Showing 534001 words to 537000 words out of 557259 words
A nutse ta gama komai,ta sake musu addu'a,ta shiga toilet nashi tayi brush sannan ta hauro gadon tana rage hasken qwayayen dakin.
Ya jita kusa dashi sosai,amma bai taba kawo zatayi abinda tayin ba a yanzun. Wata kyakkyawar runguma tayi masa ta baya,cikakken dukiyar fulaninta da shayarwa tasa y qara cika ya tokare a bayansa.
Saura kadan numfashinsa yayi qaura daga gangar jikinsa,wasu irin kaifafan kibiyoyi ta sakar masa wanda suka ratsa sassan jikinsa d wani irin matuqar sauri suka aike masa da wani nannauyan yanayi daya sakashi takure jikinsa ba tare daya shirya hakan ba.
Matseshi tsam tayi ta baya,tana bashi wata kyakkyawar runguma. Har cikin jininsa sai da yaji yadda dumin jikinta da tudun dukiyar fulaninta ya zauna sosai saman fatar bayansa.
Sosai ya riqe numfashinsa don hana kansa jin abinda yakeji yana masa yawo a jiki,amma yadda zuciyarsa ke bugawa da sauti ya sanya ta kasa aiwatar da hakan,ya kamo numfashin da qyar sannan ya tattaro juriyarsa yana dan zamewa.
"Stay away please" Ya fada da wata irin kasalalliyar murya.
Maganan tashi tazo mata a bazata,tsam tayi da ranta tana dakatawa da komai,tana jjn yadda zuciyarta ke bugawa da sauri,tana kuma jin yadda itama a yau din take jin ta dokanta dashi.
"Hamma" Ta furta a sanyaye. Qarasa janye jikinsa yayi,sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta
"I'm not in the mode,im feeling off" Ya furta muryarsa tana qara yin can qasan maqoshinsa. Idanunta da suka fara lumsheea ta ware tana kallonsa. Yau ita jadda yake cewa he's off?,off for what?.
Tana tsaka da wannan tunanin ta ganshi ya dauki babban blanket nasu da pillow ya aza saman sofa ya kwanta abinsa ya lulluba har saman kansa.
Baki ta sake kawai tana kallonsa,abun gaba daya ya bata mamaki,yau ita abben su fauzan din ke yakicewa?,ita din yake dodging?. Wani matsewa zuciyarta dake qirjinta tayi,sannan a hankali wani hawaye me dumi taji kawai ya sauko mata saman fuskarta.
Da hanzari ta sauko daga saman gadon kai tsaye,ko bedroom slippers dinta batayi ta kai ba ta soma fita a dakin da sassarfa.
Komai da takeyi yana jinta,bai kuma motsa ba har sai da yaji fitarta,kunne ya kasa sosai,kusan mintuna biyar sannan ya yaye duvet din ya sauka a hankali yana fita a dakin.
Bata duka bedrooms din hakanan bata parlor din,abinda ya bashi tabbacin sauka tayi gaba daya daga sassan nasa.
Wani qaramin murmushi ya saki,qasan ranshi yana fadin ashe babu dadi. Maida qofar parlor din yayi ya kulle abinsa ya koma bedroom din duk da yadda zuciyarsa ke jin matsananciyar kewarta.
Yaran gaba daya ya sauke daga nasu gadon,ya maidosu kan gadon nashi,ya bajesu ya shige cikinsu abinsa ya kwanta sosai yana sakin ajiyar zuciya,yana kuma jin kusancin dake tsakaninsa da yaran.
Kwata kwata bacci qaurace mata yayi,batajin zata iya jurar wannan abun. Yayi mata komai zata jure amma banda nesanta kanshi da ita,ita kanta cikin tsananin buqatarsa take,don ya riga ya horata ta wannan fannin ya kuma maidata irinsa. Abu daya ne ya sanyata ta guje masa stitches nata na CS dinta da take ganin kamar zai farke.
A haka bacci barawo ya lallabo ya saceta,cike da fata da sanya ran zai shigo har dakin ya nemeta,ko don saboda yaran ma. Sam baccin baiyi wani tsaho ba ta farka firgigit,ta shiga buda idanunta sosai tana sanya ran ganinsa ko yaran ko alamun ya shigo ya fita,amma bataga komai a ciki ba.
Ranta taji ya bacu,zuciyarta ta quntata,sai ta shiga toilet tayi fitsari ta daura alwala,ta dawo tayi nafila raka'a shida. Tana saman abun sallan tana addu'o'inta wani baccin ya sake waftarta,wanda shine bacci mafi tsaho da tayi,don bata tashi farkawa ba sai da akayi kiran farko.
