Showing 243001 words to 246000 words out of 557259 words

Chapter 82 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

526

tas ya gama duba komai,ya tabbatar komai yana a muhallin daya kamata ya zauna,sannan ya zarce falo.na biyu ya tabbatar da komai a yadda yakeson ya zama,sannan ya zarce kitchen zuwa store ya duba komai.

Sanda yake baro kitchen din hankalinsa yakai kan dining din dake jere da warmers,ya zubawa gurin idanu na wasu mintuna yana qanqance ido,kafin kuma ya sauya akalarsa yana nufar wajen zuciyarsa cike fal da mamaki.

Cak ya tsaya kan warmers din yana sake binsu da kallo tamkar wanda ke neman sunan wanda ya qera warmers din a jikinsu. Ya kusa mintuna biyu kafin ya zare hannuwansa daga aljihun ya fiddosu,bakinsa da yake motsi kadan kadan zaka kalla kasan akwai abinda yake fadi wanda duka bazai wuce addu'a ba,sannan ya miqa hannunsa a nutse zuwa ga warmer din yana furta

"Bismillah" A fili,ya murzata ya bude. Daya bayan daya ya bude komai,hatta da hot water dispenser din da tayi using ta adana tea din sai daya saka cup ya zuba ya jerasu a gabansa yana qare musu wani irin kallo na qurilla.

Ya kusa mintuna biyar a haka,sai ya saki wani siririn murmushi yana girgiza kai,ya saka hannunsa ya maida komai yadda yake kamar ba'a taba ba. Hannunsa ya miqa daga gefan table din ya ciro sticky notes guda daya,yayi gajeran rubutu ya manne mata jin warmer din ya juya da dan hanzari ba kaman dazu ba yana sauka a wajen.

"Tabbas ita din aiken maamah ce......" Abinda ya gayawa kansa kawai kenan ya gangara yana ficewa gaba daya daga falon bayan ya tsinke waya guda daya data rage ta telephone din dake parlor din.

Kowanne ma'aikaci yana tsaye a matsayarsa suna jiran dakon fitowarsa. Dukka guards dinsa suna tsaye a inda ya kamata kowa ya tsaya. A yau shigar fari kowannensu yayi,da wani irin tsarin shiga da sutura da zata bayyana alfarmar wanda suke aiki a qarqashinsa. Abdulgafar shugaban tawagar tsaronsa shi ya fara nufoshi a gaggauce cike da kuzari yana tarbarsa cikin girmamawa kaman yadda suka saba shi da mataimakinsa jordan

"Good morning sir" Ya fara gaidashi kafin muryoyinsu ya karade wajen suna gaidashi suma

"Morning.....hope you are fine?"

"Fine sir" Suka hada baki wajen amsawa

"Good" Ya maida musu yana gyada kanshi.

"Jordan" Fuad yayi kiransa

"Sir" Ya amsa yana matsowa.

"Where's abdulbasit?"

"Am here sir" Wanda aka kira da abdulbasit ya furta yana matsowa cikin shigar wani uniform da yasha banban da nasu jordan

"Have you finished?" Kai ya gyada a girmame

"Yes sir...."

"Okay,kada ka manta.....zan bar muku jordan.....jordan,ba shiga ba fita har sai na dawo ko na bada umarnin hakan. Ko waye bazai shiga ba,ko waye kuma bazai fita ba......hope i made it clear?"

"Yes sir" Jordan din ya gyada kai,don shi ya fahimci inda aikin yasa gaba,zasu maimaita salon aikin da sukayi satittikan da suka wuce kenan.

"Yi mana addu'a" Ya fada a taqaice yana duban abdulra'uf wanda kusan duk sanda qaramin meeting irin haka ya kamasu shike da alhakin hakan.

Cikin mintuna uku aka kammala kowa ya wuce motarsu,motocin suka jeru kamar kullum,security din dake kula da qofa ya wangale musu ita suka fice daya bayan daya.

"Am on the way......banason jira" Abinda ya gayawa saddiq kenan da yayi kiransa sanda suke a cikin motar,sai ya kashe wayar kawai ya maida aljihu. Titi ya zubawa ido yana fesar da iska daga bakinsa. Baya tunanin maamah zata saka a kasheshi saidai wani abu na daban,amma ita kuma fa?,may be ta tsallake gona da iri,wala'alla ta wice limit da iyakokinta,amma duka ita maamah bata gani ba?,why zata zabi mace me irin wadannan dabi'u da halayen ta kasance a tare dashi?. Tambayar da yaji ta sake quntata zuciyarsa,abinda kuma bayaso ya faru kenan don yau din yana buqatar freshness don gobe rana ce me muhimmanci a wajensa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 25


25


"Nayi zaton tare zaku tafi?" Shine abinda anni tace dashi sanda yake zaune sosai gaban abba suna breakfast dashi. Kai ya girgiza

"Ba daman hakan anni,idan munje ma zata dinga wuni ita daya ne saboda ba zama zanyi ba......akwai baqi da sauran shirin da zamuyi daga yau zuwa goben in sha Allah" Kai ya jinjina

"To Allah yayi jagora.....yasa a bude a sa'a"

"Allahumma ameen" Suka kusa hada baki wajen amsawa shi da abban.

