Showing 372001 words to 375000 words out of 557259 words

Chapter 125 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

414

qoqarin riqewa....bai hanata ba amma kuma ya soma zare duk wani qarfi da take dashi saboda dumin numfashinsa da yake sakarwa sasannin wuyanta zuwa cikin kunnenta,take kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa harda muryarta.

"Ka bari don Allah" Ta fada cikin rawar murya,sai ya dakata cak yana hautsinota ta dawo suna fuskantar juna. Da rinannun idanunsa da suka fara canza kala yace mata

"Ke kinsan girman Allahn ne?" Yafada yana dage mata girarsa duka biyun. Samun kanta tayi da kasa kallonshi,saita kauda fuskarta gefe. Hannu yasa ya dawo da fuskartata daidai saitin tasa yana dubanta.

"Uhnnn.....nace kinsan girmansa?.....kinsan aure dukansa sunansa aure a wajen Allah?,kina matar aure amma baki iya kula da mijinki ba?.....baki iya komai bafa.....idan nace komai ina nufin komai irin na mata....matan ma matan aure........kinaso na mutu ne sabreen?" Mamakinsa ya kamata,ya gama rungume rungumensa sannan yanzu ya mata wata magana ta daban?.

"Bakya kishina ne?"

"Sonka nake da zanyi kishinka?" Ta fada a tsiwace tana murguda bakinta.

Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu kusan lokaci guda,siririn murmushi ya kubce masa yana kallon baby face dinta da danjaririn bakinta data murguda masa. Ba abu me dadi ta gaya masa ba,don maganar ta sokeshi a tsakiyar zuicyarsa,saidai kuma ta masa wani mugun kyau,kuma yaji ta bakinta ko ba yawa a wannan fannin.

Sake jawota yayi ya matseta da kyau kaman zai rabata gida biyu,ya sanya yatsarsa guda daya ya fara zagaye labbanta sai tayi sauri zata turasu ciki,ya shammaceta ya hada mata da yatsan nasa,dole ta saki labban nata,abinda ya bashi daman riqo fuskarta da kyau ya kuma hade labban nasu waje daya.

Wani irin sarrafasu yakeyi a tausashe da nuna zallar qauna,abinda bata zata ba daga gareshi. Ta dauka anytime kiss abune me zafi ga labba,cikin minti biyu taji kowacce gaba a jikinta tana saki,kafin kwanyarta ta ankarar da ita suna kitchen sakamakon qarar qofar kitchen din. Tureshi tayi da sauri,ta saka bayan hannunta tana goge labban nata. Da fushi a muryarta tace.

"Banason wannan abun.....wannan ai qazanta ce" Tayi maganar ne da harara,harara data fidda farare sol din idanunta. Kamar dafi haka yaji ta zuba masa jikinsa dukka ya amsa,ya shammaceta ya jawota ya sake matseta yana same hade bakunansu,ya tattara miyau din bakinsa duka ya dure mata. Bai barta ba sai daya tabbatar ta hadiye sannan ya sake boyeta a qirjinsa sanda ta saki siririn kuka.

"Am so sorry.....inason mu sake zama abu daya ne bayan wanda muka sake zama din.....amma tunda na miki ba daidai ba.....biyani yawu na" Ya fada yana qoqarin sake kai bakinsa cikin nata. Ta gama fuskantar wayo ne kawai yake son ya mata,don haka ta fara qoqarin hanashi amma bai bata dama ba,haka ya dinga zuqe duk wani yawu dake bakinta sai da numfashinsa ya fara fita daban daban daga qirjinsa sannan ya sake ta yana maida numfashi.

"Duk abinda na miki idan bakiso zaki fara biyana daga yau......ki karbi wayarki a hannun amna" Yana kaiwa nan ya juya yana barin kitchen din saboda jin yana neman loosing control dinsa. Ya riga yayi alqawarima ransa indai ba takura yayi maqurar iyaka da zai iya shiga halaka ba.....bazai sake karbar komai ta qarfi ba....zaiyi iya yinsa ya amintar da ita.

