Showing 162001 words to 165000 words out of 557259 words
a hankali har ta isa qofar dakin nasu da tayi tsammanin samunshi a bude saboda lokacin lokaci ne da tasan suna makaranta a irinsa.
Da mamaki hadi da wata cakudaddiyar fargaba ta murxa qofar ta tura ta bude tana shigewa,saita samu kanta da takawa a hankali har zuwa qarshen falon.
Ba kowa,kuma wajen yana tsaftace kaman kullum,don haka ta juya tana sanya kanta cikin dakin tana mamakin waye yake magana haka kaman masu gulma?.
"Nayi maka alqawarin xuwa ka ganni muddin ba'a wata qasa kake ba.....zanzo har inda kake don ka tabbatar da ingancin son da nake maka!". Qididdigaggun jimlolin da suka zamewa sabreen tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta.
Wuta ce gaba daya taji ta dauke mata sanda take iya hasken waya a kunne huda.
"Anya huda ce?,meye hakan yake shirin faruwa?,d waye take magana haka?.
"Waya" Taji an rada mata cikin kunnuwanta,abinda ya sanyata xabura ta kuma sanya hannu ta yaye blanket din da hudan ke ciki,take ta bayyana kwance maqale da waya tana ta doka murmushin samun abinda zuciya takeso.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 87
Bayyanar haske cikin duhun blanket din ya sanya huda zabura,haduwar idanunta kuma dana sabreen ya sakata miqewa cikin matuqar kaduwa da zabura har wayar na neman subucewa,saidai kuma kafin yakai qasa sabreen din ta sanya hannu da zummar tarota,abinda ya bawa huda qaimi itama takai nata hannun don bawa wayar kariya.
Sabreen din ta rigata samun nasara,batayi wata wata ba ta sanya wayar a kunnenta,lokacin da Naseer keta faman maimaita kalmar
"Hello......hello baby?" Wani abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafafunta. Wannan muryar ba baquwa bace a wajenta da zata iya bacewa daga kwanyarta.......ba muryar naseer ba......maza da dama da suka taba shiga qaddarar rayuwarta,suka kuma ratsa ta DUNIYARTA bata wasa da komai daya shafesu bare ta bari ya bace mata
"Nnn......" Tayi niyyar furtawa,sai kuwa ta dunqule maganar ta hadiye ta maidata cikinta,ta sauke wayar tana katse kiran sannan ta maida dubanta ga huda dake tsaye tana fuskantarta idanunta fes kan fuskar sabreen.
"Ki bani wayata adda" Ta tattaro dukka qwarin gwiwar daya rage mata ta furta tana miqawa sabreen hannu. Saidai maimakon ta bata wayar yadda ta buqata sai ta maye gurbin hakan da ajiye mata lafiyayyen mari saman fuskarta,sanda take yunqurin maido hayyacinta cike da matsanancin mamaki ta sake sauke mata wani marin a daya kuncin nata. Gigicewa tayi duka ta sanya hannayenta ta dafe kuncin nata gaba daya,wannan baiwa sabreen din ba cikin matsanancin fushi ta turata ta koma saman gadon tayi zaman dabaro sannan ta bita tayi tsaye a kanta tana damqe hannunta a cikin matuqar dimuwa da gigita.
"Kinsan waye wannan?,kinsan waye kike tare dashi huda?....kinsan hadarin da kike shirin jefa rayuwarki dama mu gaba daya?,kinsan waye Naseer?!" Taqarasa fada idanunta a waje sosai suna nuna girma da yawan bala'in data tarko musu.
Gaba daya ido ta zubawa sabreen din tana mamakin maganganunta
"Wayeshi din?" Hudan ta fada zuciyarta a tsaurare.
"Ba sunanshi naseer ba,sunanshi bassam". Ta sake fada tana ji a ranta ya kamata itama tayi tsaiwar daka har sabreen din ta fuskanci nata zabin.
"Basma......bassam.....innalillahi" Sabreen ta furta duka a tare tana komawa qasan dakin gaban hudan ta zauna jabar.
"Tun yaushe kuke tare?,kun taba haduwa?,shine ya baki waya?,dame dame yake gaya miki?,tun yaushe kike waya dashi?!" Tayi maganar wani irin zafi yana taso mata daga qasan zuciyarta. Iya kallon da huda ke mata.....iya abinda take gani daga idanun hudan kawai sun isa bata amsar zuciyarta ta fara soyewa.
