Showing 267001 words to 270000 words out of 557259 words

Chapter 90 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

426

fuskarta dinnan me shimfidadden kyau dake dauke yau din da wani irin kwantaccen fushi. Zubawa fuskar tata idanu tayi kamar yau ta fara ganin kanta da kanta,iya kallon kawai yana motsa zuciyarta gami da tuna mata a karan kanta wacece sabreen,wani sashe na zuciyarta ya motsa yayi aikin daya jima baiyi ba,taji wani abu ya darsu a zuciyarta wanda ta jima tana yunqurin daddago dashi amma yana komawa

"Ki ajiye wannan a gefe.....yaya jikin huda?" Tayi mata tambayar da take kwana da ita tana tashi ba tare da tasan waye zata yiwa ita ya kuma basu cikikkiyar amsar da take buqata ba.

"Jikin huda?.....alhamdulillah......saidai ban da tabbacin yadda ya kamata ya kasance". A hankali ta lumshe idonta tana son yiwa amsar tambayar tata fashin baqi. Bugun zuciyarta yana son ninka gudunsa saboda samun mabanbantan amsoshi daga mabanbantan lunguna da saquna na zuciyartata wadanda basuyi daidai da fatanta dama abinda takeso taji ba.

"Mu ajiye wannan......zan dan yaba miki game da yadd kike qoqarin ciyar dashi abinda muka baki,saidai har yanzu kin gaza cimma manufar abinda kikeyi din......caring kulawa.....ba wata halitta da batasan kulawa.....dole ki fara samun zuciyarsa kafin ki samu cikinsa da jikinsa....."

".......ba wannan cikin jarjejeniyarmu.......wai shin..kina zaton ina da buqatar zuciyarsa?,ko ina da buqatar hanyar da zata sadar dani ga shiga zuciyarsa?". Tayi maganar kanta tsaye da wani irin tsauri,saboda zafi da a yau zuciyarta keyi mata,tana jin kamar wani abu me kama da gajiya da kuma fara jin takura yana mintsinin zuciyarta.

Murmushi me sauti maamah din ta saki tana gyara zamanta

"Bana fatan ki samu zama ko shiga zuciyarsa na dindindin,a taqaicema dai....banda yanayi irin na lalura banjin kinkai quality din da zan baki license na shiga zuciyar mutum me tsada,namiji irin muhammadu ba.....amma karki manta,dole ne ki sadaukar masa da komai don isa ga burinmu.....idan nace komai ina nufin komai da komai fa,na zabeki ne saboda ina da tsammanin zaki iya bada komai don cikar muradina.....koda kuwa jikinki ne...."

"Ya isa!" Ta furta a tsawace saboda jin maganar tata ta fara shallake guri,uwa uba tana neman fin qarfin kanta.

"Kibi a hankali......a yanzun duk da ban mallakeshi ba,amma zakisha mamakin abinda zai biyo baya idan har na shaida masa matarsa tana min shouting tana kuma dagamin murya....." Zafin radadin maganarta ta farko bata saketa ba,don haka bata maida hankali sosai akan maganarta ta biyu ba. Burinta shine ta furzar mata da abinda yake ranta,tana jin kamar takai maqurar da zasu dinga wasan tamaula da ita tsakanin ita da d'anta.

"Zanci gaba da ci dashi kaman yadda iya abinda yake zayyane kenan a bisa yarjejeniyarmu......daga hakan banajin zan qara akan komai.....faduwarki ko nasararki ya ta'allaqa ne da yadda na samu tabbacin lafiyar qannena" Daga haka ta katse wayar kawai tana ajeta a gefe.