Yanzunma bataga alamun ya shigo ba,kawai sai wata qwalla ta cika mata idanunta. Dama yake da ciwo kayi abandoning mutum?. Yaran sun tsaye mata a rai,tasan zai wahala ace duka tsahon daren ba wanda ya nemi nono,kawai saita sauka daga kan abun sallar ta soma takawa a hankali ta fice a dakin.
A Hankali ta bude qofar bedroom din,mamaki da haushi ya cikata fam kaman zata fashe. Wato shi ya sanya yaranshi a gaba abinsa suna sheqa baccinsu ko a jikinsu?,ita gata nan wahalalliya ta hana kanta da kanta sukuni duka saboda yaran da nasa tunanin,kawai saita saki kuka me sauti,kukan daya tasheshi ya kuma saka yaran motsawa,daya bayan daya suka farkawa tarwai abinsu,sai kuma a sannan suka fara neman abincinsu ta hanyar fara cilla qafafu suna son fara sakin kuka.
"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihinnushur" Ya fada sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta inda ta zauna gaban gadon tana musu kuka.
"Me akayi miki?" Ya tambayeta hankali kwance,tambayar data sakata sake masa hararar da batasan tayi ba,sai ya dauke kansa kawai yana sauka daga gadon a hankali ya wuce toilet don daura alwala yayi raka'atanil fajr kada ta subuce masa. Rigima ce fal idanunta yake hanga,shi kuma indai wannan rigimar ce a shirye yake da ita,ya fita jinta ma.
Ko kafin ya gama alwala ya fito dakin duka ya karade da kukansu su ukun,ga mamar tasu zaune a gabansu itama tana hawaye sosai.
Tausayi da dariya abun ya bashi duka lokaci daya,ya dake yana zura jallabiyyar jikinsa da sauri bayan ya tsane ruwan gargasarsa.
"Baki gani kuka suke kika zauna kika sakasu a gaba kina kallonsu?". Kaman jira take yayi maganar ta miqe tana nufar qofar,kuka takeyi sosai,sai ya qarasa yasha gabanta yana duban idanunta.
"Hamma raino kawai na iya dama?".
"Ni me nace miki ne Sabreen?,me kikeso kuma ehmmm?" Yayi maganar da alama shima ranshi ya fara baci. Ta kalleshi sosai ta kuma fahimci kukan yaranshi ke dagula lissafinsa,kenan yafi jin kukansu a ransa sama da nata?,wannan ya sanya ta soma neman hanyan fita kawai.
Hannu daya ya sanya ya jawota baya kafin ya saka hannuwansa duka biyun ya dauketa cak yana lullubeta a qirjinsa yana jin yadda sassanyan qamshinta ke bulale masa hanci,bai kuma direta ko ina ba sai tsakiyar gadon. Haurawa saman gadon yayi ya dauko farouq da nasa kukan yafi na kowa ya aza mata saman cinya,ya kuma tsare ta da idanun nasa. Zuwa yanzu qwayar idanun nan sun kuma na muhammadun sosai,me babban suna kuma shugaban kamfanonin jadda.168
"Feed him" Ya bata umarni nakai tsaye da husky voice dinsa. Duk wani annurin fuskarsa yana daukewa,kukan yaran yana jinsa kamar d'igar ruwan dalma saman tsokar zuciyarsa.
Umarnin ya zarce har cikin kwanyarta,saita soma nuqu nuqun fidda maman. Gani yake bata masa lokaci takeyi shida yaran gaba daya,don haka ya buda hannayenta kawai ya balle duka button din rigar tata ya zameta daga kafadunta.
Cikakkun dukiyar fulaninta da suke a tsaye,sun cika sosai irin na masu shayarwa ya bayyana,abinda yayi nasarar karya alwalar da yaketa faman tattalawa kenan.
Hannunsa ya miqa cikin dakiya ya dagoma fauzan abincinsa,nan da nan ya kama,sannan ya saki ya koma wajen su fawwaz da kukan nasu ya sassauta.
Bai nuna yaga hawayen da take zubarwa ba sam,yaci gaba da bata yaran suna sha,har sai kowannensu ya qoshi sannan ya janyeshi. Suna sha yana karbarsu daya bayan daya yana sauka dasu. Batasan inda yake kaisu ba,amma haka yake dawowa hannunsa babu su.v
Almustapha ne qarshe,don kusan ya fisu haquri,sai daya tabbatar shima ya kama sannan ya tashi yayi raka'atanil fajr din. Sanda ya idar ya gama sha shima,ya miqa mata hannuwansa yana kallon fuskarta da tayi ja saboda kukan da tayi. Miqa masa shi tayi shima,sai ya karbeshi ya kuma ajiyeshi a gefe. Hannunsa yasa yana maida mata rigarta yadda take duk da qoqarin maidawa da takeyi da kanta.
"Ka barmin abata zan mayar" Ta fadi cikin rawar murya. Wani kallo ya jefeta dashi.
