Showing 429001 words to 432000 words out of 557259 words
ba.
Abu guda daya data sani shine......tabbas fu'ad ya siyawa amna tikitin salwantar rayuwarta......don bataga ta inda zata bari itakam da ranta da lafiyarta ta hada jini da alhj hamza kibiya ba..... Idan fu'ad baiyi wasa ba a wannan karon,zata rufe idanunta tayi hukuncinta kan me uwa da wabi......zata mance da alaqar dake a tsakaninsu tunda har ya iya mancewa da matsayinta a wajensa.
Saddiq musaddiq harma da amna sai lafazin maamah din ya sanya suka fara jin abinda ke ransu yana sassauta,wanda sam ba haka bane a qirjin anni da fu'ad. Wani duba sukaci gaba dayi mata,kowannensu yana son karanto ainihin ma'anar maganarta.
Sun riga da sun sani.........banza bata kai zomo kasuwa......hakanan kowa ya tuba don wuya to tabbas babu lada.......ba haka kawai maamah zata bada amsa ga lamari me girma irin wannan ba......ba haka siddan zata miqa wuya ga al'amarin daya fado bagtatan irin wanna ba.....TABBAS AKWAI WATA A QASA.
Lokacin da idanunta suka kai kan conclusions na gwajin sabreen din sai ta fara qanqance idanunta a hankali,ji tayi kaman debi yaji an watsa mata cikin idanunta kafin a hankali taji kaifin ganinta kaman yana raguwa.
"Ciki?,sati uku?" Tambayar data samu daman motsa labbanta ta yiwa kanta da kanta kenan.
Iskar dakin taji tana mata wahalar shaqa,kamar babu isashiyar oxygen dake wulgawa ta wajen,takai hannunta wuyanta tana janye mayafin data yafa waiko yana cikin abinda ya jawo mata qarancin iska,still sai taji ba abinda ya canza.
Da gaske iska ke neman mata kadan,wannan ya sanya ta soma jan iska da qarfin gaske tana aikawa hunhunta don ta samu taci gaba da numfashi,yayin da ilahirin jikinta ya soma rawa kadan kadan.
Musaddiq ne ya fara ankara da hakan,don fu'ad tuni ya soma takawa xuwa dakin da sabreen take don kaucewa kallon tuhumar da anni ke jifansa dashi. Baida matsala da duk wani tuhuma na maamah ko kuma kalar kowanne qalubale daga gareta,damuwarsa daya yadda annin dama zata karbi abun,ko ita dinma ya shirya mata,don bayajin akwai wani abu guda daya daya dace yayi sama da wannan din.
"Lafiya?.....kaman numfashinta baya kaiwa" Anni data iso gurin ta fada tana duban hannunta wanda takardar gwajin da fu'ad ya bata ta sulale ta fadi a qasa.
Yanayin sautin anni ya sanyashi dawowa da baya,yadan daga qafa yana qarasowa wajen,sai yayi saurin matsawa wayar dake ajiye a dakin don neman daukin likita ko nurses ya soma kira.
Minti guda kacal sai ga mutum biyu tare da likita sun qaraso,saman wheelchair aka dorata sannan suka turata xuwa dakin da yake daura da wannan.
Dukkaninsu suna farfajiyar dakin daga waje,suna jira suji bayanin da likitan zai fito dashi. Duk bayan sakanni sai anni ta daga idanu ta dubi fu'ad,gaba daya ya gama warware mata zaren tunaninta. Wannan wani abune nashi na daban,tsahon zamanka dashi zaku iya qareshi ba tare da ka iya fadin gundarim halayensa ba gaba daya,yakan zo da abubuwan da hankali da tunani basu kawosu ba,yana da bada mamaki irin hakan,saidai bata taba kawowa zai iya aikata qunar baqin wake irin wannan ba.
shima kansa ya sani,duk wani kallo da anni take masa yana cure ne da mamakinsa,saidai ya sakawa kansa wannan dakiyar da juriyar da wani irin basarwa,don haka ko sau daya yaqi kallon anni,saidai yasan shi take kallo ta gefan idanunsa.
Basu wani jima ba suka fito,suka qaraso gaban fu'ad din.
"Ba wani abu bane me tsanani,kawai ta shiga shocked sosai daya sanya jininta hawa lokaci guda......irin wannan case din yana iya jawo mutuwar barin jiki ko bugawar zuciya idan yazo da akasi.....zuwa yanzu dai ita Allah ya tsallakar da ita,saidai kuma jininta yahau sosai,an mata allura ya kuma sauka alhmdlh,nan da awa daya ma zata iya tafiyarta gida.......amma fa sai tana kiyaye saka bacin rai da damuwa a ranta".
"Na gode Dr" Fu'ad ya fadi yana bawa Dr hannu sukayi musabaha ya wuce.
