Showing 411001 words to 414000 words out of 557259 words

Chapter 138 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

563

budewa kansa wasu rufaffun qofofi dake cikin lungunan zuciyarta. Yanayin kallonsa me sanyata tana jin kamar zata narke ne......ko yaya ya riqe mata hannu sai taji kaman ta mallaki farincikin duniya ne dana lahira,kwana cikin jikinsa ya zame mata wani abu na musamman ga gangar jikinta dama zuciyarta,ta yadda komai nauyin baccinta.....muddin ya saketa ko ya matsa daga jikinta sai nata barcin yayi qaura. Ta fahimci wani abu tattare dashi,yana da tsananin ibadar da duk riqon da zazzabin yayi masa hakan baya hanashi tashi sallar dare,hakanan ko meye yakeyi idan time na sallah ya shiga xai ajiye yaje yayi,koda itace cikin jikinsa duk yadd yake mararin jinsa tare da ita to zai ajeta gefe sai ya bada farillan nan ya hada da nafilar kafin ko bayan kowacce sallah.

A hankali sai taji wani quruciyar data rasa sanadin hawan girma kanta tana dawo mata. Ita dinma saita sake zama wata sakaltacciya,zuciyarta ta koma baya can sanda take da gatan ummienta da abbanta.

A safiyar ranar alhamis dinne ya bude dukka wayoyinsu shi da ita,duk da shi din taga kaman kwana biyu yana buda wani dan qaramin abu shi ba tab ba shi ba system ba yana fita outside deck yana zama yayi wayoyin da batasan da waye yakeyi ba.

Ita ta fara shiga tayi wankanta a sannan yana salatud dhuha kafin ya kammala. Tasan muddin ya kammala zaice saisun shiga sunyi wankan nan tare,abinda ta kasa sabawa har yanzu,saidai idan Allah ya bashi sa'a yayi mata kutse,takanji kamar ta koma cikin cikinta saboda kunya.

Tana gaban mirror tana shiryawa yana addu'o'insa,baice mata komai ba harta gama shirinta cikin Turkish dressing. Budadden wando me kama da Palazzo da rigarsa data sauko har gwiwa me dogon hannu.

Ta masa wani irin kyau da ya sanya ya dinga jin tsigar jikinsa na tashi,to amma ba daman yin komai saboda awa biyu kadai ya rage Lokacin tashinsu. Banda private jet nema da warhaka suna airport din.

Yana fara cire kayansa ta nufi qofa zata gudu setting room,taku uku ya cimmata ya maida qofan ya rufe ya sanya lock,sannan ya koma a nutse yana qarasa fidda kayan jikinsa. Gefe daya tayi da kanta zuciyarta na bugawa,har yau har kwanan gobe ta kasa sabawa da wannan kalar abun nashi. Yana ganinta baice komai ba,ya kammala ya daure qugunsa da towel,bata ankara ba ba kuma zato kawai taji yayi sama da ita ya fara takawa yana dosar bandaki.

Wutsil wutsil ta fara da qafafunta tana bashi excuse.

"Na gama shiryawa fa..... Please ka saukeni,zan jiraka Allah bazan fita ba" Bai kalleta bama sai daya shiga toilet din.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 107


107


"Nasha gaya miki ai......duk sanda kikayi rushing to bathroom kikayi taking shower baki jirani ba......sunan wannan wankan FAKE.....Bakisan sunna bane miji da mata suyi wanka a tare suna kamfata a mazubi guda daya?......bakisan hadis dinnan ba?" Ya fadi bayan ya zumbulata a bathtub ya dafe hannayensa duka gaban bathtub din yana zube mata narkakkun idanunsa.

Gefe tayi da kanta da idanunta da suka cika da qwallar yadda ya sanyata ta jiqe gaba daya,a tsaiwar da yayi a gabanta tana tsoron towel dinsa ya kwance batasan ya zatayi ba.

