Showing 210001 words to 213000 words out of 557259 words

Chapter 71 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

396

yadda idanuwa keci gaba da binta da kallo ba,har wasu na qoqarin gaisawa da ita,a haka ta doshi qofar gidan nasu tana tsara yadda zata kaya tsakaninta da qedarun da aka tsaida a qofar gidan.

Tana takawa zuwa qofan tana jin fargabar yau dame zasu zo mata?,don dai yadda takeji a ranta yau koda sama da qasa zasu hade sai ta fita.......don ba wani mahaluqi daya taba saka mata dokar zama cikin gida har haka tsahon rayuwarta......sai yau gashi sama ta ka wani mutum can da baisan ciwonta ko darajarta ba......yanason yayi amfani da giyar kudi ya yiwa rayuwar karan tsaye.

Tana tura qofar yana riqeta kana aka qarasa budeta. Fuskar kakkauran mutumin ta bayyana har abun yana bawa sabreen mamaki. Bata taba kawowa a lokacin irin wannan zata sameshi tsaye bakin qofar ba kamar wanda aka tsaiguntawa zata fita......waisu basa zama?,ko basa hutawa da jiddin suna tsaye suna gadin duk wani motsinta.

"Good evening madam" Abdulgaffar ya furta cikin matuqar girmamawar nan da suka saba mata magana da ita saidai kuma a dabarance yana matse kowacce hanya da zata iya rabawa ta fice daga gidan.

Ta gama karantar motsinsa kaf.......bata wani damu da gaisuwarsa ba ta azawa fuskarta wani irin halakakken bacin rai da kuma d'aurewa

"Kiramin boss dinku" Ta bashi umarni nakai tsaye da wani irin sauti da babu wasa ko kadan a ciki. Tanaso ta gwada musu girman abinda zata iya aikatawa.......tanaso ta gwada musu basu ba......koda boss dinsu ma bata daukeshi da wani tarin muhimmanci ba.

"Bani da connection dashi......idan zan kirashi saina jira anyimin iso kafin na samu magana dashi......amma ga jordan zai kira miki shi" Abdulgaffar yayi mata bayanin cikin girmamawa yana matsawa da baya.

Can qasan ranta mamaki yake kamata,wanne irin girman mulki da izzar kudi gareshi da har yaransa ma ba kowa da kowa keda daman magana kai tsaye dashi ba

"Good evening madam.......kiyi haquri ki jira kadan,yanzu in sha Allah zai amsa" Jordan ya fada yana rusuna mata. A ranta tanaso ta gaya musu ne a fili

"Qattin banza.....kun zauna kuna yiwa mutum qwaya daya bauta saboda yana da dukiya" Abinda zataso gaya musu kenan ganin yadda jordan ke lalubar muhammad fuad jadda cikin girmamawa.

A lokacin yana tsaka da hada duk wasu muhimman abubuwa nashi da kanshi,ba tare da ya bari hidiminsa ya masa ba wato me sunan malam. Akwai wasu abubuwan da da kanshi yake yinsu,duk da tarin hadiman dake gareshi. Yana sanye da fara qal din t.shirt me laushi Vshape neck,hannunta iya dantsensa wanda hakan ya sanya murdaddun damtsensa dake nuna girman daga qarfe da yakeyi suka bayyana,wandon jikinsa ma farinne duka duka tsahonsa iya qaurinsa,sai lausasan fararen flip-flops masu tsananin haske da taushi.

Cikin kowanne irin yanayi tsarinsa na dabanne,kai tsaye zaka iya cewa gayu ya ratsa jikinsa da gasken gaske.....koda kuwa bacci zai shiga zaka sameshi neat....komai nashi kuma completed kai kace ba bacci zai kwanta ba. Yadda yake a nutse cikin wani irin tsari haka komai nashi yake kasancewa,waya.yake amsawa wadda ya sakata a hands free ya ajiye saman wani zagayayyen kujera me siffar qwallo dake a gefe. Kadan ya kalli wayar,sai ya fahimci kiran jordan keson shigowa amma yana buqatar izinin haka,don haka ya katse wancan kiran ya bawa kira jordan din dama

"Barka da wannan lokaci sir" Jordan yayi maganar cikin girmamawan data bata ran sabreen,ta cika fal da mamakin wanne irin ban girma ne haka kaman yana a gabansa?,ya kasa miqewa da dukka tsahonsa ya amsa wayar.

