Showing 492001 words to 495000 words out of 557259 words
Hannu ya sanya ya dauki wayartata,ya kuma bude video din da ta ajiye masa. Murya da komai ya fita tassss.....baya buqatar neman qarin bayani,sai kawai yayi connecting wayar da system dinsa,ya shiga aikin duba ingancinsa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Yaji yana maimaitawa bakinsa yana rawa. Duk da ya jima yana hasashe.....ya jima yana kwana yana kuma tashi da tarin tulin lissafin meye da meye maamah zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya ba?,amma sai ya samu kansa da jin komai sabo a tattare dashi.....sai ya samu kansa da jin komai ya zame masa baqo.
Kaman wanda aka yiwa allurar qaimi,sai ya zabura,ya hada connection da kowa dake cikin team dinsa suka fara aiki akan kiran mutanen. Koda kowa ya gaji....koda kowa yana ganin dare yayi a barwa safiya,shi bayajin zai iya hakan......baya jin akwai abinda zai dakatar dashi daga lalubo maboyarsu daga daren nan zuwa asubahi......baya buqatar a wuce haka.
Sanda ake qwala kiran assalatu na farko signal ya harba sosai,kai tsaye kuma ya basu daidai direction na inda network da layin yake motsawa.
"Alhamdulillah" Ya furta yana zarar wayarsa da sauri. Jordan ya soma kira yace ya yiwa su abdulgafar magana......su hadu yanzun a masallaci zasu fita ana idar da sallar asubahin.
Sai daya tabbatar ya gama hada komai sannna ya miqe yana nufar toilet. Yadda yakejin jikinsa kaman yana dab da kasa responding komai......amma ya gayawa kansa sai ya qarasa aikin daya fara,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka. Cikin baqin shirt da wando ya shirya,ya jawo wani boots dinsa ya saka yana dora baseball cap a kansa. Duk wani abu da zai buqata ya hada a back pack ya rataye,ya maida baqin eyeglasses a idanunsa sannan ya fara saukowa a gurguje.
Har yakai parlor din farko wani abu ya fusgi zuciyarsa,sai ya koma da hanzari yana dosar dakunanta. Bai sameta asalin dakinta ba,sai a daki na biyu ya sameta.
Qudundune ya sameta cikin duvet,da alama baccin me jima da saceta ba,don ga cups nan da plate da tayi amfani dashi da sauran ruwa. Har ya qarasa gabanta bata motsa ba,alamu sun nuna baccin daya dauketan me nauyi ne. Saman kanta ya tsaya yana duban kyakkywar Fuskarta,wani matsanancin tausayinta ya saukar masa,ya tsugunna a tausashe ya sauke mata kiss a goshinta don baiso ya tasheta,ya miqe a hankali ya maida hankalinsa ga dakin.
Plates din ya soma tattarewa da cups din,murmushi ya kubce masa. Da gaske ciki yana canza hali da dabi'a,matar da daqyar sai yayi fama da ita take cin abinci,yau itace anywhere anyhow kama abinci take bada wasa ba.
"Allah ya qara lafiya" Ya fada yana ficewa dasu ya kaisu kitchen sannna ya fice daga gidan.
Cikin dukkanin shirin daya kamata suka gewaye area din kafin su sanya kai zuwa ainihin inda na'ura ke basu direction a kai.
Cikin qasa da minti biyar suka nannade qofar gidan suka nadeta tsaf da wani irin qarfe.
Sake kutsawa sukayi da wata irin sassarfa suna bada sanarwar suna qarqashin kamen hukuma,kada kuma wanda ya motsa a cikin su.
Tun kafin sukai ga qarasowa ciki sukayi surrender,ba yau suka fara irin wannan aikin ba,saboda haka sun tabbatar da cewa sun riga sun kamu,tunda kuma suka kai ga cimmasu har inda suke lallai ba makawa basu da sauran wani qofa na fita.
Qoqarin dakatar da fu'ad sukeyi wanda shine na gaba sanda yake qoqarin doke qofar dakin.
"Sir......it may b......." Bai iya bari sun qarasa ba ya yiwa qofar wata Kyakkyawar duka data sanyata bude kanta da kanta. Bindigarsa ya saita akan mutum na farko dake tsaye kafin sauran suma su saita ragowan na dakin. Ya jima da koyar harbi da bindiga,ya kuma mallaketa da license dinta da komai saboda dalilai na tsaro,amma ba kowa bane yasan da hakan.
