Showing 114001 words to 117000 words out of 557259 words
kamanninta sosai da sabreen.
"Don Allah yau daya ki bani aron mintunanki biyar" Ya fadi yana hade hannayensa waje guda. Mintunan biyar din da yake sanya ran a cikinsu zai qarasa dashen da ya dauko.
"Don Allah karkice aah,bazan sake neman wata alfarma ba daga wajenki ba daga wannan" Ya sake maganar yana qara marairaicewa da kyau.
Rabuwa biyu zuciyarta tayi,wani sashe na zuciyar tata yana cewa ta bashi damar.......yayin da wani sashen kuma yake cike da tsoro,tsoron da kusan kullum a cikinsa take.
Batasan yadda akayi ya shammaci rayuwarta har ta soma sabo dashi take kuma jin wasu baqin abubuwa a kansa ba,irin abinda bata taba jinsa akan kowa ba,koda kuwa cikin duniyar mafarkinta ko kuma hasashe.
Cikin qasa da mintuna biyar din daya dauka ya qarasa wargaza duk wani tunani nata. Sanda take takawa zuwa gida dauke da kalamansa masu nauyi.......ji ta dinga yi duniyar tamkar ita daya ce mace a ciki......dama haka zukatan dake da masu furta musu kalamai masu dadi sukeji?. Yau daya ta gasgata kalaman daya taba furta mata
"Har yanxu ke yarinya ce.....ba zakisan dadin rayuwa ba sai kinso kin kuma bada dama an soki......kowacce rai tana da buqatar wanda zai sota.....a lokacinne zaki karanci martaba da darajarki da kuma zamowarki cikakkiyar mace duk da qarancin shekarunki.
Hannunta takai tana shafa qaramar wayar daya bata wadda ke dauke da layi da kuma number dinsa. Ita kanta batasan adadin yawan roqon da yayi mata ba kafin ya karya zuciyarta ta aminta da karbar wayar ba
"Zanyi tafiya me nisan xango,a qalla zanyi watanni biyu ban saki a idanuna ba......bazan iya jurar rashin ganinki ba......" Kai take girgizawa a tsorace
"Yaa sabreen......"
"Ita kike tsoro?,zanje na nema dama a wajenta,kada ta rabani da abinda raina yakeso,zan roqeta ta barni na dinga jin muryarki....."
"Baka da hank......" Taji bakinta ya subuce da fadi.....sai kuma ta yiwa kanta waigi daga furta abinda tayi niyyar fada din a mugun tsorace. Yaa sabreen din da kullum kwanan duniya cikin kwatanta mata ta kaucewa sauraren kowanne d'a namiji har sai ta isa minzali?,yaa sabreen din da bata lamuncewa kowa mu'amala dasu ba komai kusancin dake tsakaninsu?,shine a yanzun yake neman kai kansa da kansa gabanta?.
"Huda......zan iya komai a kanki.....zan kuma iya komai saboda ke,ni kadai nasan zafin sonki da nakeji a raina.....don Allah ki karbi wayar nan......muryarki kawai xanji,daga gaisuwa idan kinso ki kashe wayar" . Ido ta zuba masa a mamakance jikinta kuma yana yin sanyi,wai dama haka soyayyar take?. Qwallar data gani shimfide a idanunsa suka karya duk wani qwarin gwiwa nata,kafiya da kuma dagiya,ta karbi wayar ba tare da tana da masaniyar ta karbi shiryayyen abu da zai wargaza musu rayuwa ba dukkaninsu......
Sake dafa wayar tayi sosai,qasan ranta tana jin qarin tausayinsa yadda yake faman marairaice mata,da alama soyayya ba qaramin kamu tayi masa ba. Dama wannan itace soyayyar?,dama haka akeji?,dama haka take iya canza mutum daga ainihin yadda ka sanshi?.
