Showing 234001 words to 237000 words out of 557259 words
gani ba,sun lume sun narke cikin uban suturar dake danqare da closet dinta. Chantilly veil ta yafa daya dace sosai da atamfar jikin nata.
Ta fito da wani irin kyau da kai tsaye bahaushe ke cewa qyallin goshin amarci.....saidai itakam ba days,tsabar gyaran jikin da tasha ne da kuma yadda ado ya zame mata jiki.
"Tubarkalla ma sha Allah......tabarakarrahman......kiyi haquri adda inata tankaki.....i can't control my words ne wallahi". Murmushi kadan ta yiwa amna din,zuwa yanzu sai takejin kamar ta saba da halinta ne ma,tana da saurin sabo da shiga jikin wanda take so
"Na gode" Ta fadi tana sanyawa qafafunta wasu high hill wanda kaman an yisu ne dama musamman saboda kayan jikinta. Kamar amna din ta mata magana amma sai ta bari kada sabreen din taga kama ta fiya rawar kai,a haka suka jero suna fitowa zuwa parlor din.
Yayi relaxing sosai cikin kujerar kamar wanda bacci ke shirin dauka,saidai babu ko guda daya.....wata lafiyayyar kasala ce ta saukar masa tun daga fitowarsa daga cikin dakin.
"Barka da fitowa sister" Maganar farouq kenan da taja hankalinsa,ya dauke idonsa daga email din da yake dubawa wanda duka ya raba hankalinsa gida biyu ne,daya kan ibtila'in faduwar darajar gold da diamond da suka wayi gari dashi......daya akan saqonninsa wanda kusan duka maganar dai daya ce,shirye shiryen bude company da yake tunanin jibi zai wuce abuja saboda baqinsa da yake kyautata zaton zasu fara sauka.
Farat daya ta gane muryarsa,kaman amna shima sai take kirkinsa ya lullubeta,bawai murmushi tayi ba,amna ta sassauta fuskarta sosai suna gaisawa.
"Ya kwanan baqunta?"
"Alhamdulillah" Ta amsa masa itama tana rufe handbag dinta data jefa wayarta a ciki
"Ma sha Allah....Allah ya bada zaman lafiya,ya baki ikon riqeshi" Yayi maganar yana maida dubansa ga fu'ad. Ko wajensu baya kalla tun duban farko da yayi musu bayan fitowarsu.
Batace komai ba sai amna da tayi murmushi me sauti
"Dude.....muje ko?" Farouq ya buqaci hakan
"Kuje kai da amna.....gamu nan fitowa" Ya bashi amsa bai ko daga kansa ba.
"Alright" Ya amsa masa yana daukan gorar ruwan da fu'ad din ya fito musu da ita yayi gaba amna na biye dashi.
Shuru ya shude a falon na kusan mintuna biyu,bata ce kanzil ba kaman yadda shima baice ta tafasa a sauke ba,kowa yana ji da tashi izzar da girman kan.
Ji tayi ta dauki iya adadin tsaiwar da zata iya.....ba zata dauki wannan halin nashi sam sam ba,don haka ta juya ta fara motsawa da zummar barin wajen
"Hey!....Waye ya baki izinin tafiya" Ya fada da boldness cikin muryarsa. Abun taji ya mata wani iri.......wani baqon abu guda daya cikin rayuwarta. Batasan namiji yayi mata tsawa ba saidai ma ya lallasheta......batasan namiji yayi mata umarni ba.....a kullum ita ke basu umarni.......ba'a keeping dinta ta jira mutum saidai shi yayi jiranta koda awanni nawa tayi nufin qararwa a wajen.
*DUNIYAT LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862
π π π π π π π π
_ZAFAFABIYAR_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 20
20
Tana tsara komai a sanda takeso a kuma yadda taga dama......kuma a bita a hakan.