Musaddiq ya kalla sai ya taka zuwa cikin dakin saddiq ma ya bishi. Idonsa yaketa qoqarin kawarwa daga annin don kada su hada ido ya soma takawa zai shiga ya duba maamah din amma sai sautin annin ya katseshi.
"Ka kyauta" Ta fada kai tsaye,abinda ya sakashi dakatawa daga tafiyar da yakeyi kenan. Shuru ya ratsa na wasu mintuna,sai kuma ya dawo da baya a nutse ya tsaya gaban annin.
Hannuwanta ya riqe yana zaunar da ita daidai sanda take fadin.
"Kaga irin abinda ka jawo ko?" Zame takalmin qafarsa yayi ya zauna sosai a gabanta ba tare daya damu cewa marbles bane a wajen.
"Ban jawo komai ba anni.....kuma komai bai faru ba,ko ba wannan maganar irin wannan ranar irin wannan lokacin yana dab da faruwa da maamah....... Tunda muka tashi bamu san wani abu farinciki ba sai a sanadinku.......musaddiq ya rasa abubuwa masu yawa tun yana yaro......yanzun kuma a sanadinta sai a haramta masa abinda yake buri yake muradi yake kuma so?,bayan a baya ya rasa abinda yake buri da muradin kuma duka ya haqura?" Tambayar tasa tadan taba annin,saidai duk da haka sai takejin kaman bai kyauta ba abinda ya yiwa maamah,ko ba komai ita ta haifi musaddiq din ta kawoshi duniya.
Ta bude baki zata sake magana yayi caraf ya riqe hannunta sosai,abinda bai taba yi ba. Idanunta ta daga tana duban nasa idanun,wadannan alamun bacin rai mai tsanani din sun bayyana sosai cikin idanunsa,alamun ranshi ya motsu sosai.
"Kina tunanin ga musaddiq......zan bari amna ta auri wani a waje koda baice yana so ba?,wanin da bamu da tabbas a kanshi?,wanin da ban isa na hukuntashi ba idan ya cutatar da ita duk yadda muke sonta kuwa?.........Karki sake cewa komai anni don Allah na roqeki,bakinki kada ya sake furta komai a kansu idan ba fatan alkhairi ba......indai har yanzu kin yarda kina kuma ji a ranki ni da musaddiq 'ya'yanki ne.....amna qanwata ce halak malak kamar yadda musaddiq yake....to karki sake cewa komai sai fatan alkhairi.....ko meye zai faru.....ko menene zai taso anni na roqeki ki saka idanu.....nike da alhakin hakan kuma nine zan dauka". Gaba daya ya gama kashe mata jiki,ya kuma kashe duk wata kalma da yake da yunqurin fadi. Fu'ad din wani mutum ne na daban,ajiyar Allah ne,yana da kaifi wajen komai nasa,kaman yadda nutsuwa da dattako ta mamaye dabi'arsa gaba daya.
"Kai da abba kuka hada baki ko fu'ad?" Anni tayi tambayar a sanyaye. Wani dariya ya tasowa fu'ad,yayi qasa da kansa yana murmusawa kafin ya daga kansa ya sake maidawa ga annin.
"Ba ruruwan abbanmu.....kada ki sashi a ciki anni,aikin Muhammadu ne,ni kadai na kitsa abuna.....saboda asara ce babba ace ba wata dangantaka da alaqa ta dindindin tsakaninmu da ku anni.....kun gama yi mana komai a rayuwa....kun bamu ruhi me tsafta.....ruhi bana rai ba.....ruhi na dabi'a addini tarbiyya da ilimi da kowanne dan adam yake da buqatarsa........ba wata sakayya da zamu iya yi muku sama da wannan" Shuru sukayi dukkaninsu,jinjina kai kawai anni takeyi. Duk duniya ba wanda zai kaita son hada jini da musaddiq......to amma ita fitina ba abar so bace.
"Amma anni......me kike tsoro ne duk da tarin jarumtar da kike da ita?" Ya fada cikin salon tsokana don yadan bata wani nutsuwar zuciya.
Harara ta jefa masa tana dan murmushi kadan kafin ta amsa masa
"Kafi kowa sanin ameenatu ba raguwa bace.....ameenatu ba matsoraciya bace.....fitina ce kawai ameenatu bataso,ita din me son nutsuwa da kwanciyar hankali ce".
"Na shaida hakan" Ya fada yana murmushi sannan ya sakar mata hannunta.
Miqewa tayi tana cewa
"Muje na dubata.....saika samu kadan zauna da ita,ka kwantar mata da hankali ka fahimtar da ita har ta samu nutsuwa". Murmushi kawai ya saki yana zube hannayensa a aljuhun rigarsa. Anni tana wasu abubuwan kamar batasan halin maamah din ba,kamar ita din baquwa ce a dabi'unta.
