Showing 72001 words to 75000 words out of 557259 words
don bata fiya bashi muhimmanci ba.
Sama sama ta fara jiyo hayaniya daga tsakiyar gidan nasu,saidai bata wani bada hankali ba,don ba baqon abu bane cikin gidan nasu musamman lokaci irin wannan. A hankali hayaniyar ta fara yin yawa,sai kuma ta fara jin kamar muryar huda cikin hayaniyar. Abinda yaja hankalinta kenan,ta daga kanta daga wayar tana duban nadra da itama tayi kasaqe tana sauraro,saidai batace komai ba,ko wala'alla itama tanason gane cewa muryar hudanne ko ba ita bace. Baqon abune ga dan dakinsu wato yin hayaniya ko daga murya kaman haka. Basu da abokin fada ko adawa,kamar yadda har mahaifiyarsu tabar duniya bata da abokin fadan,saidai kai kayi dasu idan kaso hakan. Hudan ce ma mai dan zafin rai wani lokaci da kuma rashin dagawa duk wanda ya shiga gonarta. Sabreen ta shafeta sosai......amma yana da wahala ka gano haka saboda miskilanci da rashin son shiga shirgin mutane.
A sannu ta tanqwarata ta koya mata hadiye fushi,a dole kuma sukaci gaba da tafiya kan wannan bigiren har kawo inda yanzu rayuwa ta ajiyesu.
"Dubamin.....kamar muryar huda nakeji" Sabreen ta fadi tana duban nadra. Da hanzarinta nadra din ta miqe,don dama abinda take jiran ji kenan daga sabreen. Bin nadra tayi da kallo har ta fice,saidai kafin dawowar nadra dakin kunnuwanta sun bata tabbacin huda ce,saita ajiye wayarta gefe tana duban haneefa
"Auta qarasa karatunki.....kada ki fito ina zuwa" Kai haneefa ta daga idanunta a raunane tana bin sabreen da kallo har ta fice.
Kusan duk wani ahali na gidan dake cikin gidan yana tsaye a tsakar gidan banda mace qwaya daya.....mace guda daya tak da koda mutum zaa dafa a gidan sai tayi niyya ko ra'ayi zaka ga gilmawarta a shiyyar tsakar gidan ma bare akai ga farfajiyar gidan.
Tun kafin ta qarasa idanuwanta suka gane mata da wadda akeyi. Huda da hadiyya......suna tsaye tsakiyar mutane kowaccensu tsamo tsamo a jiqe da ruwa,ruwan da bata raba dayan biyu ruwan wankin da hadiyyan takeyi ne da kuma wanda ke zuba yanzu haka daga famfo.
Kwalar huda na hannun hadiyyan cikin zafi da zafafa
"Zanga uban daya tsaya miki cikin gidan nan.....kibar ganin kamar kun isa kun bunqasa......kun riqar da ba'a saku ba'a kuma hanaku......ni bariki da duk wanda ke cikinta baya bani tsoro wallahi" Ta fada tana waro idanunta waje.
Idanu sabreen tadan runtse kadan tana jin wani abu me zafi yana saukar mata. Ta sani yau Allah kadai yasan adadin tarin maganganun da kunnuwansu zasu amsa cikin gidan. Maganganu ne da aka tarasu cikin qiraje ana neman ranar zubda su,amma ba'a samu ba saboda kiyayewarsu da shiga hurumin kowa sai nasu......yau kam da dama ta samu ba shakka sai iya abinda sukaji.
Bata cewa kowa komai ba sai kutsa kai cikin mutanen data dinga yi a nutsenta sanye da hijabin sallarta,abinda ya dinga jan hankalin kowa da fitowarta kenan.
Bata tsaya ba har sai data isa tsakiyar inda suke abun,a sannan ran huda yayi bacin da itama ta cakume hadiyya. Abinda ya tunzura hadiyya kenan ta daga hannunta a zafafe ta saukewa huda lafiyayyen marin daya sanya huda din sakinta ba shiri.
