Showing 51001 words to 54000 words out of 557259 words

Chapter 18 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

550

Bai sake ce masa komai ba sai ya miqe yana zaro wayarsa dake aljihun wandonsa. Iphone 16 sabuwar qira wanda babban hoton wata kyakkyawar matashiya ya mamaye ilahirin fuskar wayar. Kyakkyawar bafulatana me wani sassanyan kyau,cikin kamilalliyar shiga data qarawa hoton da Fuskarta kwarjini. Dududu shekarunta da suka nuna cikin idanunta da kuma fuskarta goma sha takwas ne.....sha takwas din da aka soma gangarawa cikin sha tara.

Kalmomin sirri ya sanya ya bude wayar,sannan kai tsaye ya tafi zuwa ajiyayyun lambobin da basu da yawa cikin wayar. Akan wata number dake dauke da sunan ABBA NA ya tsaya,ya danna kira sannan ya maidata aljihunsa yana gyara zaman Bluetooth guda daya dake manne a kunnensa yana bada hasken qyallin wuta time to time. Sai kuma ya fara takawa a hankali ba tare daya cewa musaddiq komai ba,wannan ya bawa musaddiq din daman biyo bayansa a nutse can qasan ransa yana murnar yadda aka haqura da jogging dinnan haka.

"Shi ya dauka kowa kamarshi ne me jikin qarfe da baya gajiya da motsa jiki......idan na hada qarfi ina zan kaishi" Yayi gulmarsa a ransa yana biye dashi tare da qare ma bayansa kallo.

Shi kansa yadda yake da ginannun muscles yana burgeshi yana kuma bashi sha'awa,amma bashi da juriya da qarfin halin da zai building muscles ma jikinsa kamar nashi.

"Abba ka farka?" Ya fada cikin matuqar nuna kulawa bayan yayi masa sallama.

"Okay gamu nan qarasowa" Sai ya katse kiran ta jikin Bluetooth din nasa sannna ya dan soma sassarfa yana cewa musaddiq

"Oya.... Mu qarasa gida" Kaman zaiyi kuka hakanan ya taka ya soma bin bayansa. Kafin su qarasa gidan sai da yaji kaman zai zube,cikin ransa yake ganin gaskiyar sadiq ashe da yakanyi ciwo ko ya qirqiro uzurin qarya duk sanda ya tasheshi ya rakashi jogging. Har gwara ku shiga gym room dashi,wannan idan suka faki idonshi sai su zabi machine daya su haye su kasheshi ko su rage gudunsa sosai.

A hankali suka qarasa hongdae geori cikij estate din dake unguwar. Gida me lamba ashirin,yayi tsaye yana danna bell yayin da qirjinsa ke dagawa sama da qasa yana fidda Zazzafan huci daga bakinsa. Ya jiqe sharkaf da gumi,musaddiq kuwa tuni ya zube saman step biyu dake bakin qofar gidan yana numfashi da sauri da sauri.

A hankali qofar ta bude,dattijon mutumin nan Alhaji hamza kibiya ya bayyana cikin wata lallausa kuma kyakkyawar abayar qasar morocco ruwan zuma. Ba abinda ya sauya tattare dashi sai shekaru da suka fara bayyana kansu a jikinsa.....bayyana ba me muni ba saboda daular rayuwa da kuma jin dadin da yake ciki daya zarta ya kuma ninka na shekarun baya ta hannun zaratan yaransa guda hudu dukka maza.

Da murmushi a fuskarsa kamar kullum yake kallonsa

"Ina dayan me babban suna?" Alhaji hamza ya tambaya saboda idanunshi basu hango musaddiq ba sam sam.

