Showing 474001 words to 477000 words out of 557259 words
sabrrrr.........kiyi haquri kici wannan din,i promise you da safe wancan din zakici as breakfast"
"Really?" Ta tambaya tana tsareshi da idanu.
"In sha Allah" Ya fada yana bata assurance. Hankalinta taji ya kwanta,amma duk da haka ta ture wancan din
"Banasonshi....nata yafi dadi yafi madara" Dariyarsa ya boye,yana mamaki ashe da gaske masu juna biyu suna haka?,idan madara takeso suna da ita kala kala har sai ta ture,amma ya tabbatar yace tasha din ba sha zatayi ba.
β
Tun sanda amna tabar dakin sai taji ta gaza nutsuwa sam sam,hankalinta ya kasa kwanciya,itama sai ta samu kanta da rashin nutsuwa da kokwanto.
Toilet ta wuce,ta daura alwala,ta dawo ta shimfida abun sallah. Raka hudu tayi ta zauna ta fara karanta hasbunallahu wani'imal wakil qafa dubu. Ko kadan batajin bacci a idanunta,haka kuma batasan meye ya dauke baccin a idanunta ba.
Bayan ta gama ta sake gyara tasbaharta. Bismillah hirrahamanir rahim 450 ta karanta,sannan tayi salati 450 shima. Bayan ta gama ta karanta (Allazina qala lahumunnasu innan nasa qad jama'u lakum fakshauhum fa zadahum imanan wa qalu hasbunallahu wani'imal wakil zuwa fanqalabu bini'imatimminallahi qafa 45(ko 450 idan zaka iya),ta sake karanta salati 450,sannan ya azizu ya khafi ya qawiyyu ya ladifu 450,duk inda takai guda 100 saita tsaya ta jaddada roqonta ga Allah,neman tsari daga dukkanin wani mummunan abu ko abun qi da zai iya samunta ko ya samu wani cikin ahalinta,ta sake zurfafa addu'ar samun albarka da sanya albarka a dukkanin wadannan aurarraki da akayi dama wadanda suka wuce.(addu'a ce me kyau da tsananin tasiri wajen samun biyan buqata wajen Allah,in kin zama me riqe addu'a da barwa Allah lamuranki kin huta da gasken gaske,shi zai miki komai daidai da yadda ya dace dake,sadaka ce na baku sai a sanyani a addu'a,ubangiji ya bamu dacewa).
Shafa addu'ar tayi tana jin wata nutsuwa tana saukar mata,ta miqe a nutse ta shirya don wucewa gurin abba. Sai data gama shirin sannan ta zauna saman stool,ta debo ruwa a wani babban mug ta soma karanta ayatulkursiyyu qafa ashirin da daya ta fita da mug din a hannunta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 137
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
138
Zuwa takwas da rabi na dare ya shigo gida. Tun kafin ya shiga din ya sallami kowa,don ragowar lokacinsa yana jin cewa na duniyarsa ne.
Yau din sai take jinta a cikakkiyar matar aure kaman kowacce d'iya mace. Ta shirya sosai tayi kwalliya da wani farin tattausan lace,fari ne qal babu sirkin komai a jikinsa. Ya kwanta mata sosai a fatarta,ba makeup a fuskarta,daga powder data dace da skin dinta,sai wheat lips da ya sanya pink lips dinta suke wani glowing me daukar hankali.
Sau daya tak ya kalleta yaji tana son raba masa hankali,sai yake ganin kamar canzata akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,kaman yadda yaji qamshin gidan gaba daya ya sauya.
Qugunta ya kamo,ya kasa cewa komai sai daya sada lips dinsa da nata,ya tsotse lips gloss din da kyau kaman bata taba shafa komai akai ba da wani zazzafan French kiss.
Bakinsa ya zare yana sauke numfashi,idanunshi akan fuskarta,yana jin yadda fatarta dama kayam jikinta suke fidda wani daddadan qamshin turaren kabbasa. Idan baiyi kuskure ba har gashinta data harshi baje saman kafadarta qamshin yake fiddawa.
