Showing 117001 words to 120000 words out of 557259 words
da bazata hada numfashi da ita ba,to amma kuma babu hanyar,saidai tabi zabi guda daya daya rage mata,ta koma ta zauna ta jirata har ta gama zancan tabar wajen. Wannan abunne kuma takejin ba zata iya ba,duk abinda ta niyyaci ko nufaci yi ba kasafai take bari dalilin wani ko wata ya sanyata ta juya da baya ba.
Tunda ta doso gurin ta fuskanci hankalinsa ya dauku a kanta. Ba baqon abu bane a wajenta saurin gane motsi ko manufar d'a namiji a kanta daga kallo daya tak. Dauke hankalinta da idanunta tayi daga wajen kamar bata san da zamansu ba tana wucewa ciki.
"Wannan 'yar gidanku ce itama kenan?" Ya maida hankalinsa ga hadiyya yana tambayarta wadda tuntuni idanunta suna a kanshi,cikin wani irin banzan kallo da bacin ran yadda yake kallon sabreen din
"Eh 'yar nan dince.....sai akayi yaya kuma?" Ta bashi amsa a matuqar fusace har sabreen dake gab da wucewa tana ita jiyota.
Kanta ta girgiza kawai tana sakin siririn murmushin nan nata maras sauti me dauke da tarin ma'anoni masu yawa. Itakam daga hadiyya har dukkan wani gajan baqo da zayazo wajenta bata tunanin akwai wanda ya isheta kallo a cikinsu.
"Ina kuma hudan?" Sabreen ta tambaya tana kallon sararin da tabar hudan a zaune kafin fitarta
"Ta shiga daki" Haneefa ta bata amsa. Labulen daya sakaya qofar shiga dakin tabi da kallo
"Daki kuma?,me takeyi a ciki?"
"Ban sani ba wallahi.....naga dai ta shige" Nadra da aka miqawa tambayar ta amsawa sabreen cikin rashin taqamaimen amsa
"Tun yaushe ta shiga din?" Ta sake tambayar nadra wannan karon qasa qasa.
"Baki jima da fita ba" Ta bata amsa itama da yanayin yadda tayi mata tambayar. Bata son saka ko darsa wani abu a ransu,don haka tadan sake rantabrana kallon nadra
"Rufe littafin data bari a bude din" Batayi gaggawar shiga dakin ba don kada ta barwa zuciyar yaran wani hasashe,saita koma ta bude fridge ta dauko ruwa,ta qarasa gaban first aid box dinsu dake ajiye cikin falon t dauki paracetamol ta taka zuwa dakin.
Daidai sanda ta shaqi wani sassanyan numfashi daya cika fal da farinciki da kuma shauqin soyyayya,daidai lokacin ta daga labulen dakin tana takowa zuwa ciki.
Mutuwar kwance tayi sanda idanunta suka ga shigowarta,sai ta kasa ci gaba da maganar da taso ci gaba da yi. Tana iya jinsa yana cewa
"Hellooo.....my love.....hello" Amma ta kasa kowanne motsi. Duk sautin maganarsa qwaya daya ji takeyi kamar zata saki fitsari,don tana ganin yadda sabreen din ke matsowa tsaf zata iya jin sautinsa.
"Me kikeyi a kwance bayan sallar magariba?.....kuma na barku ne kuna karatu?" Ta mata tambayar tana kafeta da idanu,gami da zama saman drawer dake tsakanin gadajen nasu. Shuru yayi daga inda yake zaune yana bin sakannin da suka kwashe da ita akan waya suna qara gudu,yana kuma sauraren sautin muryar sabreen dake ratsowa ta cikin wayar zuwa kunnuwansa tare da sake tuna masa abubuwa masu yawa da suka shude tsakaninshi da ita.