"Yauwa Jordan......ya akayi?" Ya tambayeshi kai tsaye. Sai daya dan daga idanu ya kalli sabreen din da idanunta ke cike tab da fushi,sannan qasa qasa yace

"Madam daka tura a yiwa aiki ce keson magana dakai sir"

"Madam?" Ya tambaya yanason tuna abun don ba komai yake baiwa muhimmanci ba

"Eh sir....."

"Bata wayar" Ya umarceshi kai tsaye don ya tuna inda zancan ya dosa.

"Ka matsa a wajen idan ka bata" Ya sake fadiwa jordan don bayason yayi involving yaransa cikin abinda bai shafesu ba.....hakanan yana ganin ba girmansa bane su fahimci komai ba.

Kaman ba zata karba wayar ba don tana jin kamar ta zuba a qasa data nema magana dashi......saidai kuma girma da martabar inda zataje din ya shafe komai a idanunta,don haka ta sanya nadra ta karbo wayar daga hannunsa sannan ta karba a hannun nadra din,ta taka a nutse tana dan komawa ciki duk da jordan ya matsa daga inda zai iya jinta.

A kunnenta ta kara wayar,saidai har kusan shudewar mintuna guda tim ba wanda ya cewa da dan uwansa komai.

πƒπ”ππˆπ˜π€ 𝐓𝐀 π˜“π˜ͺ𝘡𝘡𝘒𝘧π˜ͺ𝘯 𝘬𝘢π˜₯π˜ͺ 𝘯𝘦
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
𝘑𝘒𝘧𝘒𝘧𝘒𝘣π˜ͺ𝘺𝘒𝘳

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 7




Tana tsananin buqatar ta fita,ta kumayi imanin wadannan gumakan ba wanda zai musu magana suji sai wanda ya turosu.....tana jin kuma faduwar fara yin magana dashi. Sanda taji ya motsa da bisa alamun ajiye kiran zaiyi,a nutse ta bude baki ta soma magana dashi da qaramar muryar nan tata me wani irin tone

"Ban kasance daya daya daga cikin hajojin kamfaninka ba ballantana ka sanya min masu tsaro na......'yantacciyar d'iya ce kamar kowa,hakanan mutum ce dake da nata tsarin da qa'idojin da ba komai take jurewa ba......ka yiwa wadannan gumakan magana da suyi gaggawar matsawa subar qofar gidanmu". Tsayawa yayi cak da abinda yakeyi,ya harde hannayensa a qirji yana sauraronta da muryar dake nuna tamkar gargadinsa kawai takeyi kai tsaye.

Idanunsa ya lumshe kai tsaye na sakanni sannan ya budesu,yana ci gaba da jin qaramin sautinta dake magana cikin yanayi na tsiwa har sai data qarasa maganarta.

"Bakisan waye ni ba.....i can't tolerate it,dole ki koyi manners......bawai na zama dani kawai ba,manners akan komai ma,tabbas kina buqatar tarbiyya,Your attitude needs a serious adjustment.....and im not going to put up with anymore nonsense,I won't tolerate any more of your nonsense,its time to get in line" Yayi furucin harshly muryarsa cike da seriousness. Din din din da taji wayar nayi shi ya tabbatar ya yanke kiran. Ta sauke wayar daga kunnenta tana jin wani irin daci yana taso masa tun daga cikin maqogoranta har zuwa saman harshenta. Tabi wayar da kallo ranta yana mugun baci,tana jin maganganun daya gasa mata suna yawo cikin kunnuwanta.

Tana jin kamar tayi cilli da wayar ko zata samu sauqin radadin dake cisgar zuciyarta......to amma saita tuna idan tayi hakan bata kyautawa ainihin me wayar ba,wanda shima da alama komai nasa yana yine bisa tsoro da kyakkyawan bin umarni ba tare da sabawa ba.