"Those sweet lips sabrrrr....." Ya fada yana zagaye yatsansa akan shape na lips din nata,yana jin wani shauqi yana fusgarsa. Murmushi ta saki tana dan kauda kanta tanason ta karbi wayoyin hannunsa da wata 'yar kyakkyawar briefcase dinsa. Hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta da sauri.
"Nooo......my lips missed yours sabrrrr......" Ya fadi yana sake hade bakinsu guri daya.
Wani yanayi ya fara saukar musu shi da ita,har qafafunta suka fara rawa ta fara jin ba zasu iya ci gaba da daukarta. Shi dinma hakanne,don gaba daya jikinsa ya dauki shock har sai da suka zube saman sofa sannan ya zare bakin nasa.
"Your lips are the ones.....i want to kiss forever" Ya qarasa fada yana tura hancinsa wuyanta qamshinta yana bugar dashi.
"Sabrrrr.....so kike ki haukatani da alama ko?" Ya furta yana Dubanta da juyayyun qwayar idanunsa kaman wanda yasha wani abu. Fiddo idanu waje tayi tana dubansa,hakan sai ya qara mata bala'in kyau saboda yadda sukayi wani haske,eye lashes din kuma suka zame musu tamkar wani ado.
"Muffin.....me kuma nayi?.....idan na kasheka kuma na zauna da wa?" Tayi maganar ne cikin wata irin shagwaba. Hancinta yaja kafin ya lakuce mata kumatu.
"Fisabillahi zan fadi gaskiyata.....wannan qamshin lallai idan kina tare dashi zanfi tape da taya maqale miki......komai kuma zai iya faruwa ako ina sabrrrrr.......daga ina wannan qamshin?" Ya fada yana kashe mata ido. Murmushi ne ya subuce mata sosai,harga Allah da farko ta dauki turaren ne kawai saboda amna tace ta dauka,cikin irin turarukan da akayi musu ita da huda wanda.ta bakinsa tasan huda sun iso,saidai tana sakawa a burners dake lungu da saqo na gidan ta gama giving up.
Lumshe idonta tayi wani farinciki yana saukar mata,ta bude idanun nata ta saukesu akan kwalbar LAB_LAB da tayi amfani dashi,wanda daga saman kwalbar manyan rubutu ne b'aro b'aro dake dauke da sunan INCENSE BY KABO DAUGHTER.
(Kunsan ni ma'abociyar son qamshi ceπ,na muku tallan turarukan matar nan TASTED AND TRUSTED ne,duk irin turaren da kike siya ina baki shawara ki gwada nata,yayi yayi yayi,zaki kuma bawa wani labari,muddin kina da dama amma baki siya ba ina me tabbatar miki kin loserππ,confirmedππ½ππ½,ba kuma bala'in tsada gareta ba.....sai sirrin sanin kan turaren,nima dai 'yar gidan malam shehu ce bare ace na manya muke using ahtoππ,ki gwada hajjaju zaki godemin,don tabbas idan me tsoron Allah ce ke kikayi kabbasarta kika saka humra ko lab lab dinta ba zaki iya fita unguwa ba saboda fitinannen qamshi suke bayarwa,ki gwada ki godemin +234 803 211 9803).
"Saboda kai ne muffin......saboda kai ne". Idonsa ya lumshe yana sake zuqar qamshin,har cikin zuciyarsa yake sauka,wani nutsuwa qamshin yake bashi,kamar wadda aka tsoma a bahon turare.
"Kiyimin rai please sabrrr" Ya fadi yana sake cusa kanta tsakanin dukiyar fulaninta.
"Name?" Ta tambaya tana murmushi.
"Don Allah kada ki bari wani yaji wannan qamshin idan bani ba". Ya qarasa maganar yana dago kansa gami da sanya idanunsa cikin nata don ta gane har ranshi,da gaske kuma yake maganar.