"Kina tunanin hatta dressing naki zakici gaba da yinsa yadda kika saba?......idan nace komai naki zai canza ina nufin komai din......ciki harda shigar da bata dace ba.....bata kuma yi ba,ki kalli amna.....kin ganta da irin wannan useless mayafin?". Iska sosai ta shaqa har cikin ranta tana jin wani zafi.....abinda yakeyi matan wasu abubuwa ne da babu d'a namijin da ya taba yi mata shi sai shi. Sai taji haqurinta ya gaza jurewa......don haka cikin muryarta me nuna bacin rai tace
"Kana zaton baiwa ce daka shiga kasuwa ka siyo?......meye alaqarka da dressing dina?". Maganar tata ta sakashi gyara zamansa sosai. Yadan jijjiga kai
"Kin shirya wasan kenan kema?.....musu?,taurin kai.....abubuwa biyu da nafi tsana a rayuwata" Yayi maganar yana kada yatsunsa guda biyu idanunshi akanta duk da baya iya ganin fuskarta
"Bauta.....meye marabar dambe da fada?.....kina tunanin kudin da kika sacemin kimar kudin aurenki sunkai yawan haka?......banajin kinkai tsada haka.....well,ba wannan ba,ki shiga ki sauke wannan banzan mayafin ki saka sutura sosai a jikinki......karki bari na maimaita maganata......i hate it". Cak maganan ta tsaye mata a rai,wani irin bacin rai ya taso mata. Wannan ya sanya da sauri sauri ta fara yin gaba,don tanaji muddin taci gaba da tsaiwa a wajen zai iya gano lagon fushinta,abinda kuma taci alwashin ba zata taba bashi dama a kai ba.
Ci gaba da birkita closet din tayi bangaren veils cikin bacin rai,gaba daya veils din taji basu yi mata ba,sai kawai tahau tube kayan,ta kwabesu tas ta fara neman wasu daban.
Turkey dress hannunta ya fada kai,cikin shigar da tafi so kenan,sai ta fara shirya kanta cikin turkey abaya din wadda cikin qanqanin lokaci ta rufe mata jikinta ruf,ta kuma fiddo da kyakkyawar baby face dintannan.
Haka kawai sai taji tafijin dadin shigar,duk da dama tun asali ita din bata iya shigar bayyanar da tsiraici ba.....kawai dai Chantilly veil yana cikin veils din da tafi so,kuma ko a yanzun ba zata bari ya rabata dashi ba.
Motsin tahowarta ya sakashi daga kansa a nutse. Duba daya yayi mata ya kauda kanshi,sai ya miqe yana ficewa tun kafin ta qaraso.
"Ya Allah......wai BB don Allah a ina hamma ya samo adda?" Amna data kasa daurewa sanda ta hangi sabreen na takowa zuwa inda motoci ke jiransu ta fada. Iya takunta kawai saika dauka rausaya ko kuma yanga takeyi ta cikin hill shoes din data sakawa qafafunta masu igiya.
"BB.....wai dama hamma shima yana kallon 'yammata don Allah?". Boye dariyarsa farouq yayi,don sarai yaga isowar fu'ad wajen amma bai nunawa amna ba
"Me yasa kika ce haka?"
"To ai......hamma fa kaman horror yake......ina noticing nasa duka shekarun nan,Allah saiki wuce ta gabansa amma baisan wacece ke ba......to amma ya akayi idanunsa suka kai kan addana me mugun kyau haka?"
"Yaushe kika zama gulmammiya amna?" Farouq daya kece da dariya ya fada yana satar kallon fu'ad dake tsaye kawai ya kasa cewa komai. Dariyan itama takeyi
"Allah BB......ban taba ganin mutumin daya iya zaben mace ba irin hammana......da gaske hamma ya hadu tako ina,komai nasa ya banbanta dana kowa" Ta fadi hankalinta kwance batasan yana a wajen ba.