"Ina ruwanki?,wannan din ba jikinki bane.....jikin muhammad jadda ne.....naki jikin gashinan" Ya fadi yana nuna kansa da kansa da yatsa.
Wani abu me sanyi taji ya sauka a zuciyarta,har sai data lumshe idonta kadan,ya kammala maida mata ita tsaf,ya saka hannu ya dauki almustapha fawad yana tafiya qofa.
"Kiyi alwala kiyi sallah.....zanje sallah na dawo" Ya qarasa maganar yana qarasa fita. Tsaiwa yayi yayi locking qofar da new password ta yadda ba zata iya fita ba,sannan ya gangara ya miqawa salwa fawad yace a gyarashi shima kaman sauran 'yan uwansa sannan ya wuce masallacin.
A sanyaye tayi alwalar tayi sallar,tayi addu'o'inta kaman yadda ta saba. Idanunta sun mata nauyi sosai,kuma da alama rashin bacci ne isashe na kwanakin,don haka sai kawai ta koma toilet ta hada ruwa me dumi sosai tayi wanka,ta kuma nade kanta da jikinta da towels dinsa wadanda qamshin jikinsa ya kamasu sosai. Idanu kawai take lumshewa,wanxuwar towel din me manne da qamshinsa sai ya xame mata kamar shine nannade a jikinta. Wani irin azababben shauqinsa takeji ta kowacce fuska,tana jin kaman takai kanta gareshi ta roqeshi.
"Wanne irin abune wannan?" Ta tambayi kanta da kanta sanda tayi zaune saman stool a gaban madubi. Hirarta da fannah ta dawo mata fes a kanta.
"Wata macen sai ta fara haihuwa take zama cikakkiyar mace me cikakkiyar buqatar namiji..sai a sannan komai nata yake qosawa yake kuma bunqasa" Dauke hawayenta tayi da yatsanta,tana raya cewa wataqila ita din tana cikin irin wadannan matanne.
"Kamar ke kadai keda idanun kuka?,bakisan ni ya kamata na zauna nayita sheqa kuka ba?" Taji maganar sa daga gefanta wanda harga Allah batasan da shigowarsa ba.
"Taso kizo nan" Ya bata umarni kansa tsaye yana nuna mata daura dashi.
Da kallo yake binta sanda take takowa inda yake. Duk da yake shi ba ma'abocin kallon mata bane amma yayi imanin samun takun isa a wajen diya mace irin na sabreen dinsa zaiyi wahala,kaman yadda qirar jikinta tasha banban data dubban mata,don ko a yanzun da take tafiyar saika rantse ba wani yaro daya zauna a cikin ta tsahon wata tara,sai cika da komai nata ya sakeyi. Duk da yanayin halitta ma ya lura macace me gyara sosai(idan kina da kyau ki qara da wanka,karki yadda ki zauna a wargaje waike jego kike ko kin tara yara sun miki yawa,xaki banu zaki lalace fes wallahi).
"Sabrrrr.......don ni bani da gata?,don ni bani da wanda zan gayawa damuwata......don ni namiji ne bani da idon kuka?" Yafada da wata raunanniyar muryar data tilasta mata daga idanu ta dubeshi. Wani irin tausayinsa daya tsarga mata ya sanya hawaye taruwa a idanunta. Miqewa yayi,da alama baiso maganar ma tayi tsayi can.
"Alqawari nayi,tun a wancan daren bazan taba koda yatsarki ba muddin zamanmu sai kina cikin yanayin".
" Ina ciki wallahi" Ta furta da wani irin sauri bayan ta yiwa kanta kyakkyawar masauki a qirjinsa tana cukuikuyeshi. Dariya ta kusa kubce masa duk da yadda sanyin hawayenta daya sauka budadden qirjinsa da wuyan rigan ya zama V shape ya taba zuciyasa sosai.
"I can't live without you.....You're my everything,without you,I'm lost,i need you now and forever,you're irreplaceable hamma........ka yafemin hamma.....bazan sake ba hamma......na tuba" Ta qarasa fadi tana sakin masa wani kukan kisisina me tsayawa a zuciya.
Hannunsa har rawa yake sanda ya riqeta,ya sake mata wani tsatstsauran riqo yana sanyata tsakiyar qirjinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Kasa magana yayi,kasa cewa komai yayi,kaman yadda shirunsa ya isheta amsa ta hanyar bugun da zuciyarsa takeyi.
Ta yarda ta kuma amince tabbas taso ta zalunceshi,jikinta ya sake sanyi da kalar soyayyar da yakeyi mata.
"Dukka wannan bugawar da Xuciyar nan takeyi tana yine saboda ke.....ke kadai sabreen,ban taba koda sha'awar daga kai na kalli wata macen ba bare har naji ta fusgi hankalina na ko ta dace da rayuwata ba bayanke".