"Mu gama wankan na nuna miki number na Hadith din da raweeh din" Yana kaiwa nan sai gashi tsundum cikin bathtub din.

"Zakiga takan tsiya" Ya fada qasan ranshi. Shigewa jikinta yayi sosai shigewa bata wasa ba. Wasu irin abubuwa ya fara mata bayan ya samu nasarar cire mata komai data shigo toilet din dashi. Fahimtar inda ya dosa ya sanyata fara doje masa tana barin ya bari.....lokaci zai qure fa?,saidai cikin qasa da mintuna biyar ya yaudare bakinta da duk wani kuzari nasa da salon yaudarar nan tashi,tayi luf tana sauke numfashi gami da amsar saqonninsa da kyau,duk kuwa da yadda zuciyarta ke warning nata.

Shurun da taji ya kusa sanyata bude idanunta,Allah ya taimaketa batakai gayin hakan ba zuciyarta ta gaya mata ke ya tsaya yake kallo. Haka dinne,ya zuba mata idanu yana karantar yadda dafin da ya zuba mata yake bibiyar duk wani jininta da bugun numfashinta,amma qi fadi irin nata da tsananin jan girma da ajinta ya hanata zubda makamanta ta fito masa a mutum.....saidai ya shirya maganinta shima wannan karon,duk da ya samu dukkan wata shaida data tabbatar masa ya bude wata babbar qofa a zuciyarta da rayuwarta gaba daya,qofar daya tabbatar ba wani mahaluki daya taba zuwa koda kusa da ita......yayi nasarar bude zuciyarta gaba daya da wata irin nasara da bai taba kawowa a ransa ba. Saidai ya lura yadda take da wani irin aji na daban.......haka soyayyarta take ta daban.....

Ya samu aji yadda yakeso da kamun kai har fiye da yadda yake hasashen za'a samu wajen wata diya mace,komai nata me ajinne.

"Lokaci yana qurewa......quick" Ya fada yana zare jikinsa daga ita gami da barinta a yanayin data zurma dukka jikinta da zuciyarta.

Kasa motsawa tayi ko kadan,tayi shuru tana jin wani abu yana mata yawo kowanne sashe na jikinta. Karon farko da taji wani abu me kama da haushi ya tsaya mata a wuya,da haushi sanda kake expecting wani abu daga gurin wani kuma ya zamana baka samu komai in return ba.

Kasa motsawa tayi,yana wankansa hankali kwance yana satar kallonta,yadda tayi relax cikin ruwan ya masa dadi. Nan kusa yasan zai samu dukkan abinda yake buri da muradi,ya kammala wankansa tsaf ya daura towel ya nufi qofa yana cewa.

"Hurry up".

Da qyar ta bude idanunta,idanunta suna cika da hawaye,haka kawai taji zuciyarta tana karyewa,sai ta dinga jin zafin abun a zuciyarta. Dolenta ko tanaso ko bataso tasan wanka ya kamata,don bata da tabbacin bai kamata din ba.

Can qasan ranta taji wani abu me kama da haushinsa yana kamata,don haka koda ta fito ta samu ya gama shiryawa. Wani irin sassanyan kyau yayi cikin 3pieces suit saqar kamfanin Hugo Boss dan qasar Germany,rufaffen takalmin qafarsa na kamfanin berluti ya sake fitar da kimar shigarsa,ya kuma qara fidda ainihin darajar dukiya da Allah yayi masa.

Kallo guda dayan data masa kowanne sashe na zuciya da gangar jikinta ya aminta da tsananin kyan da yayi,ya kuma soma qoqarin hura wutar daya kunna mata a toilet,sai tayi ta mata don ba'ace ta maza ba,ta danne komai daga ranta ta soma takowa cikin dakin tana yin kaman bata san da zamanshi ba.