"Amma ba za'a kai mata abokin zama ba?" . Anni ta fada cikin salon nuna kulawa. Basarwa yayi don baison anni ta gane komai game da lamarin

"Ba ita daya bace anni,banajin zata damu,akwai mutane a gidan". Kai ta gyada

"To Allah ya tsare"

"Ameen ya rahman" Ya sake amsa mata.

Duka duka mintuna arba'in suka qara suka fice a gidan shi da musaddiq zuwa airport inda private jet dinsa ke jiran isowarsu.

A hankali hasken ranar dake ratsowa ta tsakanin labule ya soma qarawa dakin haske yana kuma tabbatar da bayyanar rana sosai ya wuce kai tsaye ya taddata har inda take kwance,wanda wannan shine abinda ya sanya idanunta budewa a hankali suka kuma sauka kai tsaye kan agogon dake manne a dakin.

Sha biyu na rana saura minti biyar kacal shine abinda idanunta suka gani,abinda ya sanyata ware idanunta gaba daya tana kuma miqewa da dan sauri. Bayan Hannunta ta saka ta mutstsike idonta tana sake duban lokaci,sam batasan tayi bacci me nauyi haka ba,don ko wanka bata samu tayi ba ta koma ta kwanta bayan ta tabbatar ta gama duk abinda ya dace.

Miqewa tayi tana miqa,tana jin yadda gajiya kebin duka sassan jikinta,can cikin zuciyarta kuma tana raya lallai zuwa yanzu ya debi abincin yaci,tana sake jin wani tabbaci da qwarin gwiwar komawarta zuwa ga rayuwarsu ita da 'yan uwanta.

Toilet ta wuce tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar atamfarJulius gold data zauna mata daidai jikinta da wani irin dinki da bazai takuraka ba. Sai a sannan taji cikinta yana wani yamutsawa....a lokacin ta tuna lokacin data dauka rabonta da wani abu me suna abinci cikakke. Plate tummy dinta ta shafa,sai ta miqe a nutse tana nufar hanyar fita daga dakin.

Tun daga nesa idanunta nakan stairs din har tazo ta gotata tana fita falon farkon. Tadan shaqi iskar dake kadawa tsakanin hallway stairs din da parlor din,wani qamshi ne ke kai kawo na daban wanda bata taba jin sassanyan qamshi irinsa ba,wani sashe daban na zuciyarta kuma tana jin kamar ta taba ji ko sanin irin qamshin.

Xarcewa falo na biyu tayi,tunda kuma ta fito idanunta suna kan dining din. Gudun zuciyarta ya qaru kadan,yayin da ta cika da fatan taras da komai ya tafi daidai.

Bude komai tayi,daga kallon farko ta fahimci ba'a taba komai ba.....daga nan din kuma dukka gwiwoyinta na qafa da hannu sukayi wani irin sanyi,sai taji ta kasa tsaiwa,taja kujera daya ta zauna tana girgiza dispensers din taji ko yawan adadin tea din ya ragu?. Nan ma ba abinda ya sauya,yadda ta zubashi haka nauyin yake,sai ta saka hannuwanta guda biyu tana dafe kanta,daidai sanda idanunta suka sauka kan sticky notes din dake maqale a wajen iska tana dan kadata.

Hannu daya ta saka ta ballota daga inda take liqen,ta sanya idanunta akan kwantaccen rubutun dake a tsare kamar wanda aka tafa a inji bawai hannune yayishi ba

_mission accomplished_ iya abinda takardar ta qunsa kenan. Jujjuyata ta shiga yi tanason fahimtar saqon dake rubuce a jiki amma ta gaza kaiwa ga nan,abu daya ne kawai ya tsaye mata a rai da baici din ba. A niyyarta ta koma daki ta zauna ta jira wai koda zai sauko yaci bisa rashin sanin ya dade dayin nisa cikin gajimare. Amma qaguwa dason taga yaci din ya hanata komawar,sai tayi zaune a parlor parlor din tana saka kunne akan kowanne motsi na gidan,amma sam motsin da take iya ji din ba wani motsi bane na azo a gani,don hatta da securities na gidan bawai suna kusa da ita bane bare ta jiyo motsin nasu da kyau.