Tafukan hannayenta dasu kansu qamshin suke ta saka tana dago kansa sosai. Zuwa yanzun tuni ta fara fahimtar yanayinsa....da yayi magana ko baiyi ba....idan yayin daga ina ta fito?.
"Muffin.....kana tunanin zanbar wani hanci ko wani d'a namijin daban bakai ba ya samu wannan nutsatsen qamshin?.....har abada idan kace bakaso ko farfajiyar gidan nan qamshin nan ya fita bazai fita ba......a yanzun hatta da rai ka bani DUNIYATA......Ka bani rai tunda ka kusanto da makusantana kusa dani......dame ne zan saka maka ni ameenatu?" Ta qarashe maganar zuciyarta tana karyewa da wani irin rauni.
Idanunshi cikin nata ya dora hannunsa saman mararta.
"Kin gama sakamin ameenatu.....kin gama sakamin sabreena.....kin gamamin sakayya duniyata da kika bani iri.....yara uku fa?,lokaci guda?,a qaramin lokaci har haka?,kika cikamin muradin zuciyata?......abu daya ne ya rage kiyimin,karki guje ni tsanani ko dadi.....karki bari tarbiyyar yarana ta zama abun Allah wadai......ki soni irin son da ba wanda zaki bawa katankwacinsa.....that's all" Ya fada yana dage hannuwansa sama.
Hannunta ta saka daga qeyarsa sannan ta hade goshinsu guri daya suna musayar numfashi.
"Ka samu muffin.....ka gama samunsu.....amma zan qara da addu'a ga Abba......mutumin da yayi sanadin haifamin irin wannan mijin.....ubangiji ya jiqa kabarinsa ya kuma lullube kabarin nasa da dukkanin wani nau'i na rahamarsa"
"Allahumma ameen" Ya fadi muryarsa qasan maqoshi yana sake jin ta masa kima sosai.
"Abinci ko wanka?" Ta tambayeshi ba tare data dauke goshinta a nasa ba still kuma tana zaune saman cinyarsa.
"Cin abinci sannan kazo kayi wanka yana raunana jiki my world" Idanu ta fitar tana dubansa bayan ta janye fuskarta.
"Muffin.......da gaske komai naka dabanne,tsarukanka dabanne kaman yadda naji ana gulmarka......kasan duk wani abu da zai kiyaye lafiyarka"
"Wait" Yace yana hade ransa da wasa.
"Wake gulmata?,farouq ko?" Dariya sosai ta kubce mata har tana sake riqeshi don kada ta fadi.
"Komai farouq?,komai farouq?.....BB ya kusa hutawa dai,nasan fannarshi zata siya masa 'yanci". Murmushi shima yayi yana kama hannunta suka miqe,shi kansa baisan ya wannan ranar zata kasance ba.....kowa ma ya shiga uku.
Tsaf ya janyeta suka shiga wanka kaman yadda rules dinshi yake,har ya fara zame mata jiki,ya gaya mata sunna ce kuma bazai gaji da rayata ba,don duk wanda yayi koyi da wani abu cikin abinda manzan Allah yakeyi da zummar koyin yake dashi,to tabbas yana da ladan koyi dashi.
Cikin wasu sauqaqan couples pyjamas suka shirya dukkanin farare da adon black wuya da hannu da qafan wandon da bai qarasa idon sahu ba. Kamar wasu ma'auratan daga wata qasar,suka sauka qasa tare.