Da baki ya yiwa abba cunensa,abban ya dora hannu saman baki yana bushewa da dariya

"Kai......taso dalla.....dama babu me maganinku ai sai me babban suna......tashi nace mace kawai.....koni nan da shekaru suka fara turamin ina gudun nan,kuma ka gani da idanunka.....ina zakuyi qwarin damu uwayenku mukayi?,baku da aiki sai hawa mota sai ciye ciye da shaye shayen banza" Abban ya fada yana wurga hannu. Kai ya daga da qyar yana duban abban

"Abba wallahi.....bazan iya tashi ba da gaske,qafafuna kamar zasu tsinke.....gudun fanfalaqi yau hamma ya saka mukayi" Yadda yace gudun fanfalaqin ya tilastawa abba sakin dariya,yayin da FU'AD ya girgiza kai kawai. Suna ganin iskanci a gidan wajen sadiq da musaddiq,kullum kaman basa girma,kullum kallon kansu sukeyi kaman qananun yara.

"Tunda ba zaka tashi ba ai idan wancan qadangare ya shige maka riga ai ka nema hanyar gida" Wani mugun tsalle ya doka sai gashi a tsaye kyam

"Yauwa.....dan nema ja'iri,zo ka wuce kaji me babban suna" Abban ya fadi yana komawa ciki fuad yabi bayansa yana dariya qasan ranshi. Har yanzun musaddiq yana tsoron qadangare kenan tun yarinta?,abun ya dinga bashi mamaki don shi baiga wani abun tsoro a qadangare ba.

Suna shiga yana biyo bayansu yana dube dube yana fadin

"Wallahi abba ka kusa sakani na saki fitsari a wando......yanzu inda a gaban nasreen......" Tsaf ya kame bakinsa ba tare daya qarasa ba saboda kallon da FU'AD ya jefeshi dashi,ya sosa kanshi ya sauya akalarsa zuwa kitchen da kake iya hangensa tarwai ta falon.

Saman kujera ya zauna a nutse yana warware takalman qafarsa,abban ma ya koma inda ya tashi ya zauna yana daukar mug tare da ci gaba da kurbar zazzafan tea din dake ciki.

"Sannu da gida abba" Ya sake fada yana dan jingina bayansa da kujera

"Sannu fuad shugaban 'yan motsa jiki" Abban ya amsa masa da murmushi tare da maida dubansa ga takalmansa daya cire. Duk abinda ya cire ko yayi amfani ddashi yasan ya killace shi,zaiyi wuya kaga ya watsar da kaya ko wani abu makamancin hakan. Ya tabbatar hakan baya rasa nasaba da matsananciyar tsaftarsa da kuma yadda rayuwarsa ta ginu a shekarun baya,cikin gwagwarmaya da daukar nauyi da lalurar kanshi. Yana da bala'in tsantsami shi yasa abubuwa da yawa ya gwammaci ya tsaya ya yiwa kansa. Idan ka ganshi a kitchen yana hada breakfast ko yana dafa tea zaka rantse da Allah ba shine dan marayan zakin nan ba mamallakin kamfanin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ba,wanda jaridu zuwa mujallu kullum kwanan duniya ke zumudi da rububin yin rubutu a kansa ba domin samun daukakarsu da qaruwarsu. Duk wani rubutu ko labari da wani gidan tv jarida ko radio zasu fitar akan MUHAMMAD FU'AD tamkar daukaka ce a tare dasu. Matashin mamallakin kamfanin haqar ma'adanai na diamond ne da makamantansu. Kifi daya a ruwa da manyan masu sarrafa gwalagwalai da diamond na duniya suke saka fatsarsu domin kamo kaya daga kamfaninsa saboda inganci da kyansu. Diamond guda daya daya taba tsinta a sanda yake tsakiyar bautar qasa can cikin jahar kogin nigeria.