Sha biyu daya daya da rabi biyu biyu da rabi ba wani batun motsin kowa da komai cikin gidan,zuwa lokacin ta fara sarewa da lallai bazaya sauko ba,don koda wasa bata kawo cewa wai baya cikin gidan ba. Koda zai sauko a yadda suka lissafa mata halinsa tayi imanin bazaici komai na daga breakfast din ba,wannan ya sanyata cikin mutuwar jiki ta tattare kwanukan tayi kitchen dasu ta ajjiye tana tunanin yadda zatayi da kayan abincin.

A makare ranar tayi sallar azahar......har ta idar da sallar tunaninta ya karkata ga me ya kamata tayi?,ta shaidawa maamah din ko ta barta?,kada sanar mata ya sanyata ta dauka cewa gazawa ce har ta nemi yin wani motsi akan qannenta.

Wannan tunanin ya sanyata ta share,duk kuwa da cewa wani sashe na zuciyarta a matse yake data gaya matan,amma ta danne da wani irin qarfin hali tana saka ran zai fito yaci na dare.

Tana idar da sallar la'asar ta fada kitchen,ko a sannan ma tsaiwa tayi tana tunanin wanne irin kalar abinci zatayi da zaija ra'ayinsa har haqarta ya cimma ruwa?. Sai data kusa qure tunaninta kaf sannan ta zabi abu daya,ya wuce zuwa store tana duba dukkanin abinda take da buqata.

Dab da magariba ta baro gaban dining din data cika da warmers masu dauke da abinci. Tana takawa zuwa hallway din tana satar kallon stairs din. Zuciyarta cike da mamakin wanne irin mutum ne shi haka?,wanne irin mugun baqin hali ne dashi da har zai debi wadannan wannin a qunshe a sama ba tare daya sauko ko anji motsinsa ba?

"Ko yana zuwa masallacin ma oho" Ta furta a ranta a sarari tana jan tsaki gami da tabe baki,ta tura qofar dakinta ta shiga tana addu'a yadda a daren nan data saka hope me yawa,ta zuba komai da yawan adadi.....Allah yasa a wannan daren komai ya ratsahi har fiye da yadda maamah din keso don ta samu tickets din matsawa daga rayuwarsu ita da 'yan uwanta.

Cikin toilet dinta tayi wanka,takuma shirya cikin sassaqan cotton lite material me sauqi. Sallar magariba tayi,sai taci gaba da zama a nan. A hankali yaran suka fado mata,sai taji tana kewarsu,tana so taji!muryarsu koda kuwa maamah din zata kafa mata wani sharadi na daban kafin ta barta ta gansu,wannan tunanin ya sanyata miqewa a nutse tana mamakin duka yau bata dauki wayarta bata kuma yi amfani da ita ba.

Kai tsaye tasan inda ta aje wayar tata,can ta nufa,ta daga wajen da zummar dauka,saidai kuma wayar tace daukeni inda kika ajiyeni. Mamaki kadan ya kamata,amma sai ta share tana tunanin qila ta canza mata waje ne ta kuma manta inda ta ajjiyeta,don haka ta fara bincikawa guraren dake daura da nan ko a nan ta ajiye din.

Guri hudu duka bataga wayar ba ba alamarta,ganin zata gajiyar da kanta saita ajiye wannan ta koma laluben wayarta ta asali data barta a handbag din da suka dawo da ita jiya dake ajiye saman mudubin nata tunda ta ajiye jakar. Kaf ta lalube jakar sannan ta zazzageta,saidai babu wayarta babu alamarta a ciki. Mamaki yadan sanyata ja da baya,nan ma zuciyarta ta soma ayyana mata wataqila itama ya canza mata waje ne,don haka sai ta fara jaye jayen lockers tana bincike dakin. Wasa wasa har closet dinta ta duba babu wasu alama na akwai wayoyin. A hankali ta dawo tana zamewa ta zauna daga qasan carpet din da aka qawata gaban sofa bed din tana maida numfashi.

"Ya akayi haka?,me yake faruwa?,dukka wayoyinta babu ko guda daya?" Ji tayi sam ta kasa aminta ko ta samu nutsuwa,sai kawai ta fadada bincikenta har zuwa kitchen dining area waiko ta barsu a can,saidai babu komai kamar dai yadda ta gani a dakin.

A parlor din ta zame ta zauna,tana jin wani shakka da kokwanto na shigarta. Kota wacce fuska bataga waje ko wani sarari da wani zai samu daman shigowa gida irin wannan ba.....me wasu irin madaukakan katangu da kuma gwabza gwabzan security irin wadannan ballantana tayi tunanin wani ya hauro ya shigo musu...... Da sauri ta zauna sosai tana qanqance idanunta sanda wani tunani ya fado mata.

