Showing 480001 words to 483000 words out of 557259 words
ranta.
Cikin wani irin mugun matakan tsaro jirginsu ya sauka,yayin da baqaqen motocin dake dauke da tambarin JADDA kimanin ashirin sukayi convoy cikin wani irin tsari me daukan hankali da kuma matakan tsaro sosai bisa umarnin fu'ad.
Lafiya lau suka qaraso unguwar,suka kuma jera kansu zuwa kyakkyawa kuma makadediyar harabar mansion House din alhj hamza kibiya.
Duk wani dake da jibi da ahalin alhj hamza kibiyan yayi tattaki ya fito daga cikin gidan,yayi tsaye a farfajiyar saboda girmamawa ga fannah,wadda aka fito da ita nannade cikin wata lafiyayyar Cotton lafaya butter colour da ratsin maroon.
Yana daga cikin motar amma yana iya ganin komai,yabi kowa da ido da yadda abun ke kasancewa,sai yaji wani abu yana taso masa,don haka ya maida idanunsa ya lumshe.
Lallai babu wani babban arziqi a duniya irin uwa ta gari......babu wani babban jin dadin rayuwa irin samun uwa ta gari.......alhmdlh yana godiya ga Allah a bisa dukkan ni'imomin da yayi masa,kuma ya karba cewa tasa qaddarar tana kan MAHAIFIYARSA tasa jarrabawar tana kan UWA da Allah ya bashi.
Amna dake nade cikin tata lafayar sai wani irin farinciki taji yana lullubeta,tana jin kamar suna dab da gina wani babban ahali ne,yau BB farouq dinta.....ya saddik,ya musaddiq da hammanta dukkaninsu yana da matar aure,wadannan matan kuma kowacce ana sanya ran zata basu baby,babies din da zasu taru su zame musu wata tawaga kuma family na musamman.
Kasa jira tayi a qaraso da fannah,saita taka da dan hanzarinta tana cimmata ta riqe hannunta,abinda yasa matar dake riqe da fannah din sakin hannunta taja baya,wannan ya bawa amna daman magana da ita qasa qasa.
"Welcome to alhj hamza family,welcome to jadda family adda fannah......bansan ya kuke cewa adda da kanuri ba.....anyway muna miki maraba".
"Na gode" Siririyar muryar fannah ta fita wanda ta tabbatar ita daya ta jita.
Cikin girma da martaba dangin anni dana abba suka amshi fannah aka qarasa ciki da ita,bayan anyi addu'a an kuma bawa su anni amanarta,sai annin ta sanya aka ware daki daban aka bawa fannah din ta huta suci abinci sannan sai a wuce da ita gidanta,hakanan danginta suma aka basu wani dakin daban.
Sai data tabbatar babu kowa a dakin sannan ta yaye lafayar dake kanta. Amna da huda ke dakin,hudar da sam ta kasa sakewa,ta hana kowa ma ya ganta throughout saboda surukuta da takeyi da dangin anni.
Musayar murmushi sukayi,amna ta nuna huda.
"Wannan itace huda.....qanwar adda sabreen,matar ya saddiq" Lokaci daya huda ta yiwa fannah,ta miqa mata hannu sukayi musabaha. Ita da amna sai take jinsu karon farko kaman qannenta,don ta tabbatar ta girme musu,saidai ba wani da yawa bane.
Qaramar walima akayi cikin gidan,baqi sukaci suka qoshi suka huta,sannan anni ta bawa fannah kyauta irinta surukuwa kaman yadda ta yiwa sabreen.
*_ME FARUWA!_*
Tun bakwai da rabi aka soma shirye shiryen qarasawa da fannah gidanta. Musaddiq da saddiq ne akan komai na game da shirya motocin da za'a dauketa a qarasa da ita ainihin gidanta dake maqociyar unguwarsu.
