Showing 501001 words to 504000 words out of 557259 words

Chapter 168 - ๐ƒ๐”๐๐ˆ๐˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

427

yi saman gadon shi kadai yana jin yadda kadaicinta yake neman hallakashi,kowanne sashe a jikinsa sabreen din yake buqata,kowanne bangare na jikinsa kewarta yakeyi.

"Ya salam ya al-hadi". Yana sawwara ta yadda zai iya yin nesa da ita dalilin tafiye tafiye na kasuwanci......ta yaya hakan zata yiwu?" Ya tambayi kansa da kansa.

Daga qarshe dai ya tabbatar hakan bame yiwuwa bane,ya tashi zaune yana duba qaramin kyakkyawan agogon dake saman side drawers na gadon.

"Oops" Ya furta yana dafe goshinsa,dare yayi,yayi imanin zai wahala idan bata fara bacci ba yanzun,idan kuma har ya zama silar tadata a baccin bazai yafewa kansa ba,sai ya maida kansa ya cusa tsakiyar pillow din yana qagara asuba tayi.

โ˜…Tunda ya dawo sallar asuba ya wuce gym,yana fatan hakan ya dawo masa da kuzarinsa daya rasa a kwanakin nan saboda tashe tashen hankulan da suka durfafoshi. Waya ya dauka kai tsaye ya kira Jordan ya bashi umarni ya koma gida ya dauko masa duniyarsa. Yana so nan din ya zame musu wani kebantaccen guri da ba kowa bane yasan da zamansa,da qwaqwalensu zasu huta na koda kwanaki uku ne kafin su koma cikin jama'a.

Sanda ya kammala shiryawa cikin sassauqar shirt da trouser sai ya wuce parlor. Da kansa ya shiga kitchen ya tafasa madarar shanu fresh one da turmeric dan kadan ginger da cloves ya dawo falon yana sipping kadan kadan yana kamo tashoshin daya saba kalla a lokuta irin wadannan da ake labarai na qasa.

Tashar farko cikin headline na news din hoton maamah ya gifta da anyo briefing na case dinta daga qasa. Zuciyarsa ta motsa tana bugawa da wani irin yanayi,sai kawai ya matsa remote din yana canza tasha.

Channel din daya kama sun fara news tuni,the next abinda ya faru shima dai hoton maamah ne da title tafka tafka na zargin kidnapping.....wannan channel din sun samu nasarar saka wani d'an yanki na tambayoyin da 'yan press din sukayi mata a Farfajiyar gidanta,wanda kusan duk me hankali idan ya kalla yasan maganganu ne kama kai.

"Subhanallah" Ya fadi yana sauke canza channel.

Already su sun gama,saidai.maimaicin kanun labarai da shima hoton maamah dana hajja harira harma dana fareeda da suka cika screen din. A nan ma baida buqatar yaji komai,yasan tunda haka ta faru duk inda zai kunna ma abinda zasu nuna masa kenan tamkar sunsan yana da alaqa da ita.

Wani zafi zuciyarsa ke mass,wani irin kud'a da quna take masa. Ya dauka ko meye maamah tayi....kuma ko meye akayi mata ba wani sauran abu daya rage da zai tada masa hankali a kanta ko ya qona masa rai,sai gashi bayyanarta a screen na TV dinsa yana neman hana mishi nutsuwa.

Har addu'a yakeyi......har fata yakeyi ta zabi adadin abinda take buqata daga gareshin.....mutanen dake kewaye dashi a yanzun,mutanen da yake rayuwa dasu a yanzun suna da matuqar muhimmamci a tattare dashi,mutane ne da bayajin idan wani abu maras kyau ya samesu ta sanadinsa.....ko ta sanadin arziqinsa lallai ba shakka bazai yafewa kansa ba,bazai iya jurewa ya rasa koda rai guda daya a cikinsu ba. Koda maamah ta karbi abinda takeso ta koma inda ta fito,har kullum,muddin da numfashi a gangar jikinsa bazai fasa mata addu'a ta shiriya ba darajar haihuwarsu da tayi.

Idanunsa basa wajen,amma tsaiwarta a bakin wajen yaji a jikinsa,don haka ya daga risunannun idanuwansa yana dubanta.