Cikin tsananin fushi hudan ta zabura don maida martani sabreen ta iso tsakaninsu
"Karki soma" Sabreen din ta fadi duk da ita kanta tasan marin da hadiyyan tayi shiryayye ne da ko waye aka yiwa shi sai yaji matuqa a jikinsa.
"Barta.....barta.....ta tsammaci ni din sa'arta ce,batasan ko yayartata da take kallon kanta jan wuya ba ni nasha gabanta wallahi faufau"
".....yaaya.....kina jin abinda take fadi?,kina ganin abinda tayimin?" Huda ta fadi muryarta na rawa,kuka yana shirin qwace mata amma bataso tayi kukan don bata shirya yinsa a gaban wadannan azzaluman ba. Mutanen da babu rahama tausayi jin qai ko imani a zukatansu a tattare dasu. Mutanen da d'ai basa kallon maraicinsu basa kuma kallon komai a tattare dasu face zallar sharri da mugun fata tare da mummunar makoma.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 40
Idanunta ta lumshe tana gyada kai
"Ya isa huda.....ki wuce daki.....karki sake tsaiwa a nan" Ta fadi tana duban idanun huda. Kai hudan ta jinjina,da alamu umarnin sabreen din ya mata nauyi da yawa,da alama a yau ta bata umarnin da takejin matuqar nauyin bi da dauka.....umarnin da zuciya ke raya mata kamar ta takeshi
"Aikin banza aikin wofi.....ni wallahi na riga na tserewa mutum.....duk iya barikinsa saidai ya ganni ya qyale,ba wanda nake tsoro ko shakka,hakanan babu wanda zan dagawa qafa" Hadiyyan ta fadi tana jujjuya jiki cike da jin taqamar ta daki hudan a bulus.
"Ke meya kaiki ma kulasu?,mutumin da yake kan hanyar samun kwalin degree a fannin likitanci?" Cewar bibo tana bin bayan sabreen da harara wadda tuni ta fara takawa tana barin wajen
"Qyaleno bibo....wani lokaci ajjiye karatun akeyi ai ka nunawa mutum kaima fa ka iya barikin nan ehe...tarbiyya ke sawa kake dage qafa"
"A'ahhh.....akul,zuba ruwa ki kurkure bakinki,'yar nan meye hadinki da bariki?,bariki fa?,suma jaza musu akayi.....don ko yaya ka taba bariki dai dole a samu me gado kota nono sa zuqa" Cak ta tsaya daga tafiyar data fara yi zuwa daki,bugun zuciyarta nason qara yawa dajin lafazin bibo
"Aikuwa dai an tafi lahira an bar musu gado mara amfani wallahi" Hadiyyan ta fadi tana gyara daurin zaninta tana gatsina fuska.
Lafazin hadiyyan ya sanyata waiwayowa,wani irin zafi takeji yana sauka mata a qirji,ranta yana wani irin mummunan baci
"Akul hadiyya.....kul dinki......hawainiyarki ta kiyayi ramar iyaye na...." Kammala daura zanin tayi da gaggawa ta maida hannunta ga qugunta duka tana riqe dasu,fuska da bakinta cike fal da isgili rashin mutunci da wulaqanci,idanunta tsakiyar na sabreen
"Idan naqi ji fa?,kina da sauran wani abu da zakiyimin ne sabreen?". Kai ta dauke sabreen din,tana hadiyar wani yawu me tauri tamkar dunqulallen dan waken da ya tsaya a maqogaro. Kamar ba zata tanka ba kafin ta waiwayo,a nutse ta kalli idanunta tace
"Ki gwada qinjin gargadina mana hadiyya koda na minti guda ne kiga abinda zaya faru?" Ta qarashe maganar cikin jin zuciyarta da ruhinta sun taurare. Akan batun iyayenta kuma komai tana iya aikatashi muddin hakan zai sanya ta kare mutuncinsu daga baki da aibantawar mutanen da basusan me ake nufi da daraja da kuma kimar dan adam ba
"Hadiyya.....rabu da ita.....karki sake ce mata komai don ke din tsatson mutunci ce......kuma muddin hassada tana dawainiya da mutum akan ci gaban daka samu da kulawa ta iyaye komai ma zai iyayi maka don ganin kun dawo daya kai dashi" Kalmar HASSADA ta sanya sabreen waiwayowa ta kalli hadiyyan da bibo din gaba dayansu. Banda yadda ranta yakai maqurar baci da babu abinda zai hanata murmusawa. Wata kalma ce da take daidai da hali da kuma abinda ke cin zuciyarsu a kanta,shine sukeson sanya dukkan qarfinsu su juyar da ita zuwa kanta.