A zaune suka sameta saman gadon,har sun zare ruwa da alluran da suka saka mata. Ga oxygen din da suka cire mata a gefe. Dakin shuru,banda qarar ac bakajin komai,musaddiq da saddiq na zaune saman kujera suna zaman kurame su da ita.
Kallo daya tayi musu shida annin ta dauke kanta daga sashensu,don ci gaba da kallon nasu bazai iya Haifa musu da me ido ba,hasali ma jarumtar da take jin zatayi tsaf zata iya kwaranyewa tayi nata wajen.
Shigowarsu ya sanya musaddiq da saddiq ficewa,don dama shikam musaddiq zaman ya gundureshi,hanya kawai yake nema.
"Ya jikin?,Allah ya sawwaqe ya qara afuwa" Ido maamah kawai ta runtse,batason jin sautin muryar anni sam sam. A halin da takeso ta ganta kenan,ta kuma ganta,saidai tana bawa kanta da kanta tabbacin wannan shine gani na qarshe da zatayi mata a haka,next time lallai zai zamana annin ce kwance saman gadon asibiti kamar haka......wannan alwashin saita cikashi koda numfashinta zai qare.
Juyawa anni tayi ya fita tana basu waje,ya matso gabanta kadan yana mata sannu da jiki. Idanu kawai ta zuba masa na wasu sakanni,sannan a hankali ta bude bakinta.
"Ci gaba da qirqirar sabbin kurakurai suma kuskure ne.......yayin gyaran kuskuren kuma komai yana iya faruwa da kowa ma......kasa a maidani gida.....jibi nakeso na koma nigeria" Iya abinda ta fada kenan tana yunqurin sauka daga saman gadon. Baice mata komai ba ya bita da kallo,saidai kowacce kalma data fita a bakinta ya rubutata tsaf ya ajiyeta,ya juya ya taka a hankali yana fita a dakin don cika umarninta.
Tsaye sukayi a farfajiyar asibitin sanda motar da jordan ke tuqawa da maamah din a ciki tana barin cikin asibitin. Musaddiq ya motsa don komawa ciki bayan bacewa ganinsu da motar tayi.
Caraf fu'ad ya damqo hannunsa,musaddiq ya waiwayo da sauri yana duban idanun fu'ad din. Ko sau daya bai kalleshi ba,yaci gaba da riqe hannunsa yana takawa dashi a hankali har zuwa gaban motarsa,yana isa abdulgafar ya bude masa ya tura musaddiq ciki sannan shima ya shige abdulgafar ya rufesu.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 116
______________________________
_kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun yaranki da dinkuna marasa ma'ana?_
_HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS KIDDIES WEARS,irin dinkunan yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki kuma bakisan inda zakikai ayi miki ba ko kina tsoron tsada_
_Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas dagwas_
_ready
_MS KIDDIES na nan kano gwammaja_
*TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani*
_Maza tuntubeta a nan_
+234 708 865 2858
Ko Instagram account dinta
https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA==
____________________________
116
Wadannan tsumammun idanun nasa da ya saba hukuntashi dasu tun yana qanqaninsa ya zuba masa. Wani irin kallon qurilla me dauke da tarin ma'anoni da suka sanya jikin musaddiq yin sanyi tun kafin fu'ad yace komai.
"Wanne irin tsoro nake gani cikin idanunka musaddiq?" Fu'ad ya jefa masa tambayar yana nuna qwayoyin idnunsa da yatsunsa. Tambayar tadan daburtashi,har ya rasa me zaice masa.
"Ashe kai maqaryacin masoyi ne?......bakason soyayya batason ragwantaka ba?,bakasan mata basason ragon namiji ba?,bakasan soyayyarka bata cika soyayya ba sai ka amince zaka iya fuskantar dukkan wani qalubale da hatsari akan masoyiyarka ba?,bakasan soyayya bata amsa sunanta ba sai ta samu sadaukarwa tsananin kulawa da jure duk wani tsanani ba?........you're very stupid musaddiq muddin baka xama tsayayyen namiji ba akan amna......na aura maka amna don ubanka saboda ka kula mana da ita.......ban tsaya a matsayin waliyyinka ba saboda amna ta samu wani uban bayan abba.....ni waliyyin amna ne da bazan lamunci duk wani rashin kulawa daga gareka ba a kanta......ka riqe musu yarinya da kyau.......ka xama jarumi a kanta koda kai rago ne.......wallahi wallahi bazan daga maka qafa ba idan har naga ko naji wani abu mara kyau dangane da ita a kanka ba......yiwa auren amna riqon wasa ko ka bari tsoronka ya jagoranci igiyar aurenta dake hannunka.....to kasa a ranka baka taba sanin wani me sunan muhammad jadda ba".