Idanunshi a rufe suke,sam bai kula da farouq dake zaune a parlor din ba sai da yaji muryarsa yana cewa

"Ranka ya dade sir" Yana dunqule hannunsa irin na girmamawa. Kallo daya ya masa ya fahimci zai wahala bai shiga kitchen da zummar dauko wani abun ba idanunsa sunyi masa gamo,don haka baima tsaya biye ta tasa ba ya wuce daki abinsa yana jin dariyar farouq din. Saidai qasan ransa yasha alwashin tasu ce shi da farouq din,yaga alaman bazai taba barinsa ya sake ba.....baya jin zasu qare zamansu a Maldives a wannan gidan....musamman da maamah ke dab da isowa,yana jin gidan tabbas ya musu kadan ,don haka ba wanda ya sani bayan ya sakarwa kanshi ruwa ya fito,ya yiwa Jordan maganar duba musu wani apartment din a siya zuwa nan da jibi yalwatacce sosai da yafi wannan.

Sulalewa tayi a nan tana dafe da kanta,da qyar ta iya saita kanta ta miqe tana gyara yamutsatsen hijabinta da tuni ya saukeshi daga kanta. Can qasan ranta tana mamaki,wanne irin tsafta ne dashi haka?,duk sanda yayi kusa da ita irin haka qamshin mint leaves ne ke fita a bakinsa,wanda da alama ya kama bakin nasa sosai,wanne irin freshener na baka yake amfani dashi haka?. Tsaki taja qasan ranta tana ture wannan tunanin daga ranta,ta matsa gaban sink ta ringa watsawa fuskarta ruwa don kada ta koma anni ko amna wani ya gane wani abu,sai data tabbatar taji daidai sannan ta dauki gorar ruwa daya ta fita a kitchen din. Farouq din yasan tabbas zata fito,bayaso kuma taji kunya ko nauyinsa,don haka sai ya wuce dakinsu bayan shigewar fu'ad,wannan ya bata daman shigewa dakinsu salin alin.

Qin yarda tayi ta hada ido da kowa kota zauna,sai tayi shigewarta duvet kawai tana qundundunewa waje daya. Amna tana toilet,batasan kuma ta shigowa ba sai data fito. Cikin hanzari ta qaraso dakin tana cewa.

"Albishirinki adda?" Daga can qasan maqoshinta ta amsa da

"Goro". Tana bin amna da kallo wadda ta dosota da kwalayen waya guda biyu ta zauna gefanta.

Duka biyun ta zaresu daga kwalinsu,bakinta ya kasa rufuwa.

"Ya Allah kaban miji irin hammana.....you're luckiest woman adda....." Idanu sabreen tadan fidda

"Bakwa kunyar anni amna?,yanzun da tana dakin haka zaki ce?" Dariya ta qyalqyale dashi.

"Ki zabi daya.....idan nice ma duka zance inaso......falcon supernova.....the most expensive phone in the world.....it's worth more than 77mil in naira......irinta hamma na ke using,ita kuma wannan itace ta biyun ta a tsada" Amna ta fada tana juya duka wayoyin tana duban sabreen.

Adadin kudaden kawai sai da suka sanya kanta yayi tsawa,million saba'in da bakwai?,ina zata kai irin wannan wayar?,wacece ita?,waye ubanta a Nigeria?,idam shi ya riqe matsayinsa yakai ne.....arziqinsa yakai....amma kuma ita fa?,ita da take dorin dosano?,kwanaki nawa ya rage mata ra barshi ma kwata kwata?.

Numfashi taja ta lumshe idanunta tana kullesu,ba zata iya gayawa amna kai tsaye bata so ba.....ba zata kuma karba ba,don haka tace.

"Ki ajiyesu,zan duba gobe"

"Done.....amma please ki dauki irinta hammana please adda"

"Naji" Tace da amna don kawai ta bata wuri ta shaqata.

_nikuwa nace ya kamata sabreen ki karbi wayar nan don ki gigita surukarki hajiya maamah da ita,kin bata tabbacin mallakar fu'ad da taketa fafutuka taki ce kenan_πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Tana sane ta narke tun daga daren ranar har wani daren,tayi qaryar zazzabi don kada anni tace taje suyi sallama da fu'ad da zai tashi zuwa macca kai tsaye gobe da safe. Ta samu nasara kuwa.....don har ya shigo ya musu sallama tana kwance tana baccin qarya.....duk da cikin jikinta tana jin idanunsa a kanta suna yawo,ya juya ya fice su anni suna taka masa.


