Showing 483001 words to 486000 words out of 557259 words
isa dakinsa.
"Alhamdulillah" Ya sake maimaitawa yana sauraren bugun da zuciyarsa keyi,sai ya miqe ya soma shima rage kayan nasa jikin sannan ya wuce bandaki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 142
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.....siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashin da babu irinsa_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
142
Sai da suka tabbatar an kai amarya,an kuma dawo,kowacce mota an ajiyeta a muhallinta sannan sukabar farfajiyar gidan shi da saddiq suna wucewa sassansu da tuni kowannensu shima ya kwashe komai nasa banda furniture din ciki,aka kuma shirya a tagwayen gidajensu masu tsananin kyau da fasali.
Saida musaddiq din yayi wanka don yaji dadin jikinsa,ya kuma canza kayansa zuwa sassauqar jallabiyya ta maza. Har zai tada sallah sai kuma ya fasa,ya koma da baya yana dauko wayarsa da tunda suka gama waya da amna ya sakata a charge ya kulle ya barta a dakin.
Yayi hakanne don kada ta matsa masa da kira da magiya,taje ta karya masa zuciya yayi abinda baiyi niyya ba. Sam bayajin zai barta fita a gidan,fita daya yakeso tayi,daga gidan sai gidanshi a gobe in sha Allah.
Ya tarar kuwa da miscal dinta har guda biyar.
"Rigimammiya" Ya fadi yana murmushi sannan ya koma ya zauna yana yunqurin kiranta.
Kiran farko aka gaya masa layin a kashe yake,mamaki yadan kamashi,don zai wahala ka kira amna wayarta a kashe,tunda dai su ba rashin wuta sukeyi ba,inverter ne 24/7 a gidan.
Sake gwadawa yayi aka sake gaya masa hakan,sai ya haqura ya kira saddiq zuciyarsa na raya masa tayi fushi ne dashi bai kaita ba,shi yasa ta kashe wayar don ta rama,shikam bazai iya jura ba,gwara ya lallaso abarsa,
"Huda zaka kiramin,kace tace da amna ta bude wayarta badon halina ba". Dariya saddiq ya bushe da ita.
"Man.....wannan karyar da kai haka?,'yan mazan anni na dab da zubewa"
"C'mon saddiq.....zaka taimakamin ko na shiga gidan da kaina na nemota?".
"Ni na isa?,bari na kira maka ita.....hold on kada ka kashe". Ya fada yana hada conference call .
"Hubby..." Ta furta da shagwabar data sanya musaddiq jin kunya ta kamashi.
"Love ya akayi?".
"Ina kewarka hubby"
"I know love......but mun kusa kasancewa da juna in sha Allah,awanni kadan suka rage.....kina ina?" Ya tambayeta calmly.
"Na boye a daki hubby.....kunyar anni nakeji".
"Anni love?....." Ya fada dariya na subuce masa.
"Anni ai bata da surukai sai 'ya'ya,tasha fadin hakan.....fell free please".
"I will tray hubby"
"Good girl....amna fa?"
"Tun dazun da muka karbi adda fannah ban sake ganinta ba,ina tunanin tana wajen anni".
"Thanks......bari nayi wanka.....get ready zan kiraki ki rage....." Bai qarasa jinsu ba ya yanke kiran,kada suje suyi masa baranbarama a kunne.
Still ya sake kiran saddiq.
"Ina kunyar tambayar anni please saddiq tambayar min ita"
"A nawa?" Ya sake zolayarsa
"Ka fadi price dinka" Ya fada yana jin zaquwa.
"Bari na kira maka din sai mu tsadance" Ya fada yana yanke kiran.
Minti daya kacal saiga kiran saddiq din.
"Anni tace suna tare da huda,gashi kuma huda tace tana wajen annin". Gaban musaddiq ne yayi wata irin mummunar faduwa,haka kawai yaji fargaba tana ratsashi.
