Showing 330001 words to 333000 words out of 557259 words

Chapter 111 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

3284

gidan qofar ta bude da kanta. Farin matashi ne ya bayyana wanda duka duka shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas ba,daga gefansa musaddiq ne da suka jero tare,wanda kamanninsa da fuad ta wasu bangarori da yawa suke bayyana kansu. Yana sanye da jeans da shirt yayin da musaddiq jikinsa ke sanye da jallabiyya saqar marocco,kansa kuma akwai qaramar hular da mukafi mata laqabi da tashi ka fiya naci haka ma mutumin dake gefan musaddiq din. Akwai haske sosai saman fuskar tashi dake bayyana musulunci tattare dashi.

Da sassarfa musaddiq din yake qarasowa garesu,idanunshi duka suna kan anni,yana isowa gaban nata baiyi duba da wani girmansa ba,ya bude dukka hannayensa ya rungume annin yana fadin

"I missed you so much anni......sai naji kaman ba zakuzo ba.....kwana biyu kawai amma sai naji tayi nisa" Murmushin dake shimfide kan fuskarta kadai ya isa ya gaya maka farincikin dake ranta na ganinsa da tayi,zallar qauna irin wadda ba kasafai ake samunta wajen wani ba idan ka dauke uwa.

"Kayi nisan kiwo yaro na......ka tayani roqon hammanku kada ya sake daukemin kai har haka" Ranqwafowa yayi wajen fuskar annin,yana yin qasa qasa da muryarsa don kada fu'ad yaji

"Na rantse anni nima bazan sake yarda ba.....ki jawa danki kunne"

"Kai kai......hamman?,ai kuwa kaman a kunnensa" Amna data zuro musu kai ta fada tana raba idanu. Duban amna yayi yana dan yamutsa fuska

"Bama haka dake auta......kinsan ni dake duk muna together" Ya furta yana daga mata yatsunsa biyu cikin salon son samun goyon bayanta. Fuska ta shagwabe tana cewa

"Zan iya haqura nayi shuru idan tsarabata tafi ta kowa yawa" Tayi maganar tana kashe ido daya sannan ta dora

"Idan kuma ba haka ba.....ga addana a gefe,ita zan gayawa ta shaida masa abinda kace da mijinta" Ta qarasa maganar tana nuna sabreen da yatsa.

Sai a sannan ta lura da sabreen din dake gefansu. Ya dora idonshi a kanta yana dan kafeta da kallo na wasu sakanni. Sosai yaji yasan fuskartata,ba yau ne ranar farko daya fara ganin fuskar ba. Cikin qasa da second biyar ya tuna inda ya santa. Tabbas bazai taba iya mantawa da fuskar ba.....fuskar data dinga fada saboda lafiyar anninsu.......fuskar data zama silar ceto rayuwar anninsu,to amma kuma sai yaji kaman bai kamata farat daya haka a matsayinsa na baquwar fuska a gareta yayi gaggawar tuhumarta inda ya santa ba.....ballanta ma ita din da take matsayin yaaya a wajensa.

"Tuba naki adda.....ayimin aikin gafara.....da gaske hamma baida dadi shi yasa takeson hadoni dashi" Ya fada yana hade hannayensa duka biyu waje daya.

Batasan ya akayi murmushi ya qwace mata ba,murmushin daya afku saman idanun fu'ad dake dan nesa kadan dasu yana karbar takardu hannun ahmad tare da sake karbar wasu bayanai,don tuni farouq ya wuce cikin gidan yana sake duba yanayinsa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
0818725586269


Wani abu ya hadiye da baisan meye shi ba,wato ita duk inda taga maza sakin jikinta takeyi?,a ina tasan musaddiq da daga haduwar farko xata sake masa fuska da murmushi har haka?. Idanu ya xuba mata yana kallon yadda take duban musaddiq kai tsaye.