Comb din da take taje kanshi dashi ya ajiye yan lumshe idanunsa,shan qamshinta yayi masa dari bisa dari,sai ya sake fidda mata wani kima daban a idanunsa.

Takowa kadan yayi ya tsaya daga bayanta,yana qare mata kallo,shauqinta yana fusgarsa,saidai duk da hakan yayi qoqarin controlling kansa yana boye hannayensa cikin trouser dinsa. So yake ya manna mata taji irin yadda yakeji a kanta ko yaya ne.

"Sabrrrrrr" Ya kirata da wani irin tone daya kusa tarwatsa duk wani dauriya nata. Yi tayi kaman bata jishi ba,ya leqa fuskarta ta gefe sanda take qoqarin goge ruwan sumarta. Wani dadi ne ya kusa sumar dashi,duk da qoqarin boye masa ruwan sumar nata da takeyi amma tuni shi ya gama fahimtar inda karatun ya sanya gaba. Lallai tarkonsa yayi kamu......tarkonsa ya kama kurciya. Yanason tabbatarwa da gaske fushi tayi don ya barta saman hanya?,don haka ya qara taku biyu gaba zuwa inda take yana kuma sake ambatar sunanta.

"Sabrrrr" Idanunta ta sake lumshewa gami da budesu,saidai har yanxun dai bata motsa ba bare ta amsa masa.

"My world" Ya sake kiranta yana qara rage tazarar dake tsananin su har yanxun yana leqen fuskarta.

"Duniyata" Ya fada da wani coolness daidai sanda ya isa bayanta ya kama qugunta ya riqe yana mannata da jikinsa.

Duk wata tsiga ta jikinta sai daya tasheta da iya haka kawai,to amma duk da taji haka hakan baxai sanyata saurin bada kanta ba,don haka ta hada qarfinta duka tana qoqarin turashi gami da cewa.

"I need to get dressed"

"No....you don't" Ya amsa mata yana juyo da ita gaba daya suna facing din juna,sannan ya juyata zuwa yana hadata da bango gami da ajiye mata wani zazzafan kiss.

Ta fahimci so yake kawai ya birkitata ya sake tafiyanshi kaman daxu,itakam wani irin sanyi takeji yana ratsa mata qasusuwanta da kyau kaman ana hura mata ac.

"Am cold" Ta fada tana sasssuta muryarta saboda yadda yake qara kashe mata jiki.

"I'll keep you warm" Ya bata amsa muryarsa can qasan maqoshinsa,a zafafe ya soma aje mata kisses masu dimauta nutsuwa.

Kamo hankalinta tayi da qyar tana kauda fuskarta,jikinta nema yake ya fara shaking,matakin da tasan indai takai ba zata iya qwatar kanta ba.

"Am not wearing anything under this towel" Da bugaggun idanunsa ya saki murmushi yana dafe bangon da dukka hannayensa

"I know" Ya fadi yana daga girarsa sama. Sosai taja numfashin daya aike mata da sassanyan turaren nan nasa dake kasheta,yadda ya sakata a tsakiyar yana baza mata qamshinsa da dumin numfashinsa tana jin kaman zata sume ne.

"Please" Ta fada da raunanniyar murya. Batason yaga faduwarta ko lagonta gaba daya,amma ta karanci kamar ya shiryawa hakanne.

"Don't fight it" Ya fada yana qoqarin maida bakinsa cikin nata.

"Am in towel fa...." Ta fadi tana qarasa narke masa gaba daya.

"I don't care" Ya fada kaman me rada yana jin yadda shima ya fara kunnuwa,ya sanya hannunsa yana mayar mata da gashin kanta daya rufe fuskarta baya gami da saka idanunsa sosai cikin nata kaman bazai daina kallonta ba,wani irin sassanyan kallo yake mata kaman zai hadiyeta,abinda ya sanya taji qafafunta kaman zasu watsar da ita.

