Showing 528001 words to 531000 words out of 557259 words

Chapter 177 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

517

yau din.

Sai wajen bakwai na safe ya kirashi,a lokacin yana cikin gym,ya sauko daga saman machine din da yake kai ya dauki wayar yana duba kiran. Zama yayi yana goge gumin jikinsa da qaramin towel.

"Sir......mun samu izini,amma qarfe biyu daidai na rana suka bayar"

"Good.....hakan yayi,zan kasance a airport din one din in sha Allah"

"Yes sir" Ya amsa masa suna ajiye wayar gaba dayansu.

Cikin wani baqin lafiyayyen yadi me tsada da aka yiwa dinkin kaftan ya shirya. Hularsa zuwa takalminsa dukkaninsu gray color ne,sosai yayi wani wani irin azababben kyau,kalar baqin kayan saman farar fatarsa ta zama wani abun kallo na musamman. Haibarsa da kwarjininsa sun ninka na koda yaushe saboda rashin walwalar dake shimfide saman fuskarsa.

Shi da saddiq kawai suka tafiyar,sai jordan daya zama kaman aljihunsa saboda jajircewarsa da kuma qwarewarsa a aikinsa da kuma kula dame gidan nasa.

Kasancewar juma'a ce,sai daya tsaya central mosque sukayi sallan juma'a. Yadan samu delay kafin subar masallacin,har la'asar saboda a ranar ana wani taro a nan a buja daya shafi qasa,kuma manyan mutanen daya jima basu hadu ba suka tsareshi a wajen.

Daya daga cikin drivers dinsa ne ya iso da daya daga cikin motocinsa dake ajjiye a katafaren mansion dinsa na nan abujan qirar Lamborghini. Kai tsaye jordan ya karbi driving din daga hannunsa suka qarasa zuwa cikin maitama. Plate number dake jikin motarsa kadai ya sanya me gadin bude musu qofa,Kai tsaye jordan ya qarasa parking space na gidan ya ajiye motar.

Bai fita a motan ba,har sai da daya daga cikin ma'aikatan gidan ya sanar da safuura matar uncle din sabreen zuwan fu'ad din.

Tana kitchen tana hada abincin daren me gidan,tuni ta saki girkin tana cewa.

"Ku bude masa seating room maza akai masa drinks da abinci,me gidan baya kusa,bari nazo mu gaisa". Fu'ad sunanshi kirkinsa dama kamanninsa duka ba baqinsu bane,wannan ya sanya suke matuqar girmamashi da yadda kuma ya riqe sabreen dama 'yan uwanta da kyau,duk da ba gazawa sukayi wajen riqesu ba.

Daidai lokacin fitowar sabreen kenan daga wanka bayan ta murje hadin dilka dana gyaran jiki da akayi mata,tun daga ranar da tazo mummy safuura ta soma gyarata ta ciki da waje.

Idanunta kan babbar TV plasma dake maqale a bangon dakin tana kallon waqar dani kake kama. Sosai waqar ke shiga ranta da wani irin yanayi daya sanya zuciyarta tayi wani irin laushi,zuciyar kuma ta fada wani matsanancin kewa da begen mamallakinta wato muhammad fu'ad jadda.

Ajiye towel din hannunta tayi ta taka zuwa gaban mirror tana duban wayarta dake ajiye a kai. Yawancin lokuta tunda tazo a kashe take barin wayar,saboda tana tsoron ya kirata yaji inda take yace ta dawo gida. Tanason tadan sake samun lokaci kadan,duk da tayi kewar komai daya shafesa kewa bana wasa ba,amma a yau din sai take jin haqurinta ya gaza,koda muryarsa tana da buqatar taji.

Kunna wayar tayi sannan ta zuba numbers dinsa da tuni ta jima da haddacesu,kiran ya fara gangarawa yana shiga wayarsa dake hannunsa a daidai wannan lokacin da suke gaisawa da mummy safuura.