Zabura ta danyi da jin gyaran muryarsa,tsaf ta dinke bakinta tana raba idanu
"A nan za'ayi walimar ne?" Ya fada yana jifan farouq da wani irin kallo na zaka sani ne. Dariyarsa ya yiwa control yana fadin
"No.....aike muke jira,ko ka manta kaika koromu waje zakayi ganawar sirri da madam"
"Enough" Ya fada yana tura masa murfin motar kaman zai bugeshi cikin nuna alamun ka soma wuce gona da iri. Hakan shi yayi masa,don haka yaja murfin ya rufe yana gaya masa shi da amna zasu tafi a nan.
Baibi ta kansa ba ya nufi ainihin motarsa qirar Mercedes Benz G400d baqa wul daketa daukan idanu wanda haka ke nuna sabuntarta da kuma kalar kulawar da take samu.
Da sauri daya daga cikinsu ya bude masa,kai tsaye ya wuce ya zauna sosai idanunsa na sauka a kanta. Ya tsani jira sosai,baisan me yasa take tafiya kaman ba zata qaraso wajen ba,bayan ya tabbatar taga inda ya shiga.
_wataqila da wannan take sake samun damar yaudarar maza_ tunanin daya d'arsa masa a rai kenan,wanda ya sake sanya mishi qyamarta ainun,har yakejin kamar ma bazai iya hada numfashi da ita cikin mota guda ba.
Ba zata bari ba ba kuma zata sake tayi wani abu na zubewar kimarta da mutuncinta gaban guards dinsa ba,wanda dukkaninsu haushinsu takeji. Bataga meye dalilin da zai zube qatti irin wadannan suna kewaye dashi ba kamar tsohon barawo ko wanda yaci kayan wani ba(a iya nata sanin na iya tsaron daya zama dole me harka irin nashi ace ya samu),me yasa bazaiyi rayuwa normal irin ta mutane ba?,da wannan kalar tasa rayuwar kenan itama yakeso ya tursasata ta zama haka?,tayi rayuwa irin nashi?,bazai yiwu ba kuwa.
Daidaita zamanta tayi sannan aka maida murfin motar aka rufe mata,sai motar ta dauki shuru sai sassanyan qamshinsa daya danne nata,har ya zamana duk wani numfashi da zata shaqa tare da qamshin nasa yake zuwar mata hunhunta. Tsaki ta saki a boye yadda bazai ji ba,ta maida kanta daya window din da take zaune daura dashi. Batasan sun fara tafiya ba sai da taga motar ta fara sulalawa tana nufar makeken gate din gidan suna gilma shukokin da aka qawata wajen dasu.
Basuyi nisa ba kira ya shigo masa,wanda shi ya zame masa abokin tafiya. Duka maganganun cikin harshen turanci yake yinsu da wani irin accent dake nuna zallar qwarewa gami da gogewa a yaren. Kusan fin rabin maganganun nasa ba wani fahimtarsu takeyi ba,don zuciyarta tayi nisa da wani tunani na daban. Ta wani bangaren kuma yadda yake lanqwasa harshensa ba kowanne word take ganewa ba a matsayin karatunta na wadda ya dakata daga aji biyar biyu na babbar secondary wato senior secondary school.
Sanda motarsu ke qoqarin cusa kai ta cikin babbar gate din dake da wani irin girma da kuma jan hankali,a sannan ne ya katse wayar ba kuma don ya gama ba. Ya kashe wayar gaba daya tana kallonsa ta gefen idanu,ya zurata cikin wani dan abu daya matsa ya fito ya saka wayar ya koma ciki. Adan qaramin zamansu na mintuna ta karanci abubuwa daban daban tattare dashi,kusan kaman komai nasa na dabanne kuma daban yake,saita tabe baki sanda suka isa babban parking lot na alfarma da gidan ya mallaka.