"Yau zamu fita a muraaka......still Muhammad fuad anata tunanin hukuncin da za'a yanke a kansa?". Kasa bashi amsa tayi,daidai nan wayoyinsu suka dauki tsuwwa lokaci guda kaman hadin baki.

" Farouq ne,wallahi nasan farouq ne" Ya fada a wani jigace. Sosai dariya ta taso mata,amma bata da qarfin yinta,saidai wani mamaki ya kamata da taga daya daga cikin masu kiran farouq dinne.

Kiran farouq din ita ya ceceta,sai yaja baya ya zauna yana daga wayar,ita kuma ta kwashi kayanta ta koma toilet din.

Sanda ta fito ya gama hada komai,ya bita da kallo kafin ya daga yatsansa yana karkadawa. Luggage dinta ya sauke,ya birkitata da kyau ya ciro wata oversize abaya,ya hado da wani Malaysian hijab ya miqa mata.

Bata musa ba ta karba,zata koma ciki ta sauya ya bake ko ina gami da mata nuni kan ta shirya a nan. Bata tsaya jan dogon magana ba,tunda ta fahimci makara suke gab dayi,ta shirya tsaf ya kama igiyan rigar dana hijab din duka ya daure mata sannan yaja baya yana kallonta.

"Ya salam.....How can i disguise you?" Yayi Maga nan da gaske yana jin da zai yiwu ya hana kowanne ido kallonta kome wahala zai iya bin tsarin.

"Oho nima ban sani ba" Ta fada tana tura baki gaba don da gaske tana jin haushin abinda ya matan,duk da tana qoqarin nuna bata damu ba.

Dariyarsa ya danne yasa hannu ya jawota baya yana basarwa.

"Karmu fita ki canza......if not.... I'll be open about my feelings for you....i won't feel ashamed of anyone...." Idanunta ta fidda warwaje,a yadda ta shaida rufewar idanunsa akan duk abinda zuciyarsa ta karkata akai,tasan zai iya aikata komai da komai,tana kuma tsoro da nauyin hakan. Hancinta yadan matse yana gane tsoronta.

"Don hana hakan faruwa......Handle me delicately....fine"

"Ya salam" Ta fada tana jin fargabarsa yana kamata. Hannu ya miqa ya riqe hannunta yana fadin

"Ki barshi,Jordan zai kula da komai da muk....." Bai qarasa fada ba dumin hannunta ya ratsa sassan jikinsa,sai ya dakata da maganar yana kai hannunsa goshinta da sauri.

"Ya salam......fever?,when?" Ya fada a rude. Idonta ta kada kadan,ita ta dauka ma zafin jikin bai fito ba,iya ita kadai takejinsa a qashinta.

"Bai dade ba......i will be fine" Kai ya girgixa yana yana azawa kansa laifin,yana ganin kaman maidata ruwa da yayi da sanyata zubawa kanta ruwa shi ya jawo hakan.

"No.....mu tsaya ki samu relief,zansa farouq yayi magana da......" Hannunta ta dora da sauri saman nasa hannun.

"I'll manage". Dan jim yayi yana kokwanto kafin yace.

"Really?" Kai ta gyada masa duk da yadda taji kanta yana sara mata. Bataso ace duk jama'ar dake can suna jiransa jiran ya tashi a banza saboda ita kadai,hakan sam baiyi tsari ba,sannan ita kanta bata qarfafashi yayi abinda ya dace ba.

Yadda yake riqe da ita kaman zaiyi mata tafiyar da qafafunta ya sanya mata Tsananin jin kunya,saidai gurin ta sake fahimtar na masoya ne,kowa sabgar gabansa yakeyi,a haka suka iso private boat din da iya ita dashi kawai zai fitar zuwa Conrad island su ruski motarsu su wuce airport,don ko Jordan wani boat din daban ya biyo ba nasu ba.