Bayan kammala cin abincin basu kwanta ba,dukka maganganu ne da shirye shiryen biki yaketa fama. Itadai tana gefe tana kallon zallar aikin zumunci irin ma fu'ad din,ta sake tabbatarwa bawai a banza Allah yaa sanya wannan dukiyar a hannunsa ba(Tabbas idan har Allah ya baka wadata fiye da sauran abokai ko 'yan uwanka,to ya baka ne don ka taimakesu,wala'alla duka harda arziqinsu ya saka a hannunsu don ka zama.silar ciresu daga matsi ko matsala,Allah yana sonka da yayi maka wannan baiwar,don zaka samu lada sanda kake basu ita ta hanyar data dace,don ka zama kamar wakilin Allah a bayan qasa,idan kuwa ka riqe ka hanasu yana kallonka.....tabbas! Kuma sai yayi hukunci akai, 'yan uwa dukiyarka kenan fa.....inaga wanda zai danne haqqin wani?,ina ga wanda zai cinye dukiya ko gumin wani?,Allah yasa mu dace,ya rabamu da taba abinda ba namu ba ya hayyu ya qayyumu).
Ganin ta langabe masa zata yi bacci ya katse maganan da yakeyi da kowa ya dubeta.
"Gate up ameenatu.....naga list na amna.....ke banga naki ba" Ido ta zaro,cikin muryar soma jin bacci tace
"Muffin.......nawa name?"
"Naki lefan.....naki lefen sabrrrr" Ya fada yana kama hannunta.
"Banda wanda akayimin hamma?" Ta tambaya tana dan dariya saboda ta dauka zolaya ne. Kai ya girgiza.
"A yanzun ke din cikakkiyar zabin MUHAMMAD FU'AD JADDA ce,sabon lefe sabon sadaki daga hannun jadda" Ya fada yana zame hannunsa a nata. Qasa ya saka hannunsa ya fiddo wata kyakkyawar leda ya zube kayan ciki.
Kyawawan akwatuna ne har guda shida masu daukan hankali,iya akwatun kawai abun kallo ne,ba zaka gane kuma kallo ya koma sama ba sai daya bude abun ciki.
Wasu irin sabbin designs ne na gold masu matuqar daukan hankali. Uku gold ne uku kuma diamond,wanda ta gane haka ne ta qaramar takardar dake maqale a ciki. Uku ya ware a ciki ya tura gabanta,ya bude wani jaka qarama dake gefan system dinsa ya ciro sabbin rafas na dubu d'aya d'aya na dollars a miqe kar dasu ya dora a sama.
"Wannan shine sabon sadakin ameenatu muhammad jadda.....idan tana buqatar sama da haka tayi magana......wannan kuma" Sai ya tura sauran boxes din
"Wannan kuma ladan rainon cikin da za'a yimin....duk da nasan ban isa na biyasu ba.....duk boxes daya a madadin yaro daya yake.....shima idan baiyi ba kiyi naming price dinki". Kaf jinin jikinta taji ya daskare na wucin gadi,uwar dukiyar daya zube mata kawai take.kallo tana jin zuciyarta tana raurawa,sarqoqi shida masu qololuwar darajar da batasan ya zata kimanta kudinsu ba?,ga tsabar kudi daya kusa naira million dari da sittin?. Tsoro ne kawai taji yana shirin kamata,tsoron ta yaya diyar ahmadu kamarta zata mallaki dukiya dare daya irin wannan?.
Tana shirin zamewa tayi kneeling a gabansa ya dagota.
"Kul karkimin godiya....karki qorafi,kinfi qarfin komai da zan baki,don kema kin bani abinda ban isa ni kadai na bawa kaina ba......kin soni da zuciya daya,kin tsallake duk wani gwaji da nayi miki da zummar gano dukiyar kikeso ko bata gabanki,a yanzu ba abinda bazan iya sadaukar miki ba...bare wannan da ba komai bane cikin abinda Allah ya mallakamin ba.....so komai na dauka na baki kin cancanceshi ne,addu'arki da soyayyarki kadai su nafi buqata a halin yanzu a rayuwata,Allah ya yimin komai". Qasa tayi da kanta tana jin hawaye yana sauka a idanunta,sai ya buge da tsokanarta har sai daya rakata daki,ya tabbatar ta kwanta ya lullubeta da duvet ya tofeta da addu'a. Sai daya tabbatar bacci ya soma cin qarfinta sannan ya dawo falon ya zauna yaci gaba da aikinsa.