Taso tayi tariyar maganganun da sukayi da maamah din,amma a yau sai taji gaba daya bata da buqatar tuna komai.....kawai tana jin ba zata iya ci gaba da zamowa kamar tamaula tsakanin su ba. Wani irin confidence takeji,saita miqe tana komawa bakin qofar da zummar ajewa zuwaira wayarta,ta dauka duk sanda ta dawo,don ko haduwa da ita bata sonyi. Ga mamakinta a tsaye ta sameta a bakin qofar kamar wadda aka bawa gadinta. Wani kallo ta jefeta dashi tana jin sam matar bata mata ba

"Ba wani abu da ake buqata?" Ta fada da sauri bayan ta karbi wayar ganin sabreen din na zummar shigewa ciki

"Babu" Ta bata amsa a taqaice tana maida qofarta ta kulle.

Yadda yau yarinyar ke amsa mata magana a tsaitsaye sai takejin kamar akwai abinda ta taka,akwai abinda ya bata confidence a kanta. Ci gaba tayi da juya wayar a hannunta tunaninta yana yin nisa gami da rarrabuwa kashi kashi. Wani tunani ya kutso mata cikin kwanyarta

"Me yasa ba zaki murza kambunki ba?,ki gwada qarfin iko da mulkinki ba har akan fu'ad din?" Wani sashen na zuciyarta ya bata shawara. Shuru tayi tana sauraren daya bangaren tare da juyar maganar cikin kwanyarta. Kai ta gyada tana bawa kanta tabbacin tabbas wannan din zaiyi aiki.....koda baiyi diki dari bisa dari ba to akwai yiwuwar samuwar galaba.

Tana qoqarin kiransa ta shaida masa tana buqatar ganinsa sallamarsa ta mamayeta. Tana amsa sallamar farinciki na cika zuciyarta yadda Allah ya dubeta ya jefo mata shi,saidai a saman fuskarta ba haka bane. Ranta yana hade,hakanan ta boye duk farincikinta don tanason ko meye zata gaya masa ya daukeshi da muhimmanci.

Sai daya iso gabanta ya zame yana gaidata ta hanyar tsugunawa saman qafafunta. Bayan ya gama gaidata din shuru ya biyo baya,a nutse yace

"Ba komai da ake buqata?,ba wani matsala?" Yayi tambayar data zame masa wajib duk sanda yazo gaidatan don qoqarin sauke haqqin Allah da yakejin ya zama wajibi ya sauke din.

Kai ta girgiza fuskarta a daure.

"Ba abind nake buqata.....amma matsala dai akwaita". Daidaita tsugunnonsa yayi kafin ya zame ya zauna sosai a gabanta. Duk sanda tayi wannan yanayin kota furta magana makamanciyar wannan zai wahala idan ba wani aikin bane zaya zameshi. Idanunsa yadan lumshe gami da budesu duka lokaci guda cikin qoqarin hadiye fargabarsa,yana tunkarar qalubale komai girmansa.....gaagwarmaya komai wahala da kuma taurinta,amma har yanzu zuciyarsa baya iya jure wadannan halayen da maamah din,dabi'unta suna kassarashi,ya kasa sabawa,baisan me yasa ba,ko don ita dinn wata jigo ce da abubuwanta ke tafiya ba yadda ya kamata ace sun tafi ba?.

"Wacce matsala ce?,me yake faruwa?" Ya tambayeta a nutse.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 38


_Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_

*_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa a jiki_*


38


"Muhammadu" Ta kirashi da ainihin sunansa,ba tare kuma data bari ya amsa ba ta dora

"Nikam bansan a rayuwa akwai wani abu da yafi haihuwarku da nayi muhimmanci ba" Idanu ya zuba mata yana jin tamkar ya tashi ya fita da gudu ya tserewa maganganunta,don yasan zai wahala ba kamar kullum bane,dora masa nauyi da mas'uliyyar da zai gaza dauka kota masa tauri. Kai ya girgiza,ya buda baki zai magana ta sake danneshi da kalamanta

"Bansan wanne irin rashin muhimmanci nake dashi a rayuwarku ba da har zan zartar da hukunci cikin rayuwarka,nace kum ga alfarma ko abinda nakeso kayimin ka gaza yi din,ace har yanzu maganganun ameenatu da umarninta yana zama gaba da nawa?" Ta qarashe maganar tana jin dacin haka sosai har cikin zuciyarta. Batasan wanne tozarci ma ya kamata ameenatu ta fuskanta ba aduk sanda haqanta ya cimma ruwa,har yanzu idan tayi hasashen abinda zata saka ta fuskanta sai taga wannan hukuncin yayi kadan.