"Kowa ya cire abinda yake jikinsa,bindiga ko wani qarfe ku zube a nan" Shugaban tawagar ya fada yana daka musu tsawa. Jordan ne ya soke tashi bindigar sannan ya fara zagayasu daya bayan daya cikin qaqqarfan takun nan nasa don tabbatar da kowa ya cire komai dake a jikinsa.
"Hamma....." Muryar amna ta daki kunnensa da wani irin sauti galabaitacce.
Idanunsa ya daga da zafin nama yana maidashi inda sautin yake. Amna ce ke takowa a hankali jiri yana kwasarta daga wani daki dake cikin babban dakin. Maida bindigarsa yayi da wani mugun zafin nama yana dosarta,wanda baikai ga isa ba qarar sautin bindiga ya tashi a dakin.
Cikin tsarewar ubangiji ya bashi ikon kaucewa ya kuma ture amna ya wuce ya bula bango ya nutse a ciki. Cikin qasa da second biyu Jordan ya masa wani irin duka,ya kama hannuwansa ya murdesu ya maidasu baya ya karbi bindigar,sannan ya daki gwiwarsa ya zube a qasa.
"Zakasan kayi mistake........idiot!" Jordan ya fada cikin tsananin fushi yana masa wani mummunan dauri.
Amna ya daga da hannu bibbiyu,ya cire rigar daya dora daga saman rigarsa yana yafa mata saboda yadda take gayarta haka,ba dankwali bare mayafi. Wani irin zafi zuciyarsa takeyi,ya riqe amna da kyau suna takawa kafin ya kalli jordan
"A yau nakeso su fadamin waye ya sanyasu wannan aikin,a yau basai gobe ba!" Ya fada da tsananin zafin zuciya.
Yau din ta koma masa lovey dovey dinsa,ta koma masa amnansa sak ta shekarun baya,ta mance da wani surukuta a tsakaninsu,ta lafe kanta saman kafadarsa tana rera kuka.
Ita kadai tasan ya takeji a zuciyarta da qirjinta,nata duka me sauqi ne,tana tausayin fu'ad ne a sanda sakamakon binciken ya fito sunan MAAMAH ya zama suna na farko cikin wadanda suka assasa dauketa. A baya wani tsoron matar takeji......a yanzun kuwa sai zuciyarta gaba daya ta qeqashe a kanta. Tayita kwanciya ne bayan ta farfado saboda tsoro,saboda tanason ta tsira da mutuncinta. Tana tsoron ta nuna musu ta warke batasan meye next step nasu ba.
Maamah tayi waya dasu har sau ba adadi......taji kuma muryarta ta sake tabbatarwa da cewa tabbas din itace. Abun ya matuqar bata mamaki ita kanta,ya kuma girgizata.
"Wacce irin zuciya ce a qirjinta?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance.
Wani abu me zafi da tauri ya dinga hadiyewa,kai tsaye ya bada umarnin wucewa da amna asibiti don a duba lafiyarta.
Kasa zama yayi ko tsaiwa waje daya,yana jin kaman ya sanya kai dakin da likitoci suka rufu a kanta suna checking dinta. Bashi da wani qwarin gwiwar sanarwa kowa an samu amna din har sai ya tabbatar da cikakken lafiyar amnan,har sai ya tabbatar da cewa ta kubuta da mutuncinta da lafiya da kuma cikakken hankalinta.
A qalla sai da suka kwashe awa guda kafin su fito,cikin lallashi Dr aswad yace mishi.
"Karka damu sir.....komai nata lafiya yake,ba wani abu daya sameta,saidai jikinta da yayi weakening saboda hodar cocaine da suka shaqa mata me yawa.......but shima idan tasha ruwa sosai jikinta zai koma normal in sha Allah".
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya maimaita yana jin zuciyarsa tana quntata. Cocaine kuma?,abar da yayi imani ko a ido aka ajiyewa amna ita ba zatace gata ba.
Dakin ya koma,tana kwance tana bacci,ruwan da suka saka mata saboda samun qarin kuzari yana shiga jikinta. Wayarsa ya laluba ya fara kiran number abba.
Daidai lokacin yake rufe shafin alqur'anisa,inda yakai qarshen suratu yaseen daya dauki gabarar karantata tunda abun ya faru sau wani adadi. Ya samu wannan sirrin daga bakin malam,wanda fu'ad ya raba kudi sosai aketa addu'a da kuma roqon Allah akai.
Bismillah yayi sanda yaga kiran daga fu'ad ne.