"Ya akayi haka?....amma,ina zuwa" Musaddiq ya fadi yana yanke kiran,sai ya zura flip flops dinsa yana fita a dakin.
Kacibus sukayi da saddiq wanda ya fasa wankan shima ya zura tasa rigar.
"Ko wani dakin ta shiga bacci ya dauketa" Saddiq din ya fada shima yana jin haka siddan tsoro yana kamashi.
"Haka nake tunani"
"Muje cikin gidan" Saddiq ya fada yana yin gaba musaddiq da yakejin kaman an sabule masa gwiwoyinsa ya bishi a baya.
Harabar gidan ba kowa don kowa ya gaji ya wuce makwancinsa,baqi suna can shiyyarsu a bangaren baqi na gidan,a haka suka kutsa sassan anni.
"Kira anni kice ta sauko" Saddiq yace da badawiyya me aikinta,ta amsa da to. Harta fara haurawa saddiq ya dakatar da ita yace ta dawo sai ya haura da kansa.
Ya samu annin tana cire dankunnayenta da sarqa,saita juyo da mamakin ganinsa a irin wannan lokacin tana kallonsa.
"Ya akayi saddiq?"
"Amna fa bata wajen huda anni,kota gaya miki tana wani gurin?,dakunan wajen nan kuma mun duba kafin mu shigo,wayoyinta switched off". Yankewa gaban anni yayi ya fadi,hannuwanta data miqa kunne don cire dan kunnenta sai taji sun mata nauyi dole ta ajesu tana dubansa.
"Kun gama duba gidan nan gaba daya?". Kai ya girgiza.
"Kusan ko ina dai anni" Hannu kawai ta miqa ta dauki mayafinta ta yafa tana cewa.
"Muje". Tare suka sauko dashi,ta dubi musaddiq.
"Qarfe nawa ta kiraka kira na qarshe?".
"Takwas da rabi anni mukayi waya,tace zataje gidan BB nace ta bari if possible zan dauketa na kaita taga gida mu dawo....idan bai samu ba tayi haquri,na saka wayar charge saida muka gama komai na koma daki na samu miscal dinta me yawa,na kira kuma wayar a kashe take". Wani abune ya tsargawa anni,a jikinta kawai taji wani baqon abu yana shirin faruwa,don amna bata taba irin wannan ba. Koda garden na gidan zata shiga saita gaya ma anni ballanta ace ta fita ko tayi nisa da gida irin haka.
"Kiramin duk masu aikin gidannan" Anni ta buqata tana duban badawiyya. Da sassarfa ta juya,ba jimawa sai gasu kafataninsu,annin ta leqa daga qofar falon ta gaya musu,matan su bincike cikin gidan,mazan kuma wajen gidan dama kewayensa,saita koma cikin falon ta zauna kawai tana jin qafafuwanta suna dab da gagara daukarta.
Kimanin mintuna biyar matan suka dawo,saidai kowacce abinda take gaya mata shine.
"Bamu ganta ba"
"Ba kowa a dakunan"
"Bata nan". Shuru kawai annin tayi tana jan hasbunallahu wa ni'imal wakil tana dakon dawowar mazan.
Jimawa kadan suka kammala nasu duban suma,har zuwa qofar gidan. Kasa tashi annin tayi,don haka tace musu su shigo parlor din kawai.
" Mun duba duk inda ya dace ace mun duba din,tun daga cikin gidan nan har street din daga farkonsa har qarshe amma bamu sameta ba,bamu samu kuma komai nata ba"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,hasbunallahu wa ni'imal wakil" Anni ta fada tana runtse idanunta,fargaba tana kamata.
Gaba daya rasa abun yi tayi,hakanan kuma ta rasa abun fada kwata kwata,kwanyarta ta daure tamau kamar bata tunani me kyau ba tunda take.