Numfashi taja ta sauke,lokaci daya yadda zata sauya daga ainihin yanayinta yazo mata,saita bata fuska
"Banajin dadi ne". Inda hankalinta cikin jikinta yake a lokacin ba shakka babu abinda zai hanata jiyo sautin fitar murmushinsa.
Ko iya hakan yana gwada masa samuwar matakin nasara daga gareshi. Ta yadda ya bibiyi diddigin rayuwarsu.....a yadda bincike ya fito masa.....basa iya boye mata komai.....komai girman laifinsu ko gaskiyarsu.....komai tsanani ko maslaharsu.....ba wani abu da suke iya lullube mata shi,yau gashi ya fara taka matakin nasara......ta koya qarya saboda shi.
"Me yake damunki haka nan da nan?" Cikin qwarewa wajen iya bankado abinda ke lullube ta tambayeta. Tambayar data sanyashi jingina bayansa da kujera yana jiran jin amsa ta biyu
"Kaina ne yake ciwo" Sai ya tsinci muryar sabreen din tana bada amsar da hudan ce ya kamata aji haka daga bakinta.
Yadda ta bada amsar ya sanya huda daukewar numfashi daga jikinta na wucin gadi,tare da sanya Naseer tattara hankalinsa akan wayar,kadan kadan fargabar kada ya zamana ta gano meke lullube tana son saukar masa.
"Ga magani tashi kisha" Ta sake cewa da huda tana miqa mata kofin ruwan dake hannunta tare da satches na maganin.
Ruwan da maganin duka tabi da kallo,ta fara motsawa kadan sannan ta miqe da sauri ta zauna tana sakin wayar. Santsin pillow din ya sanya ta zame ta kuma sulale ta sauka a gefen cinyarta saita matsa kadan tana qarasa danneta.
Ci gaba tayi da dubanta har zuwa sanda ta balla maganin tasha,sai ta miqa hannu ta karbi rayuwar ruwan da maganin itama ta balla ta sanya a bakinta tabi da ruwa
"Ba abu mafi sauqin fade irin ciwon kai.....amma ki sani,yawan kiran sunansa yana iya jawoshi koda babu shi a wajen" Ta fadi tana qarasa sauke idonta a kanta.
Tsoro da fargaba ya sake cikata,saita lumshe idonta tana son dasa gaskiyarta a zuciyarta
"Nima zamana kenan na jishi ya saukar min,na dauka nadan lokaci ne xai sauka idan na kwanta"
"Allah ya sawwaqe" Ta fada a taqaice tana takawa a hankali hadi da ficewa daga dakin.
Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fidda idanunta waje,tana iya jin yadda bugun zuciyarta ke kai kawo wanda ta tabbata tsoro razani da kuma firgici ne ya haifar mata dasu.
*****Tsakanin asabar da kuma lahadin yana da isashe lokacin da zaiyi shirin komawa bakin ayyukansa zuwa litinin,wannan ya sanyashi maido da dukan ayyukansa da suka tsaya sakamakon tafiyar da yayi.
Shi kansa yasan satin da zasu shiga din ba satin zama bane,babu hutu sam a tattare dashi. Aikine me yawan gaske,don bayajin zai zauna ya huta har sai yakai ga gacin kammala komai ya kuma bude kamfanin da a yanzu shine cikar burinsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 63
Sassanyan yammaci ne dake bada wata irin iska me dadin shaqa da samar da nutsuwa ga zukata,hakan ya sanya zaman wajen yayi masa dadi ,wanda tun bayan sallar azahar ya zauna a nan din. Yau din zama sukayi sosai da mu'allim,wanda shi yake kula da bangaren masu buqata ta musamman da kuma neman taimako. Ya karba list na mutane masu yawa,ciki harda list din anni dana maamah wanda ya jima yana kallonshi.
Sunaye na mutane barkatai,wanda yafi kyautata zaton an shirya sunan ne kawai an kuma shigar. Ya karba takardar da zummar zai duba din,don hatta da numbers na wayoyinsu dake a jiki kallo daya yayi musu yaji sunfi masa kama da lambobin bogi.