Sam baya qaunar ta dinga sanyo maganar anni cikin maganganu da ayyukansu,don bazai iya tuna sanda anni ita tayi magana a kanta ba indai ba alkhairi ba.

"Muhammadu.......yanzu ni da hannuna na baka amanar yarinyar mutane......na roqeka ka mu'amalanceta kamar kowanne miji da mata.......ka kyautata mata ma faranta mata,ka jata a jiki amma haka ga gagara?,ka kasa cikamin wannan alfarmar da zata bayya a irin kima da martabata a idon yarinyar?". Qasa yayi da kansa,shi maganar ma nauyi tayi masa sosai akai. Ta wani gefen kuma ranshi da zuciyarsa suma motsa. Yanzu har taurin kan yarinyar da tsaurin idonta yakai ace ta kawo ma maamah qararsa?,har da maganganu irin wadannan marasa dadin ji?. Sai data gama dukkan wani fada baice komai ba,har sai da tayi shuru sannan yace

"Kiyi haquri,in sha Allah za'a sake yin qoqarin gyarawa da canzawa". Ya furta a taqaice. Har cikin ranta yadda ya amsa mata haka a sauqaqe ya faranta mata sosai

"To Allah yayi albarka" Ta fadi kalmar da bazaice when last da yaji ta fada ba. Muryarsa a sanyaye ya amsa mata,sannan ya miqe yana mata sallama yana fita daga falon.

Tun kafin ya qaraso Jordan ya wangale masa qofa,da wani irin zafi ya isa ya shige motar Jordan ya maida murfin motar ya rufe. Suit dinsa na sama ya fara ballewa yana zareta daga jikinsa saboda wani irin zafi da yakeji tun daga zuciyarsa har cikin fuskarsa. Iske me qarfi ya fesar daga bakinsa bayan ya zuqi wata

"Wanne abune meqarfi da girma a tsakaninsu bayan wannan?" Ya jefawa kansa da kansa tambayar yana motsa labbansa.

"Ita ta shiga jikin maamah ko maamah ce ta shiga jikinta?" Ya sake maimaita tambayar da ba wanda zai iya bashi amsarta. Yanzun har matsayinta da girmanta wajen maamah yakai ya samu sanyawar albarkar maamah din saboda dalilinta?,wanne aiki take mata haka me faranta rai bayan abinda yake suspecting?. Tunanin daya rakashi kenan har cikin office dinsa,ya kuma wuni yana tayashi zama,duk kuwa da uban tarin ayyukan daya samu suna jiransa. Duba documents da sanya hannu cikin wasu takardun,wasu takardun suna da buqatar hankalinsa da nutsuwarsa kafin yakai ga sanya hannu,da qyar ya hada hankalinsa bayan sallar la'asar ya soma duba wasun,bayan ya yiwa kansa matsayar matakin da zai dauka.

Komawa tayi ta sake kwanciya bayan sallar la'asar din,tana lissafin nan da awa daya koda rabi zata shiga kitchen saboda shi.....saboda mutumin da ba ganin girma qima ko martaba sam sam tsakaninsu. Idanunta ta runtse,a yau tana jin wani zafi zafi na yadda maamah ta bautar da ita. Batasan me yake tilastata lallai saita yi sai kuma ta cika muradin maamah din ba. Tsaki taja tana bude idanun nata,sai suka fada saman gift din da anni ta bata ranar da suka je.

Dan murmushi ta saki qasan zuciyarta,matar ta kwanta mata a rai,tana da wani irin calmness me taba zuciya nutsuwa da kuma wani irin kwarjini. Tashi tayi tsam ta daukosu ta dawo ta zauna saman abun sallarta data tashi ta soma budewa tana tuna fuskar matar da takejin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanzu.

