Showing 189001 words to 192000 words out of 557259 words

Chapter 64 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

467

bayanta. Murmushi ya saki yana mata nuni da daya cikin lausasan kujerun dake ajiye a wajen. Ta taka a hankali ta zauna tana kallonsa da murmushi,fuskarta na nuna wani irin excitement

"Hamma.....zuwa nayi ka gayan favourite colour da kakeso a sawa matarka a lefe......and then ka fadi dame dame zaa zuba?,lissafin anni ya qure,tace nazo na sameka naji naka ra'ayin". Ido ya lumshe yana sakin murmushi,ya fuskanci sun daukaki abunnan,da gaske suka dauki komai,kuma da alama gagarumin shiri sukeyi.

Dukkan abinda suka aiwatar shi ko daya ma baizo kansa ba,ya manta dasu cikin ma hidimar neman aure,ko ita kanta yarinyar yana mantawa da zamanta sai idan wani abu ya gilma ko sun tada zancan.

"I don't have anything to say......the choice is yours" Ya fada da tsararren accent din nan nasa dake nuna gwanancewa wajen iya sarrafa harshe.

Murmushi sosai amna ta saki tana gyara zamanta cikin nuna doki

"Thanks hamma......bari na zabawa addana classy kaya" Ta dora hannunta saman paper din ta soma zana list.

Da sauri yaja baya sanda yake yunqurin fitowa daga dakin,idanunsa akan bibo wadda ta afko dakin kamar an tunkudota. Fadowarta dakin bai hana sabreen maida kanta taci gaba da takawa zuwa cikin dakin a nutse ba.

Maganganun bacin rai ne fal zuciyarta da zataso amayarwa da kawu rufai din,to amma tanata dannar zuciyartata saboda yiwuwar wanzuwar tata manufar. Sassauta fuskarta tayi tana fuskantar kawun sosai idanunta cikin nashi

"Banda abun rufai......ai ba'a yiwa 'ya'yan yanzu dole......tunda dai yarinyar nan tace batayi bataso ka qyaleta mana,gida cike fal da 'ya'ya......nan nan hadiyya idan kace ita zaka bashi.....wallahi tsaf zaa katse karatun nan duk da muhimmancinsa.....duk kuma yadda take sonsa....ai aure shine gaba da komai a wajen yarinya". Tayi zancan tana jaddada masa muhimmancin maganar da kuma gaskiyar abinda take fada. Hannu yasa ya kama habarsa yana dubanta

"Wato har yanzu dai ba zaki daina hali ba bibo?,kin saurari komai kenan?"

"Kaga rufai kada kayimin mummunar fassara.....saboda Allah don kawai yarinya ta nuna batayi......na bada shawarar kada a shiga haqqinta saika nemi canzamin magana?". Karon farko kawu rufai din yaji jikinsa ya sanyaya da bibo din,ya kalleta sosai cike da mamaki

"Bibo"

"Rufai" Ta amsa masa da sunansa kamar yadda shima ya kirata da sunanta

"Bari kiji na gaya miki......sabreen suka nema ba wata 'ya cikin gidan nan ba..."

"Suka nema ko kuma ka nemo Mata?" Tayi zancan tana yada kanta gefe cikin salo na watsa habaici.

Wata dariyar takaici kawu rufain ya saki

"Gwara ki fito kai tsaye ki fadi abinda yake ranki bibo......ki saurareni da kyau kiji.......sabreen bani na nema mata miji ba.....farinjininta da qashin arziqinta daga Allah ne,don haka bani da hurumin musanya musu da wata.....saiki dage da addu'a kema Allah ya azurta taki 'yar da koda yaron mijin Sabrina ne". Maganar tayi masifar sosawa bibo rai,harta kasa masa shuru sanda yake qoqarin fita daga dakin. Ta saki shewa ta daki cinyarta

"Ahayye......lallai sai yau na sake yarda kai din dan kunama ne.....kuma ka cika cikakken butulu......to bari kaji,ka tsallake yaranmu kaf ka tafi nemowa wancan tsintacciyar magen miji saboda tsabar qwarewa wajen munafurci da tsugudidi.....wallahi indai ina da rai na ci maka alwashin sai hadiyya ta auri mijin daya kerewa na sabrin"

"Allah ya bada sa'a......ko mafarki kikayi hakan ta faru lallai kin cika me sa'a" Ya bankada labulen ya fadi mata sannan ya juya abinsa zuwa tsakar gidan don ya sarrafa kayan da aka shigo dasu din. Ta gefe daya ya dauki dukka maganganun sabreen ya azasu akan mizanin abinda baida muhimmanci sam sam,saboda shi din yasan waye muhammad jadda.....kuma duk inda takai ga kafiya da jin kanta to la shakka daidai yake da zamaninta.