"Abba......an karbo amna,lafiyarta qalau alhamdulillah,amma muna asibitinmu tana dan shan drip saboda jikinta ba qwari"
"Allahu akhbar......alhamdulillah.....tabbas ubangiji yayi gaskiya da yace ku roqeni zan amsa muku,Allah kaine abun godiya,sannu sa qoqari muhammadu.......inajin bazan shaida musu ba sai wannan drip din ya qare tukunna ta farka,ni zan taho,kafin sannan ina sanya ran qila ta farka".
"Hakanma yayi abba" Ya furta yana katse kiran. Farouq ya kira da temporary line din da yake using nashi a kwana biyun. Kalamansa dukka irin na abban ne......saidai ya cika da mamakin abinda ya sanya fu'ad ya tunkari gagarumin aiki irin wannan bai gaya masa ba.
"Ba lokaci dude.....na matsu na dawowa da anni autarta....besides ma waye zaiyi gangancin dauko ango ya sanyashi a hadari irin wannan bayan bai gama tantance ma zaqin duniyar daya shiga ba?" Murmushi ya sanya dole farouq din ya saki,sai ya yanke kiran shima murmushi yana subuce masa.
Saidai kuma cikin qanqanin lokaci murmushin ya tsaya masa cak,yaji gabansa yana faduwa,sai ya sake lalubar number wayar CP.
Dab da zata tsinke ya daga,yayi apologizing na fu'ad.
"Ba komai.....nace zaiyuwu zuwa nan da azahar na zauna da dukka mutanen nan?".
"Yes sir......zai yiwu,a gida ko a nan?".
"If possible akaiminsu gida,zanwa abdulfattah waya ya bude musu masauki.....waccan dayar matar dake wancan gidan....me take da suna ma?"
"Bibo ko.....habiba mu'azu"
"Yes......itama a daukota,a hadamin ita a cikin su".
"Okay in sha Allah" Ya fada suna yanke wayar.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 148
*_NACE BA......._*π§π½π§π½
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*ππ
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*ππΎππΎ
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
148
Ba jimawa sai ga abba,shigowarsa kenan farouq shima ya shigo,abinda ya sake zaunar dashi suna tattauna yadda abun ya kasance.
"Amma don Allah me babban suna......zuwa yanzu ya kamata ka daina tunkarar abubuwa haka kai tsaye,bakai kadai bane yanzun kaman baya daka saba abunka gaba gadi,yanzun akwai nauyi akwai iyali da suka dogara dakai".
"In sha Allah abba" Ya fada ne kawai,amma bayajin akwai wani abu da zai hanashi sadaukarwa da iyalinsa ranshi da lafiyarsa muddin yana raye din.
Lokaci ya duba,bayason ya saba magana idan ya yita,don haka ya miqe yana duban abban.
"Abba zanje gida....don sanda na fita tana bacci ne,yanzun haka nasan tana can da tunanin inda naje da kuma inda amna take"
"Maza ka koma kayi mata albishir,ubangiji yayi muku albarka,ya kareku daga dukkan sharrin zamani.....ya tsare gaba"
"Ameen abba" Sai ya juya ga farouq yana bashi hannu,shima bashi yayi sukayi musabaha suna duban juna,a tare a kuma lokaci daya murmushi ya subucewa kowannensu. Farouq ya gode Allah da abba yake a wajen,ya tabbatar da sai fu'ad ya taba masa iya shege komai qanqantarsa.
"Ka gayawa su musaddiq saisu dauko anni tazo ta ganta itama hankalinta ya kwanta"
"In sha Allah oga" Harara yadan balla masa,yasan da biyu ya fadi kalman oga din,sai ya juya yana fita a dakin.
Tunda ta farka daga baccin takejin ta samu sassaucin qunci da bacin ran da takeji. Kai tsaye daga gadon kitchen ta wuce saboda yadda yunwar data tasheta a baccin ke neman sabautata. Koda ta duba agogo sai taga ashe ta zarta lokacinta ne. Tana cin abincin tana sake sallamawa lamarin ciki,tayi imanin banda cikin a yanayin da take ciki a yanzun ba abinda zai sanya ta iya sakawa cikinta abinci.
Tsaf ta cinye ma'u na satar kallonta.
"Ko a qara miki?" Kai ta girgiza.
"Doughnuts dina kawai nakeso......ya qare ragowan na cinye yanzu da tea,don Allah ma'u ki sakamin order,kwali sha biyu nakeso" Ta fada tana goge hannunta da towel jikinta sam ba wani kuzari sannan ta juya tana fita a kitchen din ma'u ta bita da kallon mamaki.