Fuskar wayar kawai ya kalla,yadan zubawa kiran idanu yana mamakin ya akayi ta kirashi a daidai irin wannan lokacin?. Yasan tabbas batasan yazo ba,don ga mummy din a zaune a gabansu ballantana yayi tunanin itace data shiga ciki ta gaya mata.

Kife fuskar wayar yayi,har ta gama rurinta ta katse ba tare ma daya sani ba.

Da dan mamaki ta sake daukan wayar tana sake kira,ta saka a handsfree ta ajiye tana jin yadda bugun zuciyarta ke daduwa. Still bai daga ba,abinda bai taba faruwa ba kenan a tsakaninsu. Komai yawan aiki ko uzurin dake gabansa kiranta na dabanne,to amma batasan wanne irin aiki ya samu da yawa haka a lagos din ba,don haka sai ta ajiye wayar ta miqe da nufin shiryawa,idanunta kan su fauzan dake bacci dukkaninsu su ukun abinsu.165


Tana bude luggage dinta hamra diyar mummy safuura ta tura qofar dakin da sallama ta shigo.

"A tashi HAMFAAL(hamza/farouq/almustapha)". A marairaice Sabrina ta dakata da daukan kayan da take shirin yi ta dubi hamra,don tunda taji tace hamfaal to dukkaninsu take nufi.

"Amma dai antynsu fawad ayimin rai don Allah......ina shirin karance littafin girke girken nan yau duka gaba dayanshi zaki jiqamin aiki?" Dariya sosai hamra tayi,don ita sam bata ma qaunar yaran suyi bacci. Bata gajiya da rainonsu,zuwansu ne yasa ta fara jin gidan nasu a mazaunin gida sosai.

"Ayyah.....yau ba laifina bane......daddynsu ne yazo ganinsu". Dum!,taji qirjinta ya buga,gabanta yayi wani wawar faduwa,tsoro kuma taji ya saukar mata. Ta fidda idanu waje tana tambayar hamra.

" Please hamra......banason wasa"

"Serious adda......yana seating room,yanzun suka gama gaisawa da mummy" Ta fadi tana takowa ciki saboda shigowar me aikinsu da zata tayata daukan yaran.

"Gasunan.......ga abun daukansu can" Sabreen ta fadi tana nuna mata tattausan abun daukan guda uku farare qal dake ajiye a gefe.

Tsaf suka nadesu suka fice dasu,saita bisu da kallo har suka bacewa ganinta sannan ta maido dubanta cikin dakin tana sauke nannauyan ajiyan zuciya.

Tsoron yadda zata tunkareshi takeji sosai,amma dole haka ta qarfafa gwiwarta ta som shiryawa cikin mutuwar jiki da rashin kasala.

Dukkanin yaran ya aza saman qirjinsa ya rungumesu yana shaqar daddadan qamshinsu daya cakude dana mamarsu da yake iya jiyowa cikin jikkunansu
(Shi yasa wannan yake zama babban abun kaico ga macen da take jego amma wai don wani kayan takaici da baqinciki ka rasa qamshi a jikinta,to wannan qarnin da qarin da kikeyi haka jikin yaronki zai zama,kada kiji haushi kada kuma kiyi mamaki idan kikaga yaronki sam baida farinjini duk da kuwa kyakkyawa ne,hakanan kada kiyi mamakin ganin ana rububin daukan yaron wata kuma bayan baikai yaronki kyau ko saka sutura me tsada ba,don Allah mu kula da wannan,qamshi rahama ne,koda kuwa iya keda hancinki ne ma 'yar uwaπŸ˜‚πŸ˜‚).

Bugawar zuciyarsa ya canza sosai daga dumin yaran kawai,sai a lokacin ya sake fahimtar yayi kewarsu bata wasa ba.

Ajiyar zuciya a jejjere ya dinga saki kafin daga bisani ya saukosu. Saddiq ya karbi abbanshi hamza. Da fuskarsa da tasu ya manne guri guda,ya basu tattausan kiss a goshinsu.