"Anyi maka.....amna ma na tabbatar tsokanarka take,don kullum cikin kewarka take,nasha labarinka a wajenta sosai". Ta fada har zuciyarta tana mamakin family din. Kowa na gidan kenan me kirki ne,shi kadai ne maras kirki,maras fara'a,marason jama'a?. Ta tambayi kanta sanda idanunta ya sauka a kanshi. Cikin sa'a idanunsu suka sarqafe guri guda,kusan tare kowa ya dauke dubansa daga kan dan uwansa,sai ya miqa hannu yana karbar takardar hannun ahmad. Da yaren dhivehi asalin harshen mutanen qasar ahmad din yake masa godiyan da batasan ta mece ba. Ga mamakinta sai taji ya maida masa shima da yaren sannan ya
ya soma takawa shima yana wucewa ciki da qasaitaccen takun nan nasa. Tana jin muryar musaddiq yana fadin

"Godiya nakeyi" Tare da maida kansa ga anni.

"Zan kamaki,saikin gayamin dalilin da yasa kina kewata amma baki taba fadimin ko sau daya ba".

"Diyata zo mu wuce ciki,wadannan idan kika biye musu zaki wuni a tsaye ne kam" Anni ta furta tana saka hannunta ta kamo hannun sabreen suka fara wucewa cikin gidan. Duk kunyar anni sai ta kamata,tayi qasa da kanta tana biye da ita. Batasan wani abu a duniya da takejin nauyinsa haka ba kaman annin,tana da wani kima a idanunta na musamman.

"Yanzu nake shirin leqawa na kiraki ki shigo ciki......wancan shirmammiyar tunda ta hadu da dan uwanta kuma ai shi kenan.....may be daga nan ma yawo zasu wuce iyayen zumudi".

" Saddiq....." Fu'ad dake zaune hannun kujera yana duba takardun daya karba yayi kiran Sadiq dake qoqarin daukan ruwa a fridge. Samun kanta tayi da lumshe idonta,batasan me yasa muryarsa take mata nauyi da yawa ba,ba ita ya kira ba,amma sautin kiran yakai mata har tsakiyar qirjinta. Muryarsa tana da wani irin amo me ratsa mutum koda ba dakai yake magana ba.

"Na'am" Sadiq yabar abinda yakeyi ya waiwaya yana dubansa,bai daga kai ya kalleshi ba yace

"Fita ka gayawa musaddiq kada suje ko ina"

"Okay" Ya fada yana ajiye ruwan gami da kama hanyar fita. Numfashi kawai ta aje tana tabe baki,kowa a sake yake amma bandashi,ya iya bada umarni,daga wannan sai wancan,kuma yana iya gama magana dakai kaf ba tare da ya kalli fuskarka ba,ta rasa wanne irin mulki ne haka a cikin jininsa?. Idan kuma muguntarsa ya motsa,ta lura kowa ma da idanu yake hukuntashi,ko don yasan akwai wani abu me nauyi a cikin kallonsa oho?,saita dauke kai gefe tana tabe baki,idanunta kuwa suka sauka kan wani glass door wanda daga nan kana iya hangen wani ruwa nesa kadan dasu dake lullube da farin yashi kaman ta miqa hannu ta kamo.

"Gidan ya miki anni?" Ya fada yana sauke takardar daga fuskarsa bayan ya gama jan ajin nasa.


"Tubarkallah ma sha Allah" Anni ta fada cikin walwalar data bayyana har saman fuskarta tana kallon kowanne sashe na gidan

"Allah ya qara rufa muku asiri duniya da lahira.....Allah ya ninka albarka cikin rayuwarku"

"Allahumma ameen" Suka fada shi da farouq a kusan tare.

"Anni ta shiga ta huta.....akwai awa kusan daya da rabi kafin sallar magarib.....inajin yau ba wanda zai fita sai gobe idan Allah ya kaimu" Ya fada yana duba agogon hannunsa sannan ya sauke.

Cikin aljihun trouser dinsa farouq ya sanya hannu ya ciro key,ya kuma nufi wani daki cikin dakunan dake parlor din,ya bude dakin ya tura qofan yana duban amna

"Ja luggage dinki dana anni kikai muku ciki" Yace da ita daidai sanda take shigowa, Amsa masa tayi to tana yin yadda yace din,ya waiwaya yana kallon musaddiq da musaddiq

"Bude dakin can musaddiq ku sakawa addanmu nata kayan" Ya fadi yana miqawa musaddiq din key din,sannan ya kalli Sadiq

"Saka mana namu a dakin musaddiq sai muyi squatting......addanmu ki shiga ki huta" Ya fada cikin murmushi da girmamawa fal muryarshi,qasan ransa kuma wasai da yadda plan dinsa ya tafi daidai.