Tayi wani irin kyau da shigar mutanen turkey,wasu irin riga da wando da dan hijab dinsu me suturce jiki. Ya sauke idanunsa akan cikinta,sai yaga kaman ya qara tasawa,kaman ya qara girma a kwana daya tak da yayi bai ganta ba. Wani sanyi da rahama yaji yana sauka a zuciyarsa,sai ya miqa mata hannuwansa yana lumshe idanunsa,abinda ya bata tabbacin lallai yana buqatarta kusa dashi.

A nutse ta tako,wanda tun kafin ta iso inda yake qamshin nan nata,qamshin kabbasar nan tata ya soma kasheshi daga inda yake a zaunen(incense by kabo daughter....duniya ne sis,ki gwada ko sau daya,basai nace miki gobe ki koma ba,wannan tasted and trusted ne,bawai just normal tallan da bakasan ya kan abun yake ba(+234 803 211 9803).

Kasa dauke idonsa yayi daga kanta saboda wani salon tafiya da takeyi da yake fusgar hankalinsa,har ya qagu ta qaraso inda yake ya shaqi ni'imtaccen qamshin nan da yakejin inama kowanne second da zai shude a rayuwarsa zai samu daman shaqarsa?.

Kaman tasan da hakan,tana zuwa dab dashi saita cake ta tsaya,ta yamutse fuska,ta turo lips dinnan nata ta kuma juya masa qeya.

Ya masa nisa ya tsaya tambayarta abinda ya faru,don haka kanshi tsaye ya miqe,ya taka ya zagayo gabanta. Tsaiwa yayi yana duban kyakkyawan fuskarta data soma nuna yanayi na masu ciki,yasa hannuwansa duka biyun ya kama kunnensa.

"Na tuba......bazan qara ba" Kafadarta ta maqale.

"Ni saidai kayimin tsallen kwado".

"Done madam" Ya fada yana dan ja da baya still idanunsa a kanta.

Hannuwan rigarsa ya tattare,ya durqusa a nutse ya tattare qafafuwan wandonshi,sannan yayi bismillah ya tsugunna ya fara.

Da idanu take binsa,tanaso taga alamun ya gaji amma saita lura kaman ko a jikinsa. Bata rai tayi ta soma buga qafa.

"Ni ban yarda ba Allah.....so nake ka gaji fa". Murmushi ya kubce masa,da gaske mata rigimammu ne,suna kuma rigimar da ba dalili,musamman masu juna biyu,don haka yana kaiwa qarshen bangon ya zube warwas yana numfarfashin qarya gami da jujjuya kanshi.

Dariya dole ta kubce mata da abinda taga yana yi din,ta qarasa gabansa tana dan dukan qirjinsa a tausashe.

"Wannan duka cuwa cuwa ne......kawai yi kayi kawai badon haka bane". Dariya me siririn sauti ya saki,sai kawai ya jawota jikinsa,yayi mata kyakkyawar runguma yana fadin.

"Na gaji da wannan qwalelen da kikemin,qamshi duka ya buwayi hancina,amma kin hanamini jinsa yadda ya dace?,haka akeyi?" Ya qarasa fadi yana yaye hijabinta ya salubeshi ya wurgar gefe sannan ya cusa fuskarsa tsakanin wuyanta da qirjinta.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



๐ƒ ๐” ๐ ๐ˆ ๐˜ ๐€ ๐“ ๐€
_Zafafabiyar_

ฬถBฬถOฬถOฬถK ฬถ2

โฑงษ„โ‚ฒษ„โ‚ฅโ‚ณ

๐™‹๐˜ผ๐™‚๐™€ 152


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



152


โ˜…K'arfe goma da rabi na safe motocinsa suka shiga farfajiyar harabar asibitin. Shi da duniyarshi ne,wadda tayi kyau abinta cikin wata tsadajjiyar cotton lace lafaya me asalin tsada da taushi. Butter color ne da aka yiwa adon maroon da golden,wannan ya saka takalmi da handbag da earrings data sanya duka suka kasance maroon color,kalar daya zauna sosai a farar fatarta dake glowing saboda cikin dake manne a jikinta.