Gaba daya jikin musaddiq yayi laushi tubus......yana tsananin qaunar amna,irin qaunar da bai taba yiwa kowa irinta ba,to amma kuma tsoron fitinar maamah yana neman dakushe masa komai,duk da yaji cikin ransa ruwa da iska.....ko zaa saka kanshi gabas a yanka bazai iya rabuwa da auren amna ba.
Qofa yasa aka bude masa ya nuna masa hanya,musaddiq ya kalli fu'ad din sai ya sauka salin alin daga motar,yasan ba lallai a yanzu ya wani bawa ban haqurinsa muhimmanci ba.
Abu guda daya tak daya tuna yaji ya kwaranye masa duk wani bacin ransa.....cikinsa dake kwance cikin mararta wanda ita kanta batasan dashi ba,murmushi ya subuce masa ya sauka a hankali daga cikin motar yana komawa asibitin.
A hankali ya tura qofar falon yana shiga,idanunsa suka fada kan anni. Tana tsaye da takarda a hannunta tana dubawa,shigowar tasa ya sakata daga kai ta kalleshi.
Wani kwantaccen farinciki me ban mamaki ya gani saman fuskarta wanda bai taba ganin irinsa ba. Ya zare idonsa yana duban takardar sosai. Takardar dazu ce da maamah ta saki,take ya fahimci dalilin wannan murmushin,kawai sai ya shafa sumar kansa,karon farko yaji kunyar annin ta saukar masa,ya taka da dan hanxari yana wucewa cikin dakin.
Sosai murmushi ya subuce mata,ta saki sassanyan ajiyar zuciya tana jin zuciyarta na wankewa daga dukkan wata fargaba da bacin rai.
"Ubangiji ka rabasu lafiya,ka yiwa abinda aka samu albarka" Ta furta a sarari tana ninke takardar.
Wani sanyi ne yaji yana ratsa zuciyarsa sanda yayi ido hudu da ita. Tana zaune tsakiyarsu huda......haneefa tana gefanta a zaune hannunta cikin nata. Hira sukeyi irin hirar da kana kallon fuskarsu zakasan qauna da soyayya gami da shaquwa irinta 'yan uwantaka ta huda su. Murmushi ne kawai ke fita a fuskarta,wani irin murmushi da yake sake qawata fuskarta da wani irin lallausan kyau me daukan hankali.
Jingina jikinsa kawai yayi da jikin qofar,ya langabar da kansa yana qare mata kallo. Kallo yake mata irin kallon da mutum yakewa DUNIYARSA a sanda tayi masa dadi.....irin kallon da mutum yakewa ruhinsa a sanda yake tsananin buqatarsa da kuma sonshi. Duniyarsa rayuwarsa dama nutsuwarsa gaba daya yake gani tattare da ita.
Daren jiya yake tunawa,wani irin dare me tsayawa a tsakiyar zuciyar masoyi,ta shayar dashi wani zazzaqan abu da bai taba hasashe ko mafarkin akwai irinsa ba sai a lokacin.
Cikin jikinta ta dinga jin kamar akwai wani ido na musamman dake kallonta. A hankali tayi slow da hirar tana watsa idanunta cikin dakin,sannu a hankali ta hango fuskarsa a tsakiyar qofar yana qare mata kallo. Murmushi ya sakar mata wanda ya qara mata nauyinsa,sai ta danyi qasa da kanta,shi kuma ya tura qofar gaba daya yana shigowa.
Tsam momma ta miqe tana fadin
"Qaraso mana......dama masallaci nakeso mu wuce ai,ita ta riqemu wai lallai zamu barta ita kadai,tunda gaka kazo alhamdulillah" Momma ta fada cikin yanayi na surukuta tana maida takalmanta.
A nutse ya qarasa gaban gadon ya bawa haneefa dake zamowa tana sauka daga saman gadon hannu fuskarsa qunshe da murmushi yayi bump din hannunta data miqa masa yana kuma amsa gaisuwar huda da basu hadu da ita dazu ba
"Muna da meeting anjima" Ya fada yana dubansu,sai suka sanya dariya suna bin bayan momma bayan sun amsa masa da
"Yes hamma". Shi da ita duka da kallo suka bisu har suka fice,shine ya fara dawo da dubansa kanta kafin itama a hankali ta maida duban nata kanshi.
"Karki ma fara cewa zaki tambayeni akan mene" Ya rigata fadi,sai murmushi ya qwace mata tayi qasa da kanta.
Idonsa ya lumshe a kanta sannan ya taka a nutse ya jawo kujera zuwa gaban gadonta. A hankali ya zauna yana sake matsowa kusa da ita har gwiwoyonsu na gogar na juna,ya saka lausasan tafukan hannayensa a nutse ya kamo nata cikin nasa yana murzawa a nutse.
"Ameenatu"