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 30


Dan bautar qasar da bai wuce sati biyu a camp ba.....wanda ya fita yawon ganin gari shida shaqiqin aboki amini kuma dan uwansa farouq hamza kibiya. Haka kawai yayi sha'awar bin daya daga cikin matasan da farouq ya saba dasu a teburin me shayi wanda duk dare sai yaja fu'ad koda kuwa bayaso,suje su zauna su sha hira suga yanayin gari da mu'amalar mutanensu. Da fari fu'ad baya so,daga bisani ne ya sake a hankali bayan da yayi tunanin wannan karin maganar ta bahaushe

"Tafiya mabudin ilimi". Ba yadda zaiyi ya samu ilimin muddin yana nade a camp da kuma dakin. Abinda yafi damunsa yake hanashi fitar yadda 'yammatan camp din nasu harma da cikin garin suke da son wasa da wargi gami da son shigewa mutum. Shi kuma abu guda da yafi tsana kenan kaf fadin rayuwarsa. MACE halitta guda daya da ba kasafai yake mata uzuri ba a rayuwa.....halittar da yayi amanna ya kuma saddaqarwa kansa su da KUDI tamkar rai ne da bugun numfashi. Halittar da ya gama karatunta cewa tafi bawa KUDI muhimmanci sama da komai.....kwadayyar halitta me son kanta.....mara tausayi kuma mara imani koda akan dan cikinta ne kamar dai MAAMANSA.

Farouq yaso hanashi binsu inda suke haqar a sirrance saboda sanin tsananin risk din dake wajen. Bawai iya barazanar fadowar rami bisa kan me haqa ba.....a'ah.....hatta na a tsakaninsu suna iya farde wanda ya tsinta din suyi kashe mu raba da abinda ka samu.

"Farouq......ragon namiji shike tsoro.....faduwar gaba asarar namiji......ba'a haliccemu don mu kwanta ko mu zauna iyayenmu su dinga bamu suna mana wahala ba.....an halicci Muhammad fu'ad don yayi gwagwarmaya ya kuma fuskanci challenges a rayuwarsa.......na fara gwagwarmaya tun daga sanda na fara fahimtar Muhammadu sunana ne......na fahimci kuma MAAMA itace ta haifeni......" Ya qarasa maganar wani abu yana tsirgawa daga tsakiyar muryarsa har cikin qwayoyin idanunsa

"Wai anni bata hanaka zancan maama dinnan ta haka ba?" Farouq yace da fu'ad a sanyaye. Wani malalacin murmushi ya saki ya sunkuya yana ci gaba da daura boot din qafarsa da kyau. Ta yaya MAAMA zata bar zuciyarsa wai?,ta yaya?har abada sai randa qasa ta cike idanunsa.

"Na shirya zan wuce sai na dawo" Ya fada yana miqewa tare da zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban farouq. Harara ya watsa masa sannan ya miqe da hanzari

"Ina zan barka ka tafi kaje ka bace ka jamin jarfa a wajen abba......qafata qafarka.....idan ma zamu bata mu bata tare" Yayi maganar yana miqewa.

Miskilin murmushinnan nasa ya saki ya juya yana kada kai. Ya sani shine dai kawai a gaba kafin abba da yake qorafi akai,kawaidai bazai iya barinsa ya tafi bane ya barshi,wanda wannan daya daga cikin danqon qauna da 'yanuwantaka dake a Tsakaninsu.

Yana shiryawa yana mita har ya kammala suka sulale suka fice daga gidan da aka musu masauki ba tare da kowa ya sani ba.

"Ni bansan me zakayi da wata mahaqa ba.....dukkanmu abba jira yake mu kammala wannan service din ya bude mana namu kasuwancin"

"Ta yaya zaka zama cikakken dan kasuwar da yasan daraja da kimar dukiya baka iya gwagwarmaya ba?.kana daga zaune ba tare da ka tara komai ba?" Fu'ad ya masa tambayar yana kallon hanya kawai ha tare daya kalli farouq din ba

"Gwagwarmaya cikin wadannan qedarun?,don kawai Samuel ya gaya maka za'a je da kai?,suna da hadari fa fu'ad?" Murmushi ya kuma saki hankali kwance,har yanzu kuma bai kalli farouq din ba ya sake bashi amsa

"Muhammad fu'ad dan arewa.....ya fisu hatsari.....zaka gane hakan idan sukayi yunqurin yin wani abu". Maganarsa ta tabbata kuwa a wajen farouq.

