.
Batasan baccin yayi awan gaba da ita ba,har tasbhar hannunta ta sulale ta fadi da hasbunallanu wani'imal wakeel data kasance ta qarshe a harshenta.
Dukkanin daukacin asibitin harda dakin ya dauki shuru,dare ya fara nutsawa awanni suna gudu......a irin lokacin da bayinsa nagartattu ke neman kusanci dashi saman darduma,ashararan mutane kuma suma ke nasu aikin saboda neman duniya da abinda yake cikinta.
Daya daga cikinsu ta samu nasarar kunnowa dakin,ta murda handle din a hankali cikin sanda. Sanye da suturarta ta dazu,suturar qarshe data shigo dakin dasu babu abinda ya canza,daidai da takalminta da kuma dan qaramin hijabin kanta,saidai a yanzu akwai baqin face mask saman fuskarta koma bayan dazu.
Kai tsaye ta wuce parlor din ta kuma tunkari dakin da sabreen ke kwance,ta saka hannu ta bude qofar dakin tana shiga. Daga bakin qofa ta tsaya,ta qarewa kowa kallo,ta kuma tabbatar dukkansu sunyi nisa a baccinsu. Ajiyar zuciya ta saki hakan yana bata nutsuwa da kuma qwarin gwiwar aiwatar da abinda ya shigo da ita,taci gaba da matsawa zuwa gadon da sabreen ke a kwance.
Daidai inda ruwan dake saqale a hannunta ta isa,ta tsaya ta zuba masa idanu. Bisa qa'ida ruwan yake diga kaman yadda ya dace,aiki biyu zatayi a ciki,ta gaurayashi da sinadarin dake aljihun rigarta,ta kuma qara gudun ruwan dake shiga sassan jikinta,wannan shi zai saurin hautsina tsarin jikinta,ya kuma taimakawa sinadarin wajen yin aiki a jikinta da gaggawa.
To amma ta wani bangaren tafison ta fara tabbatar da inda wayar take......wayar itace babban burinta na farko,wanda iya ita kawai idan ta mallaka kaman yadda akayi mata alqawari ya isheta kudin aikinta koda ba'a qara mata komai ba.
Ta tsakanin annin da sabreen ta wuce tana miqa hannunta locker gefen gadon,durqusawa tayi ta soma binciketa a hankali. Sai data hautsine komai bata ganta ba,wannan ya qara gudun jinin jikinta energy dinta ya qaru fiye da yadda ya kamata ya kasance. Tana bala'in son wayar,don itace cikar burinta. Miqewa tsam tayi ta sake wucewa ta tsakaninsu,hannunta gefe da gefen sabreen din ta soma lalubawa ko a nan ta ajiyeta.
Kaman wadda aka tasa ta dinga jin wani sauyin yanayi tattare da ita tamkar wadda aka canzawa muhalli daga wanda take ciki,jin hannu ta gefan kafadarta ya sanyata murmurewa daga yanayin bacci zuwa rayuwar zahiri. Baqon turaren da takeji a hancinta ya sanyata budewa idanunta qanqanuwar qofa da zata iya ganin wanda waye haka keda kusanci sosai a kusa da ita?.
Dr mubeena kamar take gani,amma kuma qamshin da yanayin nutsuwar sam ba ita bace......saidai a idanu a kallon dake a fusge tabbas Dr mubeena ce.
Tabo wayar da hannunta yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya,ta saka hannu ta jawota ta jefata aljihun lab coat din jikinta,sannan ta fiddo hannun da syringe da wani irin ruwa a wata mitsitsiyar roba.
Tas ta soma zuqe ruwan a syringe din,wanda tana dab da kammalawa anni ta motsa bakinta dauke da HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL Tana shafa fuskarta da tafin hannunta.
Fitar hasbunallahu din ya daki qirjinta,ya kuma sabbaba mata faduwar allurar dama robar ruwan,abinda ya sake sakawa sabreen matuqar ankara da ita,ta sunkuya da sauri ta dauki syringe din qirjinta yana dokawa.