Tunda aka fara jera motocin daga harabar gidan zuwa qofar gidan amna ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana bala'in son zuwa gidan ya farouq,wannan yana daya daga cikin mafarkanta tun kafin tasan rayuwa zata juya lokutan aurensu guri guda,tun kafin ta taba tunanin zata kasance qarqashin igiyar auren yaa musaddiq a wannan lokacin.
Yadda kowa ya shirya haka ta shirya,tanason ta tambayi ya musaddiq ko shi ya dauki mota subi ayarin kai amare,a qalla tana tunanin bazai hanata ba,tunda zai wahala idan ta shiga nata gidan ya barta fita da wurwuri,don musaddiq din wani irin tsaro ne dashi tun wancan lokacin ballantana yanzu data zama mallakinsa.
Zaune tayi tana gwada wayarsa,sai data kirashi a qalla sau hudu sannan ya daga.
"Ya akayi baby doll?" Cikin shagwabar nan tata ta narkar da kai.
"Besty.......gidan amarya please,don Allah muje" Idanunsa ya waro waje kaman tana gabansa.
"What?.....aah karmu fara haka dake babe.....zakije amma bayan munyi wasu watanni" . Kukan shagwaba ta sakar masa wadda ta qarasa susutashi,da qyar da ban baki ta shawo kansa.
"Amma kinsan anni zatayi fada ko?".
"Karka gaya mata please,nayi alqawari muna zuwa zamu dawo". Shuru ya danyi,bayan wasu sakanni yace.
"Ban miki alqawari ba gaskiya babe... Kema amaryarce kaman kowa,kodon kinga ban tada rigima a kaiki yau ba?"
"Am sorry besty....don Allah"
"Nace banyi alqawari ba,but ki jirani idan hali ya yiwu zan miki magana saiki fito" A haka suka rabu da musaddiq,duk sai taji ranta ya jagule,tunda taji ya fadi hakan probability na rashin zuwanta yafi na zuwan nata yawa,saita buga tagumi tana zaman jiran tsammani,har sanda aka shigo aka fita da fannah alamun tafiya zasuyi.
Kasa zama tayi,ta lafe a farfajiyar gidan tana ganin yadda motocin suke tashi suna ficewa. Ta duba agogo,ta tabbatar tunda har musaddiq yakai wannan lokacin baice ta fito ba to tayi loosing chance dinta,tabbas bazai kaita ba.
Hawaye taji ya silmiyo mata,daya daga cikin talalar aure kenan,idan dane anni kawai zata gayawa ta fice abinta.
Ko a yanzun ma ji tayi ba zata iya haqura ba,tunda duka motocin gidansu ne zata iya basaja ta bisu,idan an tashi dawowa da dangin amarya ta biyosu ba lallai a gane ta fita harta dawo din,don haka ta silale a hankali tabi ta jikin motar dake fita daga gidan ta saje a jikinta suka fice tare.
Sai data fita din tahau raba ido,ba wata mota a wajen duka sun dauki hanya wata nabin wata,caraf idanunta suka sauka kan wata baqa guda daya dake fake a gefe,sauri take kada musaddiq ya cimmata yace ta koma gida,don haka bata lura da number ba irin ta gidansu bane kawai ta doshi motar kai tsaye.
Sosai abun ya musu dadi,ya kuma yi musu sauqi na ganin ta kawo kanta da kanta,sai ya bude motar kawai yana jiran isowarta,wanda tana isowar ta bude bakinta da zummar tambaya sai kawai ji tayi luuuu an jata cikin motar an maida qofa an rufe. A gaggauce ta bude idonta tana son gani ko musaddiq ne yake mata wasa?,saidai fuskar data gani din a gabanta ba wata alaqa ta kusa ko ta nesa da imani a tare dashi bare a alaqantashi da sunan musaddiq ma.....kafin kuma ta sake tantance komai,sun badeta da wani abu da ya sanyata atishawa,cikin qasa da second biyu ta daina fahimtar komai.