"Dake nake magana huda!" Ta furta da wata gigitacciyar tsawa data ratsa hudan ainun ta cakude da radadin marin da baibar fuskarta ba har yanzu.
"Ki barni yaa sabreen.....ki barmin zabina......bassam ya cancanta,shi nakeso kuma yayimin alqawarin bani kulawa kaman yadda iyaye ke bawa 'ya'yansu......banyi wani abu da ba daidai ba fa,kema kin tsara rayuwarki ne daidai yadda kikeso......kina kuma abinda kk ga dama a sanda kikeso.....ni ko nadra ko haneefa akwai wanda ya taba tsaidaki ko ya hanaki?,ni mene ma nayi?,abinda ban taba wuce layin bayan gidanmu ba?,ban taba zuwa hotel ko joint joint ba.....ba'a taba ganina da wani d'a namiji a cikin mota mun kebe b.......".
Sake saukar wani lafiyayyen marin da yafi na dazu shi ya daukewa huda dukkan wata kalma da zata ci gaba da fita a bakinta. Marin da wannan karon ya jawo digar jini daga hancin hudan,muryar sabreen din kuma dake shaking tace
"Huda?.....kinyi hauka ne?,eh idan ma haukar kikayi kisan wadanne kalamai zaki gayamin.......nice sabreen da na baki tazarar shekara kusan biyar cikin rayuwarki.....nice sabreen da na sadaukar da walwalata farincikina da martabata saboda kuji dadi!....nice sabreen dana hana muku kuka......nice sabreen dana hana muku jin yunwa da wulaqanta.....nice sabreen dana zame muku garkuwa......nice sabreen dana maye muku gurbin uwa da uba wanda kece ta farko daya cancanci ta zama shaida akan hakan......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu na shaawa ko burgewa a jikinki da d'a namiji zai gani ya burgeshi......na zame miki garkuwa a sanda baki da wani abu da zaki amfana mini face zallar qauna da 'yan uwantaka fa fisabilillahi......wanne sauran kulawa kike buqata da ban baki ba?,wacce sauran qauna ce da tafi wannan girma da fadi?......soyayya huda?.....kin san wanne abune da yafi tarwatsa rayuwar diya mace?,kinsan wanne abu ne yafi zama girman nadama cikin rayuwar 'ya mace?,kinsan mene ne mabudin nadama......wahala da azabtuwa da zuwa da qaddarar da bata sauyuwa cikin rayuwar mace?......ba komai bana face SOYAYYA kuskure na gaba da rayuwar kaso casa'in dake afkawa shine AURE......namiji!.....bashi da imani......bashi kuma da tausayi.....namiji BUTULU ne dake iya bijirewa halasci komai girmansa.......namiji halittar data fi kowacce halitta son kanta cikin duniya.....halittar da babu imani cikin ruhinta ta fannin azabtar da ruhin diya mace.......samun salamar rayuwaki ki rayu ke daya.....baki saka kanki cikin sabga ko sha'anin kowanne d'a namiji ba......wannan wani karatu ne da rayuwa tayimin bayan gushewar abba da ummina.....mutum na farko da ya fara qoqarin bata rayuwata shine ALHAJI LAWAN......" Da wani irin kallo huda ta dubi sabreen,saidai ta kasa furta komai
"Eh....alhj lawan maqoci kuma aboki ga mahaifinmu,......tun daga wannan rana na fara karatun waye namiji?,daki bayan daki kinsan komai kafin na fara sakaya wasu al'amuran daga idanunki saboda samun damar saituwar tunaninku.....huda!......dago kanki ki kalleni da kyau!" Ta furta da gasken gaske,abinda ya sabbabawa hudan duban nata da idanunta da suka hada hawaye masu yawan gaske
"Ba suna kirana karuwa ba?,ba cewa suke ina yawon ta zubar ba?,ba cewa sukeyi nayi cikin shege yafi sau a qirga ba?,ina bin maza?,ina sata?,ba haka suke bada shaida ba?......to na barsu da Allah na kuma barsu da ranar da zasu tsaya gaban Allah su baida shaida akan hakan......ni aminatu ahmad na rantse miki da girman Allah ban taba bawa kowanne d'a namiji kaina ba.....ban taba sanin d'a namiji ba ban taba kwanciya da kowa ba,idan kuma na taba....."