Tun isarsu gurin komai ya fara bayyana. Da wani irin kallo ayarin suka fara binsu saboda ganinsu baqin fuska kuma 'YAN AREWA dake yara yaran hausa. A haka aka soma tafiyar har zuwa kebantaccen wajen da suke haqar ba dare ba rana don samo ma'adanai. Samuel shi ya dauki dukkan wani risky ya shige gaba aka barsu har suka isa gurin cikin wadanda aka aminta da shigarsu wajen.

Duk inda fu'ad zai motsa farouq yana biye dashi,sam wajen shi baiyi masa ba,hakanan a tsorace yake da wajen,shi sai ya zamana kamar me gadin fu'ad ne a wajen. Duk wani motsi da za'a yi a wajen ko wani da zai tunkarosu hankalinsa yana wajen.

A hankali ya tura kansa ramin da fu'ad ke ciki wanda yayi zurfi

"Mutanen nan fa hankalinsu a kanmu yake,duk wani motsinmu suna ankare dashi"

"Karka damu" Kawai yace dashi saboda wani abu daya fara hanga wanda ya dauki hankalinsa matuqa.

"Farouq" Fu'ad ya kirayeshi da wani sauti me jan hankali wanda yaja hankalin wanda ke ramin daura dasu ya kumayi tsai yana jiran jin dalilin kiran.

Tura kansa farouq din yayi yana cewa

"Menene"

"Na samo.....na samo" Ya fada da wani irin excitement,yayin da zuciyarsa da kwanyarsa suka cika da mamakin samun abinda bai taba zaton zai samu ba koda kuwa a mafarki. Har a qasan zuciyarsa ya gwada zuwa wajen ne kawai don samun experience da karantar yanayin yadda irin rayuwar yake.

"Duba ka gani farouq" Ya fada yana miqo masa. Farouq din da hanzari ya dira ciki yana toshe bakin fu'ad

"Keep quit fu'ad.....ka tono masifa" Ya fadi a tsorace. Da wani kallon mamaki yabi farouq din

"Kaman ya?"

"Kamar yadda ka sani.....kowa dake nan wajen abinda yake zuwa nema kenan kwana da kwanaki.....kana baqo wanda aka yiwa alfarma.....zuwan farko kayi kacibus da abinda yake dukkansu shine burinsu?. Akwai shugaba a cikinsu wanda duk wanda ya samo sai yabi qarqashin umarnin shugaba......zai kuma danqashi a hannunsa....." Tsaki fu'ad yaja saboda dokokin rainin wayo da yaji farouq yana karanto masa wanda shi baisan dasu bama,don ya fishi zama da hira da Samuel

"Su sukamin wahalar?,ko an gaya maka nazo nan dinne don na yiwa wani qaton zindiqin arne aiki?.....let's go mu wuce gida" Ya fada yana kama ramin tare da nufar hanyar fitowa.

Sanda yayi tsalle ya qarasa fitowa baima lura da wadanda suka kewaye ramin ba,har sai daya gama karkade jikinsa yaji sadiq daya fito daga bayansa ya zungureshi.

Lafta laftan yare masu mummunar siffa tun daga halitta zuwa zuciya. Mutumin da alamu suka nuna shine shugaban yana tsaye a gaba. Ya sake matsowa gaba kadan ya miqawa fu'ad hannu..

Sarai ya fahimci abinda yake nufi,amma yadda yake kallonsu da dukkan wani motsi nasa cikin izza da nuna isa ya sanyashi jin har cikin ransa bazai taba iya bashi abun ba. Ballantana abinda yake wahalarsa kuma guminsa ne. Ko daya babu me haqqi a ciki bare yayi tunanin cinyewar zai zama laifi har a wajen Allah.