A yanzun ya gama shigar da komai cikin laptop dinsa da kusan zaiyi wahala ka ganshi ba ita. Tana dauke da muhimman bayanansa da kuma sirrika sosai a ciki.
A yanzu da yake zaune yana karbar kira ta kai tsaye ta cikin system dinsa. Video call ne da daya daga cikin kamfanin narka gold da wankeshi daga qasar china,farouq ya tako yana isowa farfajiyar.
Kujera yaja ya zauna,sannan ya fidda wayarsa yana duba saqonnin WhatsApp da tun daxun ya sauka da zummar zai koma din. Hira sosai suka shiga yi da fannah,don kusan duka saboda ita din ya hau. Jifa jifa yana mata gajeran voice note don kada ya janye hankalin fu'ad da baqonshi.
A nutse ya kammala amsa kiran,yayi disconnecting sannan ya maida dubansa ga farouq. Idanu yadan zuba masa,yana mamakin yadda yakejin dadin soyayya gaba daya,wai shin mene a cikinta har haka da take iya maida mutum wawa ne?.
"Ya dai?" Yaji muryar farouq din yana katse masa tunaninsa
"Am just wondering...."
"For what?" Farouq ya katse masa magana yana maida masa tambaya murmushi dan kadan yana fita a fuskarsa
"Yadda mutum me hankali yake komawa kaman soko.......wannan abar farouq It doesn't make sense wallahi" Ya fadi iya gaskiyarshi,gaskiyar da har saman fuskarsa zaka hangeta kwance quru quru.
Dariya ce sosai ta qwacewa farouq har yana duqawa,abinda ya sanya fu'ad tsaiwa ya zuba masa ido yana kallonsa.
"To abun kuma ya fara cin qarfina,to be sincere ka fara bani tsoro sama dana baya.......nafi tunanin kuma yanxun bawai aljana bace ta aureka ba,tunda koda aljana ce saida soyayya ai ko?"
"Kai ka sani qaton banza" Fu'ad din ya fada yana jifansa da wata harara data sake sanyawa farouq ya fashe da dariya,don irin wannan hararar kawai yake iyayi masa idan ya quleshi ya kaishi bango.
Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi don kada ya jawowa kansa jagwal ko yaqi bashi hadin kai akan batun da yazo masa dashi,ya sani sarai kadanne daga aikinsa ya murje idanunsa,musamman yanzun da har ya shiga gonarsa ya kuma tsokaneshi.
"Mu ajjiye wannan batun.....ina nan dai inayi maka addu'a.......na saka a duba mana ticket zuwa abuja Saturday in sha Allah......already ma nayi payment zai mana printing ne kawai"
"Bazanje ba" Ya bashi amsa kai tsaye yana qoqarin shutting down system dinsa idanunsa saman screen din.
Fuska farouq din ya narke yana koma masa kalar tausayi
"Sai na tafi ni kadai.....amma kuma idan ta tambayeka,zan bata labarin ka saba Alqawarin da mukayi da kai ne" Yakai qarshe yana zuba ma side na fuskarshi idanu.
Shuru yayi kawai bai sake cewa komai ba,wanda alamu ke nunawa farouq zaiyi wahala yace bazaije din ba. Sau tari shuru a wajensa alamu ne na accepting abubuwa,idan baya so kai tsaye zaice baiso kuma bazaiyi ba kaman yadda yanzu ya fada mishi da farki,yana sane kuma ya sanyo zancan cika alqawarin......don ya sani shi din mutum ne da ba abinda ya tsana irin qarya sam sam,idan kanaso kaga tunzurarsa ko fadansa to kayi masa qarya.
"Ya ake ciki maganar ginin?" Farouq ya sanyo masa maganar da yasan yanzun itace a gabansa sama da ko wacce. Sai kuwa ya qarasa kashe system din ya rufeta yana dora fararen idanunsa akan farouq din.