_masu karatu kuyi haquri nayi baqi ne yau din,mu tara gobe in sha Allah......sai ince kowa ya shirya,ranar da kuke jira ce ta tunkaro mu_
Sonsoπ«Άπ½π₯°π₯°
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 141
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET........siya ko saidawa,reposting ko sari_*ππΎππΎππΎππΎ
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
141
Tsararren gida ne da akayi masa wani irin qawataccen gini mai dauka hankali. Tun daga qofar gidan zuwa cikin gidan dole ya burge me kallo saboda yadda komai yake a tsare da wani irin yanayi me jan hankali. Komai favourite na farouq aka saka,fu'ad yayi masa ba zata kaman yadda shima yayi masa.
A hankali ta rufe turaren data gama fesa masa tana dubansa,yayi masifar kyau cikin wani lallausan yadin vicuna da aka yiwa riga da wando da wata 'yar sama me kama da alkyabba. Tsadajjen dinkin hannu da aka shiryashi da zare me daraja.
"Kayi kyau muffin" Sabreen ta fada tana lumshe idonta gami da budesu akan fuskarsa. Hannunta ya riqo a tausashe yayi kissing dinta
"Soyayyarki ce ta saka my world.....but bakisan kin fini kyau ba?" Ido ta zaro waje kana ta saki dariya tana girgiza kai gami da ja baya
"Zolayata kake muffin.....ta yaya haka zai kasance?,kar ka tsaida BB hamma......yau ranarsa ce aje a miqawa sister fannah shi" Murmushi ya subuce masa ya soma zura rufaffun takalmansa tana daga tsaye tana morewa kallon abinta. Sai ya fito fes kaman wani shaihin malami.
Har bakin mota ta masa tattaki,bayan ta tabbatar an saka komai a motar daya dace a kaiwa amarya da angon. A yau kadai data sanya order Youghourt da sauran wasu snacks daga wajen deeja beerva aka kawosu tsaf.......sai ta dinga jin sha'awar koyon duka nau'in wadannan abubuwan. Ta duba handle dinta na tiktok da Facebook,ita dai a rayuwarta zata iya cewa batasan mace kamarta ba. Komai ta iya,idan nace komai ina nufin komai da komai din,kama daga kayan gashe gashe,girke girke,kayan mata da na mazan ma da zaki hada da hannunki.....kayan maqulashe,man kitso,man shafawa kai duk wani abu da dan adam zai buqata musamman mace cikin rayuwarta. Hatta fannin gyara mu'amala da zamantakewar auratayya ta hanyar shawarwari. Kai tsaye ta nemeta ta number dinta ta yanke yin register da ita,kafin ta qara nauyi tanason ta zama cikakkiyar mace tako ina,itama ta hada wadannan baiwawwakin.+234 907 927 4454
(Ba sabreen ba,ni kaina magana ta gaskiya na jima banga mutum irinta din ba,akwai qaruwa sosai tattare da ita,in sha Allah bazan gajiya da kawo muku duk wani mutum da zamanku tare dashi zai amfaneku kuda iyalinku ba).
Home service takeso sukayi tsada ta gama komai. Tun bata ganta ba kirkinta a iya waya kawai yasa hankalin sabreen sake kwanciya da ita.
A nutse ya kashe motar gaban gidan,duk da mai tsaron gate din gidan ya dage qofar tun isowarsu.
Ango farouq dake zaune a seat me zaman banza.....sanye da wata danyar dakakkiyar shadda da iya kallo kawai da idanu zai ganar dakai kudin data lashe.
"Ya ka tsaya a nan kuma?". Girarsa kawai ya dage masa yana zare key din.
"Muje na taka maka kawai.......sabrrrr tana jirana"
"Muma dai Allah ya kawomu dadin abun ko?" Farouq ya fada yana bude side dinshi ya fice.
Da ido farouq yabi kyakkyawan kwandon da fu'ad ya dauko da kansa.