Idanunta ta lumshe tana qoqarin daidaita fitar numfashinta,yayin da idanuwansu dukka su ukun yake zube a fuskar yayar tasu.

"Kiyi haquri adda" Haneefa dake tsaye sosai a gaban sabrin din ta fada fuskarta kamar zata saki kuka. Duk da ba komai ta fahimta ba,amma kusan ta saba da hayagagar kawun,wanda duk sanda ya yita cikin falon nasu to wani fada ne ko tashin hankali......tun bata fahimta har ta gane komai sannu a hankali.

Cikin zuqar numfashi daya ta dawo da dukka jarumtarta tana sake gayawa kanta. Ita din 'yantacciyar 'ya ce.....ba property din kowa ba ballantana a ajiyeta a sanda akaga dama a inda kuma akaso.....sannan a janyeta ko a sauyata a duk sanda buqatar hakan ta taso.

Murmushi ta saukewa fuskarta,ta miqa tattausan hannunta tana shafar kumatun haneefa din

"Komai bai faru ba auta.....ku koma parlor ku kunna tv,nasa an gyara muku receiver din". Kai ta gyada a sanyaye,ta waiwaya ta kalli nadra da huda,sai ta juya tana ficewa suma suka bi bayanta,duk kuwa da cewa fuskokinsu sun nuna sam zuciyarsu bata gamsu da abinda ta fada ba.

Kanta ta cusa sosai cikin lallausan pillow dinta,ta shaqo qamshin ciki tana fesarwa ta baki. Wacce irin qaddara ke bibiyarta haka?,ta kowacce fuska barazana rayuwa takeyi mata da lamarin aure?,tabbas ko sama da qasa zasu hadu ba zata taba aminta da wannan shirin wasan kwaikwayon na kawu ba......kamar yadda ta gama shirya komai don bacewa wadancan azzaluman matan.

Kamar ana jira takai nan wayarta ta dauki qaramin sauti tana haske......ta daga kanta a nutse ta zubawa wayar idanu. A nata zabin bata da sauran wani dangantaka ko dalili naci gaba da sauraronsu.....to amma yaqi dan zamba ne.....wannan wata rubutacciyar magana ce data jima da haddaceta tare da adanata cikin dictionary dinta.

Sai data zauna sosai sannan ta daga wayar ta sanya a kunnenta tana cije labbanta.

"Salamu alaikum" Tayi sallama da muryar nan tata da tun randa ta fara furta mata manufarta a kanta ta haddaceta tsaf......sannann ta sakayata a gurbi na musamman da take ajiye dukkan wasu abubuwa da suka zame mata dole takatsantsan dasu.

Cikin wannan miskilancin nata daya zame mata jinin jiki ta amsa mata. Hakan sam ba damuwar maamah bane.......tana da tarin abubuwa da takeson sake sani tsakaninta da fu'ad.

"Ina fata zuwa yanzu dukiyar auren d'ana ta ruskeki?". Tadan shiga mamaki kadan,kamar zata tambaya amma miskilanci ya hana,sai ta zabi ci gaba da yin shuru har zuwa sanda maamah ta fahimci ba zatace komai ba.102

"Magana nakeso nayi dake masu tsananin muhimmanci.....naso ta kasance fuska da fuska.....to amma inason dauke idanu da hankulan mutane daga kan plan da dukka ma wani tsare tsare namu......na tsinci cewa yarona da nake nemawa ke shima ke yake nemawa kansa......abune me matuqar mamaki da daure kai.....nayi mamaki kaina ya kuma daure akan ya akayi hakan ta faru?.....ban samu wani tsoro ko kuma fargaba ba......saboda dukkan wata alama da zata bani cewa auren soyayya ne ake shirin qullawa babu shi......ya akayi kikasan muhammad jadda?.......meye naku shirin akan aurenku..... Duk da ba lallai ne na sani ba......amma zan gaya miki abu guda daya a taqaice......koma meye kuka shirya ke dashi ki tabbatar shirinku baici karo da nawa ba".

Sosai kanta yayi wani irin daurewa,sai taji kamar ta fara daina gane komai. Tana nufin ita din mahaifiya ce ga.......ya salam......." Ta furta cikin zuciyarta da murya qasa qasa. Wai su din wadanne irin mutane ne wadannan?,da d'a da uwa dukkaninsu kowa da irin kalar tasa alqiblar?,da d'a da uwa kowannensu nada karkatacciyar manufa?,kuma duka ba'a kan kowa ba?,a kanta?.