"Aah yaa sabreen" Huda da kuka ya kecewa ta fada da hanzari tana dora hannunta saman bakinta yayin da dukka hannayenta ke rawa.
Wani qauna da tausayi na 'yan uwantaka ke tsirgawa kowannensu. Daga ita har huda din hawaye ne da kuka ya ballewa kowannensu har zuwa wani lokaci
"Me yasa kika boyemin wani abu daya shafi rayuwarki huda.....bayan hudubata kullum a kanku itace.....komai girman matsala ko qanqantarta.....kome girman abu da qanqantarsa da kukaga alamun zai afka cikin rayuwarku.... Alkhairi ne a idanunku ko sharri ban yarda a boyemin ba?.....kinsan wayeshi?". Kai kawai huda ke kadawa ragowar hawayen idanunta suna sauka tana jin wani abu maras dadi cikin qirjinta
"Sunansa na asali shine naseer bawai bassam ba......yayi amfani da sunan bassam ne saboda sunan dana bashi nawa shine basma a madadin sabreen......dila ne na qwayoyi da cocaine da dukkan wani nau'in kayan maye,yana dillancinsu da safararsu zuwa qasashe masu yawa ta wannan qazantacciyar hanyar ya tara duk wata dukiya da yake qafafa da ita. Ya qware ainun wajen ta'ammali da mata duk kalar wadda ranshi yayi mishi.....yarinya ko babba musulma ko Christian,koda kuwa ba harkarki bane idan wani abu a kanki ya darsu zai sanya a dauko masa yarinya yayi mata fyade......a irin haka muka hadu,kuma na zama sanadiyyar daya buga gagarumar asarar da har yau ya kasa murmureta bayan kuma ba haka ya tsara ba......yayi zaton ya samu irin matan barikin da zai kashema kudi ya gama da tenure dinsu ya sallamesu........tashi d'aya na bace masa bat......yana da balain naci da bibiyar da nayi imani ita ta bashi daman gano ni wace da inda nake......yayi nufin yin ramuwar gayya ne a kanki huda....saidai kuma naci alwashin sai nayi silar qarar da ragowar rayuwarsa a gidan maza tunda har bai daddara ba ya dawo cikin hurumina.......yaso kuma taba killataccen gold din da hannu vai isa yakai gareshi ba".
Ta sani ta kuma dade da sani zantukan adda sabreen kamar rubutu ne saman dutse.......bata qarya komai runtsi komai wahala,don haka maganganunta akan waye bassam naseer sukayi matuqar tsoratata. Jikinta ya sake daukan rawa.....wannan shine dalilin da ko yaushe yake qoqarin yadda zai shirya haduwarsu tana rushewa?.
"Ki rabu dashi don Allah adda.....kada ki sake jefa kanki cikin hadari.....". Bata saurareta ba ta jefa mata wayartata zuciyarta na mata wani irin ciwo da kuma son daukar fansa
"Bakin alqalami ya riga ya bushe......kirashi ki jaddada masa zaku hadu da yammacin litinin,saidai kice kina tsoron kada a gane kin fita a gida.....kuna da event a wani guri dab da wajen acan kikeso ku hadun" Tayi maganar tana qoqarin yago paper cikin wani memo dake saman bedside din hudan tana rubuta mata sunan wajen.
*_LITININ DIN DA MUTANE DA YAWA SUKA CIWA BURINTA.....LITININ DIN DA ZATA ZANA QADDARORI CIKIJ RAYUWAR WASU,WASU QADDARORIN KUMA DA SUKE ZAMA MABUDIN QOFOFI MASU TARIN YAWA GA RAYUWAR WASU.....MABUDIN FARA GWAGWARMAYA DA TIRKA TIRKAR DA ZATA JA MANA RAGAMA HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN.....ZAMU GANI WAYE LITININ DIN ZATA ZAMEWA FARAR RANA KO AKASIN HAKAN?_*
_KUCI GABA DA BIBIYAR 'YAN MUTAN HUGUMA_π₯°π₯°π₯°
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Matsalarki inda zaki samu ingantattun kayan kitchen na kece raini cikin farashin rangwame da rahusa me kama da KYAUTA?_*
*CHINA*
*DUBAI*
*INDIA*
_Duk kasu a sanqame a waje daya,amintattun kaya nau'i daban daban masu daukar hankali don qawata kitchen,siyan daya ko sari_
*_Ko damuwarki kayan kitchen DESIGNERS na alfarma da kece raini?_*
*_maza garzaya cikin gidan HUGUMA UTENSILS UNIVERSE,domin kuwa ta shirya tsaf dom share muku hawayenku da galla gallan kayan kitchen cikin qanqanin farashi_*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub
__________________________
PAGE 88
Lokacin da motarsu ke shan kwanar layin nasu wayarsa ta dauki tsuwwa. Kaman bazai dauka ba amma sai ya miqa hannunsa,saboda duk kiran daya shigo ta wannan wayar yana da tabbacin yana da alaqa me qarfi dashi.