Tana jiyo bibo tana ci gaba da soki burutsunta,sai bata bi takai ba,ta dinga takawa a hankali abinta har ta wuce zuwa dakin su.
Wani zafi da zugi zuciyarta takeyi mata. Wani irin radadi data jima bata ji irinsa ba saboda kawar da kanta daga harka da sabgar kowa a gidan. Tana kallon yadda huda ke zaune tana kuka amma batace mata komai ba. Tasan kukanta guda biyu ne,na tadda hadiyyan taci mutuncinta dasu gaba daya amma sabreen din ta hanata maida martani.
Ita nadra da haneefa sukayi sallansu,don har suka idar huda din tana zaune tana kuka. A hankali ta maida idanunta kan hudan,tana jin tausayinsu dukka yana kamasu. A hakan a sanda rayuwa ta fara musu kyau. A hakan a sanda ta jajirce akansu.....a sanda basu nemi komai a gurin kowa ba......a sanda asirinsu yake a lullube ba tare da sunyi ROKO ko bara ba.....ba kuma tare da sun nema komai a wajen kowa ba......ya rayuwa zata kasance musu a sanda dukka babu wadannan ababen data lissafa?.
"Ki tashi ki dauki pure water kiyi alwala cikin kitchen" Tace da ita tana ci gaba da sauke kanta qasa. Abubuwa ne cunkus masu yawa qasan ranta. Har tayi sallar nadra ta zuba musu abinci daga ita har hudan ba wanda ya samu damar sanya komai a cikinsa. Ta kama haneefa ta tsefe mata kanta,don ba abinda take bari suyi cikin unguwar,bata bari kowacce kalar mu'amala ta hadasu da kowa,tana kaffa kaffa da komai nasu,ta nesanta su da mu'amala da kowa don kiyaye jinsu da kuma ganinsu,tana dubansu tace musu
"Gobe zamu fita kitso,ke nadra kece me nauyi,bazanyi jira ba me yawa don da wuri zamu dawo gida in sha Allah".
"To" Suka amsa mata gaba daya. Ta miqe a nutse ta barsu a falon,don tasan ba zasu kwanta yanzu ba har sai sun gama kallon film din da ake haskawa.
Numfashi ta sauke me nauyi sanda ta zube ruf da ciki saman gado tana lumshe idanunta,sai takejin fitar numfashin tamkar raguwar radadi ne daga zuciyarta. A haka idan ka kalleta zaka dauka bacci takeyi,amma idanunta biyu tana ci gaba da sauraron motsin su nadra jifa jifa daga falon. Radadin da rayuwa ke tafe dashi take tunawa daki daki. Ba wani majibancin al'amari da zata sanya kanta saman kafadunsa tayi kuka.....ba wanda zata amayarwa da irin radadin da takeji.....ba abokin shawara.....ba abokin raba dadi da akasinsa,sai nauye nauye dake aje saman kanta masu tarin yawa.
Har suka kammala komai sukayi shirin bacci suka kwanta tana jinsu,sai da kusan bacci ya daukesu sannan ta miqe don samawa kanta abinda zataci,daidai lokacin taga motsawar huda.
"Huda?" Kai tsaye tayi kiran sunanta don ta tabbatar batayi bacci ba kenan. Abinda kuma ke alamta mata bacin ran da take ciki ne har yanzu yake nuqurqusarta.