Ita kanta mamakin kanta takeyi yadda ya iya canzata gaba daya cikin qanqanin lokaci haka,amma kuma hakan fa yana nufin nan da shekara daya ko biyu kenan aure zatayi?. Tayi aure kuma yana nufin tabar yaa sabreen?,tabar nadra tabar haneefa?.
To wai ta yaya ma zata fuskanci yaa sabreen din da shi?,tace mata me?,bayan tsahon tasowarta idanunta basu taba gwada mata yaa sabreen din tana soyayya ba da kowa ma ballantana aure?,kullum zancanta yadda zasuyi zuzzurfan karatu kuma su zama wasu a gaba......wannan qudurin zai cika kuwa?.
Eh.... Wata zuciyar ta bata amsa daga wani gefan
"Shi karatu ai baya hana aure......kaman yadda aure baya hana karatu" Ta tuna da wata hira data jiyo 'yammatan ajinsu sunayi,abinda ya sanyata sakin murmushi kenan dai dai sanda take sanya qafarta cikin falon nasu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 61
Dai dai lokacin sabreen din ke aje wayar mashkur wanda ya sanyata a lissafin yadda komai zaya kasance.
Shine mutum na farko daya matsanta mata da son ta bishi wani guri wajen garinsu. Da fari yaso ace dubai suka wuce,saidai tayi duk wata hikima tata ta kansile tafiyar da a baya ya tayar dayi musu shirinta gadan gadan. Baisan wace ainihin sabreen ba.....shi yasa ya gaza fahimtar dukka wadannan shirmen basa gabanta. Taqi kadan take jira ta yasar da qwallon mangwaro ta huta da quda.
A matse take.....kuma cikin matuqar buqatar kudaden saboda aikin ayshatu data tabbatar gab zuciyarta take ga kaiwa ga matakin da zata daina moruwa. Ko a jiya data ziyarci gidan jikinta yayi sanyi.......ta kuma sare sosai da yanayin jikin nata,har sun fidda rai da ita a wunin ranar,amma da yake shi rai idan yana da sauran shan ruwanshi a gaba to tabbas fa sai ya sha.
Motsin shigowarta ba tare da sallama ba ya sanyata daga fararen idanunta ta zubesu a kanta.
"Meye hakan kuma yau?" Tayi mata tambayar tana duban fuskarta wani abu yana darsuwa a ranta.
Fuskarta da fara'a ta juya tana fadin
"Au.......mantawa nayi wallahi" Saita tsaya daga qofar tana yin sallamar kamar yadda suka saba.
Sai data danyi jim kadan sannan ta amsa mata,ta bude labulen ta shigo,sabreen ta bita da kallo can qsan rabta wani abu yana kai kawo
"Sannu da gida" Ta fada tana nufar hanyar dakinsu,don sam ba'a sake take ba,Allah Allah take ta samu waje ta yiwa wayartata ajiya me kyau. Tasan halin yaa sabreen din qwarai da gaske,tana da mugun fikira da saurin dago wani abu dake a boye,a yanzun haka kallonta da takeyi din gani takeyi kaman tana kallon wayar ne tarwai bisa idanunta.
Bata iya amsa mata ba,tadai bita da kallo har zuwa sanda ta wuce dakin. Janye dubanta tayi daga bakin qofar dakin tana sauke numfashi. Bataso taji kokwanto ko shakka ko kadan akan 'yaruwarta......to amma haka kawai jikinta yake bata wani yanayi daban wanda bata saba jinsa ba akan huda din.
Duk da tasan ba kowa a dakin amma hakan bai hanata kallon gabas da yamma hagu da dama na dakin ba kafin ta ciro wayar daga aljihunta,ta kuma daga katifarsu daidai inda tafi kwanciya ta jefa wayar. Tana dagowa sabreen na daga labulen dakin ta shigo hade da sallama.
Wani mummunar faduwa gabanta yayi,ta amsa da sauri tana kuma waiwayawa,sai suka hada idanu da ita. Tsoronta ya qaru,ta dinga ji kamar ta ganta ne sanda take ajiyar.