Littafin farko ta dauka daya qunshi addu'o'i akan kowanne abu,harkokinmu na yau da kullum. Shafin farko ta bude,sai ta dinga tuna zamanin da ummensu ke raye,Lokacin da take tsaye a kansu kai da fata,ba batun fashin islamiyya ko wani abu da yayi kama da wannan. A duk dare itace malamarsu,zata zauna a tsakiyarsu saita tabbatar kowanne karatunsa ya zaunar masa akai,musamman karatun addini da a nan tafi qarfi,na bokon tafi jiran abbansu idan ya dawo,musamman idan ya zamana itace da girki,idan ba ita bace dole saita dauki uzuri an bata lokaci.

Hannu tasa ta shafi addu'ar farko da sam ta mantata cikin rayuwarta,ummensu itace ta fara koya mata ita tana kuma iya tuna lokacin har yanzu,sai ta tashi ta koma saman sofa ta zame kadan tana bin addu'o'in daya bayan daya tana dubawa suna kuma sake tuno mata da kansu.

Sosai takejin dadin karatun,don ya debe mata kewa me yawan gaske. Babu zato daga saman kanta din,daidai wata kyakkyawar qaramin luxury stand taji qaraurawa tana kadawa. Zubawa wajen ido tayi,wata mulmulalliyar na'ura ce da take zubi da telephone. Tunawa tayi amna ta taba dagawa tayi kira zuwa parlor sanda sukazo,sai a sannan ta tuna na'urar sadarwa ce da aka shiryata duka gidan da kuma tsakanin dakunan gidan har zuwa Kutchen,wannan ya bata qwarin gwiwar saka hannu ta daga ta sanya a kunnenta.

"Ranki ya dade......malamarki ce tazo,sabuwar malamar da yallabai ya daukar Miki saboda karatun yamma".

"Malama kuma?" Ta tambayi kanta da kanta cikin tsananin mamaki tana son tuna yaushe sukayi wannan maganar da shi?.
"Duk cikin salon da zai miki mugunta ya cusguna miki ne kaman yadda ya dauki alwashi". Ido ta lumshe tana budesu sannan a nutse tace mata

"Ki sallameta zuwaira......ko kuma ta jira wanda ya tattagota din" Daga nan ta kife wayar tana komawa ta zauna qirjinta a quntace.

Wannan abun da yayi me yake nufi kenan?,ita din jahila ce?,ko batasan komai ba saishi zai sanya a karanta mata?. Wannan tunanin ya tsaidata,sai data gama baqin ran da bacin ran sabon salon wulaqanta mutum daya bullo dashi......hakanan ba don taso ba ta miqe tana wucewa kitchen.

Tana shiga zuwaira na fadowa,sai ta waiwayo tana kallonta. Cikin jikinta wani abu ya bata,ta yaya duk wani motsinta zuwairan kamar tana biye dashi ne?

"Ranki ya dade dame za'a taimaka miki dashi?" A nutse ta juya kawai ta fara aikin gabanta,kamar ba zata amsa mata ba sai kuma ta tura mata lettuce da cabbage carrot da peas tace ta gyara ta yanka mata.

Zaman kurame kawai sukeyi cikin kitchen din,zuwaira nata satar kallonta tana son ta dan tabota da magana don ta gina alaqar sabo a tsakaninsu amma bataga wannan fuskar ba sam

"Tashin hankali" Zuwairan ta fada qasa qasa,daga ita har mijin haka fuskokinsu suke kamar na shanu? Ta tambayi kanta,ita dai har yanzu bata taba ganin fara'a ko dariyar dayansu ba.