Qasa qasa ta amsa mata,sai ta umarceta ta tashi ta zauna. Ba musu ta yaye abun rufar ta miqe ta zauna tana dubanta. Takawa tayi zuwa gaban gadon ta zauna idanunta a kanta. Ta zuba mata idanu na wasu mintuna ta zuba mata,abinda ya yiwa hudan nauyi tayi qasa da kanta,ta buda bakinta a hankali tana jin tsanar gidan dama duka mutanen ciki
"Kiyi haquri adda"
"Yanzu meye ribarki huda?,wace riba kikaci bayan kin tsaya kin biyewa hadiyya?,shikenan kalaman da kunnuwanki keson ji daga bakinsu kinjisu hankalinki ya kwanta?". Hankalinta taji yadan tashi,tsanar rayuwar gidan tare da ci gaba da rayuwa ma a cikin gidan duka tana saukar mata. Ta girgiza kai idanunta suna tara qwalla me yawa
"Ba haka bane adda......bakiji abinda suke fada a kanki bane?,bakiji mummunan jifa da qazafin da sukeyi miki ba?" Ta fada hawaye na saukar mata.
Yawu itama ta hadiya tana qoqarin hana nata qwallar fita,duk da ba qaramin abu bane yake sanya fitar hawaye daga idanunta ba
"Ki barsu suyita fada mana huda?,meye zai gutsireni?,mene ne kena zai gutsireki?......shin kin manta su din su waye?,ko kin manta ne huda?" Kai ta girgiza qwaqwalwarta na tunano mata abubuwa da dama daga halaye da dabi'un mutanen gidan.
"Wannan ya zama lokaci na qarshe da zaki sake maida kai cikin shirginsu"
"Kiyi haquri" Ta fada bayan ta gyada kai
"Ya wuce......ki kwanta hakanan" Ta fada tana dan taba kafadarta.
Dukka wayoyinta ta dauka harda ma wadanda ta basu hutu na satittika dana watanni,sannan a nutse ta wuce zuwa falon. Bata zauna ba sai data zuba abinci,duk da cin abincin nata har kullum tamkar wasan yara yake. Takan tuna umminta duk sanda ta zauna irin haka zataci abinci
"Kedai saidai addu'ar shiriya sabreen.....yarinya kamar mage?,ki dinga lasar abinci?,zakici ba zakici ba?,shi yasa kikejin jiki idan ciwonki ya tashi". Numfashi ta sauke,ta saka hannu tana goge qwallar data cika mata idanu.
Babu wani lokaci ko yanayi da zaizo bata tuna umminta ba. Ba wani dan qaramin sakan ko minti da zaizo ba tare da tuna umminta ya sanyata zubda hawaye. Bangwaye guda biyun da zubewarsu ya sauya rayuwarsu daga wani abu izuwa wani abun na daban.
Kunna wayoyij tayi gaba dayansu ta kuma jeresu a gabanta,ta jawo abincin tana qoqarin tilastawa kanta ci,idanunta na yawo tsakanin fuskokin wayoyin. Haske kusan dukansu suka dinga yi alamun shigowar saqonni zuwa gareta kena. Ta saba da irin hakan duk sanda ta baiwa wayoyinta hutu toba shakka zata samu saqonnin da basu da adadi. Da yawansu tana gogesu ne ba tare da tako duba ba,d'ai d'aiku daga ciki take tsaiwa dubawa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Arewabooks:@Huguma_*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
__________________________
PAGE 41
Kusan a tare wayoyi uku suka dauki ruri dake nuna alamun ana kiranta.
Mashkur mikail da ya'aqoub,abubuwan farautarta da batasan waye a ciki zai fada komarta ba. Ta dinga bin sunayen da wayoyin da kallo cikin canki cankin wanda zata fara daga wayarsa a ciki har sai da suka katse,sai ta barwa ranta wanda ya soma sake kira. Saidai kuma cikin rashin sa'a sai ga mashkur da mikail suna kiranta lokaci guda. Plate din hannunta ta ajiye,ta sanya hannu tana daukan kiran mikail. A lissafinta shine mutum na farko da takeson saukewa daga layinta. Dukka wani binciken halayya nasa suna gwada mata tsantsar dacewar ya karbi sakamako da horo yadda ya dace. Ita kanta batasan adadin abinda zata diba daga gareshi ba,saidai ko banza ta sanya zata sanyasu a muhalli da guraben da suka dace.