Fu'ad da farouq dukkaninsu suna gidajensu da matayensu,abba kuma baya nan,a yadda sukayi magana a safiyar gobe qarfe takwas zuwa tara jirginsu zai sauka. Kai ta girgiza,ba wanda zata bari ya sani a cikinsu,ba wanda zata dagawa hankali.
"Anni ko su yaa fu'ad za'a kira?" Saddiq da tuni hankalinsa yayi qololuwar tashi ya fada. Kai ta girgiza tana miqewa.
"Ban yarda ku gayawa kowa komai ba a darennan,don ba abinda hakan zai amfanar saidai ku daga musu hankali,bayan koda sunzo ba zasu yanke abun yanzu yanzu ba,sai wanda ya qaddara faruwar hakan ya qaddara warwarewar lamarin...." Ta fada cike da tauhidi da qarfafa imaninta,duk kuwa da cewa ita kadai tasan abinda takeji.
"Kuje kuci gaba da kula da aikinku....kuma ku wuce zuwa safiya ko asuba muga abinda Allah zaiyi" Annin ta fada tana duban kowa.
Kowa din ya juya ya fice,amma banda musaddiq dake qame a wajen,tamkar ma baisan abinda yake faruwa ba.
"Musaddiq" Anni ta kirashi cikin dakiya. Kansa kawai ya daga ya kalli annin,don yasan baida sautin da zai iya amsa mata.
"Kayi haquri kaje ka kwanta"
"Kwanciya anni?" Ya tambayeta kaman baya fahimtar hausa.
"Ta yaya zan iya kwanciya bansan halin da take ciki ba?,anni ina aka kaita?,waye ya dauketa?,me tayi musu?,me sukeso?,amna ce fa?.....kwata kwata shekararta nawa?,waye ta tsarewa wani abu?" A nutse anni ke karantarsa,ta fahimci kaman abun yanason fin qarfin kwanyarshi ne,don haka ta kira saddiq.
"Ko baka kwanta ba kaje kayi addu'a musaddiq mu barwa wayewar gari" Tsam.ya miqe ba tare daya kalli koda saddiq dake jiransa ya tashi su tafi ba.
"Ina zaka?" Saddiq ya zaburo yana tambayarsa gami da shan gabansa.
"Zan fita nemanta ne,tunda kai baka damu da ita ba" Ya fada da alamun tashin hankali muraran akan fuskar sa. Kai saddiq ya girgiza
"Akwai hadari a fitarka musaddiq,tunda ko su waye sukayi hakan bamu sansu ba,bamusan dalilin daya sanya suka aikata hakan ba,bamusan kuma meye manufarsu ko target dinsu ba".
"Ko report sai naje na shigar,ba zasu dauke mana mutum.sukutum da guda mu kulle qofofinmu mu kama bacci ba kaman kaza suka dauka" Anni ta fahimci da gaske abun ya soma haurawa tunaninsa ne,don haka ta tako gabansa tana kiran sunansa.
"Kanason jefa amna a hadari bayan wanda take ciki?" Kai ya girgiza da qarfi.
"Yayi....to kada ka soma wani motsi ko aikata komai har sai munji daga bakin yayyenku.....qila fitar da zancan shine zai zama namu kuskuren.....kayita karanta ya hayyu ya qayyumu birahmatika astagis". Kafin ta dire ya kama,a hankali sai yaji hankalinsa yana daidaita,ya miqa hannu ya kama hannun saddiq da kanshi yana cewa
"Muje".
A parlor dinsu ya zaunar da saddiq shima ya zauna yana matsowa dab dashi,ya kalli saddiq din sosai muryarsa tana Rawa
"Saddiq tsoro nakeji su waye?,tsoro nakeji karsu cutar da ita,saddiq munaji muna gani a hannunsu zata kwana?,wanne irin gurin kwanciya zasu bata?" Wanne kalan ruwa da abinci zasu bata?" Sosai saddiq ya riqe hannunsa yana fadin.