Sunan Musaddiq ne ke yawo saman screen din. Ya sake zama sosai yana daga wayar sannan ya karata a kunnensa.
Kafin yace komai muryar Musaddiq din da sautin sallama ya ziyarci kunnensa. Ya amsa masa a nutse.
"Hamma kun dawo ne?" Ya tambayi fu'ad din
"Muna dab da shiga gida.....wani abu ne?" Siririyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
"Hamma muna asibiti" Yanayinsa ne yadan canza kadan ya bude baki yana tamba cikin fargaba
"Asibiti?,kai da wa?,waye ba lafiya?"
"Maamah ce hamma......muna dawowa nida abba saiga kira da asibiti.....wai an kai ta ta fadi"
"Ta fadi?" Ya maimaita kalmar cikin mamaki
"Eh hamma" Shuru kaman bazaice komai ba,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya
"Me ya sameta?,ko kuma me sukace yana damunta?". Kai Musaddiq ya girgiza yana sauke idanunsa akan hajja harira,sai ya miqe kuma a hankali yana tura qofa ya fice daga dakin.
"Wasu bayanai likitan ya fara,saidai yace yana da buqatar ganinmu ni dakai a tare don yayi mana gamsashen bayani"
"Alright.....zan shigo" Ya amsawa Musaddiq yana sauke wayar a kunnensa.
Guri daya ya zubawa ido yana kallo qwaqwalwarsa na tafiya zuwa wani nazari. Ya bude bakinsa a nutse da zummar bawa driver umarnin wucewa asibitin,sai kuma ya lumshe idonsa yana tuna wani abu daya faru a shekarun baya wanda sai daya sanya shi sauke wani numfashi me nauyi,kana a hankali ya hadiye kalmarsa yana maida idanunsa ga gate din gidan da suke dosa.
"Waye a asibiti ba lafiya?" Farouq da yake amsa waya sanda fu'ad ke wayar ya tambaya bayan ya kammala wayar yana duban fu'ad
"Maamah ce" Ya bawa farouq din amsa a gajarce ba tare daya kalli farouq ba.
"Maamah kuma?,amma inaga ya kamata ace mun juya akalar tafiyar tamu zuwa asibitin ko?"
"Ba yanzu ba farouq.....na gaji,sai na huta tukunna......kaina kaman zai tsage da abubuwan dake cushe akai".
"Duk da hakan bai zama hujja na kasa zuwa dubata ba.....ka huta din idan mun dawo......janar....." Ya qwallawa driver nasu kira wanda ya rage gudun motar saboda kawowarsu tafkeken gate din gidan alhaj hamza kibiya
"Sir" Ya amsa masa a a ladabce
"Juya motar nan mu koma titi" Ya bashi umarnin idanunsa saman wayarsa yana lalubar number wayar Musaddiq don yaji a wanne asibiti suke?,don ya tabbatar yace fu'ad zai tsaya tambaya zai bata lokacinsa ne kawai.
"SAMHG hospital kuke?" Ya tambaya Musaddiq ga zaton suna can din. Kebantaccen asibiti ne da ake duba iyalin gaba daya bayan asibitinsu na cikin gida da fu'ad keson maidashi babba ya fadadashi sosai cikin sabon ginin mansion house din da yake musu yanzu haka
"Okay.....turon address din" Ya fadi yana kashe kiran.
A haka zakayi zaton kunnuwa da hankalinsa basa tare da farouq din,saidai kuma har yayi wayar ya gama yana saurarensa. Ta yaya za'a kaita wani asibitin da ba nan ne asalin inda kowa yake zuwa ba?. Tambayar da ya samu wani guri na musamman cikin kwanyarsa ya adanata.
