Showing 504001 words to 507000 words out of 557259 words
rasa diyarta......wannan sakayyar ya kamata ta samu ta bangarenmu?" Ya qarashe maganan da alamun abun yana masa mugun d'aci.
"Dude.....na taba zaginka?.....inajin zan fara wannan karon" Farouq ya fada ba tare daya dubi FU'AD ba.
"Ashe har akwai banbanci tsakaninmu da ku?,ashe har akwai abinda zamu yiwa anni ta tsanemu kenan indai zata tsaneku ko.taji haushinku akan abinda baku kuka aikata ba.....ka saka a ranka ma tun wuri ka sake gayawa kanka cewa....ni dakai mahaifa daya muka kwanta aka haifomu tare,kaman yadda musaddiq da saddiq suka kwanta mahaifa daya aka haifosu tare......har abada ba wani banbanci". Shuru kawai FU'AD yayi,har abada baisan da meye zaiwa wadannan bayin Allah sakayya ba.
"Ya kamata ka duba yanayin jikin nan nata da kyau,anni nata yimin fada tun jiya......ina ganin ma kamar qasar ya kamata a fidda ita....saidai kaje zaka gani,hawan jini yayi mata mummunar kayarwa" Ya qarasa fada da sautin jimami a muryarsa. Kai ya kada yana nazarin abun,hawan jinin da baida labarin sadda ta sameshi,ya sake kada kai yana tuna wata kalma data taba fadawa abbansu randa ya dawo result din kamuwa da hawan jini.
"Kadanma ka gani......shi talauci in gaya maka idan ya samu ciwo yaga gurin zama kenan....duk talaka da hawan jini yake qarewa,kaga somi somin daukan hanyar mutuwa kenan,ciwon qoda,hanta,zuciya,lalacewar hanji duka daga hawan jini yake farawa......bari na fara tanadi don kaina" Tayi maganar tana miqewa abinta ta barsu a dakin da takardarsa da magungunansa a leda.
Bai amsawa farouq ba,illa wani nannauyan numfashi daya sauke bayan ya gama tuna wannan,sai shima farouq din bai sake cewa komai ba. Ya sanshi,a dabi'arsa ba komai yake baka amsa ba,idan kuma kaga bai baka amsar ba to lallai baka da buqatar bada amsar ne.
Dab da zasu shiga reception na asibitin da zai sadasu da sassan asibitin,sanda guard dinsa ke clearing masa hanya ya tambayi farouq.
"Inasu saddiq?" Harara ya balla masa.
"Zama zasuyi jiranka?,kwanan amna daya a asibiti abba yace kowa ya dauki matarsa su wuce gida". Ido yadan fitar.
"Me yasa abba bai bari amna jikinta yayi qwari ba?" Ido farouq ya zuba masa sannan ya bushe da dariyar mamaki.
"Kana tsoron kada ayiwa qanwarka abinda ka yiwa diyar mutane ko?,to abba yace ta qarasa warkewa a dakinta..
..kaga malam ka barshi shima ya shana......wannan lamari baya buqatar shamaki ko shishshigi fa" Farouq ya fada yana dan shafa gemunsa cikin nishadi. Dunqule hannu FU'AD yayi yakai masa duka
"Sai yanzu kasan haka kenan?"
"Fes kuwa" Ya amsashi yana dariya. Mur FU'AD yasha ganin su sabreen sun kusa da inda suke,farouq kuma yaja tunga.
"Wucewa zamuyi gida.....zamuzo muku ziyara once kafin mu wuce honeymoon" Ya fada cikin salon tsokana yana bawa FU'AD hannu.
"Sai kunzo....Allah yasa muma ku samemu" Ya amsa masa yana bagararwa.
"Iyeeee.....lallai mutumin nan.....baku gaji ba?"
"Kai ka sani" FU'AD ya fada yana danne murmushin daya taso masa.