A jirkice yayi mata sallama da muryar data sanya ta saka masa ayar tambaya. Ta daga wayar daga kunnuwanta ta duba fuskar wayar tana mamaki
"Bayan neman mata harda caca da harqallolinsa harda shaye shaye?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,sai ta maida wayar kunnenta kawai tana saurarensa.
"Sai yaushe zaki bani dama ne?......ina tsananin kewarki......ina son kasancewa dake" Abinda ya fada kenan yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Katse wayar tayi tana jan dogon tsaki. Baci kawai takeji ranta yana yi kota ina tare da azalzala mata akan mikail. Sai ta jawo wata qaramar waya daga gefanta wadda bata hasken komai ba ta turawa JIB qaramin saqo. Tana jin ya kamata aikinta ya fara ta kansa.
Yadda mashkur yaketa kiranta ba daga qafa ya sanya ta share kiran ya'aqoub ta daga nashi. Kiran ya'aqoub din ma bata mata rai yakeyi,ta tabbatar dukkan wani magidanci me mata irinsa a yanzun yana cikin gidansa ne koda a dakinsa ko a sassan yake. Taga maza da yawa da halayensu,daya daga cikin halayyar tasu kuma da tafi baqanta mata rai take tunzurata shine wannan. Wai ta yaya ma zatayi Aure?,bayan bataga komai ba a tattare da mazan sai munanan dabi'u dake girgiza zukatan matan su haifar musu da muguwar illar hawan jini ko ciwon zuciya?,ko mummunan zawarcin da har ki mutu bazai fita a tarihinki ba?. Har abada tana kallon zaman 'ya mace me cikakken 'yanci a yayin da ya kasance babu igiyar wani a kanta.
"Saura kadan ki kashemin raina muhseena......hala bakisan girman soyayyar da nake miki ba har yanzu?......kinsan Allah?,banqi a daren nan ace an daura aurena dake ba?"
"Aure?" Ta furta a hankali tana jin kalmar tayi mata girma da yawa.
"Yes aure muhseena....." Ya maimaita fada yana gyara zamansa cikin tattausar sofa din da yake kai. Yana fatan samun gamsashen amsa tare da mamakin kansa yadda yarinyar ta sauya masa tsari gaba daya.
"Gaskiya ne" Ta amsa masa a taqaice tana aje numfashi.
Hira ya dinga qoqarin janta dashi,duk da ita din bame doguwar hira bace amma ta dan sake masa,don itace hanya guda daya da take dashi da zata haska mata hanyar gano gurbin da zata dasa bomb dinta.
"Kiyimin alfarma daya mana......ki gaya min credit dinki na yimin rakiya dubai for just one week......ni kuma nayi alqawari zan biya ko nawa ne" Ya fada yana sake jin kowacce gaba tasa tana narkewa da sha'awarta da sonta. Yanajin koda bata shirya aurensa ba......zai kashe mata ko nawa ne suyi irin rayuwar da yake muradi......idan da yiwuwar ta zama tashin a gaba sai ta zama.....idan ma hakan bata samu ba yana ganin duk inda ta kwana sha ne muddin ya tsira da abinda yake qulafucin samu.
"Zan baki dama kiyi tunani......sannan ki yanke ko nawa kikeso muhseena.....ko nawa ne muddin raina zaikai ga muradinsa".
Maganarsa t qarshe kenan data sake sanyawa sabreen mummunan zato ga maza......maganarsa ta qarshe data sanyata ta kusa raba dare tana kuka......ta kuma dinga godewa Allah ta wasu fannin.
Mashkur din data tura masa mabanbantan mabuqata da buqatar neman tallafin da duka duka baikai ko digo cikin abinda ya mallaka ba yasa aka