"Ban gane ba" Fuad din ya furta cikin dakiya da jarumta

"Ka miqo diamond din daka samu aka ce...!" Daya daga cikin wadanda ke daura da ogan ya furta murya a kausashe yana sake matsowa dab da fuad din saboda nuna masa tsananin buqatar abun da suke da,da kuma nauyi da girman abinda yake dauke dashin.

Cikin qasa da second biyar ya gama fahimtar motsi da niyyar kowa. Tabbas!.....tabbas babu abinda yafi dacewa dasu muddin yana da buqatar tsira da wanann abun face tserewa

"Ka shirya farouq.......ka shirya gudun tsira da rai.....ko mu ko su,ka qarfafa zuciyarka da gangar jikinka" Ya furtawa farouq qasa qasa tare da damqe hannunsa da kyau.

Kaduwa sosai farouq yayi da abinda yaji fu'ad din yana fada.....yasan halinsa muddin ya fadi sai ya cika.....amma kuma abinda zasu aikata din mugun ganganci ne da zai iya zama ajalinsu.

Bai gama sauke wannan tunanin ba yaji qarar wani abu timmmm sannan yaji an finciki hannunsa. Sanda zai duba sai ya samu fuad dinne ya kaiwa ogan nasu mummunan naushi har sai da yakai ga zubewa qasa war was,da wannan ya janye hankalinsu suka tsallakesu,saidai ko taku uku basuyi ba aka samu wadanda suka rufa musu baya bayan fusatacciyar tsawar da ogan nasu ya buga musu wadda har yanzu yana zaune a qasa

"Catch them!!" Ya fada qarajin hasaso asarar dake tallafe dashi tare da tsoro da razanin rasa abinda yake tamkar shine cikamakin burin rayuwarsa.

Wani irin gudu tamkar a indian film fu'ad ya dinga yi,abun har yaso yafi qarfin farouq banda shi dinma yaci sunan me sunan.

"Mu tsaya fu'ad.....harbi sukeso su fara"

"Wa ya gaya maka ana gudu da waiwaye?......just run!!,run kawai.... Kada ka sake waiwayawa". Ganin kamar farouq din ya fara karaya ya sanyashi yin wani juyi ya maida farouq din gaba shi yana biye dashi.

Da gaske dai suka fahimci zaratan samarin 'yan arewan guda biyu na niyyar kufce musu,sai kawai suka fara harbi,harbin da ya gigita farouq qwarai da gaske ya kuma dinga kiran sunan fu'ad akan su maida musu abinsu.

"Basu isa ba....don ba abinsu bane,arziqi ne na ubangiji daya shimfida a qarqashin qasa saboda bayinsa,ba don su kadai Allah ya ajjiyeshi ba" Ya fada a zafafe cikin yanayin gudun yana sake fusgar hannun farouq da kyau. Wani irin samfurin gudu da fu'ad din keyi riqe da hannun farouq sai daya zama abun kallo a wajen farouq din. Bai taba tsammatar iyawa ko qwarewa haka a tare dashi ba wajen sanin kurdawa tsakanin manyan dutsuna da qananunsu ba sai a sannan. Bayan shafe dogon lokaci suna fafatawa Allah ya basu nasarar kufce musu

"Park zamu wuce mu kwana a can daga can muyi gida......ba park na kusa da nan ba,ta gaba da nan" Fu'ad ya fadi yana kallon farouq

"Ya zamu bar camp kuma bamu dauki komai namu ba......sannan kuma......"

"Kana tunanin sun qyalemu ne?,kana zaton idan muka koma can din zasu barmu mu kwana da ranmu?" Fu'ad ya tambayi farouq wanda da alama baisan girman ta'addanci irin nasu ba.

*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login