Kanta da taga ta dauke shine abinda ya bata relief,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya ta fara fidda uniform din jikinta.
"Huda" Tayi kiran sunanta sanda ta zauna bakin gadonta.
"Na'am" Ta sake amsa mata tana sakin rigar uniform dinta data kama zata fidda.
Idanunta ta zube mata,kafin tace komai haneefa da nadra sun shigo,wanda already sun rigata dawowa harma sun sauya uniform dinsu zuwa kayan gida
"Gashi yaa" Nadra ta fada tana miqa mata Leda
"Kuje falo a samu plate a juye yasha iska,gani nan fitowa" Ta amsa musu tana binsu da idanu har suka fice kafin ta maida dubanta ga huda
"Zo nan huda" Ta umarceta tana ci gaba da karantarta. Ba musu ta ajjiye dan kwalin hannunta sannan ta tako ta zauna a inda sabreen din tayi mata nuni.
Zuba mata idanu tayi tamkar yau ta fara ganin fuskarta,abinda ya sake sanya ma huda fargaba da shakku
"Kinsan na tsani nayi tambayar meke faruwa?,akwai matsala?......a bani amsa da babu komai....bayan kuma da matsalar.....akwai kuma abinda yake faruwar" Ta qarashe maganar idanunta har yanzu cikin na hudan.
Har cikin qashinta taji tambayar tata tamkar taba hango komai tar tar,saidai kuma wani sashe na maganarsa ya bata qwarin gwiwa tare da hikimar kaucewar tuhumarta
"Tunda har akwai tsoron yaa sabreen a ranki,bai kamata ki bari a yanzu tasan muna tare ba,har sai mun sake shaquwa da junanmu.....ta yadda koda ta tashi rabamu,tausayin yadda mukeson junanmu zai sanyata ta haqura......akwai lokacin da na ware da zamu sanar mata......kinga koda kuwa na girme mata nesa ba kusa ba.....amma dole nayi mata biyayya kema na tayaki yi mata biyayya ko ba haka ba?" Wasu daga cikin kalamansa da a yau suka sake sanyawa ta sake masa. Yadda ya mutunta mata yayar da duk duniya bata da abu mafi girman daraja irinsa.....bata jin zata kasa sonshi a ranta.
"Me yake faruwa huda......kome qanqantarsa kada ki boyemin" Ta furta tana kallonta.
Kanta ta girgiza tana narke fuskarta
"Me kika gani yaa sabreen......?" Itama kanta ta kada zuwa gefe guda gami da cije lips dinta na qasa,daga qasan zuciyarta ana gaya mata lallai akwai wani abu da ba dai dai ba.
"Canji nake hangowa dan kadan huda......wanda kowanne canji cikin rayuwa daga kadan kadan yake farawa" Ta amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana.
Zama tayi sosai hudan tana dubanta
"Ba komai yaa sabreen fa.....idan ma akwai din ni bazan boye miki ba"
"Kin tabbata?" Ta jefa mata tambayar da wani nannauyan sauti dake tabbatar mata tambayar me girma ce dake dauke da tarin fassarori da ma'anoni.
Kalamansa sukaci gaba da bata confidence,har ta daga kai cikin tabbatarwa
"Na tabbatar" Ido ta lumshe tana gyada kai
"Shikenan" Sai ta miqe itama tana daukar daya wayar tata wadda ita ta shigo da ita dakin.
Mika'il takeson tabowa.......tana da buqatar fara kawar dashi daga layin,koda kudin visa passport da bill na asibitin ta samu daga gareshi,idanma so samu ne ya zamana komai ya fita daga jikinsa,ta yadda duk abinda zai samu daga bangaren mashkur din zai zamana tamkar ribar qafa ce.
Akwai abubuwa da yawa da yake list dinta wannan karon da takeson yi,wanda kuma yana da buqatar muquden kudade. Akwai mutane da yawa data kwana biyu bata gansu ba,tanason a wannan karon ta jiqa kowa yadda ya kamata.