Harde hannayensa yayi kawai a qirji yana qarewa farouq kallo,wato abinda ya tsara ma ran shi zaiyi kenan?,shi yasa koda ya buqaci picture ko video na gidan ya hana mishi gani.

Yasan sarai shi fu'ad din yake kalla,ya kuma shiryama koma meye zaice ko zaiyi,don haka ya basar yaqi kallonsa kaman baisan ma yana a wajen ba. Fridge kawai ya bude yana duba meye da meye a ciki yana kuma masa lissafin me dame ya kamata su ajiye na kwanakinsu a qasar. Wani haushi ya cikashi,ya cika yayi fam da rainin hankalin da farouq din ya shirya masa. To amma a yadda yaga farouq din ya tabbatar ya shiryawa duk wani rigimarsa ne,so dole ya fara bin komai a hankali,tunda basu kadai bane,akwai anni,bazaiso kuma anni taji ko taga komai ba.

"Wanne irin gida ne wannan farouq?" Ya fada calmly yana qoqarin danne takaicinsa. Sai daya ajiye gorar hannunsa sannan ya waiwayo yana dubansa

"Me fa?" Yayi tambayar kansa tsaye. Sai daya lumshe idonsa ya bude lokaci guda yana jin takaicin rainin wayon farouq da idan ya motsa tsaf xai iya cewa ma bai sanka ba.

"3bedroom?,why not a siya me 4bedrooms farouq?"

"Akwai baquwar halitta ne a cikinmu da bata samu waje ba?". Kai fu'ad ya girgiza yanason gajarce maganar,don ciki yakeso ya shiga yayi bacci ko na awa daya ne

"Babu.....amma dakunan sunyi kadan.....kafi kowa sanin bana iya hada daki da kowa ba ko tun ba yau ba?"

"To dawa na hadaka.....kajimin mutum zaimin sharri" Rainin hankalin farouq yakai masa ko ina,yana dab da bashi naushi idan baiyi wasa ba,sai ya ware hannunsa daga qirji yana dubansa

"Ka canza plan dinnan,ta koma dakinsu anni tayi squatting tare dasu,saddiq su kwana da musaddiq.....kai kuma muje mu kwana tare". Baya yaja da sauri yana zare ido kaman yaga abun tsoro.

"Mu kwana da kai?,alfanun uban me zanyi maka fu'ad?,me zakaji da kwana da namiji gardi dan uwanka bayan ga halalinka a gefe?" Maganar ta fara girmar kunnuwan fu'ad,tun ba yau ba yasan farouq idan baiso ba tantirin kansa ne,baisan sanda hannunsa yakai kan cup din da saddiq yasha ruwa ba ya jefeshi dashi,Allah yasa yana da zafin nama ya cafe

"Na rantse da Allah xan ruguza maka kai......kai wanne irin dan iska ne?,maganan da nake maka daban yadda zaka juyan zance daban?,ta yaya zan kwana da wata alhalin muna muhalli daya da anni?". Dariya tana cin farouq amma ya maze

"To ba dole nace haka ba?,ga mace me namiji zai maka?,nima bazan kwana da gardi ba,ka cire riga wannan qattin muscles din naka suyita bawa mutum tsoro.....in fact ma ni na fara rehearsal na yadda zan fara kwanciya daga ni sai fannah ta....anni kuma da kake magana akwai wanda zai kaita son ganinku tare....ko turmusheta kayi a gabanta ai saidai tabar muku gurin da gudu.....banson gulma banson k......" Bai qarasa ba yaji saukar abu a qeyarsa,agogon hannunsa ya kwance ya sake jifansa dashi don ya rasa dame zai jefeshi wannan karon.

Dafe wajen yayi ya waiwayo yana dubansa fuska a hade

"Amma dai kasan wannan zallar cin zali ne ko?,ni nakar xomon?,kaje ka yiwa anni bayanin abinda yasa zaka aikota kwana da ita daki daya mana da kanka".

"Ya isheka farouq" Ya fada yana nunashi da yatsa,alamun ya fara qureshi.

"Oho" Ya fada yana sungumar ruwansa yayi dakinsu baiko sake waiwayoshi ba.