_Turqashi......maamah bisa hanya_

_komai fa yana shirin faruwa me karatu_

_idan nace komai.ina nufin komai maπŸ˜‚_

_pages din gobe masu zafi ne,kada ka yarda su wuceka_

_Ya zata kaya tsakanin maamah da sabreen ga anni a tsakiyarsu?_

_yaya zata kaya sanda maamah ta fahimci zazzafar soyayyar sabreen a idanun susutaccen d'anta?_

_shin zata iya dauka?,ko zata cika qudurinta na rabasu?_


_Shikenan fareeda ta haqura?,ko zata sake wani motsin?_

_waye da waye ne suka shiga hannu?_

_ita kanta fareedan ta sha ko kuwa?_

_akwai ragowar zafafan al'amura fa masu karatu,muje zuwa ga gangarar labarin_🧏🏽




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 89




89



Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana dan dafe goshinsa,duk wani energy nasa yaji yana tafiya,ta yaya zai iya tafiya wani qasar ba tare da sunyi sallama da ita ba?. Ya sani ya kuma fahimci tana sane duk tayi hakan,wayarma daya batan baiga alamun ko guda daya a hannunta ba. Iska ya sake furzarwa yana jin tsoron kada dai furucinta na rannan ya zama gaske da tace bata sonshi. Sai ya zura hannunsa a aljihunsa ya fito da wayarsa ya fara kiran number amna.

Ita da anni ce kawai a dakin,annin ita ta karbi wayar saita miqa mata tana cewa.

"Hammanku ne......basu tafi ba kenan" Ba zata iya musu da annin ba bata kuma fita ba bayan ta bata wayar bare ta aje wayar yadda ta saba masa. Ta latsa ta sanyata a kunnenta,ta motsa labbanta a hankali tana amsa yin sallama.

Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar sautin sallamartata. Yayi jarumtar daidaita yanayinsa don bayaso ta fahimci komai,don yana son komai zai gaya mata ta daukeshi da muhimmanci.

"Ina kika shiga?" Ya mata tambayar a gajarce data rasa amsar da zata bashi. Shuru tayi tana kame kamen abinda zata gaya masa,bata samu ba har ya sake cewa.

"Kinsan tafiya zanyi yau really?" Can qasan zuciyarta tayi qaramin tsuka tana cewa

"To mene ruwana da tafiyarka?,ka wuce mana ta can ma karka dawo Maldives,amma a fili sai ta zabi jan bakinta tayi shuru.

"Alright......yayi kyau....ina wayar dana bawa amna ta baki?,baki dinne bata yi ba?". Ya sake tambaya da wani irin shan qamshi da bata taba ji ya mata ba,hakan sai ya mata kwarjini gami da taba zuciyarta.

"Ta bani" Ta amsa masa a hankali kaman wadda batason tayi magana. Amsan ta bashi haushi kadan,don shi daya yasan yadda ya matsu da jin muryarta amma taja wayar ta ajiye.

"Bakiga daman amfani dashi ba kenan?.....well....bazan miki komai ba a yanzun.....amma kika sake har na dawo na samu wayar a yadda na baki ita.....sai nayi punishing naki ta hanyar da bame iya karbanki......and idan ma kin bude kin fara using da ita....if kika ce zakimin abinda kikemin a wayar anni da amna bawai kin tsira bane.....take care of your self......byee" Ya fada yana sauke wayar. Sai a sannan yaji zuciyarsa ta koma daidai,duk da ba irin wannan sallamar yaso suyi ba,amma at least ya samu nutsuwa kadan. Bayaso ya fiya zafafa mata da yawa....don baida tabbaci ko yaqinin zuciyarta ta karbeshi,saidai ko meye yana da yaqinin bazai qyelata haka ba,sai yayi mata dashe da kuma ginin da bazai kankaru ba.