Idanu anni ta zuba mata a mamakance,duk da ta juya mata baya bata iya ganin fuskarta. Mamakin yadda suka canza tsari ne na Shigowar likita dakin mara lafiya haka kai tsaye?.
Kaman Dr mubeena take gani......amma kuma abun da mamaki,Dr mubeena da ta musu sallama sai bayan sallar asuba?,me ya dawo da ita?,kuma ta shigo dakin ba tare da sanin kowa ba?.
"Dr akwai allurar data rage ne?" Kai ta gyada mata kawai tana qoqarin qarasa zuqe ruwan a syringe din a gaggauce don ta qarasa cika aikinta.
Hakan bata samu ba kuwa,don hannu sabreen takai mata cikin shammata ta daki hannunta,da syringe din da ruwan sukayi gefe suka watse,abinda ya darsa wani abu da gaggawa a zuciyar anni,ta miqe sa wani irin zafin nama ta damqo kafadarta tana juyo da ita.
Kallon kallo suka yiwa junansu,tana shirin kubcewa anni,annin ta saka hannu ta yage face mask din fuskarta ta.
Baquwar fuska ce da bata santa ba.....kaman yadda ya bayyana fuskar bata Dr mubeena bace.
"Wacece ke?!" Tambayar da anni ta mata cikin madaukakim sautin tsawa daya qarasa farkar da ma'u ta miqe ta zauna sosai ta yunqura ta tashi.
Kai matar ta girgiza,ta juya da gaggawa tana nufar qofa,saidai tuni ma'u ta rigata isa qofar ta danneta ta kulle ta zare key din.
Raba dubanta take kan fuskar anni tana zaro ido waje,hankalinta ya soma tashi tana tunanin girman hadarin da zata shiga muddin ta bari taje hannu.
"Kiban hanya na fita ko kuma na illataku!" Ta fada da wata gurbatacciyar hausa da zata baka tabbacin wani yaren ce daban ba cikakkiyar bahaushiya ba.
Daga annin har matar ba wanda ya zaci haka,saukar kakkauran plastic plate din da sukaci abinc dashi dazu ma'u ta sauke mata a tsakiyar kai,sai gata ta zube qasa warwas zubewar data sanya wayar sabreen silalowa daga aljihunta.
A hankali sabreen data sauko daga gadon ta dauki wayar tana juyata,iya daukar wayar kawai ta bata kowacce irin amsa da take buqata koda matar batace komai ba.
Matsawa anni tayi da hanzari tana kiran security emergency line cikin qasa da minti daya sai gasu sun bayyana a dakin.
Kiran security din ya tayar da kusan duk wani security alert na asibitin,kasancewar dakin babban daki ne,yana cikin VIP rooms da asibitin yake dasu.
Cikin qanqanin lokaci qofar dakin ya cika da security da wadanda ihun security alert din ya tashesu. Kusan kowa yasan wacece a dakin a cikinsu,suna da masaniyar mahaifiyar wace a dakin,don haka fitar security alert daga dakin ya zamana kaman tashin hankali a wajen kowa.
Sanda chief of security service na asibitin ya shigo dakin yana neman ba'asin abinda ya faru ya girgiza. Cikin matuqar tsoro da kuma kaduwa ya shiga bawa anni haquri.
"Am sorry maaa.....muna dukkan iyawarmu wajen bawa madam tsaro,bamusan ya haka ta faru ba.....amma ni da kaina banyi minti talatin da shiga office ba bayan ba gama zagaye na tabbatar kowa yana kan aikinsa,hatta shige da fice na asibitin nan tun bayan faruwan abun muka sake saka ido akai....amma zamu duba in sha Allah,zamu kuma binciketa har sai mun tabbatar daga ina take?,meye kuma ya shigo da ita dakin......muna masu bada haquri". Kai kawai anni ke jinjinawa tana duban matar wadda tuni ta jiqe da fitsari,ainihin mummunar suffarta dukka ta fito saboda yadda tayi wurjanjan da kuka da tsananin tashin hankali. Haquri kawai take bayarwa hannuwanta a sama kaman me addu'a. A haka suka jata suka fice da ita,sabreen ta koma gefan gadonta ta zauna kawai rungume da hannayenta kanta yana cakudewa.