Kira farouq din ya sakeyi,a wannan karon anni ya kira. Dab da zata tsinke ta daga da cikakkiyar sallama da muryar nan tata ma'abociyar kwarjini da nutsuwa.
"Mun dawo anni.....amma mun wuce asibiti dubiya,kada ki jimu shuru"
"Waye ba lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa
"Maamah ce" Ya amaa mata kai tsaye
"Subhanallahi......amma ba wanda ya sani cikin gidan nan......ince ko jikin nata da sauqi?"
"Ban sani ba anni,sai munje yanzun zamu gani"
"To don Allah kuyi mata sannu,idan akwai wani abun kuyi gaggawar sanar mini"
"To anni" Ya amsata yana sauke wayar. Dubansa yakai ga fu'ad,har yanzu waje daya yake kalla,yadda yayi dif kaman baya wajen,haka fuskarsa ta nuna kaman baisan me ake magana akai ba.
"Fu'ad" Farouq ya kirayeshi sanda suka isa farfajiyar asibitin,guards dinsa kuma nata kai da kawowa wajen tabbatar da tsaron wajen kafin fitowarsa.
Idanunsa dinnan masu bala'in kwarjini ya daga ya zubewa farouq su. Yanayin kallonsa yana da matuqar kaifi da saukar da dafi,idanun suka so yiwa farouq din kwarjini,saidai wannan din ba baqon abu bane a wajensa,abune da ya riga ya saba dashi tuntuni.
"Ako yaushe ka dinga tuna cewa taci albarkacin kalmar UWA.....zata kuma ci gaba da cin wannan Al Farmar koda meye tayi maka" Idanunsa yadan ragewa kaifi kaman zai lumshesu sai ya fass,ya sake budesu sosai saman fuskar farouq din. Wannan maganar inda farouq din yasan mugun famin da ya yiwa ciwonsa da baiyita ba,har maqogoronsa sai da yaji yawu yana neman daukewa,ya tattara dukka wani yaqi da yakeyi da yanayinsa sannan ya bude bakinsa
"Inda ace a yau za'a zare wannan kalmar tsakanina da maamah......da har abada ba zata sake ganin fuskar muhammad fu'ad ba muddin kuwa ya haifu daga tsatson jadda.....a lokacin daya miqa mata dukkan soyayya da yarda......a lokacin ta nuna masa cewa DIYA MACE MAYAUDARIYA CE.....BA KUMA ABAR YARDA BACE,bata barshi haka ba har sai da tayi silar......." Ji yayi bazai iya qarasawa ba.....ji yayi wannan sirrin bazai iya furtashi ga kowa ba,sai kawai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya zura qafafunsa yana fitowa ba tare daya jira me budewar ya bude masa ba.
Tun bai qaraso bakin qawatacciyar balcony din da aka yiwa dakin ba musamman saboda shan iska da hutawar me lalura da me jinya ba ya hangeta zaune ta hasken fitilun da aka wadata wajen dashi. Kanshi ya dauke sarai,yana jin har qasan ransa ya washi matar. Ba zaya gaya mata gogayya da duniya ba.....kaman yadda bazai gaya mata sanin takan duniya ba. Bata tunanin akwai wani yanayi da zai nuna mata a yanzun da zai tunzurata ta janye rayuwarta daga cikin tasu har sai ta cimma nata gacin.
"Sannu da zuwa.....ashe ka qaraso" Hajja harira ta furta cikin tsananin nuna kulawa tana miqewa daga saman kujerar da take kai.
Kanshi ya dauke yana maidawa ga Musaddiq daya taroshi tun daga farkon balcony din
"A nemo likitan......yazo da gaggawa don ina da abunyi" . Sosai maganar ta daure kan hajja harira wadda kwarjininsa ya hanata sake cewa komai. Lallai ya kamata kafin ta zurma kanta da yawa ta sake karantar kowanne taku da motsi nasa domin samun isar muradinta cikin sauqi.
"Waye a cikin dakin?" Ya sake jefa tambayar ga Musaddiq. Saidai kafin wanda aka yiwa tambayar ya amsa hajja hariran ta rigashi amsawa cikin matuqar alhini
"Basu barin kowa ya shiga don har yanzu ma bata farfado ba". Duba daya tak ya yiwa hajjan yayi taku uku ya isa gaban dakin,ba tare da jiran umarni ko bada dama ga kowanne likita ba ya murza handle din ya tura kansa ya shige.