Qasa tayi da kanta tana jan mayafin data lullube kanta dashi sanda take hangar wasu mata suna bullowa daga wata qofa da tafi kusa da parking lot din,kafin takai gayin komai amna ta bayyana ta kama murfin tana budewa,abinda ya bata daman jin maganganunsu. Muryar amna ta fara ji
"Inna uwaisha......ga addan namu.......ku fito mana da ita a hankali" Ta qarasa fada tana qaramar dariyar dake nuna zallar farincikinta
"Kinyi qoqari auta sannu.......kin gama naki" Wadda aka kira da uwaisha ta fadi tana matsowa gaban motar
"Kamar gaske" Sautin muryarsa ta fita a hankali ya furta sanda kan sabreen ke qasa tana jin wani fargaba haka kawai na haduwa da mutanen da batasan su kuma meye nasu kalar halin ba,sunan auta da taji an ambata sai ya sanya duka tsigar jikinta ya tashi,haneefa da tun da safe take kokawa da tunaninta ta fado mata.....ko yaya ta wuni?.
"Zallar karamci da girmamawa da mutuntawa muke gabatar miki" Abinda inna uwaisha ta fada kenan kamar tasan abinda sabreen ke wassafawa qasan zuciyarta. Miqa mata hannu inna uwaishan tayi tana fadin
"Sauko a hankali nayi miki jagora zuwa ciki,ki shirya don kowa na dokin jiranki". Bata musa ba ta sakawa inna uwaishan hannunta
"Fatabarakallahu ahsanul kaliqeeen......da iya lallen nan ma kawai an tashi kaina yallabai". Inna uwaishan ta fada tana dariya dariya idanunta akan muhammad fu'ad dake qoqarin ficewa a motar sannan ta maida dubanta ga amna data dage mata gira alamun Yes.
Inna uwaisha na daya daga cikin makusantan anni da suka daukeshi tamkar d'a,duk da cewa tana da jika qwaya daya amma idan kaga suna raha da amna saika dauka yaya ce da qanwarta,hakanan suma ta daukesu duka mazan gidan. Bai iya cewa komai ba,sai dan motsawa da labbansa sukayi alamun murmushin dole kawai ya sanya qafafunsa ya fice daga motar.
Kunnuwanta kawai ke iya jin surutansu amma idanunta suna a rufe. Batasan ina suke nufa ba saidai idanunta na iya kallon lullubabban luxury marbles din dake shimfide a wasu sassan na gidan,a haka taji sun isa wani daki da a nan inna uwaisha tace da ita
"Fell free sabreen.....ki shirya amna zata tsaya dake,idan kun kammala zan dawo mu wuce wajen taron,kowa ke yake jira". Kai ta gyada a hankali,cikin ranta kuma tana zancan zucin wanne shirin kuma zata sakeyi bayan na jikinta.
Sanda amna ta gabatar mata da komai na shirin shuru kawai tayi tana bin kayan da kallo......shin da saninsu wanne irin aure ne akayi suke wahal da kansu haka da kashe kudade da hidima?,ko kuwa kallo kawai sukewa abun irin duban bangon littafi ga idanuwan da basusan meye a cikinsa ba. Wata lafiyayyar Moroccan gown dake da wani irin ado na daukan hankali......saidai kuma duk da adonnan nata sam bata da nauyi ko kadan. Hade take da wani irin hijab dan qarami da yafi mata kama da na Indonesia ko Malaysia.....a ciki batasan wanne ne ba. Komai na kayan fari ne qal da wani irin haske me daukan hankali. Ita kanta bayan ta gama shiryawa batasan lokacin data dauka tana kallon kanta ba,sai take ganin kamar ba ita ba.....duk da kusan komai ma yana zuwa mata ne da wani irin ba zata da bata taba zato ko kawowa cikin rayuwarta ba.
Amna ce ta fara shigowa wadda fiye da dazun a yanzunma ta susuce wajen yabawa sabreen din.
"Inna Allah kwanan nan hamma zai manta da wani gold da Diamond"
"Maza dai ya jiki" Inna uwaisha ta fada tana riqe hannun sabreen suna nufar qofar fita.
Suna shiga wajen tasan sun iso,duk da kusan kowa na zaune a nutse ana sauraren jawabi daga bakin malamai.
"Muna yiwa amarya barka da shigowa". Maganar data dauki amsa kuwa cikin hall din,ta kuma bawa maamah damar fara gyarawa tsaf don bayyanar da kanta a wajen.