Wani lafiyayyen yadi ne a jikinsa fari qal me taushi,wanda baida kauri ko nauyi ko kadan,hasalima kana iya hangen fara qal din vest din dake sanye a qasan rigar. Kusan komai nasa fari ne yau,hatta da takalmi da kuma agogon da yayi amfani dashi dukka farare ne,sai wata hula saman kanshi irin ta mutanen qasar Morocco wadda itama fara ce kaman kayan jikinsa.

Tunda suka fito daga gida take satar kallonsa,ya mata wani irin fitinannen kyau kamar yau ta soma ganinsa,sun maidashi kamar wani jarumin fina finan india.

Waiwayowa yayi gareta sanda motar ta qarasa tsayawa sai suka hada idanu. Ta janye lumsassun idanunta daga kanshi tana sauke boyayyen murmushi da wata 'yar kunya can cikin idanunta.

"Sabrrr" Ya kirata a tausashe da wani kwantaccen sauti yana dubanta duk da data dauke fuskarta a wajen.

"Na'am" Ta amsa masa ba tare data waiwayo ba.

"Sabrrrr" Ya sake fadi yana jin shauqin kallonshi daya samu tana yi.

"Na'am hamma" Ta sake amsa masa still ba tare data waiwayowa din ba.

"Please mana sabrrr" Ya fadi a shagwabe har abinda ya fusgi hankalinta ta waiwayo tana sakin dariya.

"Hamma shagwaba?" Ta fada pink lips dinta dake qyallin man lebe yana fadada da fara'arta. Girarsa dukka biyun ya daga mata yana duban qwayar idanunta.

"Kina kallona ina jin dadi.....kuma sai kawai ki dauke kanki?". Murmushi ta sakeyi,a hankali ta motsa labbanta.

"Kayimin kyau muffin,kayimin kyau sosai......kyanka da kamalarka suna sake tsananta kishinka a raina.....wani lokaci ni kadai ina tunani......ina tunanin ranar da zaka raba wannan soyayyar......wannan qaunar......wannan kulawar......wannan jikin........wannan baiwar da wata diya macen......iya tuna haka kawai idan nayi sai naji kaman zan zauce,sai inji kaman numfashina zai tsaya,sai naji komai ya dainamin dadi.....kokwanto me yawa sai ya cika zuciyata......iya tunawa kadai idan nayi nakejin haka.......ta yaya zan iya fuskanta da d'aukan haka a gaske?" Ta qarasa maganar tana maida dubanta cikin idanunsa.

Idonta kawai ya kalla ya fahimci ainihin zallar gaskiyarta......idanunta kadai sun gaya masa da gaske take......duk abinda take fada din ainihin gaskiyarta kenan.

A hankali ya miqa hannunsa daya ya kamo fuskarta yana dubanta da kyau,yanayin fuskarsa ya sauya zuwa ga yanayin wanda zaiyi magana me muhimmanci.

"Kin aminta daga wannan tsoron,kin aminta daga wannan firgicin har abada.......bazan taba iya jurewa ba naga ruhin da yake tsananin sona yana wahala har haka akan abinda nake da ikon yi masa ko bashi ba......sabreenn,mace daya tak qwaqwqqara na roqi Allah ya bani......nagartacciyar mace na nacewa Allah da roqo ya bani,koda zanci wahalar samu ko nemanta.....koda zan jima banyi aure ba amma dai ta gari nakeso......nasha wahalar.....na kuma fuskanci qalubale.....kuma Allah ya bani ke.....ke kadai kin gamsar dani,bana buqatar qari......kece reality na......bana buqatar gaibu.....muhammad fu'ad naki ne ke kadai har abada........muddin kina nan a sabreenn dinnan dana sani baki sauya hali da dabi'a ba....."

"Koda na tsufa?". Ta fada idanunta suna rau rau da cika da hawayen farinciki

"Ko deboki akeyi a shanya a rana sai yamma tayi a maidaki daki.....ballantana ma ina miki kyakkyawan fatan tsufa me kyau.....baka mummunar tsufa....baka tsufan banza muddin ka riqe Allah kayi rayuwa irin wadda Allah da manzonsa suka tsara".