β
Sake juya rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan gold tana bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne zube a jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo anata yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah maisharif babaghana .
Sake buda katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a yi komai,shima abu qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a hada da zaman ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba za'ayi ta'adin dukiya ba qarya ne.
"Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da ameenatu?" Ta furta ta daga kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya jinjina mata
"Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje tana ajiye katin.
"Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita gidanta.....sai washegari da ameenatu zata gudanar musu da walima haka ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci.
Wannan karon qaramar dariya ta saki.
"Hakan nima yayimin.....amma kuma dan jahannama.......bazan iya jiran washegarin ba......inaso ranar juma'ar ta zama rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso ranar ta juye musu daga farinciki zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar tonon sililin baqincikinsu". Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi.
"Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai zame musu abun lissafi da irga har qarshen kafuwar zuri'ar"
"Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake wuyanta. Sarqa me tsananin kyau tsada da daraja.
"A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka ne......bayan kudaden da zaku cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace masa bayan ya karbi sarqar,ko a hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar kudade ne masu nauyi akan sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin dadin yadda zai rabauta da riba biyu.
_uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye zaiyi farinciki waye kuma zai shiga sasarin baqinciki?_
_Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana dab da fitowa fili_π₯Ή
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 139
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
139
*_WEDDING VIBES_*
*_KANO & MAIDUGURI_*
Idan aka ambaci umar farouq kibiya,wani mutum ne me wasu irin halaye nagartattu,iya mu'amala da mutane da kuma Tarin abokai,duk da kusan kowanne aboki da zai shigo rayuwarsa yana qoqarin tantance cancantar wanzuwarka a rayuwarsa.
Bikin ya karade kafofin sadarwa masu yawa,ya kuma shiga jerin sahun bukunkunan da kowa yayi amanna zai bada wani irin salo me qayatarwa,duk da ba wani abu me yawa aka tsara za'ayi ba.
Tun lahadi ya yiwa maiduguri tsinke ta jirgin jadda wings,yayin da ya saukewa fuad saboda yanayin hannunsa. Su ahsan da sauran abokansu sune suka zame masa groomsmen.
Duka komai dasa hannun fuad aka kammalashi da wani irin dattako da nuna tsantsar 'yan uwantaka,sunyi fuad din zai taho ranar zaman ajo sai kuma da farouq ya sanya ya masa alqawarin zaije har gurin,saboda yasan halinsa,tun asali dama shi bameson ire iren wadannan abubuwan bane.
β
A nutse suke takowa zuwa farfajiyan da motocin da zasu masa rakiya zuwa airport daga can su zarce Maiduguri. Hannunsa sarqafe cikin nata,kwana biyu din da zaiyi sai yake jin kamar wanda zaiyi shekara biyu ne. Ita kanta duk sai takejin kamar ta sake masa kuka,kewarsa takeji tun bai tafi ya barta ba,duk da takan ji dama dama idan ta tuna in ya tafin itama zata wuce gidan anni don shirye shiryen biki,wanda idan an dauko fannah an kawota nan din,walima za'ayi gagaruma guda daya da anni ta shirya,zasuyi yini randa za'a sauka da fannah,walimar kuma washegari ce,to amma ita din a yanzun ta zama kamar auntyn amaren gaba daya da angwayen. Tuna su huda na tare da itan yana rage mata wani kadaicin,duk kuwa da cewa ba wanda ya isa ya cike wannan gurbin nasa.
Baiko kulaa ko damu da mutane a wajen ba,ya ajiye mata tattausan kiss a goshinta bayan duka sallamar da akayi a ciki.
"Saina dawo?,ki kulamin da kanki sosai,if possible ki dawo gida ki kwana,banaso na tuna cewa baki dakinki kinji please" Kai kawai ta iya gyada masa,don idan tace zatayi magana kuka ne zai qwace mata.