"Da alama wannan aikin adda ne ko?" Farouq din ya fada yana jin wani girma da kimar sabreen suna hauha a ranshi.
"Eh.....ai ta rantse sai wannan tsohon tuxurun ya morewa angwancinsa".
"Ta fiyemin kai ai hundred percent" Farouq ya fadi yalwataccen murmushi na subuce masa.
"Thank god da babu yadda za'ayi dani ai" Fu'ad ya fadi yana yin gaba yana barinsa da wani nannadadden kwali da shima ke cike da tarkacen kayan qwalama.
A veranda din farko fu'ad ya cake yana miqa masa kwandon.
"Meye haka dude.....ka qaraso ku gaisa mana"
"Da wa?" Ya fada yana zaro idonsa waje.
"Fannah" Ya amsa masa kai tsaye.
"Allah you're mad farouq.........kawai sai in shiga gidan mutane kai tsaye har can ciki?.....kaga forget about it please...........ka shiga da cikakkiyar sallama please.....don't forget to recite addu'an da miji yakewa amaryarsa a daren farko......don't forget to pray two Raka'at........fatan alkhairi ". Wani qaunar dan uwan nasa yaji yana kamashi,sai kawai ya rungume fu'ad din cikin jikinsa yana fadin.
" Thank you dude.....thank you,Allah ya cika maka muradinka".
"Kukan zakayi tun yanzun?,akwai sauran awanni" Ya fada jin muryarsa kaman ta karye. Dariya farouq ya saki da risunannun idanunsa yana janye jikinsa daga na fu'ad. Hannu fu'ad din ya sanya yadan daddaki kafadarsa,ya zura hannunsa a aljihu ua fiddo wayoyin farouq din. Latsesu dukka yayi ya kashesu sannan ya miqa masa su yana masa magana da ido akan
"Ka barsu a kashe,kada ka kunna". Sannan ya juya a nutse yana fita a gidan gami da bawa guards umarnin su kulle ko ina a gidan.
Yana takawa zuwa cikin gidan yana jin wani yanayi yana ratsashi. Wani yanayi daba kowanne zai fahimta ba sai wanda yake a matsayi irin nasa.
Da cikakkiyar sallama a bakinsa,tare da qarin addu'ar
"Allahumma adkhilni mudhkala sidqin,wa akhrijni mukhraja sidqeen,waj'alni minladunka suld'anan naseera,rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzileen" (Addu'ace me kyau ga amare ko angwaye yayin shiga gida,ko idan kunyi sabon gida a sanda zaki shigeshi).
Yana yaye curtain din falon duk wani colors da tsari na dream parlor dinsa ya bayyana,lafiyayyen murmushi ya subuce masa.
"My dude.......miskili kafi mahaukaci ban haushi" Ya samu kansa da yiwa fu'ad kirari qasan zuciyarsa. Kowanne taku nasa sai yakejin wata rahama da nutsuwa tana saukar masa,wani irin farinciki yana lullube ilahirin zuciyarsa.
Qawatattun bedrooms din nasu har guda hudu ya dinga budewa daya bayan daya,sai ana biyar din sannan ya ganta.
Nannade cikin laffayar nan da zata baka tabbacin asalin kanuri dince ita,turararren qamshinta daya dumame dakin kuma ya sake gaya maka still KANURI CE.
Sallama ya sake jaddadawa,can qasan maqoshi ta amsa,saidai shi yaji abarsa,murmushi ya sake subuce masa,sai kawai ya duqa yana sabule rufaffen takalmin Gaziano & Glirling dake qafarsa,ya rage saura socks kawai wadda ita tayi masa jagoranci har zuwa bakin gadon da take zaune.