"Haqiqa ba wata kyauta da zaka bani a rayuwa bayan wannan......ba wata kyauta da tafi wannan.....ka amintar dani daga tsoro na.....na gode.....na gode".

"Ni banason godiyarki" Ya fada yana zare jikinsa daga rungumar data masa,ya kuma zura qafafunsa ya fita waje,saidai ya babbake bakin qofar motar ya zube hannayensa a aljihun rigarsa ya zube mata fararen idanunsa.

"Me kakeso hamma?" Ta tambaya a sanyaye. Yadda tayi sanyin ya bashi dariya,ya kalli qasa ya dara kadan sannan ya dubeta.

"Kici gaba da haifamin yara turmus....bibbiyu uku uku hurhudu harma biyar biyar". Idanu tadan waro waje kafin murmushi ya subuce mata,kyau tayi masa sosai,sai ya miqa mata hannunsa yana duban idanunta.

"Me kika ce?" Dora hannun nata tayi saman nasa ya taimaka mata ta fito sannna ta amsa masa.

"Ka tayani da addu'a Allah ya bani masu sauqi,kuma Allah ya bani ikon tarbiyyantar dasu"

"Zakk iya in sha Allah......am by your side.......na tsaya miki akan komai sabreen,na tsaya miki,duk wani kalar jin dadi kulawa da riritawa kikeso....duk wani kalar rayuwa ko kalan abu da kikeso a rayuwa umarni kawai zakiyi yazo gareki......kaman yaddana taba yowa kaina alqawari saina cikashi in sha Allah.....zan maida matata ta zama sarauniya cikin mata....zan sakata da kanta ta dinga jin ita din ta dabance a cikin mata....zata zama wata gimbiya tauraruwa me haskawa.....shalelen mata wadda mata zasu dinga jin duk ita suka rako duniya....komai mulkin mace dukiya ko nasabarta idan tazo inda kike zataji ta koma tamkar baiwa a gabanki......abu uku zuwa hudu ne kawai nake buqata. Ki soni har abada har Qarshen numfashi so na fisabilillahi.....wuya ko dadi kar ya zama silar rabuwarmu.

"Na biyu kiyita haifamin yara kina basu tarbiyya,sahihiyar tarbiyya data dace da addini."

"Na uku ki bani kulawa.....idan zai yuwu ki fifitani sama da kowa harda yaran da zamu haifa ma". Wannan gabar sai data sakata sakin dariya.

"Daddyn yara yada haka?" Sassanyan Murmushi daya qara masa kwarjini da kyau ya saki,kafin ya bata amsa wannan karon sai daya jawota jikinsa suna iya jin hucin numfashin juna.

"Saboda shi daddyn yafi yaran son mamar tasu.....sannan shi daddyn yafi yaran sanin tsadarta da kuma darajarta......abu na qarshe shine ki tsaremin kanki.....ki tabbata a matsayin DUNIYAR MUHAMMAD FU'AD JADDA har Qarshen rayuwarmu". Tun b'a je ko ina ba da wannan kalaman nashi na qarshe ya qarasa tashin kanta. Tun ba'aje kuma ko ina ba ta dinga jin kaman zata narke da wata irin soyayya da qauna me tarin yawa. Tun a nan wajen tasan tabbas tayi sa'ar miji.....an haifota cikin sa'a.....kalar sa'ar da sai mace me tsananin sa'a take samunta.

Baya yaja kadan,yasa hannuwansa yana gyaggyara mata lafayar jikinta.

"Banaso ko ina ya fito.....komai nawa ne.....you're mine and only mine,all rights reserved".

"Kowa ma ya sani.....basai ka yita maimaitawa ba yallabai" Muryar farouq ta sauka daga bayansa.

Baiko waiwaya ba,kaman ma bai fahimci farouq dinne ba yaci gaba da gyara mata lullubin,a nutse yace.

"Har yanzu ba zaka daina yimin kutse ba kenan farouqu.....wannan....." Bai qarasa ba saboda idanun da sabreen ke juya masa tana masa nuni da bayansa. Da ido shima ya tambayeta,tayi qasa da muryarta kamar me rada.