Dr mubeena ta qaraso inda allurar da robar suka fadi ta sanya hand gloves ta daukesu,har yanxu ita kanta a tsorace take jikinta kuma rawa yake. Mamaki ne yake qara kasheta na yadda akayi amfani da kamanninta da komai nata aka shigo dakin za'a cutar da iyalin jadda.
"Zanje dashi lab mu gwada muga meye ma taso zuba mata cikin drip din". Dr mubeena ta fada tana duban securities din guda biyu da suka rage a dakin. Juyawa tayi ta kalli anni da sabreen.
"Ku kwantar da hankalinku,babu abinda zai faru in sha Allah,zasu dan xauna kadan daku kafin daga waje kafin security dinku na gida su iso....don anyi alerting nasu abinda yake faruwa".
"Sannu Dr" Kawai anni ta iya fadi Dr mubeena ta juya ta fice da sauri Dr kamal da yake on duty yabi bayanta abun shima yana girgizashi. Case ne da makamancinsa bai taba faruwa cikin asibitin ba,sai gashi yau yana shirin faruwa akan matar mutum mafi girma da kima cikin idanunsu banda Allah ya kiyaye.
Ajiyar zuciya me nauyi sabreen ta sauke tana dora hannunta saman cikinta a hankali. Wat qqqarfar soyayyar abinda take dauke dashi ya ratsa mata zuciya irin wadda bata taba ji ba,wato tako ta ina farautar rayuwarsu akeyi?,so ake a salwantar dasu gaba daya?,kowa rayuwarsu ta tsone masa idanu ta kowacce fuska?.
"Nayi alqawarin baku kulawa da dukkanin qarfina da kuma iyawata.....nayi alqawarin kula daku har zuwa sanda zaku taka doron qasa......da ran mahaifinku ko babu.....da kulawarsa ko babu......zamu zame masa madubi kuma ababen alfahari in sha Allah" Tayi maganar ita daya tana sakejin kaman wata sabuwar alaqa na qulluwa tsakaninta da abinda ke cikinta da batasan meyeshi ba.
Batasan hawaye takeyi ba saida muryar anni ta ratsata.
"Ki rage damuwa da gaske sabreen ko don diyoyin cikin ki.....karki cutar dasu....Allah shike riqe da kowanne bawa yake bashi kariya....musamman idan ka sallama masa ka kuma miqa masa al'amarinka". Tayi maganar a tausashe tana goge mata damshin fuskarta.
Ba wanda ya iy komawa bacci,abinda ya sanyata yanke shawarar yin alwala,ta daura alwalar ma'u ta shimfida mata abun sallah. Ta jima tana kaiwa Allah kokenta wanda tayi Imani shine sarki guda daya da baya maida hannun bawansa ba tare da ya amsa addu'arsa ba. Sanda ta idar tana zaune kanta a qasa,tana jin tattaunawar guards din fuad daga parlor din dakin. Kusan kowannensu zuciyarsa a kusa take,muryar abdulgafar ce ta qarshe.
"Daga yau koda wasa ba wanda zai sake gigin zuwa kusa da inda take ma......daga gobe zuwa jibi ko da numfashinmu da jinin jikinmu zai qare sai mun lalubo duk inda oga yake,a cikin qasar nan ko africa ko a wacce nahiya ta duniya ma".
Numfashi ta sauke a hankali,ta jawo wayarta tana lalubo number musaddiq. Dole ta fara taba mata nutsuwa kaman yadda tayi musu,dole ta taba kwanciyar hankalinta ko yaya ne,saboda itama tasan kifi na ganinka me jar koma.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 123
123
Cikin qasa da awa daya ta gama turawa saddiq komai da komai da take buqata,sannan ta sauka tana lalubo rubutaccen qur'ani dake kan wayarta.