Eh dole ace ciki yana saka wasu hauka,batasan ya zatayi da doughnuts kwali goma sha biyu ba,doughnuts din matar da madarar ciki kawai ta isheka ta sanya kaji ka qoshi koda kuwa rabin guda daya kaci,ba qaramin jarumi bane wanda zai iya cinye guda uku ba,komai cinka kuwa idan har kaci ukun nan ba sauran space nacin wani abincin saboda ka gama qoshi.
"Allah ya raba lafiya" Ma'u ta fada tana jawo waya ta soma lalubar number wayar maman ummee kada a samu akasi.
Wata lafiyayyar kasala ta saukar mata,sai kawai ta yada zango saman sofa din falon. Zuciyarta na cike da mamakin yadda bataji motsinsa ba ko kadan......hakanan kuma bataga alamun ma ya nemeta ba.
"Kodai da gaske yana shirin rejecting maganata da kuma qaryatani kaman yadda mamansa tasha shan alwashin hakance zata faru?"
"Ga alama kuwa.....ya fara doubting akan abinda kika fada". Fada ne ya kacame tsakanin sassan zukatanta guda biyu,daga qarshe taja qaramin tsaki,ta jawo landline ta soma neman number gidan anni saboda tata wayar a hannunsa ta barta.
Daya daga cikin masu aikin ce ta daga,cikin girmamawa ta gaida sabreen.
"Hadani da huda ko.nadra ko haneefa"
"Okay maa" Ta amsa mata a ladabce. Dukkaninsu ta kawo mata,suka bata lokaci sosai suna hira kafin suyi sallama.
Daki ta koma donyin wanka,sai a sannan ta lura an kwashe duk wani datti kwanuka data zubar. Mamaki yadan kamata,amma saita samu assurance na shine ya shigo din ya fidda kayan.
Tsaf ta gyare dakin,ta wadatashi da qamshi daya qarawa dakin wani irin sukuni da nutsuwa,sannan saita wuce tayi wanka. Tsaf ta shirya cikin wata chiffon gown maras nauyi,ta lalubo Malaysian hijab ta saka sannan ta fita.
Kaman ba zata haura saman nashi ba amma ta daure. Tasan bai kamata ta barshi haka bata gyara ba,kaman yadda bai kamata ta bari wani ko wata su hau ba.
Tsaiwa tayi tana qarewa parlor din kallo. Komai yana nan a zube inda yayi amfani dashi,da alama ma a nan parlor din ya kwana,saita taka tana tattareshi tsaf,ta kuma sanya vacuum cleaner ta tsaftace saman dukka ta gyare masa toilet din. Sanda ta gama azahar ta kawo jiki,cikinta kamar an mata yasa,dole ta sauko dining din qasa neman abinci.
Tunda lalurar nan ta kamata ma'u ta haddace,bata taba barin dining din wayam ba komai,kaman yadda bata barinta ta dawo sake cin abinci ta samu maimaici.
A nutse ta zauna ta zuba da nufin soma cin abincin amma kuma sai taji ta kasa. Azahar ta sako jiki sosai,ina yaje?,abunda tun fara shaquwarsu bai taba faruwa ba.
Ta juya abincin har batasan sau nawa ba amma ta kasa kaiwa bakinta,kaman ahakan ake jira ya faru sallamarsa ya ratso parlor din.
Duk da hautsine yake amma kallo daya tayi masa shigarta taji ta burgeta ta masa mugun kyau. Baqi da baqi a jikin fari,saidai duk da hakan saita wani basar ta dauke kanta tana amsa masa sallamar tan jira taga da wanne irin yanayi ya dawo gidan.
Tsam ta miqe sanda taji alamun takowarsa nan dining din,ta tura kujerar tana nufin wucewa,saiji tayi anyi mata wata Kyakkyawar damqa na tare da bata lokaci ba kuma ya mata wata Kyakkyawar runguma da ta sanya qamshin turarensa mai matuqar sanya nutuswa isa ga hancinta.
Saman wuyanta ya aje fuskar ta,kullum alfahari yake d wannan qamshin nata da yasha banban dana kowacce mace.
"Kina bisa wuyana oum triplets......a yafemin,na leqo kina bacci,banaso kuma na katse wannan daddadan baccin nan.....yaya babies dina" Ya fada yana zamewa ya duqa a gabanta yana yaye rigarta.
Maganganunsa daya saba yi da cikin nata yayi da nufin da yaransa yake magana,ta dauka zai tashi kaman yadda ya saba,sai kawai ya jawota yana tsokanarta ta cibiyarta. Janyewa tayi da sauri ya saki dariya.yana miqewa.
"Anga amna"
"Serious hamma....serous?" Girarshi ya dage mata,saita