Tsayata yayi a bakin qofar amenity din,suka gama sallama da fannah,sukayi exchanging phone numbers sannan ta tako ta sameshi. Hannunsa ya sanya cikin nata ya riqe gam kamar wadda za'a qwacewa ita,har sai data daga idanunta ta kalleshi suka hada idanu,idonsa ya dauke,sai mamaki kadan ya kamata,kaman ya manta gaban surukarta maras lafiya zasu shiga?,bazaiyi alkunya tafin hannunsa cikin nata ba,ta bishi kawai yana tura qofar gami da sanya qafarsa a ciki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 153
*_NACE BA......._*π§π½π§π½
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*ππ
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*ππΎππΎ
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
153
Har yanzu da take zaune saman wheel chair din bata daina qoqarin motsa kowacce gaba ta jikinta ba,duk da hakan baida wani amfani ko qanqani a tattare da ita,kaman yadda bai kawo wani ci gaba a yanayin da takejin jikinta ba. Ta sake tattara duk qarfinta a karo na babu adadi don ta samu koda bakinta ne ta motsa tayi magana,amma kamar dai mintunan da suka shude ko motsi bakin baiyi ba bare akai ga fitar wani sauti.
"Innalillahi......na shiga uku!" Shine abinda ta furta cikin zuciyarta,don babu damar yin magana a bayyane bare wani yaju furucin nata.
"Wai da gaske ne?,da gaske ne ni mariya?,bazan iya yiwa kaina komai ba?,da gaske ne ni mariya bazan iya tafiya ba?,da gaske ne ni mariya bazan iya yin magana da kowa ba bare a jini ko a fahimceni?" Tambayoyin kenan da suka cika mata kwanya da qirji tsahon kwanaki ukun kenan,kuma bata da wani me iya jin tambayoyin bare ya amsa mata.
Tun daga kwanaki ukun zuwa yau ko sau daya bataji ta gamsu ko ta nutsu da maganganun likitocin ba da suketa maimaita maganar hawan jini ne wai ya kamata ba. Tafi amincewa da cewa tabbas wannan abun daya sameta jifa ne......asiri ne kawai akayi mata saboda kada taci arziqin d'anta. Mutum biyu take zargi,hajja harira ko ameena hamza kibiya.
Duk duniya wadannan mutanen biyu bata da wani abokan adawa sama dasu,bata da wani abokin takun saqa sama dasu. Duk da kuma tana zargin ameena din,amma zargin nata yafi qarfi akan hajja.
"Na rantse da Allah na warke hajja bazaki sha ba.....ba zaki tsira ba....ko ke ko ameena duk wanda yake da hannu cikin maida rayuwata abun tausayi cikin qididdigaggun daqiqu" Taci alwashin cikin ranta tana jin wani abu yana tokare mata a wuya me tsananin zafi.
Checking nata likitan yakeyi yana rubuta bayanan cikin folder dinta yana hada mata da bayanai duk da yasan bawai zata iya bashi amsa bane,amma yasan tana ji tana kuma fahimta,maidawar ne ba zata iya ba. Duk abinda yake fadi sam bata bashi hankalinta bama bare ta tantance ma'anarsa,a nata ganin maganin warware sihiri tafi buqata fiye da wadannan tarkacen na'urorin da aka zube mata aka. Tayi imani ba wani hawan jini daya sameta,kawai komai da akeyi din wani bata lokaci ne na daban,tunda ko hanyar bakin zaren bata ganin alamun daukoshi.
Kaman kowanne kebantaccen dakin asibiti me cike da tsari shima haka yake. Gadaje guda biyu qananun sofas guda uku da plastic chairs guda biyu suma.
Yadda idanunsu suka sauka a kanta haka itama idanunta suka sauka a kansu. Wani zazzafan abu ya taso ya lullube mata zuciya.
Sosai ta kafe sabreen da idanu tana dubanta ba tare data dauke dubanta daga kanta ba ko na second guda. Ita kadai tasan me takeji akan yarinyar......tana kallonta a matsayin silar komai.....tana dubanta a matsayin wadda ta assasa mata dukkan wata musiba da take ciki. Gaba daya maganganu akanta da boka ya gaya mata suka fara dawo mata d'aya bayan d'aya.
"KINYI KUSKURE!" Kalmar farko da ya fadi mata kenan a kanta,ashe tabbas da gaskiyarsa......da gaske yake kuskuren tayi.....to amma koma meye wannan kuskuren zata tabbatar ta maidashi kansu muddin lokaci da dama suka sake waiwayarta.