"Kai mishi wayarsa" Tace da nadra tana miqa mata wayar,sannan ta miqe tana gyara jakarta tabi bayan nadra zuwa qofar gidan,tana jin yau saita nuna masa iyakarsa ta hanyar fita,idan yaso ya tashi duniyar a yau kowa ya huta.

Nadra ta rigata isa,ta bashi wayar dake ringing,yana duba me kiran yayi hanzarin dagawa tare da matuqar rusunawa yana fadin

"Hello sir" Idanunshi suna sauka kan sabreen,sai ya miqe yana sauraron umarni daga wayar yana kuma kallon sabreen wadda ke tafiya cikin tsananin fushi,har kuma ta samu nasarar sanya qafafunta a qofar gidan.

"......idan naga sabanin haka ka kuka da kanka" Qarshen maganarsa kenan data jawo hankalinsa zuwa ga sabreen wadda ta dauki hanyar barin layin sosai bata tsaya koda waiwayarsa ba ballantana wayarsa da yakeyi,tana jin bata da lokacinsu gaba dayansu.

Da sassarfa abdulgafar ya jefa wayar a aljihunsa ya juya da sassarfa yabi bayanta. Daga yadda yau boss din ya masa magana ya tabbatar akwai magana a qasa. He's speaking seriously,yasan abinda ya fada da gaske yake.

"Madam.....ah.....am,madam sorry......listen please" Ya furta bayan ya cimma bayanta. Nuna ma tasan yana biye da ita a wajenta bata lokaci ne,bata da lokacin batawa ta saurareshi daga shi har boss din nasa

"Madam please ki tsaya ki saurareni,am going to loose my job.....please listen to me". Maganar ya taba mata zuciya........yanzun nar rashin imaninsa yakai ace ya kori mutum bakin aikinsa saboda wani abu daban ya faru?. Daga yadda yake maganan kawai ya gaya mata da gaske yake fadi,don haka tadan sassauta tafiyar ba tare data kalleshi ba tace

"Ina jinka"

"Please madam ki koma gida.....kiyi haquri ba yadda muka iya.....haka boss ya tsara......"

"Wannan kuma bazai yiwu ba,idan baka da abun fada ka koma yafi maka sauqi" Daga hakan taci gaba da tafiyanta. A nutse take ratsa layin,yayin da idanun 'yan sanya ido ya soma yin caa a kanta. Ba yadda zaka kalleta ita da abdulgaffar din kace ba body guard dinta bane,saboda yake take mata baya yana maida takunsa duk inda ta dauke ba tare da sunsan abinda ya sanya ya biyota ba,take tsegungumi suka fara tashi,masu rade radi akan irin mijin da zata aura a yau suka samu tabbacin hakan

Da alama zazzafa ce itama tamkar boss din nasu,ya hanga ya hango babu wani sauran abinda ya rage masa illa ya kira oga farouq,don haka yana biye da itan yayi kiransa,yayi kuma bayani a taqaice.

"Turawa hood location ta watsapp...zaizo da mota ya kaita.....idan yazo din give me a call.....zanyi magana da ita" Yayi maganar haushin fu'ad yana kamashi.

A ganinsa tunda batu ake na aure koma meye ya kamata ya ajiyeshi a gefe,batun aure ya wuce wasa.....ya kuma wuce tunanin mutum.

Wani irin aiki ne da ake yinsa da umarni da kuma doka. Iya tsaiwar da tayi tana jiran ababen hawan da batasan dalilin da yasa duk wanda ta tsaida sai ya wuce ba.....wanda qwarewar aiki irin na abdulgaffar ya sanya yake musu alama me nuna gargadi kan tsaiwar tasu,take suke wucewa abinsu.

A hankali motar ta rage gudu tana qarasowa gabansu,wanda tun kafin takai ga qarasowar abdulgaffar ya ganeta. Motocin da dukka suka jibanci familyn muhammad jadda da kuma gidan alhj hamza kibiya ba boyayyu bane,don hatta da plate number dinsu na dabanne da wani irin kebantaccen tsari na daban.