Kaman yadda ta saba kebe kanta a dukkan lokaci irin haka da ya shafeta. Yanzunma can farfajiyar gidansu ta wuce bayan ta rabbatar ta sallamesu da dukkan abinda ya kamata. Me home work yana yi,me bita da hada haddar da zaya bayar a islamiyya ma yana nashi.
JIB ta kira,kamar ko yaushe layinta layine na musamman da ita kadai ke kiransa dashi,hakan ya sanya baya missing call,don muddin yaga kiran yasan akwai abu me muhimmanci.
Gaisuwar ban girma yayi mata kaman yadda suka saba sannan suka shiga tattaunawa kai tsaye akan ayyukan da takeso ta gama dasu
"Ka sani,ba kasafai nakeson dadewa da mutum ba.....nafison nayi na gama a wuce gurin ya sake sabon lale.....ciwon aishatu shine abinda yafi dagamin hankali najeeb......banason sanadiyyar wani ayshatu ta rasa ranta......inason sama mata lafiya tare da mata tanadin rayuwa da zata manta abinda ake kira da tsanani talauci ko wahala". Can qasan ransa yake hadiye wani abu,yana cika da mamakinta ako yaushe,tana yawan sanya ranta da kanta a risk,bawai don saboda jin dadinta ko walwalarta ba......aah......tana yin komai ne kawai don jin dadin wasu.
"Zamu kammala da izinin Allah......amma a wannan karon indai komai yayi kyau,adadin kudaden an samesu daidai ya kamata kema ki inganta rayuwarki sama da yadda kike a yanzu". Dan qaramin murmushi ne ya subuce mata,har jib yana iya jiyo sautinsa kadan
"JIB.....kune a gabana......har yanzu inajin mutanen dake tare dani ban kaisu matakin daya dace sukai ba". Zuciyarsa ce ta karye girmanta na dada qaruwa a ranshi
"Ko yanzun ma me ya rage?,kinyi mana komai,tunda muna iya tsaiwa da qafafunmu......mu ya kamata mu tallafeki kikai inda ya dace kikai din.....kusan dukkanmy burinmu ki samu nagartaccen miji......"
"Mubar wannan maganar jib yanzu" Ta katse numfashinsa. Murmushi kadan ya saki,shima kansa yasan ya taba inda batason aje. Sau tari yakanyi mata uzuri......koda shine yaga abinda ta gani,yaji kuma abinda taji ba shakka iya hukuncin da zaima rayuwarsa shine nisantar kowacce diya mace,saidai kallo daga nesa,indai ba qaddara me qarfi da zata hada tarayyarsu guri guda ba.
"Zakibi mashkur abuja bayan mun gama da mika'il" Ya furta a nutse bayan shurun daya gifta a tsakani na wasu 'yan mintuna
".....banason tafiyar nan jib"
"Itace hanya guda daya mafi sauqi da zamu kammala komai hankalinmu kwance......na sani baki taba bin kowa ko ina ba......amma a yanzun zakije,na miki alqawarin ba abinda zai faru,zan baki kariya da support harki dawo,zan bi bayanku idan ta kama......kwana daya tal zaki bani zan kammala aikinsa.....mashkur din nada tsananin wayo fiye da yadda kike tunani......amma kuma kinsan kutsa kai asusun mika'il yafi na mashkur hadari da kuma tsauraran matakai da sai an masa shiri na gasken gaske?" Shuru tayi tana son fasa maganganunsa daya bata su a cure. Kanta har ya soma dan hargitsewa,sai ta gyara zamanta kadan tana cewa
"Ka rudar dani jib......mashkur nada wayon da lallai sai an bishi qafa da qafa kafin cimma nasara......mika'il sassauqan wayo ne dashi......amma nasu account din yana tattare da tsaro sosai haka ne?"