Cikin wani tattausan milk material ta shirya,tayi wani irin sassanyan kyau,jikinta na fitar da tattausan qamshin nan nata na incense by kabo daughter da yafi qauna. Glowing kawai skin dinta yakeyi na masu danyan jego,ga cikakken hutu ga kuma gyara da takesha,wanda hatta da abun shanta mummy safuura na daban take bata na gyaran mata. Kanta ba dankwali sai qaramin mayafin material din data yafa saman kan nata,wannan ya bawa sumar kanta me sulbi daman fitowa ta gaban goshinta.

A parlor ta samu mummy safuura,saita nuna mata wani kyakkyawan glass bowl me murfi

"Dauki wannan ki tafi masa dashi......."

"To" Kawai tace da mummy a sanyaye.

Tun daga qofar setting room din ta lura ba alamun takalmin mutum ko daya,saidai duk da haka bata kawo komai a ranta ba ta taka a hankali ta shiga parlor din.

Wayam ba kowa cikin setting room din,sai tattausan mayataccen qamshin nan nasa. Bugawa zuciyarta ta dinga yi d'ai da d'ai d'ai,indai batayi kuskure ba a nan din hamra ta fadi mata an saukesu,to amma ina suka shiga?.

Mugun sanyi jikinta yayi,tayi taku biyu tana isa saman daya daga cikin kujerun ta zauna sannan ta ajiye bowl din hannunta. Wayarta data fito da ita ta zaro ta soma kiran mummy safuura. Bugu biyu ta dauka

"Ya akayi sabreen?".

" Mummy.....banga kowa a seating room din ba.....ba kowa" Ta qarasa fada a sanyaye.

"Kaman yaaya?,yanzun hamra ta baro parlor din fa" Mummy safuura ta fadi da dan mamaki a muryarta.

"Alla ba kowa mummy" Ta sake fada tana dora tafin hannunta saman goshinta,tsoro yana kai kawo a zuciyarta bayan wani hasashe da zuciyarta tayi mata.

"Bari ina zuwa" Mummy ta fadi tana cike da kokwanton abinda sabreen ta fada. Wayar ta ajiye,tana shirin miqewa daya daga cikin yaran gidan ya shigo. Fuskarsa washe da madaukakiyar fara'a,hannunsa riqe da rafas na dubu daya sabbi kar a miqe.

"Mummy.....baqonku ya tafi.......yace a baki haquri sauri yake,lokacin tashin jirginsu yana dab da qwacewa,yana gaidaki da kyau,ya mana kyakkyawar sallama,yau duka mu masu aikinki muna cikin alheri dumu dumu,yace a baki wannan" Ya fada yana miqa mata envelope din dake daya hannun nashi.

"Waya bawa yaran ya dawo dasu?" Ta tambayeshi tana miqa hannunta.

"Gaskiya dasu naga sun fita......ba da mamarsu suka tafi ba?" Batasan amsar da zata bashi ba,sai kawai tace dashi

"Madalla.....ka dubamin idan uba ya gama wanke motarnan" Ta fada tana karbar envelope din.

Budeta tayi a hankali,saiga sabbin dollars a ciki miqaqqu. Ido tadan fitar cikin mamaki,me yasa sam mutumin nan bai iya qaramar kyauta ba?.

Komawa tayi ta zauna tana ajiye envelope din a gefanta,mamaki yana cikata. Ya zaiyi da yaran daya tafi dasu?,bai tsaya koda ganin mamansu ba?,bai kuma gaya mata zaije dasu ba?,kada dai ya zamana sabreen yaji tayi ita ta amsheta bata sani ba,ko kuma wasa takeyi da aurenta?. Kai tsaye ta dauki waya ta kira sabreen.

"Dawo ciki ina parlor" Bata ko iya amsawa mummy ba,ta kashe kiran kawai ta miqa bata ko bi takan furar data ajjiye ba ta fice.