Shuru ne ya ratsa falon bayan wucewar farouq din,sai motsinsu kadan kadan da yake jiyowa daga dakunansu. Maganar gaskiya farouq ya cuceshi,inda kuma yasan da wannan da tuni ya sanya an canza musu gida da yafi haka yawan dakuna kafin su qaraso. Miqewa yayi abisa dole yana soma dosar dakin,abu daya ya sani shi bayason takura,yana son bajewa sosai ya sake a duk inda ya zabi rayuwa,so wanzuwarta cikin dakin kuwa bazai bari ya zama silar hanashi sakewa ba.


*Maamah*


Sake juya tickets din hannunta tayi guda biyu tana sake qare masa kallo. Mamaki da wani irin dunqulallen baqinciki yana yayyanka zuciyarta. Ta rasa wanne hamshaqinne ya juya tafiyar daga farkonta ta koma qarshe?. Maldevis shine waje na farko da zasu je a qa'ida kaman yadda ta samu tabbacin dukka iyalin gidan alhj hamza kibiya can suka wuce.....saudiyya kuma shine waje na qarshe da zasu ziyarta daga nan kuma sai gida Nigeria,amma wanne hamshaqinne ya karkatar da tata akalar tafiya daga saudiyya kafin ta sauka maldevis sannan su rankaya su wuce turkey tare?.

"Hajiya ameena.....tabbas wannan aikin ameena ne" Ta fadi tana jin wutar qiyayyar matar tana sake ninkuwa a ranta. Zazzafar iska ta furzar tana fitar da idanunta waje irin na zallar takaici da kuma tunani. Ita kuwa ta yaya zata dagawa ameena qafa?,ta yaya zata bar ameena taci gaba da shaqar iska cikin aminci?,ba ragi tsakaninta da ameena har abada......yadda bata barta ta samu cikakken iko da mulki da 'ya'yanta ba.....tabbas haka zata zama silar tarwatsa nata ahalin gaba daya,duk wanda ya gaya mata cuta ba shakka ita mutuwa zata gwada masa,sai kawai taja wayarta tana laluben fareeda,tana jin wannan karon a gaban idanun ameenatun zata gwada mata nata izzar da qarfin mulkin kasancewar uwar data dauki cikin fu'ad tayi naqudarsa ta kuma haifeshi.......a gaban idanun kowa zata gwadawa sabreen ta isa da danta......zata nuna mata kuma tana da ikon sanya yaronta ya auri mata d'ai d'ai har guda uku rigis bayan ita.

Shuru fareeda tayi tana sauraren bayanan maamah,saidai kuma zuciyarta cike fal da bacin rai da baqin kishin sabreen. Wata zazzafar iska ta furzar tana ajiye bututun shisha dinta ta gyara zamanta

"Maldives ai gida ne......ina da sauran visa din qasar da ban gama cinyeta ba,muddin na samu ticket jibi warhaka ina can......ko ba ticket zan sanya daddy yamin hiring private jet......kya sameni a can" Daga haka ta yanke wayar tana latsa wayarta ba bata lokaci tana neman number wayar daddy din nata.

Tafasa kawai zuciyarta takeyi,wannan karon da zafi zafinta zata shiga,zata budewa sabreen aiki sosai kaman yadda zata budewa fu'ad,tana jin komai mai sauqi ne......amma zata bari ta tabbatar da samun private jet ko ticket to Maldives.

Bugu daya rak ya daga,ba kasafai ta fiya masa sallama ba,kusan sallamarta kiran sunansa ne

"Daddyyyy.....maldevis" Ta fada da wata irin shagwaba kamar yarinyar da aka Haifa jiya jiya

"Mamana......maldevis a daren nan?"

"Daddy gobe......ina da sauran visa na da kamin last two months.......ticket kawai daddy nakeso......please daddy,it's an urgent need daddy". Murmushi ya saki yana juya kai kafin yace

"Wani irin emergency issue ne haka ya taso mamana.....nifa mamana yanzun duk hankalina yana kan aure,kiyi aure haka mamana.....ki zabi duk kalar mijin da kk so zan tsaya miki" Maganar sai taji kaman tazo akan gaba,ta saki dariya tana cewa

"Nayi maka alqawari daddy.....indai na samu wucewa Maldives gobe ko jibi,ina dawowa zan gabatar maka da mijin da zan aura"

"Really mama na?!" Ya tambaya da excitement cikin muryarsa

"Yes dad.....na taba maka qarya ne?" Ta sake fada cikin narke murya

"No mamana......bani minti goma.....i will get back to you"

"Thank youuuuuuu" Ta fada da sautin dariya tana sauke wayar.