Bai bari motar ta qaraso gabansu ba ya kirayi farouq din,sai komai yazo a daidai,isowar motar gabansu da kuma matsawa da yayi daura da ita ya saka wayar a handfree yadda idanunta zasu iya ganin wayar

"Ranki ya dade......Allah ya taimakeki,tuba muke,kunyi magana da boss yana cikin fushi ne.......ayi mana alfarma kiyi haquri,ga driver da mota nan ya iso,ki shiga ya kaiki duk inda kikeso,tuba muke,tuba muke" Ya maimaita har sau biyu yana hade tafukan hannayensa guri daya.

Batasan me ysaa ba,amma sai taji tasss ta sauka daga fushin da takeji. Yanayin maganarsu dama komai nasu ba daya bane,batasan kuma waye ba......sannan batasan nasabarsa dashi ba.....amma da iya lafuzan bakinsa kadai ta tabbatarwa kanta yasha banban dashi tako ina.

Batace komai ba ta soma takawa tana nufar motar da tuntuni suka wagale mata qofar suna tsaye suna jiran isowarta,tadan dubi security din kadan ta kauda kai tana tabe baki. Su kuma a haka rayuwarsu zata qare?,basa da aiki sai ta'ammali da murda murdan garadan da babu rahama akan fuskarsu?,idan kuma suna tsaye sai kace gumaka?,wacce irin rayuwa zata shiga ne?. Da wannan tambayar ta shiga cikin motar suka maida murfin suka rufe.

Duk da yadda ranta yake a bade,zuciyar kuma bata tare da komai amma hakan bai hanata fahimtar banbancin inda ta shigo ba. A hankali ta kalli wani sashe na motar,cikin ranta tana jin zallar tsagwaron banbanci. Batayi kuskure ba idan tace tsahon rayuwarta bata taba tsammanin da gaske akwai mota irin wannan a nigeriar mu ba,cikin motar bai mata kama da komai ba saida wani qawataccen madaidaicin falo na alfarma,idan ba yaye labulen window din kayi ba zata ko dan jirin motsin motar kadan ba saika tsammaci cikin wani killataccen falon kake. Taja numfashi a boye tana saukeshi,duk da ita kadaice a nan amma saita killace ganinta. Bangare daya zuciyarta tana bugawa da samun tabbacin lallai da gasken da kawun ke fada su din ba qananun mutane bane......amma ta yaya suke bibiyan rayuwarta?,me yasa sai ita?,me suke tunanin tana dashi wanda zata iya basu?. Amsar dai kamar kowane lokaci.....hasashen kaman na kowanne lokaci shine AKWAI WANI ABU A QASA.

Da wani irin makirin narkakken murmushi ta maida murfin qawataccen akwatin ta rufe bayan ta gama ganin suturar alfarmar da aka tsumata da wasu tsatsube tsatsube na musamman da suke a mazaunin matakin farko na fara tunkarar shirin data yiwa rayuwar mutum biyun.......sanadin wato sabreen.....da kuma maqasudin wato muhammad fu'ad.

"Komai yayi hajja........suturar million biyu kam baa kashe kudinsu a banza ba.......yanzu zuwaira za'a aika?.....inajin kamar nayi tattaki naje nakai Mata da kaina,don inaso ta fahimci muhimmancin sanya suturar nan" Tayi zancan da wani irin muhimmanci cikin sautinta,tana tuna bayanan bokan da bata dana biyunsa a yanzu haka

_".......tana sata a jikinta ta fara zuwa hannu fa hajja......hakanan shi Kansa fu'ad kallon farko da zaiyi mata da suturar zai jarabtu da sonta,abinda zai bada damar gudanar da aikinmu cikin sauqi,zai karbi komai daga hannunta yaci ya kuma sha ba tare da wani matsala ko tangarda ba"_

Murmushi hajja ta saki tana dora qafarta daya saman daya

"Tafiyar zuwaira ita daya yana nuna aiken bame daraja bane,hakanan zuwanki da kanki zai jefa shakku a idanun mutanen da hankulansu ke kanmu irin aminatu hamza kibiya......wannan saqon babbar aminiya kuma amintacciya ya kamata ta isar dashi" Murmushi me sauti ya qwacewa maamah,ta bawa hajja hannu suka tafa tana fadin

"Allah yabar mutum da nasa.......bari na yiwa usama magana" Ta fadi tana dauko wayarta dake ajiye gefe ta fara lalubar number wayar usaman.