Abubuwa ne da yawa suke yawo a zucoyarsa da idanuwansa sanda suka iso gabanta. Kallon da take binsu dashi tana raba idanunta tsakanin fuskarsa da tata kadai ya gaya masa komai. Akwai maganganu masu yawa saman harshenta,akwai saqonni masu nauyi cikin zuciyarta wanda dama bata bata daman furtasu ba......saidai duk wani yanayi nata.....duk wani motsi nata karantaccen abune a wajensa da koda da idanu tayi magana zai wahala ya gaza fahimta.
"Sannu" Ya furta mata yana dubanta. Ido ta lumshe sannan ta budesu,qwaqwalwarta na dawo mata da haduwarsu ta qarshe. Maganganunsa da sam basuyi mata ciwo ba kaman yadda babbar damar daya bata ta kubce mata tayi mata ciwo......wata irin gagarumar dama da bata tunanin zuwanta da subucewarta haka lokaci guda ba.
"Barka da zuwa sir" Likitan ya fada cikin girmamawa.
Waiwayawa fu'ad yayi ya kalleshi.
"Yauwa sannu da qoqari" Ya fadi yana jawo kujera gaban gadon maamahn.
Sabreen ya waiwaya ya kalla sannan ya kalli kujerar.
"Zoki zauna" Ya fada cikin nuna kulawa. Nauyi abun yayi mata,sai takejin kamar idanuwa ne da yawa a kansu. A darare ta matso tana tsarkake sunan Allah ta zauna,tasbihin da tunda ta shigo dakin takeyinsa da kallo daya data yiwa maamah. Tsaf kamannin maamah din suyi wani irin juyewa,qasa da awa saba'in da hudu kacal?,iya wannan ya ishi bawa girmamawa ga ubangijinsa da kuma sallamawa lamarinsa. Tsoron Allah taji yana sake shigarta,wani bangare na tausayin maamah din ya karyo mata.
"Sannu.....ya jikin?,Allah ya mayar kaffara" Ta furta a hankali tana son karantar yanayin kallon maamah din a kanta.
Kafe sabreen din tayi da idanuwa,tana jin wannan dubiyar da addu'ar gaba daya akwai isgili a cikinta. Akwai maganganu masu yawa data jima tana tanadin gaya mata,akwai maganganun data tanada saboda rana irin wannan.....ranar sa sabreen din zata tona mata asiri,ta kuma yaye lullubin sirrin dake tsakaninsu wa fu'ad......a ranar ta tanadi abubuwan fada masu yawan gaske a kanta. Saidai kuma ranar tazo mata da wani babban akasi......akasin da babu daman cewa komai gareta,sai kallo da da idanu,dukkan wasu kalmomi nata suna mata kai kawo tsakanin qirjinta da wuyanta amma fitarsu ya zame mata wani jan aiki.
Kallon fuskar sabreen din kadai wani gagarumin baqinciki yake ajiye mata,saidai sanda ta dauke idanun nata da zummar kauda kanta sai suka fada kan dan matashin cikin dake kwance a jikinta wanda batasan sanda har ya fara bayyana kansa ba.
Kulle idanun nata tayi tana jin yadda bacin rai yake hautsinewa a qirjinta yana kuma bin kowanne sashe da jini ke gudanar mata yana aike mata da saqo kowanne sashe na jikinta. Batajin zata iya ci gaba da kallonta zaune haka a gabanta,inda tana da baki da zata gaya mata cewa ta tashi ta matsa daga gabanta ne,amma bata da wannan damar yanzu haka banda ta kulle idanun.
Sallamar da aka sakeyi ita ta tilasta mata sake bude idanun nata. Musaddiq ne a gaba,amna na biye dashi a baya sanye da baqar abaya data fito da hasken amarcinta da kyau,duk kuwa da 'yar rama kadan dake tattare da ita. Kallo daya tak zakayi mata ka karanci a tsorace take,tana daga bayan musaddiq din,duk inda ya tsoma qafarsa ya dauke nan yake ajiye tata. Hannunta riqe da nashi hannun daya bar mata shi ta baya a haka suka shigo.