Lips nata ta cinje tana duban wayar gami da saqa abubuwa iri daban daban akan fu'ad. Zuwa sannan ta gama karance halayensa na girman kai da izza,yana da tsananin taurin kan data tabbatar ita din kanta shaida ce,taso koda bata aureshi ba ya bata hadin kai su mori quruciyarsu tare,amma martanin da yayi mata ya mata ciwon data jima tana riritashi a zuciyarta.

"Tabbas saina biyo masa ta bayan gida,idan baiyi wasa ba sunansa ne zai fito a next newspapers da magazine ba na waccan karuwar matar tasa ba......tunda shine garkuwarta.......shi din ya kamata na taba qarfinsa" Ta fada da murmushin mugunta tana murza yatsunta bayan ta tabbatar da hukuncin daya fado ranta shine abinda ya kamata ta zartar.

Qarar wayarta ya dawo da hankalinta,ta daga da sauri ganin me kiran. Wani ihun murna ta saki sosai tana jin dadi

"I love you daddy......thank you so so much......bansan ma ya zan gode maka ba" Ta fada duk a rude saboda jin dadin samun ticket na tafiya Maldives jibi. Tana Lagos don haka ba ita babu bin jirgi zuwa Lagos din,kawai kanta tsaye jibi zata bi qatar Airways zuwa can

"Ki kawomin miji kawai bayan kin dawo"

"Baka da matsala dad....." Ta fada tana yanke kiran.

Tun a daren ta gama komai,ta gama hada komai ta kuma tanadi komai gudun samun matsala goben kada ta tashi da uzurin da zata tashi ba'a daidai ba har ya jawo ta hada kayanta ba daidai ba.

*_hmmmmmm,uhmmmmmmmmm_*



69


Wani abu ya hadiye da baisan meye shi ba,wato ita duk inda taga maza sakin jikinta takeyi?,a ina tasan musaddiq da daga haduwar farko xata sake masa fuska da murmushi har haka?. Idanu ya xuba mata yana kallon yadda take duban musaddiq kai tsaye.

"Anyi maka.....amna ma na tabbatar tsokanarka take,don kullum cikin kewarka take,nasha labarinka a wajenta sosai". Ta fada har zuciyarta tana mamakin family din. Kowa na gidan kenan me kirki ne,shi kadai ne maras kirki,maras fara'a,marason jama'a?. Ta tambayi kanta sanda idanunta ya sauka a kanshi. Cikin sa'a idanunsu suka sarqafe guri guda,kusan tare kowa ya dauke dubansa daga kan dan uwansa,sai ya miqa hannu yana karbar takardar hannun ahmad. Da yaren dhivehi asalin harshen mutanen qasar ahmad din yake masa godiyan da batasan ta mece ba. Ga mamakinta sai taji ya maida masa shima da yaren sannan ya
ya soma takawa shima yana wucewa ciki da qasaitaccen takun nan nasa. Tana jin muryar musaddiq yana fadin

"Godiya nakeyi" Tare da maida kansa ga anni.

"Zan kamaki,saikin gayamin dalilin da yasa kina kewata amma baki taba fadimin ko sau daya ba".

"Diyata zo mu wuce ciki,wadannan idan kika biye musu zaki wuni a tsaye ne kam" Anni ta furta tana saka hannunta ta kamo hannun sabreen suka fara wucewa cikin gidan. Duk kunyar anni sai ta kamata,tayi qasa da kanta tana biye da ita. Batasan wani abu a duniya da takejin nauyinsa haka ba kaman annin,tana da wani kima a idanunta na musamman.

"Yanzu nake shirin leqawa na kiraki ki shigo ciki......wancan shirmammiyar tunda ta hadu da dan uwanta kuma ai shi kenan.....may be daga nan ma yawo zasu wuce iyayen zumudi".

" Saddiq....." Fu'ad dake zaune hannun kujera yana duba takardun daya karba yayi kiran Sadiq dake qoqarin daukan ruwa a fridge. Samun kanta tayi da lumshe idonta,batasan me yasa muryarsa take mata nauyi da yawa ba,ba ita ya kira ba,amma sautin kiran yakai mata har tsakiyar qirjinta. Muryarsa tana da wani irin amo me ratsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login