Sai da suka kammala komai sannan ta fidda magungunan zata cakuda kaman yadda ta saba. Ta bude murfin ta karkata gorar,sai kuma ta tsaya cak. A hankali ta daga idanunta ta zubesu akan zuwaira data tsaida komai tana son tabbatar da zubawar. Karon farko da cikin jikinta taji kamar nauyin idanuwan wani yana kallonta zatayi abinda bashi ya dace ace tayi ba akan wani,duk kuwa da tasan jirgi daya shine ya debo zuwaira da ainihin me kwangilar,amma a yau saita ji wani nauyi.

"Zaki iya bani space?" Ta jefa mata tambayar taba dinke girarta sosai fiye da dazu.

"Au to....to ranki ya dade" Ta fada adan daburce sannan ta juya tana fita a kitchen din. Haushi ya sanyata kwarara da yawa,idan komai ya qare ai a huta,taga ta inda zata tuhumeta kuma,sai taja tsaki tana jefa roban a shara sannan ta juya ta fice tana baiwa zuwaira dake falo umarnin taje ta jerasu,sai ta wuce kai tsaye zuwa dakinta.

Itama din a gaggauce ta shiryasu tana kallon kayan,baki ta tabe,tana jin haushin yadda lafiyayyen abinci irin haka yake salwanta,ga nasu iyalan can cikin yunwa da buqatar abincin da baikai wannan bama,amma akan mutum daya anata asarar lafiyayyen abinci irin wannan. Hankalinta ta maido jikinta da sauri,saita juya tana barin falon cikin son kiyaye dokarsa da tsoron kada ya dawo ya sameta a wajen kamar yadda ya shardanta mata.

K'arfe Tara da wasu mintuna motocinsa suka tsaya a farfajiyar gidan bisa halastaccen parking da kowanne driver na kowacce mota ya qware akai. A nan harabar gidan ya barsu ya wuce ciki shi dame sunan malam,wanda iyakarsa qofar parlor din farko ya juya shima yana komawa cikin guard da security na gidan dake qoqarin tabbatar da tsaro da lafiyar kowacce mota kafin masu tafiya su wuce a sake tabbatar da tsaron gidan sannan a maidashi a rufe kaman yadda yake,shida da fita kuma sai da izinin masu gidan.

A hankali yake ratsa falon farko zuwa na biyu kafin ya isa stairs dinsa. A gajiye yake don duk sanda yayi dare irin haka a company to tabbas cinkoson aiki ya riqeshi ne.

Tun daga nesa yana taka stairs din ya hangi maqullin maqale jikin qofar,ya isa a hankali ya sanya hannu ya cire sannan ya tura qofar parlor din. A nan zarginsa ya tabbata,mug din da yayi amfani dashi a daren jiya yana zaune abinsa dirshan saman side table din,yayin da dish din da yayi amfani shima dashi yake zaune saman dining abinsa hankali kwance.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

39

_Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan Allah S A W ya ambaci ranar juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA YA ROQA DIN". sai manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana baida tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_



Wani bacin rai ne karon farko ya sauko masa,ba abinda ya dawo masa akai sai abinda ya faru a dazu. Yadda maamah ta fitittike tana jaddada masa yadda takeso ya mu'amalanceta ko ya kula da ita,amma ko kusa ko alama shi baiga alamun tasan darajar kalmar aure ba koda kuwa auren 'yar tsana aka daura,ballantana shi data deba kudaden da ranta keso,karamci kuma ya sanya suka qara mata da wasu abubuwan da shi kansa baisan me su anni suka kashe ba.

Duka sai yaji abun bai masa ba bai kuma zauna masa akai ba,ya kamata ya qara bata lesson. Yana takawa zuwa bedroom din nasa yana watsar da kayan hannunsa,kama daga socks takalminsa suit briefcase dinsa da sauran tarkacen daya shigo dasu. Wani budewa hancinsa yakeyi yana tsukewa saboda bacin rai,ya tsani raini ya kuma fahimci halinta ne,ya tsani rashin kunya ya kuma karanci dabi'arta ne. Bai dakata ba sai da yayi wanka,ya hadawa kansa fruit salad a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login