"Ina fata kin fahimta?" Maamah ta tambayeta ganin koda tarinta bataji ba.

"Akwai wani abu me muhimmanci daya dace ki fadan ki fadi ba?" Ta motsa labbanta a nutse tana tambayar maamah duk da yadda kwanyarta da zuciyarta suke cakude da rudani.

"Shikenan.....qaramar magana ce kuma gajeriya,amma me matuqar muhimmancin daya kamata ayi mata riqon tsauri" Qaramin murmushi ta saki me sauti,sautin daya ratsa ta wayar ya isa kunnuwan maamah. Wai ta yayama ita zata tsaya a dinga tambulin da rayuwarta tsakanin UWA da DANTA?. Ta yaya ma zata tsaya ta zuba musu idanu suna yin yadda sukaga dama rayuwarta?,rayuwartata da ba mallakin kowa bace ba kuma wanda yake da iko da ita?. Rayuwar da aka fusgeta da qyar?,tsananin kuma nisan kwana ya kawota inda take zaune a yanzu?.

Isar murmushin kunnuwan maamah ya haifar mata da 'yar fargaba kadan,saidai kuma lafazin sabreen din ya danne dimuwar

"Baki da damuwa.....ki qirga kwanakin kawai da kike jiran komai ya kasance"

"Da kyau.....naji dadi dana sameki ame saurin cika alqawari.....sati uku.... Sati uku kadai ya rage ki zama daya daga cikin familyn jadda......nasan kuma bakisan wanne irin family zaki shiga ba......cikin qasa da sati daya kafin sannan ina buqatar ganawa dake don ki karbi jadawalin tsarin yadda nakeso komai ya kasance". Idanu ta lumshe ta kuma budesu lokaci daya tana gyada kai. Karon farko a rayuwarta da tasan murmushi yana iya fita daga fuskar dan adam a yayin da yake cikin bacin rai.

"Baki da matsala" Ta furta da ma'anoni daban daban.

"Okay.....inason ki saki jikinki.......bayan hidimar dashi da uban goyonsa zasuyi miki......karkiji nauyin tamabayata komai......ko nawa kike da buqata a shirye nake dana kashe miki shi......inaso surukata tafi kowacce suruka daga cikin surukan sanannu kuma attajiran families.....biki zamuyi na kerewa sa'a.....irin bikin da zai kauda zato da kuma dukkan zargin me zargi a kanmu".

"Ba damuwa bane....na fahimci komai,amma ina buqatar hutu........zamuyi magana wani lokacin" Ta qarasa fada tana yanke kiran ba tare data jira cewar maamah din ba. Gefe tayi jifa da wayar tana nutsa hannunta cikin sumarta

"Ya ilahi.....ya akayi dukka haka ta kasance?ya akayi komai yazo a daidai?" Tayi zancan a fili

"Kiyi aurenki adda......kiyi aurenki" Taji muryar huda dake rawa,wadda ke tsaye daga gefanta.

Hannayen nata ta zare daga sumar,ta daga kanta a hankali tana duban huda dake tsaye. Idanunta cike fal da hawaye,ta qaraso da sauri ta tsugunna gaban Sabreen gami da riqo hannayenta

"Adda....."

"Shshsh" Ta dakatar da ita tana dora yatsanta akan lips dinta.

"Nayi aure a wannan situation din kike fadi huda?.....na kaiku ina?.....waye zai kulamin daku?"

"Allah......Allah ne adda" Ta amsa mata har yanzu muryarta na rawa.

"Na sani huda.....na sani,amma kinsan wanne irin aure ne wannan auren nawa?.....rayuwar addanki sukeson jefawa cikin wani game da ake bugashi tsakanin D'A da UWARSA.game din da ba wanda yasan meye ainihin ma'anar bugashi,zasu tsoma rayuwar aminatu a ciki bayan bata cancanci ta fuskanci raba uqubar rayuwar kowa ba.....me nayi da zasu nemi na zama silar cutar da dayansu?". Tana kaiwa nan sai ta samu kanta da kecewa da kuka,wani nannauyan kuka me siririn sauti,irin kukan data dauki sama da shekara shida tana tarashi a qirjinta,don bata da kafadar da zata kwantar ta fiddashi ta rage wannan radadin.