*MAAMAH*

Kaman wadda bata da aikinyi haka ta dinga bin diddigin shudewar kowanne awa da minti na zamansu a gurin da delay din fu'ad na qarasowa gurin. Ba shakka banda idanunsu ameenatu a wajen ba abinda zai hanata komawa gefe tayi kuka koda na minti ashirinne,wataqila ta samu sassaucin abinda takeji cikin zuciyarta.

Yau ita mariya ta wayi gari karyar farautarta ta farauto abinda take da muradi ta sakashi a gaba tana wasa dashi yadda taga dama?. Yau ita mariya ita ke zaune tana jiran dakon isowar yaronta?,wata macen bariki ta riqeshi tsahon wasu kwanaki?,a yau da take jiran qarasowarsa kuma sai time din da taga daman ganinsa kowa zai ganshi?,ita kuwa idan batayi taba rayuwar mutanen nan biyu ba ai tayi asarar zuwanta duniya.

Guda gudan baqinciki haka ta dinga hadiyarsa tana korawa da yawun bakinta,tana sake tsarawa da shirya yadda zata gigita rayuwarsu duka su biyun idan sun sauka Nigeria. Tana jin kamar idan ta jira su koma ya mata nisa,don haka ta koma gefe ta zaro wayarta tana duba wata number tana jin gwara ta shirya komai tun yanzu,ta yadda komai din zai fara da wuruwuri. Sauran ma'aikatanta dake hannun yanzu haka dukansu bata da wata damuwa a kansu,tasan akwai babban aiki a kansu daba wanda ya isa ya furta sunanta da sunan toxarci ko tona asiri.

Tana qoqarin kira wani kiran ya shigo. Matsanancin mamaki ya kamata ganin sunan fareeda yana yawo saman screen din,bata tsaya jinkiri ba ta daga wayar tana kiran sunanta.

"Na'am....ya kike?" Tayi namijin qoqarin tausar kanta ta karya harshenta ta tambayeta.

"Ina kika shiga fareeda?,bayan kinsan babban aiki muka tunkara?" Sake hadiye wata guduma da taxo kan harshenta tayi,tasani cewa banda tana tausar kanta ta samu isa ga dalilin kiran da tuni ta jima da daddannawa mariya zagi.

"Kowanne aiki ma yazo qarshe......kowacce magana anzo qarshenta......kowanne al'amari dadinsa da wuyarsa sun qare..... Kedai kawai turamin date din da zaku iso Nigeria,da airport da zaku sauka,kano ko Lagos ko abuja". Daga kai tayi tana duban musaddiq dake nesa kadan da ita.

"Musaddiq" Ta kirashi tana sauke wayar,waiwayowa yayi sannan ya fara takawa a hankali har ya iso gabanta,a tsume ta danna kan number ta miqa masa wayar.

"Kayi confirming na date din komawarmu da airport din da zamu sauka ka rubutamin a nan ka tura". Wayar ya karba yana kalla,number ba suna,hakan yadan saka shakka cikin ransa,amma ta wani sashen kuma daya tuna kalmar UWA UWA CE sai ya rubuta kaman yadda tace din,ya tura bayan ya gama kalle numbers din tsaf sannan ya miqa mata yana barin wajen.

Details din daya rubuta take kalla

"Me fareeda zatayi dashi?" Taji tambayar ta tsargo mata. Cak ta tsaya tana son laluba amsar amma kuma saita kasa. Wani sashe na zuciyarta sai taji yadan shiga fargaba kadan,sai kuma daya sashen ya taso ya danneshi yana gaya mata.

"Fareeda masoyiya ce....wataqila akwai mafitar data samo mana,zatayi abinda ni na kasa yi wataqila"
(Ni kuwa nace ummm inji me ciwon haqori......ba girin girin ba tayi mai dai,maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta).

Aje wannan tunanin tayi tana tureshi gefe,ta kashe wayar tana ajeta da zummar ci gaba da lissafin sai yaushe zata bar fu'ad din ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login