'"Zauna a nan" Mummy safuura tace da sabreen tana nuna mata gefanta. Sam fuskarta ba alamun wasa a ciki.

"Sabreen" Ta kirata a tsanake.

"Na'am mummy" Ta amsa mata kowacce hanta dake cikinta tana kadawa.

"Ki gayamin gaskiya,da iznin mijinki kikazo nan koba da izininsa ba?" Shuru tayi tana juya maganar mummy,nadama da tsoro suna cikata.

"Ki fadamin gaskiya,don kinfi kowa sanin halina bani da sauqi,ba ruwana da wai kedin 'yar 'yar uwar mijina ce.....bata yadda za'ayi baban yarannan yayi tattaki yazo har nan,ya kuma dauke yara ba tare da sanin mahaifiyarsu ba" .

Wannan abun wani baqon abune wajen sabreen din,ballantana ita din da sam sam bata son tashin hankali ko kadan.

"Da saninsa,saidai baisan nan zamuzo ba,kuma har mu kwana" Take ran mummy safuura ya baci sosai,ta zubawa sabreen idanu tana jin kaman ta rufeta da duka.

"Me yasa?" Ta tambayeta a taqaice,irin taqaicewar data nuna mata batason wani dogon sharhi ko dogewa.

"Mummy tsoro nakeji".

" Wani irin tsoro kuma?" Ta fada tana zare mata idanu waje.

"Ciki mummy,inaso na huta......shi kuma haihuwa yakeso akai akai".

"Haihuwarce ke bakiso saboda mamarki kuda yawa ta haifa?". Kai ta girgiza saboda tasan magana mummy ta gaya mata a fakaice.

"Hutawa kawai nakeso na danyi mummy sab....."

"Gafara can dalla ki rufemin baki malama,"Amma ban taba raina wayonki ba irin yau sabreen......ni'imar da Allah yayi miki kika sanya qafa kike shureta?.......ashe baki da hankali ban sani ba?,idan muhammad jadda beso haihuwa a dukiya da lafiyar da Allah ya bashi ba......ki gayamin me zaiso?,sometimes mata ku kuke kirawa kanku kishiya wallahi" Idanu a waje ta daga kai tana duban mummy jin ta ambaci kishiya.

"Yes....kishiya,ga abinda mijinki yakeso amma ke kullum kina opposition party nasa.....me zai hana ya nemo wadda ra'ayinsu da komai nasu yake daidai?......to wallahi bari na rantse miki,nima yau dinnan basai gobe abbanku ya dawo ba,ba zaki sake kwanar mana a gida ba.......sauqinki daya na sakaki a jirgi na maidaki gida a ranar yau,muddin kika sake ya dawo yaji abinda ya faru saikin gwammace bakizo abuja ba....zan rufa miki asiri bazan gaya masa ba,shine kawai abinda zan iyayi miki" Kuka sosai ya qwacewa sabreen,komai ya dagule mata cikin lokaci qanqani. Kafin mummy ta nema musu ticket a gama komai nononta duka ya ciko yanata damunta,alamun dake nuna mata tabbas su fawwad sun tashi.

"Me zai basu idan sun farka suna jin yunwa?,ta yaya zai iya kulawa dasu?" Tambayar data dinga yiwa kanta kenan,harta kasa jurewa ta tambayi.mummy safuura.

Duk da yadda tayi laushi lokaci guda ta bata tausayi amma saita jefa mata harara sanda take hada mata sauran kayanta.

"Ke kika sani,ban sani ba" Ta fada cikin jin haushi.

Haushin kuma bai hanata ta hadawa sabreen din komai ba

"Idan kinje kin nutsu kinwa kanki fada na miki bayani". Abinda kawai tace da ita kenan. Da kanta ta dauketa a motarta har airport,bata kuma dawo ba sai data tabbatar da jirginsu ya tashi qarfe takwas na daren ranar.