Ko yaya ne tanaso ta karanta ko zata samu sassaucin zugi da radadin da zuciyarta take mata,don ta dade da fahimtar babu wani abu dake bawa jiki da zuciya nutsuwa irin karatun alqur'anin.
β
Zuwa sanda gari ya qarasa haske abba ya iso,already su musaddiq dama tun cikin daren suka qaraso,saidai da safen musaddiq yadan fita sannan ya dawo.
Dr mubeena ta shigo da sakamakon gwajin,a sannan sabreen din tana zaune ana gyara mata cannula dinta data goce. Idanunta a runtse tana jin radadin yadda ake luguiguta qarfen allurar cikin Jikinta.
"Guba tayi attempting zuba mata.....wadda take bin jiki a hankali ta lalata kowanne organ na jikin dan adam......alhmdlh da ubangiji bai bata nasara ba......inda hakan ya faru to fa da saidai addu'a kawai....poison ne da bashi da magani a nan qasar ko makari kwata kwata". Kai kawai sabreen ke gyadawa tana sake girmama rashin imani da rashin tausayi irin na wanda ya dauki nauyin abun. Zuciyarta tayi wani mugun karyewa fu'ad jadda yana fado mata. Allah ne kadai yasan a wanne yanayi yake a yanzu?,a wanne irin hali yake?.
Da sassarfa take saukowa daga saman nata kaman zata hada matakala bibbiyu. Duk sanda taga kiransa tasan tabbas lamari ya baci,ba kasafai take sanyashi ayyuka ba.....ba kuma kowanne lokaci bane take bashi aiki na sai aikin daya kasance babba.
Yana tsaye tsakiyar falon,hannunsa goye a bayansa yayin da idanunsa ke lullube da baqin gilashi.
"Me ya faru?,ya ake ciki?". Baqin hannunsa ya saka yana cire glass din nasa,bakinsa da yake baqiqqirin ya motsa.
"Aiki ya baci,kuma komai na iya faruwa saboda ta fado hannu a sanda kowa yake abun zargi ne". Hannuwa bibbiyu ta sanya yana dafe qirjinta dake wani irin buga mata,duka idanunta a warwaje tana jin tashin hankali yana zagayata.
Wannan shine aiki na qarshe da take sanya ran samun nasara a kanshi,aiki na qarshe da take da kyakkyawan fata da hasashen indai ya tafi daidai ta gama da matsala daya cikin matsalolin rayuwarta guda uku,aikin data kwana jiya batayi bacci ba tana jiran jin kyakkyawan sakamako a kansa.
"Waye ka bawa aikin?,ina fatan sunana bazai fito ba?" Ta tambayeshi zufa tana yanko mata tana jin kan an mata wanka da ruwan zafi. Kai ya girgiza yana dubanta.
"Ko sunan wanda na bawa aikin bazai fita ba bare sunanki bare nawa,don da kika bada aikin na bawa wani shima ya bawa wani shima wancan wani ya bawa sannan aka bawa yarinyar......nasan yarinyar amma ban bata aiki kai tsaye ba saboda gudun qwacewar rana irin wannan......amma.abinda yafi bani mamaki,itadin expert ce,bata taba missing target ba tunda ta fara aiwatar da irin wadannan ayyukan sai yau ta silarki" Yayi maganar abun yana tsananin bashi mamaki na yadda ta fadi warwas a qaramin aiki irin wannan.
Ajiyar zuciya ta sauke,ita komai ba damuwarta bane......kama yarinyar ko tsallakewarta,nata damuwar shine samun tabbacin nata kubutar da kuma tsiran.
Kujera ta samu ta zauna tana juya tambayarsa. Me yasa rashin nasarar yarinyar da faduwarta bai tashi afka mata ba sai da aiki yazo kansu?. Tambayar data kasa samun amsarta kenan,saidai kawai ta sakawa ranta akwai wani boyayyen abu na daban da sabreen din ke amfani dashi.
"Labari na gaba" Ya fada yana fiddo jaridar