Zuwanta wajen aysha da dawowarta....farincikin data samu na ganin yarinyar ta dawo cikin cikakken hayyacinta da wata lafiya data sanya kumatunta cikowa shine ya haifar da sakewar fuskarta,ya kuma saka mata farincikin da ta kusa mantawa da abinda ke tunkararta a gobe.

Kallon masu kallo da idanun masu sanya idanu tun daga qofar gidansu da lafiyayyar motar ta ajiyeta bai dadata da qasa ba,har zuwa sanda ta isa tsakar gidan,ta kama matakala tana haurawa zuwa saman nasu.

Tana sanya qafarta sukayi kacibus da momma dauke da tray da lemuka da ruwa akai.

"Yauwa yanzu nake shirin kiranki......kina da baqi suna qasa,ki hanzarta ki samesu" Ta gaya mata tana rabata zata wuce

"Baqu momma?,su waye?,daga ina kuma?"

"Kinga duka wadannan tambayoyin ki adanasu idan kinje kyayi musu.....me lalle ma ke take jira tunda kika fita". Ambaton sunan me lalle saiya fara dagula mata lisssafi,bayan dirje fatar da aka dameta dashi na kwanaki kusan goma yanzu kuma wani me lalle ne na daban zata zauna yi?,salon a bata mata hannu da qafar da bata shirya diga musu komai ba?.

Ganin momma tayi gaba har tana gangarawa qasan stairs din ya sakata itama ta laqume dukka tambayoyinta tana wucewa ciki. Zuciyarta fal da saqe saqe ta sauya abayar jikinta zuwa wata sassauqar doguwar Riga cotton me gajeran hannu data zauna daidai jikinta,ta dauki qaramin hijab daya tsaya mata iya kafadu ta maqala ta juyo tana saukowa.

Dukkansu su biyun suka amsa mata sallamar idanunsu a kanta

"Tubarkalla ma sha Allah" Zuwaira da tayo rakiya ta qarfi da yaji don ba haka Hajja taso ba ta furta kyan sabreen yana bugar da ita. Duk yadda take jin hira da yadda aka tsara komai bata taba kawowa kyan yarinyar yakai haka ba,ta dauka maamah din nada tsananin wayo......zata dauko yarinyar da bata da cikakken siffa gudun juyewar reshe da mujiya. A iya sanin data yiwa halittar 'ya'ya maza masu jarabtuwa da kyakkyawar mace komai kamewarsu kuwa. Sanda suka iso gidan batayi tunanin gidan masu matsakaicin qarfi da gata irin wannan yana qunshe da kyakkyawar sura har haka ba,taci gaba da qare mata kallo yadda shape me qirar Coca-Cola ya fita sosai ta cikin rigar ta wajen qugunta.

Duk kallon da zuwaira ke qare mata hankalinta baikai ba,saboda hankalinta daya tafi akan hajja da suka fara hada idanu. Ta yaya zata manta fuskar matar?,bayan tana a wajen sanda sukazo da tallar qazamtacciyar hajarsu?,kuma kusan itace tafinta a wajen matar dake iqirarin mahaifiya take a wajensa.

Yadda sabreen din ta tsareta da idanu tana zama a dosane a hannun kujera irin yadda takeyi idan zuwan mutum magana ko mu'amala dashi baiyi mata ba

"Sannu ko?" Hajja ta fada tana qaqaro murmushin dole. Wani irin kishi me girma ya sauko mata akan Sabreen din. A haduwarsu da suka taba yi qwaya biyu hankalinta bai taba kaiwa kan sassanyan kyan da yarinyar ke dashi ba. Wani irin halakakken kyau dake boye a kowanne sashe da kuma halittarta. Anya wannan ba kuskure bane?,idan har tayi saken daya fadawa sonta rabasu kuwa zai zama abu me sauqi kuwa?.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login