Kan hannun nasu idanunta suka fara sauka,wannan karon yunqurin miqewa tsaye tayi ta gwada tata jarumtar na UWA kuma wai MAHAIFIYA,saidai kuma kash......ba wani abu nata daya motsa balle akai ga batun tashin. Gumi sosai ya dinga karyo mata saboda abinda takeji a zucoyarta,bala'i da masifa ne fal idanu da zuciyarta,donme musaddiq din zai debo mata diyar alhaji hamzan yazo mata da ita?,auren da sukayi kadai bai ishesu ba?,har sai sun qara qunsa mata baqincikin ganin kasantuwarsu a tare?.
"Akwai buqatar ki saka nutsuwa da kauda duk wani bacin rai daga zuciyarki don a samu a ceto lafiyarki yadda ya kamata" Likitan ya furta yana dubanta,gumin dake fita a fuskarta kadai ya gaya mishi akwai wani abu daya motsa zuciyarta,duk da baisan ainihin meye ba.
Tana labe a bayansa suka qarasa gabanta,ya gaidata gami da yi mata sannu. Leqowa amna tayi daga bayansa tana mata sannu itama,suna hada idanu ta koma bayan mijinta ta lafe. Ko kusa ko alama bata qaunar ganin matar,anni ce ta kirata ba tare da sanin musaddiq din ba tayi yaqi da ita akan ta bishi idan zaije ta dubata.
"Komai lalacewar tuwo ba'a sauya masa suna.....musaddiq baida wata uwa bayan mariya,koda ya nuna miki baya sonta wannan wani yanayi ne ya kawo haka.....batun abinda tayi miki kuma darajar addu'a bata samu galabar komai a kanki ba,sannan kuma hakan ya zame mata wani sanadi ne na tonuwar kowanne sirri....kina tunanin ke kika yiwa kanki haka?,ko kadan,darajar addu'a ce da duban zukata da Allah S W T yayi". Wannan maganar ita ta sanya amna yin qundumbala ta biyoshi.
"Any progress?" Fu'ad ya tambaya yana duban likitan. Ajiyar zuciya kawai ya sauke sannan yace.
"Idan zai yuwu muje muyi magana daga office ko?" Juyawa fu'ad yayi ya yiwa musaddiq inkiya,shi kuma ya waiwaya yana duban amna. Muryarsa can qasa cikin sigar lallashi ya fara magana.
"Calm down dear......ga adda sabreen ku zauna tare da maamah......ba abinda zai sake faruwa,yanzun zamuje mu dawo.....okay?" Ya fadi yana dage mata dukka girarsa gami da riqe fuskarta tsakanin hannuwansa. Kai ta gyada masa,sai ya sake mata murmushi yaja da baya yana juyawa gami da bin bayan fu'ad. Saura kadan numfashinta ya qwace mata,wani tashin hankali ya sake sauko mata.
"Shima musaddiq din haka yake?" Maamah ta tambayi kanta. Wani irin yanayi ne da batasan musaddiq dashi ba,soyayya muraran da mace a gabanta?.....wacce irin baqar rana ce wannan take gani?. Dukka yaranta guda biyu da iyasu ta mallaka a duniya,kowannensu ya dulmiya cikin soyayyar wata diya macen daban ba ita ba?,wani irin so me zurfin da bataga kwatankwacinsa a kanta ba a cikin idanunsu?.
Shuru dakin ya dauka,sabreen tayi qarfin halin sakin murmushi ta kalli amna.
"Ga guri ki zauna amarya.....kada angonki yazo ya tuhumeni na bar masa me a tsaye" Ta fadi tana ganin yadda amna din taqi sakewa. Ita kanta ta zama tamkar baquwa a gurinta. Murmushi ta maida mata,ta tako a nutse ta samu gefan sabreen din ta zauna tana qoqarin sakin fuskarta.