Hannuwanta dake lullube da kyakkyawan zanen lalle ya kalla,baisan sanda ya ajiye wayarsa da keys dinsa gefe ba,ya miqa hannu yana dora tafin hannunsa saman nata tafukan hannayenta ba ya riqesu sosai. Wata sheshsheqa ya saki gami da nannauyar ajiyar zuciya duka lokaci daya,wanda suka fito tare da kalmar
"Alhamdulillah". Karon farko a rayuwarsa da hannunsa ya soma taba na fannah bayan ta zama halalinsa......karon farko da sukayi kusaci da juna har irin haka,duk da yadda yake tsananin sonta,yake kuma shauqinta,itama kuma haka,amma dukkaninsu sun killace hakan,sun kuma boyeshi qasan ransu,ba wanda ya bari dan uwansa ya fuskanci hakan.(qalubale ga matasanmu)
"Babarbariya ta" Ya fada a tausashe da wani taushi da baisan yana dashi ba. Wani suna qwaya daya da ba soyayya ba da yake kiranta dashi,yake kuma mata tsananin dadi.
"Taimaki wannan dan bawan Allahn a bude masa wannan fuskar mutanen maidugurin ya kalla" Ya fada yana zamewa,sosai ya zauna a gabanta gami da komawa kalar tausayi,ya koma kaman wani dan almajiri,sai yakejin tun yanzun kaman zai fara sakin kukan da fu'ad ke cewa ya riqeshi tukunna. Kafada ta maqale ba tare datace komai ba,sarai ya gani,duk saita rudashi.
"Roqo nake badon halina ba" Ya fada yana riqe hannayenta da kyau cikin nasa.
Murmushi ya qwace mata,duk da fargabar da take ciki,sai ta zame hannunta daga nashi a hankali ta sanyasu tana janye lafayarta baya ba tare data daga kanta ba.
"Kan uba!....subhanallah" Ya fada yana wani wantsalawa cikin wani irin mamaki. Fannah ta shammaceshi,tunda suka fari soyayyarsu har suka qare bazaice ga wani shape nata daya taba gani ba,koda da wasa kuwa,a yanzun saiga wata ajiyayyar kyakkyawar halitta kuma dukka mallakinsa ce?,yayi yadda yakeso?. Hannu ya miqa zai zame lafayar daga kafadarta,yanason ya sake ganinta sosai sai ya janye hannun da sauri yana murmushi,yana jin kaman wani shock ke jansa.
"Dan sake budemin please fannah.....i wanted to see you all". Wuyanta ta langabe alamun aah,ai baibi ta kanta ba sai gashi ya dawo gabanta. Hannuwansa duka ya sanya ya dagata,ya miqa hannunsa gefan qugunta inda ta daure lafayar ya wareshi,ya kuma zarce da wareta gaba daya daga jikin nata.
Tsaf ya ware kayarsa,sai yakejin wani abu yana ratsa sassan jikinsa.
"Subhanallazi lam yattakiz waladan wala saheeba" Ya tsarkake girman zatin Allah a abinda idanuwansa suka gane masa karo na farko(qalubale gareku mata,wata sai ran bikinta ma take fidda shape din gaba daya mazan duniya dana media su tayashi kalla).
Ji yayi idan ya qara koda second daya bai sanyata a jikinsa ba kaman zai mutu,sai ya jawota gaba daya cikin jikinsa yana lullubeta da hannuwansa,qamshin jikkunansu suna cakuduwa guri guda.
"Alhamdulillah,first halal hug" Ya fadi a bayyane yana sake godewa Allah da yadda ya bashi iko ya tsare mutuncinsa.
Sai da yayi da gaske ya zame jikinsa,don ya fahimci wannan al'amarin bame sauqi bane,idanma har za'a biyewa ta zuciya da gangar jiki,tabbas dukka addu'o'innan da musulunci ya koyar da sallolin ba zasu samu ba.
"Ki shiga toilet ki daura alwala,ki rage wannan nauyin na jikinki kizo muyi sallah" Ya fada yana tattare mata lafayarta guri daya. Dama gurin tsira take nema,don haka da sauri da sauri ta wuce bandakin ta turo qofar.
Wani wawan tsalle ya buga bayan ya