"Ending month dinnan nake sanya ran gini zai kammala,sai preparation kawai na budewa wanda shima banaso ya wuce watanni biyu.....duka engines da sauran kaya next week zasu iso in sha Allah" . Kai farouq yake jinjinawa,yana matuqar yabawa da hazaqa da qoqari irin na fu'ad din.
Tun farko yasan idan don ta shine bazai iya ba......don haka ma ya saki wannan ragamar kawai ya miqawa fu'ad din,don tunda shi ya faro barota shine zai iya. Qaramin murmushi farouq din ya saki,fu'ad ya dage masa gira alamun tambaya
"Ba komai.......kawai na tuna temple run dinka ne......rigimammen dan bautar qasar da yaje garin wasu ya musu barna.....ya kuma gudo da abinda suke ta buri da nacin samu......Allah inda a zamanin yaqe yaqe ne zakayi barna da yawa fa" Maganar dole ta sanya murmushi kubcewa daga fuskar fu'ad,ya zauna sosai yana sake duban farouq
"Mazantaka a zuciya take farouq......sannan dukkan namiji muddin zai amsa wannan sunan dole kalmar TSORO ta fita daga dabi'arsa......bai halatta ba sam sam namiji ya zama me tsoro ba..... Idan hakan kuwa ta kasance a matsayinsa na shugaba kuma jagora,dole al'amura su lalace..... Adinga ganinsu kuma ba'a yadda suke ba".
Duk da tsananin gajiyar dake a jikinta bayan dawowarsu daga wajen boka DURGUJI amma hakan bai sanyata zama ta huta ba bare akai ga batun kwanciya. Kai kawo kawai takeyi tsakanin kitchen da dakunanta cikin sabgar dafawa da saukewa. Wani tsari da takeson fara qirqiro dashi a yau din,don shine hanya guda daya da zata samu ayyukan da aka tsara mata su tafi yadda takeso.
Ta bata lokaci sosai tana son tuna wanne abinci da wanne abinci sukafiso ta dafa musu lokacin quruciyarsu?. Da qyar ta dinga tuna wasi abubuwan da suma shafesu saboda yadda ruhi da zuciya suka jima da yin nisa daga rayuwarsu dama komai daya shafesu.
Tayi lissafin abubuwa guda hudu duk da tasan sunfi hakan,saidai sauran ta barwa ranta zata nemi ganin ma'aikatansa da yake yawan rayuwa dasu don samun wasu amsoshin. Anni ce tasan wadda zata samu amsar kai tsaye daga gareta,saidai zuwa yanzun tana jin cewa tafi qarfin anni ballantana ta sake neman wani abu daga wajenta akan 'ya'yan da ita tayi cikinsu ta kuma haife abinta. Alwashi taci......tana nan kuma riqe dashi......hakanan ba zata runtsa ba ba kuma zata huta ba har sai ta samu cikar wannan alwashin nata.
Tana aikin masu aikinta suna mamakin shigarta kitchen yau da kanta. Duk kallon da suke binta dashi bata samu nasarar tantancewa ko kuma kula ba,saboda hankalinta yayi matuqar nisa akan maganganun da suka tattauna da durguji.
_"sau daya nakewa mutum aiki na gama dashi.....muddin kuma nayi aiki baici ba yana da wahala na sake na biyu indai ba sa'a ka taka ba......aikinki me hatsarin gaske ne......duk abinda kikaji ko kika gani kada ki wuce wata guda kacal baki dawomin ba"_
Ita batun sake aiki da rashin sakewar duka ba damuwarta bane,tunda ta riga data sani kudi suke juya akalar kowa su kuma sauya tunaninsa. Muddin zata zube masa kudi ta tabbatar duk taurin kansa sai ya sake waiwayarta. Kawai abinda yake damunta a yanzu shine yadda zata samu dawowar hankulansu a kanta,ta yadda cinsu da shansu zai dawo qarqashinta,wanda wannan shine abu guda daya tal da zai sanya aikinta ya tafi yadda ya dace.