Ashar maamah keda muradin narka musu ganin suna hira qasa qasa a gabanta amma bakin yaqi buduwa,game kula kuwa zaiga yadda idanunta suka kada sukayi jajur,daga amna har sabreen ba wanda ya kula a cikinsu,don sabreen din nata qoqarin jan amna da hirar da zata sakata sakin jiki.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
154
"Shekararta nawa tana fama da hawan jinin nan sir?" Likitan daya gaji da ganin abun mamaki tsakanin kwanaki ukun ya tambayi fu'ad. Kafadunshi duka biyun ya dage yana son gano dalilin tambayar.
"Ba wasu shekaru bane,idan ya dade wata daya....."
"Hamma duka baifi sati uku bafa" Musaddiq ya fadi yana duban fu'ad. Dauke dubansa fu'ad yayi ya maida ga likitan alamun
"Kaji amsar tambayarka?".
Kai ya jinjina cikin matsanancin mamaki. Tunda yake kaf a tarihin aikinsa bai taba ganin mutumin da jininsa yahau har haka kuma yake iya ci gaba da rayuwa ba. Matakin hawan jininta yakai mataki na qarshe,wanda daga wannan stage din saidai mutuwa bama stroke ba.....uwa uba kuma tun a kwanakin da aka kawota yake ta qoqarin ganin jinin ya sauka amma yana nan a inda yake,ba wani ci gaba. Ya gwada duk wata basira tashi da dabarun aiki amma abun ya cimma tura.
"Sir......munyi mata dukkan abinda ya dace amma ba wani ci gaba ko nasara koda alamunta kuwa,abinda yafi bani mamaki shine......yadda hawan jinin yayi mata wata mummunar rafkiya karo daya,nayi zaton tsohon ciwo ne ma,sa'annan duk wani hanya na sauke jinin wallahi yaqi sauka,abinda yake dada bani tsoro shine,ci gaba da qin saukar nasa zai iya zame mata sanadin matsaloli kala daban daban,don a yanzun haka tsoro nake kaman qodarta tana son harbuwa,bansan me yake faruwa ba,nidai ban taba cin karo da case me kama da nata ba tsahon shekarun dana dauka a bakin aiki.......amma abinda nake tunani.......anya ba wani abu babba data sanya a ranta?,ko wani goal da takeso ta cimma a rayuwarta?,wani matsala dake bata mata rai?". Wani murmushin takaici ne ya qwacewa fu'ad,wanda tunda suka shigo office din yana tsaye kawai hannayensa zube a aljihun wandonsa.
Likitan yayi tambaya a muhallinta,duk duniya shike da amsar wannan tambayar tasa,saidai abune da bai shafeshi ba,koda ya shafeshi ma labarin zai zame masa wani baqon labari da ko a duniyar hikayoyi bai taba jin irinsa ba. Uwa nason mallakar d'a kota mallaki abinda ya mallaka kota halin qaqa?,uwa nason tarwatsa rayuwar 'ya'yanta ta hanyar rabasu da abokan zamansu?......rabo na jikokinta dake manne a mahaifar surukarta kuma fatanta yabi rariya?,BURIN UWA TARWATSA RAYUWAR 'YA'YANTA ta rabasu da uwa da uban goyonsu da suka zamewa rayuwarsu suttura?,wacce irin uwa kenan wannan?,baya ga wasu boyayyun al'amura da fadinsu ma baida dadi koda a baki ballantana ga kunnuwa?.
"Me take buqata?,me ya kamata ayi?" Ya yankewa likitan dogon tunani da zallar mamakin daya fada
"Tana buqatar kulawa ta wurwuri......kulawa ta gaggawa saboda gudun rasa wasu bangarori na jikinta,kamar idanunta kunnuwanta ko qoda ko kuma hanta".
"Yanzu me kake gani za'ayi?" Ya sake tambayar likitan,yana jin wani tsoron girman Allah yana kamashi. Amsa kuwwar muryarta yakeji a shekarun baya yanzu haka.
"Shi hawan jini ai baka rabuwa dashi sai ya lalata maka ji gani qoda ko hanta.......kai kam gaskiya kaman bakayi sa'ar rayuwar duniya ba?,daga wannan sai wancan?" Tayi maganar tana tsaye a kan abban nasa sanda duniya tana tsaka dayi mata