Ringing biyu wayar tayi ya daga yana sakata a kunnensa
"Ya kamata ka qaraso wajen walimar fa.....akwai mutanen da zaku gaisa dasu"
"Bana kusa"
"Kaman yaya?" Farouq ya tambayeshi a mamakance
"Eh.....kaman yadda kaji bana kusa,uzuri ya kamani nadan fita"
"Why.....you know......"
"Anni zata fahimceni idanma kai baka fahimta ba.....sai na dawo" Ya amsa masa yana katse wayar ya maidata ya ajiye. Shi a yanzun kasuwancinsa shine abinda yafi damunsa shine kuma gaba da komai,bai takurawa kowa ya matsawa kowa ba,don hatta da saddiq daya Kamata ace a yanxun suna tare suna duba al'amuran da suka taso musu bai masa magana ba,bai kuma ce komai dashi ba saboda yaga ya sanya kanshi cikin hidimar bikin sosai,ya bashi lokaci ya qare ya dawo hayyacinsa.....tafiya ce dai dasu tsakanin jibi da gata,kuma bazai dage masa qafa ba dole ya shirya su wuce. Girgiza kai kawai farouq din yayi,halin fu'ad saishi,baisan ma yaushe ya fita din ba bayan sun shigo cikin gidan tare. Ya sanshi sarai ya kuma sani,wani irin mutum ne shi da kasuwancinsa ke gaba da komai idan ka dauke shi anni abba da su saddiq,amma koma meye yana ji a jikinsa,yana Kuma fatan duk yadda yakai ga gujewa auren da bashi wani rashin muhimmanci ya zame masa silar shiryuwa da saituwa kaman kowanne magidanci.
A nutse farouq ya ratso cikin mutane ya yiwa anni rada. Kai kawai ta gyada sanda idanunta suke kan sabreen dake zaune waje daya bata ko qwaqwaqwaran motsi. A iya haka tana iya hangen nutsuwa a tare da ita,sannan haka kawai takejin qaunar yarinyar cikin ranta.
Tana iya hangen wasu abubuwan ta cikin mayafin dake lullube saman kanta,a sanda walima tayi nisa..... Kai kawo na mutane ya qara yawa tata zuciyar cike take da lissafe lissafe kala kala. Lumshe idonta tayi sanda aka fara gabatar da miqa gudunmawa ga amarya,wato kowa zaizo ya zube mata tasa gudunmawar adan wani babban qwarya dake ajiye a gabanta maimakon yin liqi,wanda daga nan za'a fara gabatar da lectures akan zaman aure. Numfashi ta sauke daga can cikin hunhunta,duk cika da batsewar mutanen dake a wajen bata hangi wani nata ko mutum daya ba. Sai takejinta bare a wajen da wani irin rashin sukuni da takura.
*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862
π π π π π π π π
_ZAFAFABIYAR_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 21
21
A nutse aka fara zuwa daya bayan daya ana zube sabbin 'yan dubu dubun fil a miqe cikin bundles dinsu a gabanta. Ta rasa tsakanin burgewa da rashinsa wanne takeji cikin zuciyarta?,duk da ta hangi tarin nutsuwa da kamala a komai na taron.
Idanunta ta sake dagawa a hankali ta cikin mayafin tana kallon bakin qofar shigowa gurin dake facing dinta......tamkar abinda ake jira kenan saita hangi huda na shigowa. Da farko ta dauka kaman gizo idanuwanta sukeyi mata ko kuma me kama da ita ne,saidai shigowar nadra da haneefa ya qarasa kore mata dukka shakkun data soma ji cikin ranta. Wannan bai saketa ba taga abinda ya kusa doka zuciyarta saboda firgici.....maamah ce.......tana biye dasu da dukkan alamun da zasu gwada maka tare suke......tare suka shigo,don waiwayawa haneefa tayi da alama kiran sunanta tayi,sai taga ta riqe hannunta haneefa na mata murmushi tana