"Exactly boss lady" Ya fada yanason jefa raha cikin zancan. Ya jefawa fuskarta murmushi kadan kuwa,sai taja dan qaramin tsaki
"A ajjiye wasa jib.....na soma gajiyawa da wadannan hadarurukan......inason muyi babban aikin da zan huta nima hakanan na kula da rayukan dake gabana da kyau"
"Haka nakeso miki nima......bari na qara miki wani bayani kadan......mika'il yana riqe da ragamar babban account din dake mallakin wani kamfanin sarrafa diamond......kamfani ne ne matuqar qarfin jari da huldodin kasuwanci da qasashe daban daban.......kusan rabin kudin wannan kamfanin asusunsa mika'il yana da access dashi.....hakanan duk wani kudi da zai shiga ko ya fita yana da access da hakan.....a bincikena na lura yana wadaqa da kudin yadda yakeso,saidai kuma yana bi ta hanyar lura da saka tsantseni ta yadda ba lallai a gane hakan ba,saboda mahaukaciyar riba da matsiyatan manya manyan kudaden da kamfanin ke samu a kowacce rana....."
"Matsiyata.....manya manya?" Ta jefawa jib tambayar. Qaramar dariya ya saki
"Sorry......maqudan kudade"
"Okay......naji kana amfani da wasu kalmomi ne.....eheeen......kaga kenan komai zaizo mana akan daidai?"
"Haka nake tunani......amma ki bani kwana uku,zan duba yadda zamu kutsa cikin asusun.....amma shima dole ku hadu a ranar Koda na awa daya zuwa mintuna talatinne......ki sassauta riqon tsaurinki kiyi kaman kin sakar masa komai....."
"Mtseewww....ya isa don Allah" Ta dakatar dashi,don zuwa yanzun abubuwan sun fara barin kanta,tana ji kawai lokaci ya tunkarota da zata maida kai sosai ga 'yan uwanta. Dukkansu girma suke qara yi,kuma suna da buqatar attention dinta sosai fiye da wanda take basu a baya.
Jib na 'yar dariya yace mata
"Shikenan......cikin kwanaki ukun zaki iya jina koda wanne lokaci,kibar wayar a bude,ki kuma fara shirin zuwa abujan.....nima zanyi nawa shirin"
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 62
"Yayi" Ta amsa masa a taqaice tana katse kiran.
Shuru kawai tayi tana jin yadda iska ke kai kawo a farfajiyar wajen. Yadda iskar ke kadawa sai take jin kamar kwatankwacin yadda tata rayuwar ke garawa kenan,daga hagu zuwa dama,daga dai dai zuwa rashin daidai,amma a yanzun cikin ranta takejin lokaci yayi da zata tsaida komai.....ko a iya haka ta tabbatar tayi qwarin da rayuwarsu ba zata tagayyara ba.
Tunda ta tabbatar ta fita zuwa farfajiyar gidan ta rufe qur'aninta,ta kuma miqe da hanzari ta wuce zuwa cikin dakinsu.
Cikin mintuna qalilan ya cire dari darin da take na amsa wayarsa da takeyi cikin dakin. Tun tana a tsaye tana kai kawo da kuma leqe tsakanin labulayen dakin har ta koma ta zauna sosai a gefen gadon tana sauraren kalamansa dake da wani irin dadi suke kuma sake samun matsugunni me kyau a zuciyarta.
Yadda dukka kalamansa suke a tsaftace,ba wani kalma ko furuci maras kyau ya sanya take sake jinsa sosai cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma yana yabawa kamalarsa da kamewarsa.
Ba wani abu me muhimmanci da zaman zaiyi mata,don haka ta yanke duka tunanin tana miqewa daga inda take din tana nufar cikin gida don komawa dakinsu.
Tun daga nesa kadan dab da qofar da zata sadaka da ainihin tsakar gidansu ta hangi hadiyyan. Ta ganta sarai zance takeyi,wanda dama takanyi din lokaci bayan lokaci.
So samu tabi ta wata hanyar