K'arfe tara da minti ashirin da uku daidai na dare cave din airport ya saukesu a qofar gidan muhammad fuad jadda. Karon farko da taji tana fargabar shiga gidan,abinda bata taba ji ba tun bayan data amsa cikakkiyar sunan matar muhammad fu'ad jadda.

Bata sake fahimtar waye take aure ba......bata sake fahimtar girman matsayin da Allah ya bata ba sai da suka tasamma shiga unguwar.

Tun a main get na shigowa unguwar suka fara fama da tambayoyi na securities dake tsaron kowanne gate na unguwar. Yawancin gurare saita laqo tayi magana sannan suyi salute nata su dage musu su wuce,abinda bai taba faruwa ba kenan,don duk inda zasu plate number din motocinsu ne kadai amsarsu,amma yau din sai da tasha bayani kafin su samu su iso qofar gidan.

Gaba daya masu gadin gidan mamaki ya kamasu ganin madam guda a cab. Cikin rawar jiki da kuma girmamawa suka bude motan suka shiga fidda luggage dinsu zuwa cikin gidan.

Tun a veranda ta sallami nannies dinsu fawwaz,cikin fargaba ta dinga takawa zuwa cikin gidan,tana jin kamar ta kirasu su tayata bawa fu'ad din haquri.

"Barka da dawowa......tun daxu nake zuba idanun ganin fitowarki ai" Muryar ma'u ta sauka a kunnenta.

Dukka dauriyarta ta tattaro ta sakar mata murmushi

"Yauwa ma'u......ashe kina ciki"

"Eh na shigo ne na zare socket na freezer dincan,kayan ciki duka sun qanqare,kada mu tashi girki gobe qanqara ta hana ciro komai......ya hanya?,dazun na dan jiyo qushin qushin din mutanen nawa". Dan murmushin yaqe ta saki,ta san tana nufin su fauzan ne.

"Kinsan basa rabo da rigima idan sukaso,duka su ukun saisun hade maka kai" Dariya ma'u tayi.

'"Ai inajin sai wajen gobe zamu hadu dasu,Allah ya huta gajiya uwar dakina"

"To ma'u na gode".

"Ba'a buqatar komai ko?" Ma'u ta tambaya.

"Babu ma'u,bari na qarasa ciki" Da haka sukayi sallama ta wuce parlor na biyu kai tsaye ya doshi hallway dinta.166


Wata matsananciyar kewar yaran takeji tana damunta,tanajin kaman ba awanni kadai ta dauka bata gansu ba,ji take kaman shekara bata gansu ba,wani qaunarsu tana sake taso mata kaman ba zata iya qara minti daya cikakke bata gansu ba.

Kai tsaye dakinsu dake hallway din ta bude,bata gansu ba a ciki,hakan ya bata tabbacin suna samanshi kenan.

Kaman ta wuce dakinta amma sai taji ba zata iya ba,ta soma takawa zuwa saman nasa tana qoqarin dake zuciyarta..

Ta kusa minti uku bakin smart door din sannna ta matsa inda tayi scanning nata,kai tsaye kuma ta bude kanta da kanta tana bata daman shiga.

Scenes din watannin baya da suka shude ne suka shiga dawo kata kanta sanda ta hangeshi zaune saman minotti sofa dinsa.......watannin da take a matsayin sabreen dinta ta ainihin,wannan sabreen din wadda babu qaunar Muhammad fu'ad ko qanqani cikin rai da zuciyarta.

Yana zaune gabansa ya bude apple system dinshi har guda biyu,da alama kuma aiki yakeyi sosai,koma ya jima a zaune a wajen,don ya saye idanunshi da farin glass din nan nasa dake bada kalan light blue sama sama wani lokaci wanda ke taimaka masa wajen zuqe hasken screen din.

Kansa ya daga a nutse yana gyara zaman glass din a fuskarsa,lokaci guda kuma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login