"Idan har haka ne shine kenan ya dauke wayoyin?,yaushe?,garin yaya?,a ina kuma ya samu damar aiwatar da hakan?" Tambayoyin dake danqare a kanta kenan data dinga juyasu.

Idanunta ta maida tana duban sashen da stairs dinsa suke,zuciyarta na bugawa kadan kadan,tana jin kamar ta tashi ta haura ta sameshi a can,taji meye hujjarsa na daukar mata wayoyi,bayan hakan ba huruminta bane?.

Bata fahimci cewa gidan ba kowa ba......ita daya ke rayuwa a cikinsa duk girmansa ba sai da sha daya na dare ta gota a idanunta. Sai a sannan taji wani irin tsoro ya soma mamayarta sanda zuciyarta ke bata hasashen ita daya ce qwallin qwal a gidan. Wani irin karyewa zuciyarta tayi,tsoro yana sake shigarta sanda take qudundune cikin duvet dinta. Bata taba kwana ita daya ba koda cikin dakinsu ballantana a gidansu gaba daya ba.....wanne irin azzalumi ne shi da zaya fita yabarta a gidan da yafi qarfin zaman mutum hudu ma yace ta kwana ta rayu ita kadai?.....ba wayar da zata kira wani ballanta taji sassauci......koda ta duba wayar girke dake parlor din da zummar ta sadata da security din da suke waje taji ko zata samu aron waya daga hannunsu cikin rashin sa'a ta samu an yanke sadarwarta,ba zata iya yin magana da kowa ba banda dakunan dake cikin gidan.

Kanta ta cusa cikin pillow din tana jin yadda bugun zuciyarta ya qara tsananta sanda karen dake wani sashe daban na gidan ya tsananta haushinsa. Bata taba tunanin akwai halittar tsoro a qirjinta har haka ba sai yau.....ashe dukka jarumtar da take zaton tana da ita ba jarumta bace.....ko tace ta tsaya ne kadai ta bangaren saita maza daukan darasin rayuwa da sanin ciwon rasa wani abu da xukata suke tsananin so da qauna.

Batasan ya akayi ba ta samu da qyar wani takurarren bacci yayi awon gaba da ita.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 26


26



Kwana daya kwana biyu haka awanni suka dinga juyawa da ita cikin gidan,cikin wani irin matsanancin shuru kewa da kuma kadaici. A hankali ta dinga jin wani matsanancin takura,ta yaya zata zauna irin haka ba waya ba gilmawar kowanne dan adam?,tv kuwa sam taqi ta kalleta bare ta gwada kunnata. Da farko ta dauka zata iya jurewa,amma sannu a hankali saita fahimci ashe mutum rahama ne a kusa da kai,koda kuwa ba wata mu'amala da zata hadaka dashi. Tayi dukka juriyar da zata iyayi sai taji haqurinta ya soma gazawa. Wani danqararren bacin rai ne yake cinta game dashi wanda qilan inda yabar mata wayar ma a wannan karon batajin akwai abinda zai mata shamaki daga kiransa ta zazzage masa abinda yake cikinta. Ta yaya ita din da ta kwashi shekara aqalla biyar zuwa shida,ba wata ranar banza da zata fito ta fadi bata fita ba.....yanzu kawai rana tsaka ta wayi gari da mummunan kulle irin wannan?. Ko a baya batata ji a ranta akwai wani lokaci da zayazo a sanyawa qafafunta irin wannan sasarin ba,ba lissafin aure kwata kwata cikin kanta shi ya sanya bata kawo yiwuwar afkuwar hakan a kanta ba koda sau daya.

Ranar data cika kwana na hudu,tun qarfe goma na safe taji takai maqurar da ba zata iya jurewa ba. Sha daya da rabi daidai ta kammala shirinta cikin atamfa. Ta taka a hankali zuwa inda take da tabbacin ta ajiye kudinta data shigo dasu cikin gidan,ta bude locker din ta zura hannunta don debosu,don ta gama tsarawa kanta zata taka ta fita ta samu napep duk kuwa da cewa tasan area din kwata kwata yana da wahala kaga abun hawa na haya.....to amma ta gwammace tayi tattaki zuwa babban titinsu tayita jira cikin rana har ta samu abun hawan da zai kaita gida. Zuciyarta da tunaninta gaba daya yana kan taje ta binciki lafiyarsu huda.....kowanne dare dasu take kwana dasu kuma take tashi,suna cikin aminci ko kuwa aah?......da qyar ta iya jure wadannan kwanakin suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login