"Kayita maimaita fadin ha hayyu ya qayyumu din kamar yadda anni tace......bamu zalunci kowa ba in sha Allah ba wanda Allah zai dorashi a kanmu".
Sun jima yana riritar musaddiq kafin ya samo nutsuwarsa 'yar kadan,saidai ko cikakken zama ya kasa bare ayi maganan kwanciya,kai kawo.kawai yake tsakanin qofa window zuwa farfajiyar gidan,yana jin kamar ya zura da gudu ya tafi neman amanansa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 143
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
143
β
A nutse ya shafa addu'a daga sallar asubar da suka idar shida fanna din tasa,koda bai kalli madubi ba yana iya jin yadda qwayar idanunsa suka tasa,wanda bana komai bane saina kukan farinciki daya dinga yi a daren jiya. Yaso yayi haquri ya kauda kai saboda walimar da za'a gudanar a yau,amma inaaaa.......ya gaza jurewar,har sai da yakai ga inda zuciya ruhi da gangar jiki suke muradi.
Juyowa yayi gaba daya gareta,tana zaune a takure,kanta a qasa tana duban yatsun hannuwanta.
Ita dinma fuskarta duk ta tasa,saboda kusan tare akayi kukan,tana yi yana tayata. Idanu ya lumshe ya budesu yana jin nishadi yana saukar masa. Kullum cikin zulumin yadda zai taddata yake,saboda ya sare da halayen 'yammatam yanzun duk da cewa yana da cikakken yarda da dabi'unta,to amma wani lokaci abun ba'a kama bane ko siffa.
"Taho nan flower" Ya fada da sassanyan muryarsa yana miqa mata hannunshi. Bata wani musa ba ta miqa masa nata,don tana buqatar inda zata jingina taji dadin zaman.
Jawota yayi zuwa jikinsa yana rungumeta tsam,yana jin wata shaquwa tana tsaga jikkunansu,yana jin kamar ta tabbata a rungume a jikinsa kaman haka.
Qoqarin gaidashi takeyi,ya amsa mata yana shafa kanta ya amsa cikin kulawa. Sosai ya dinga jero mata addu'o'i,kanta a qasa tana amsa masa da matuqar alkunya. Mintuna kusan goma sha biyar suka debe a haka kafin ya gyara mata zamanta,ya ciro alqur'ani guda biyu ya bata daya ya dauki daya.
"Ko na minti biyar ne flower,saboda mu bude wunin rayuwarmu na farko da neman albarka". Ya fadi yana miqa mata. Rainon anni ne wannan ta saba musu da farawa da qur'ani,kaman yadda yasan itama fannah din 'yar gado ce wajen iya sarrafa harshe a qur'ani.
(Ina kira a gareku iyaye,kiyi qoqari a mazauninki na uwa ki wadata kwanya da harshen 'ya'yanki da qur'ani,su zama gwanaye wajen karanceshi daga bango zuwa bango,idan da hali suna karantawa suna fahimtar ma'anar,saboda hakan yana taimakawa wajen zaunar dashi a kansu yana kuma taimakawa wajen sake jin asalin gard'insa da dadinsa. Allah ya sani ina mamaki naga babban mutum babbar mace ko sangamemiyar buduwa musulma,amma ba zata iya karance miki qur'ani daga bango zuwa bango ba,ko ba zata iya biya miki wani adadi me yawa ba,don kwanyar da aka horata da qur'ani zaka sameta da kaifin basira da fikira me tarin yawa,Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da yaranmu akan hakan,ya shirya mana zuria kafatanin musulmi Allahumma ameen).
Suna kammalawa kira yana shigowa wayar tasa. Fannah ce ta miqo masa da hannu biyu ya karba yana murmushi
"Allah yayi miki albarka" Saidai sunan daya gani mamaki ya kamashi,baiyi zatonma zaa kirashi da safe da wuri haka ba shi yasa ya bude wayar.