"Like kaman shi da fannah ne hamma" Shuru ya danyi sannan ya dage girarsa yana sauketa,yaja da baya daga gabanta sannan ya waiwaya.

Fannah dince,tana a gefensa kanta a qasa,kunya kaman zai kasheta. Tasha labarun soyayyar sabreen da dude enshi,amma bata dauka haka sukejin DUNIYOYIN nasu daga su saisu ba sai a yau din. Tun daga nesa data hangi yadda guard dinsa sukayi musu qawanya take mamaki,ta dauka zallar tsaro ne suke bashi,ashe su suna qarfafa tsinkar fule da fulawar da akeyi ne daga tsakiya. Abun ya bala'in burgeta,sun kasheta sun kuma tashi kanta,har ta dinga murmushi duk da kunya da nauyin FU'AD da take danji,don yana mata kwarjini sosai.

"Qaton banza......ka taho da diyar mutane amma ba zakamin magana ba?" FU'AD ya fada yana hade girar sama data qasa shi a dole babba. Fannah ta qwaci farouq da dariya ta hanashi bashi amsa.

"Barka da yamma hamma". Qasan ranta tana mamaki dama yana taba barkwanci haka?,idan kaga face nashi a news ko a news paper ko a wani taro na kasuwanci ba zaka dauka yana murmushi bama bare akai ga barkwanci,kaman bashi ba.

"Barka kade amarya.....ya baqunta da sabon guri?" Ya fada cikin kulawa da girmamawa.

"Alhamdulilah hamma....yame jiki?,Allah ya qara lafiya yasa kaffara ne" Fannah ta hada duka ta fada don kwarjininsa ya mata yawa.

"Ameen" Ya furta yana jin kalmar kaffara din data fada tayi daidai da a roqawa maamah ita din.

Gaba yayi suna jerawa da farouq bayan fannah ta qarasa wajen sabreen suka jera suma suna gaisawa. Karon farko kenan da suka fara ganin juna face to face,saidai kowaccensu yanayin nutsuwar dayar tayi mata.

"Ayi mana afuwa,bamu samu haduwa ba,yanayin yazo da ciwon boss,ba daman nayi nisan zango na barshi,sai yau Allah yayi muka hadu" Sabreen ta fadi tana dan murmushi.

"Aiba komai.....ana tare ai,shekaru masu yawa a gaba muna fatan hakan,yana da kyau a kula da boss sosai ai.....kema kuma dole ki rage zirga zirga ai saboda naki yanayin" Fannah ta fada tana murmushi. Mamaki yadan kama sabreen,wai cikinta ya soma fitowa ne?duk da fannah din midwifery ta karanta dama,saita dora hannunta saman cikinta.

"Cikin 'yan uku daban yake ai adda.....sauri girmansa da kuma yawan satittikan da yake dauka a haifeshi,baya kaiwa dadewar cikin twins ko single baby" Ta fada da muryarta maras hayaniya. Kai sabreen ta girgiza,bayanin na fannah ya gamsar da ita,ta kuma fahimta,da alama kuma zata amfana da ita sosai.

A hankali suke takowa shida farouq din suna tattaunawa.

"Mun jima a asibitin,gida zamu wuce.......amma kunyi cikakken magana da likitan da yake ganinta?" Farouq ya tambaya da dan alamun damuwa kan fuskarsa.

"Banganshi ba.....bansan wanne likita ke ganinta ba.....sai yau na samu shigowa asibitin".

" Why?" Farouq ya tambayeshi yana nuna rashin jin dadinsa,duk kuwa da cewa yasan komai,saidai muddin dai maamah tana raye....muddin dai maamah din sunanta mahaifiyarsu ko sau daya bayajin akwai Randa zaice yayi mata wani rashin kirki ko me tayi.

"Farouq.....Allah ne ya kiyayeni......da taimakon Allah da taimakon sabreen,banda hakan nima da tuni yanzu ina nan inata checking BP na......saura kadan jinina ya hau,ciwo zuciyata ta dinga yi,banda dauki da Allah ya kawomin na bani mace ta gari......hutawa nayi na kwana uku farouq,bansan da wanne fuska zan kalleku ba kuda anni.....mahaifiyata ta zama silar da saura kadan anni ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login