Wayar tabi da kallo kafin ta ajiyeta a gefanta. Sau tari idan yana wani abun sai zuciyarta ta dinga gaya mata plan ne kawai da siyasa irin ta 'yan kasuwa,kamar kawai yanaso yaci gaba da mata wayo yana amfana da jikinta ne. Har yanzu ta gaza gasgata kanta wai mutum kamar muhammad fu'ad da mutunci ko arziqi ba shine silar gamuwarsu ba ace dare daya don kawai ya amshi budurcinta ya koma haka ba. Kulawa qauna soyayya da wani irin mayataccen yanayi da bata taba ji ko gani ba. A duk mazan da sukayi alaqa dasu a baya bata taba ganin wani abu na musamman kebantacce tattare dasu irin wannan ba. Da gaske wannan shine son?,da gaske wannan din ake kira da soyayya ko kuwa yaudara ce zallarta?.

_to masu karatu ku bata amsa_


β˜… *_Makka/Jeddah_*


Tafiyar awa biyar zuwa shida ta kaisu garin jedda,a nan ya tsaya yayi wanka ya saka hirami ya dauki niyyar umararsa. Daga nan kuma lafiyayyen train ya daukesu kai tsaye zuwa makka.....motar da aka tanadar masa ta qarasa dashi masauki cikin hotels mafi tsada dake dab da harami.

Fairmont makkah clock Royal tower nan ya zaba,ko maamah dinma yasa an maidata can,hotel ne dake da kusanci sosai da haram,kai tsaye daga dakinka kana iya hango ka'aba. Baida gurin sauka duk zuwan da zaiyi sai nan din,saboda samun kusanci da Allah da samun daman yin addu'o'insa sosai koda cikin dare ya farka. Sau tari yakan jima gaban window din dakinsa yana qarewa dakin Allah kallo,cike da shauqi da tsoron azabarsa da kuma fatan samun rahamarsa,yana jin inama yayi zamansa a nan ya qare rayuwarsa.

Nutsuwarsa da samun salamar ruhinsa daban yake jinsu a ransa duk lokacin daya shigo wajen,yana jin kansa sosai kusa da Allah,don haka koda ya iso wucewa yayi kai tsaye yayi dawafi da sa'ayi yayi sallarsa raka'a biyu ya sauke umararsa. Bai nema ganin maamah ba sai daya sauke faralin umran da bayajin zata isheshi. Zuwa yanzu baisan sau adadin nawa yayita ba.....bayajin kuma zai daina yin nata muddin da numfashi a jikinsa da kuma damar zuwan.

Dakinsa ya koma royal suit ya sallami abdulbasit da abdul gaffar da abdus sabur wanda su ya sanya suzo su zauna tare dashi. Hiraminsa ya cire ya nema wasu kayan ya sanya yana duba lokaci. Akwai gajiya sosai tattare dashi,yana buqatar ya hutawa kwanyarsa sosai don ya samu space din yadda zai iya tunkarar ko meye maamah zata zo masa dashi. Labulen dakinsa ya daga,idanunsa suka sauka akan dakin Allah,wajen tarwai yake da cikakken haske kamar kullum,da tarin bayin Allah masu neman duniya dama lahirar gaba daya. Bayason wani babban abu ya faru tsakaninsa da maamah a irin wannan wajen,dole yana buqatar neman taimakon Allah.

Nannuyar ajiyar zuciya ya sauke sanda fuskarta ta dawo masa tarwai cikin idanunsa. Idanunsa akan ka'aba din,ya sanya hannunsa saman qirjinsa ya dafe yana jin yadda qirjin nasa ya cika da soyayyarta,a hankali ya furta.

"Ya raheem......kada ka bawa mahaifiyata galaba a kaina muddin da sabonka da kuma son zuciya tazo". Sai ya dakata yana jan numfashinsa sosai.