"BB ba'a ga amna ba tun daren jiya......ga musaddiq nan ya rikice mana,kaman yanason rasa nutsuwarsa,ka sanar da hamma don Allah" Abinda saddiq ya fada kenan yana katse Kiran.
Innalillahi yakeso yaja,amma kuma bayaso yayi abinda zai tashi hankalin fannah daga wayewar garinta a rana ta farko,ballantana yasan mata da rudewa qwarai,dan qanqanin abu sai su maidashi babba,don haka ya miqe tsam da wayar a.hannunsa yace.
"Ina zuwa" Ya soma takawa yana fita a dakin. Tadan bishi da kallo kadan,sai kuma ta miqe tana ninke abun sallar da suka idar.
Wani dakin daban ya bude ya shiga,sannan ya fara qoqarin kiran fu'ad yana kuma laluban kayan da zai sauya a jikinsa,idanunsa akan agogo yana duba qarfe nawa.
Su dimma rufe alqur'aninsu kenan,don a yanzun shine malaminta. Tayi sauka tun kafin rasuwar mahaifinsu,tana da tilawa a kanta,amma sai yanayin karatunsa da qira'arsa suke mata dadi,wannan ya sanya ya zame mata malami duk bayan sallar asuba suke tilawar abinda ya sawwaqa tare.
Wani lokaci ido take zuba masa idan yana karatun. Komai Allah ya bashi,duk wata baiwa da take nuna cikar dan adam ya sameta,abu guda daya ne ya masa cikas da naqasu shine MAHAIFIYA.
Kashingidar da yayi da wannan damar ta samu ta zame jikinta zuwa kitchen. Wata irin mahaukaciyar yunwa take fama da ita a dan tsukinnan,ko cikin dare ta tashi abinci takeci,ba jimawa kuma take rasa komai,cikinta yake yayewa tasss kaman an mata yasa.
A tsaitsaye ta hada oats ta madara tasha,kafin sannan saiga ma'u ta shigo.
A mutunce suka gaisa,zuwa sannan ta fara gane inda sabreen tasa gaba na bawa mijinta kulawa da karan kanta.
"Me zamu dafa?"
"Ummm.....bari muga.....bari na fara dafa masa paw paw tea tukunna" Ta fadi tana nufar tsararren store dinsu.
Duk kusan ganyayyakin da yakesha akwai a ciki,busassu anyi packaging nasa cikin wani leda ta musamman da ake kawowa daga china. Packet na Paw paw leave din ta dauko ta dawo,ta wankeshi da kyau ta tafasa ta juye masa cikin wani Traditional English tea set sannan tace da ma'u.
"Ki fiddo naman kai bari naje na dawo".
Ta shiga daidai sanda ya fito daga toilet yana goge ruwan alwala. Idanunsu suka gauraya waje daya,kowannensu ya sakarwa dan uwansa lallausan murmushi.
"Barka da tashi sleepy head" Ta fada cikin salon tsokana. Fadada murmushinsa yayi har fararen jerarrun haqoransa suna fitowa.
"Barka kade my super girl" Ya bata amsa yana karbar tea tray din yana ajiyewa saman drawer. Hannunsa ya miqa mata yana jawota cikin jikinsa,saidai kuma sulalewa tayi ta tsugunna tana gaidashi. Amsa mata yayi cikin murmushi kafin ya miqa hannu ya sake jawota ya rungumeta tsam,fitinannen qamshin kabbasarta na incense by kabo daughter daya hautsina har cikin gashinta da kuma lab lab dinta suna tashi da wani sassanyan qamshi daya manne a fatarta.
"Fatan shalelena ta tashi lafiya.....addarmu.......matar babban yaaya" Yadda ya fadi maganan ya sanyata tuntsirewa da dariya,ya sake kamota yana qanqameta a jikinsa.
"Ina yara na?,fatan sun tashi lafiya?" Ya furta yana qoqarin dage rigar baccin jikinta.