"Nayi maka alqawarin xame maka aljannar duniya koda shine xai kawo qarshen bugun zuciya dana numfashina" Lafaxinta na qarshe kenan daya iya tantancewa,ya dauketa cak ya ajiyeta inda yafi wayo sannan ya fara rabata da towel din jikinta.
Wata irin sassanyan safiya ta bashi.....wata irin safiya me tsayawa a Xuciyar masoya.....
"Can i have you for breakfast today?" Ya fada da wata narkakkiyar murya dake wani irin rawa.
Yana dire tambayar ta tabbatar masa da abinda yake buri,abinda yake fata yake kuma tsananin buqata. Shi da ita kowannensu da zafinsa yazo,shi da itan gaba daya ba wanda bai gigita dan uwansa ba da wani irin zazzafan salo daya sake tabbatar masa itace DUNIYARSA shima shine DUNIYARTA. Gaba daya ta canza masa,ta kuma caza masa kwanya,yana jin tamkar yaune ranar farko a rayuwarsa daya fara kasancewa da ita. Ta gigita duk wani tunani nasa......ya sake fahimtar cewa lallai macen datasan kanta haihuwa ko shekaru basa saka kimarta zagwanyewa,a yanzunne ya sake gamsuwa da lallai sabreen dinshi ta zama cikakkiyar mace.
Tana kwance luf saman qirjinsa sanda komai ya kammala,kalar alqawuran da yake zayyano mata ya sanyata sakin wani sassanyan kuka,nan ya sake lalacewa wajen lallashin kayarshi.
Sanda taga lokaci bayan ta kalli agogo batasan sanda ta wantsalo daga gado ba ta nufi bandaki tana fadin
"Su fawad" Miqewa yayi ya bita toilet din da towels dinsu.
"Ina da nufina dana daukarwa su fawad nannies,kwanan nan kuma zan qara guda daya kowacce taji da guda daya,lokaci na lokaci na ne.....banaso nayi sharing nasa da kowa" Yaso ya bata dariya,saboda yadda yayi maganar da gaske.
"Ayi musu afuwa naje na dubasu,don zuwa yanzun ya kamata ace an dubasun" Bai amsa mata ba ya turata cikin bathtub din kawai yana sake maqale mata.
Tsaf ta shirya cikin atamfa riga da zani,shigar data jima bata yita ba. Shi kansa yau din saita masa kyau sosai,ta maqala wasu sabbin design na earrings na gold marasa nauyi a kunnenta da siriryar sarqarsu saman dogon wuyanta,abinda ya sake mata kyau kenan.
Ido ya saka da baki yana kallon kyakkyawan dokin wuyanta,tunda aka fidda design din shi sai yau yaga kyansa saman wuyanta,ya tako a hankali ya sumbaci wuyanta nata,abinda ya dauke mata wuta na sakanni.
"An bani izinin sauka na dubasu?".
"An baki duniyata" Ya fada cikin kulawa da shauqin qauna.
Basa dakinsu koda ta duba,don haka saita yanke duba parlor dinsu.
"Salwa.....Allah yasa ba rigima suke miki b......" Bata samu daman qarasa fadin abinda yake bakinta ba komai ya maqale mata yadda ta zuba mata idanu itama haka ta zuba mata,cikin wani irin kallon me cike da matsanancin mamaki da gigita.
Maamah ce zaune saman wheelchair dinta,an dora mata farouq fawwaz da almustapha fawad saman cinyar tata. Yatsanta cikin nasu yatsan tana tabawa a hankali,duk da bacci sukeyi amma idanunta yana kansu gaba daya.
"Ba wata rigima hajiya......tun dazun suna hannun kakarsu,har sukayi bacci.......fauzan ne ma yaqi zama gashican an goyashi" Salwa ta bawa sabreen amsa.
Maamah ce ta fara cire idanunta akan sabreen din sannan itama sabreen din ta dauke kallonta daga kanta cikin matuqar mamaki jikinta yayi wani mahaukacin sanyi.
"Tun yaushe tazo?" Ta tambayi salwa da harshen larabci data tabbatar maamah bataji murya qasa qasa
"Mintuna kusan arbain kenan,a rubutunta tambayeni ma haka kuke barin yaran a qasa gurinmu kuna sama?" Salwa ta fadi tana murmushi. Ta fada ne saboda yadda taga maamah din tana qarewa yaran kallo,kallon dake nuna zallar qauna da shauqi da kuma kulawa. Tunda tazo idanunta yana kansu,bata kuma saukesu ba ko sau daya.
Kai sabreen ta jinjina,abun yana sake fadada mamakinta.
"A samo mata abinci da abinsha" Ta fadi tana maida hankalinta kan maamah tana takawa cike da qwarin gwiwa.
Ganin maamah a gidan nata ba abu bane me sauqi,ba wani abu