"Ya ubangiji.....kaine mahaliccin zukata.... Kaine ke iya jujjuyasu a duk sanda kakeso,ya rabb,kafin kowa sanin menene abinda ke zuciyata na ainihi a kanta,ban aikata mata komai ba don na zalunceta ko na cuceta ba,ban aikata mata komai saboda qiyayya ko abisa sanina ba....ya rahman....ka sanya mata matsananciyar soyayyata a zuciyarta,ka sanya ta soni irin son da nagartacciyar uwa kewa d'anta......irin son da bashi da misali.....irin soyayyar da na jima ina fata da burin samu daga wajen macen aurena.....ya ubangiji,na gode maka abisa kowacce ni'ima da kayi a gareni.....na yadda cewa mahaifiyata itace jarrabawar rayuwata......na rasa soyayyarta soyayya ta ainihin da aka santa daga zuciyar uwa zuwa 'ya'yanta.....ya Allah yadda kayimin madadi da anni.....na roqeka kayimin madadi da ameenatu sabreen.....ka maidata sanyin idaniyata......Allah ka azurtani da salihan yara ta tsatsonta.....ka sanya albarka cikin kowacce tarayya da zanyi da ita....Allah ka wankemin idanuna da samun qarin 'yan uwa nagartattu bayan su musaddiq,wato yaran da ameenatu zata haifamin" Ya qarasa addu'ar labbansa suna sanyi,zuciyarsa tana jin wani irin sassauci da sauqi,a take kuma sai kewarta ta cikashi. Baisan me ya sanya dukkanin burinsa a yanzu ya fara karkatawa kan samun 'ya'ya ba......abune daya jima a ranshi,amma halin maamah da yadda ta watsar da rayuwarsu ya kashe wannan burin. Yana ganin duk macen da zai dauko ma haka zata kasance akan 'ya'yansa kaman yadda maamah tayi musu ta kuma yiwa abbansu.

Sakin labulen yayi a hankali,yana ji a jikinsa tamkar dukkanin addu'o'insa sun amsu,sai ya koma ya zauna bakin gadonsa yana daukan wayarsa.

Maamah din yaso kira don ya shaida mata ya iso,amma cikin rashin sa'a sai ya kasa samunta. Hakan ya masa dadi,don ko ba komai zai samu ya matse gajiyar daya debo,don haka ya aje mata tex kawai,sai ya tsinci kansa da neman layin wayar sabreen din.

Bai taba zaton zai samu wayar a bude ba,bai dauka zataji warning dinsa ba,amma ga mamakinsa dab da zata tsinke aka daga. Lumshe idanunsa yayi yana jin qarin wani sassaucin da rangwamen yana sauka a zuciyarsa,ya koma da baya ya kwanta akan gadon bayansa bayan ya sanya pillow qasan kansa.

Shuru kawai tayi tana sauraren iskar dake fita ta wayar.

"Baki iya sallama ba?.....me yasa kullum kike maida kanki yarinya sosai?" Ya tambayeta a tausashe yana jin ba dadi baqin halayenta. Ta maida kanta wata sokuwa a gabansa,ba dogon magana sam.....musu ko tsiwarma sai taga dama takeyi masa su.

"Assalamu alaikum" Ta samu kanta da masa sallamar. Qasan ranta a tsorace take da maganansa kadan kadan. Tanaso su rabu ba tare daya sake taba jikinta ko ya kasance da ita ba......amma ta duba ta dubo ba wani hanya daya rage illa ta bishi ta yadda ya bullo mata,ba tare daya ankara ba zai wayi gari babu ita.

Wani sauti na daban yakeji yana shiga kunnensa tamkar yau ya fara jin amsuwar sallama.

"Amincin Allah kema ya tabbata a gareki DUNIYATA.......gani kusa da dakin Allah.....me kike buqatar na roqa miki?". Ya fada da wani kwantacce kuma sassanyan sauti da shauqi da kewa suka cikashi.

Har cikin jikinta taji maganarsa ta mata dadi,tana da tarin buqatun da zata roqa a wajen Allah idan har qaddarar zuwa wajen ta tabbata a kanta. A yanzu dukka ta qosa subar Maldives,tana jin nauyin tambayar amna wanne guri zasu je next.....amma a nata zabin a ture dukka kowacce qasa a barta a tsakanin saudiyya zuwa madeena. Tana tsaka da wannan lissafinne taji muryarsa yana cewa.

"Na roqo ubangiji yasa ki soni....irin matsanancin son da ba zaki iya rayuwa ba tare dani ba.......na roqi Allah ya sanya ki zama madawwamiyar ni'ima a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login