Tana kammala white rice sai ta kasa haquri ta fita a kitchen din. Dakin gadonta ta wuce ta samu saman sofa bed ta zauna tana latsa wayarta. Number fu'ad din ta fara kira,daidai sanda yake zaune suka ci gaba da tattaunawa da farouq yana nuna masa tsarin taswirar ginin kamfanin.
Fararen idanunsa ya daga yana azawa saman wayar. Zubawa wayar idanu yayi yana kallon yadda sunan ke wucewa ta saman screen din. A duk sanda zaiga shigowar kiranta sai yaji wani abu tun daga qasan ransa har tafin qafafunsa. Inda yana da iko bazai daga wayar ba sam sam,to amma wata fuskar tafi gaban mari
"Ina zuwa" Yace da farouq yana daukan wayar ya daga ya saka a kunnensa.
Cikakkiyar sallama tayi da kwantacciyar murya da zai iya cewa ya manta rabon da yajita daga bakinta,wani abu guda daya sake jan hankalinsa,saidai bai hanashi amsa sallamartata ba hadi da dorawa da fadin
"Barka da yamma" Dan murmushi ta saki kadan
"Yauwa barka kadai Muhammadu" Ta fada cikin nuna kulawa
"Ka wuni lafiya kai da dan uwanka?,tunda har yanzu ban cancanci a kullum naga lafiyarku ba......hasalima kamar kuna mantawa ne da rayuwata" Yadda tayi maganar ya taba ransa kadan,yaji sautin da amon da ya jima baiji daga gareta ba
"Kiyi haquri ba haka bane" Ya maida amsa wani abu yana kai kawo a ranshi
"To idan ba haka bane yaya ne Muhammadu?,kamanhar yanzu kun kasa manta abinda ya faru ne kawai" Idanunsa ya lumshe kawai yana saurarenta. Zuciyarsa nadan qara bugun da takeyi yana jin wani abu sosai can qasan ransa da kuma wani sashe na zuciyarsa
"Idan zaku iyayimin alfarma,inaso ana gama sallar ishai ku shigo kai da musaddiq....inason ganinku duka ku biyun"
"In sha Allah" Ya amsa mata kai tsaye. Wayar na a kunnensa har ta yanke Kiran,sai shima ya zame wayar daga kunnensa yana kallon screen din.
Sanda ya daga idanunsa sai suka hada ido da farouq,murmushi farouq din ya sakar masa kawai. Har yanzu bai taba saka baki ko shiga lamarinsa da maamah ba,infact ma shi bai taba masa magana a kanta ba,ko yaushe shida sadiq suna qoqarin kiyaye iyakokinsu ne.
Wani irin murmushi ta saki bayan ta ajiye wayar idanunta akan qofa tana jin wani farinciki yana shigarta. Nasara ce a kusa take shanshanarta......kuma jikinta yana bata komai yana kusa da qofarta.
Plan dinta guda uku ne qwarara,ta fara da wannan na farkon,idan yayi aiki shikenan,idan baiyi ba zata wuce plan B,idan shima yayi aiki shikenan,idan kuma shima baiyi ba tana da plan C......wanda shine tsororuwar shiri mafi tsauri da tauri.....plan din data tabbatar zai yamutsa hazo iya yamutsawa........ita kuma zata saki dukkan wata iyaka da ikon da Allah ya bata don ganin tabbatuwar plan din da kuma wanzar dashi.
Ranta fes,Zuciyarta wasai ta ajiye wayar ta koma kitchen tana shirye shirye shirye gadan gadan.
Haka kawai yakejin yanayinsa wani iri,jikinsa da zuciyarsa dukka ba'a sake suke ba,a haka ya shirya cikin