A yau hudan ta zame mata wannan kafadar,har ta zama jarumar data dinga sharewa sabreen hawaye dukka jikinta yana rawa

"Daga yau zamu dinga raba wannan tsananin da quncin adda......ba zaki sake kuka ke kadai ba....kiyi haquri kada su nadra su jiyoki"

"Ba wanda zai rabamu huda.....dole na nemana muhallin da zamuyi nisa da dukkan wannan qullin.....bazan fuskanci wannan abun ba". Tayi maganar tana zare kanta daga kafadar hudan,ta miqe tsaye kai tsaye tana dosar bakin gadonta.

𝙒 𝘼 π™Ž 𝙃 𝙀 𝙂 𝘼 𝙍 𝙄


*******Daidai lokacin da su huda suka wuce tahfeez a safiyar asabar din. Ta shirya kanta tsaf cikin turkey dress da suka maidata tamkar daya daga cikin kyawawan 'yammatan turkey din.

A nutse take rufe qofar parlor dinsu,ta zuge qaramar jakar hannunta ta jefa key din duk da yadda takeji a jikinta akwai idanuwa masu yawa a kanta cikin jamaar dake zazzaune a tsakar gidan.

Tsakanin jiya da yau din ta karanci an samu yawaitar jama'ar dake zama a tsakar gidan nasu. Wani irin zama da yake kama da zaman gulma tsurku da kuma zunde.....a wani yanayin kuma yafi kama da zaman jajantawa da kuma jimamin da batasan ma sunayi ba. A nata ganin dukkan kai kawonsu bazai wuce akan tatsuniyar qirqirarren aurenta da kawu ya gabatar cikin gidan ba,labarin daya girgiza kowa cikin gidan harda 'yan uwanta da suke uba daya wanda suke aure a wani gidan.....lamarin da inda suna da yadda zasuyi suka tsige mata shi me yiwuwa ta sanyasu cikin jerin masoyanta da bata da kamarsu.

Idanuwa sunyi yawa a kanta sanda take ratsawa tsakar gidan,idanuwan dake cike da hassada da jin haushinta,sannu a hankali ta samu ta isa ga soronsu ta bulla farfajiyar gidan da zata danganata da gate na qarshe na gidan.

Motar dake lullube cikin tempol qarqashin rumfar data kasance ma'ajiyar motor mahaifinsu sanda yake raye idanunta suka fada.....

Ido ta dauke daga kanta tana jin wani zafi yana ratsa zuciyarta. Da gaske yake kawun kan lallai saita karba komai harda motar da anata idanun daidai take da motar daukan gawa.

"Komai ya kusa qarewa" Ta fada qasa qasa sanda take gifta motar,tana buqatar isa inda tayi niyya don shirya yadda zata nesanta kanta da qannenta da wannan Cakwakiyar da ake shirin tsomata.

"Ke.....ina zuwa?,ina zaki haka?" Muryar kawu rufai ta ratsa dodon kunnenta,kawun dake tsaye qofar wani daki dake can qarshen katangar gidan. Dakine da ashekarun baya mahaifinsu kr jibge kayan abinci a ciki.

Duba daya tayi masa ta kauda kai taci gaba da takawa abinta don fita. Ya fahimci maganarsa sam bata dadata da qasa ba,hakanan sautinsa bazai taba dakatar da ita ba,don haka ya saki aikin gyara kwalayen da yasa akeyi ya tako da sassarfa cikin burin cimmata.103


Har ta murda hannun qofar ta bude sai kuma ta dakata saboda wani tunani da yazo mata. Tsaf kawun zai iya binta waje ya tara mata jama'a,don shi din bai ita magana qasa qasa ba.

"Ina zaki nace ke aminatu" Yayi tsaye a gabanta yana fada idanunsa a kanta yana daure fuska.

"Kin tambayi mijinki?,da izininsa koda saninsa zaki fita?" Ya sake jefa mata tambayar da gaske yana adan tsorace.

"Mijinki" Kalmar tayi wani amsa kuwwa cikin kunnenta. A duk sanda taji ya ambaci wannan Kalmar sai abun ya zame mata wani irin baqon abu.

"Bazan hanaki fita ba.....amma sai na tabbatar da izininsa kika fita din,don a yanzu ke amana ce a hannunmu,bazan Kuma yi wasa sa wannan amanar ba har sai na tabbatar ta fita daga hannu na".

A nutse ta daga ido ta kalleshi,abun yana bata mamaki gaba daya,wai yau kawu shike haqiqancewa haka akan lamarin da ya shafeta?,wai yau shike tambayarta ina zata fita?,lallai kudi sun zamewa rayuwar wasu bayin jarabta. Abune da bata taba sanyawa cikin kanta ba......wai akwai wata rana da zata zo har wani ya damu da inda ta fita ko kuma ina zata je?.

"Ki sanar dashi sannan kije duk inda kikeson zuwa din" Ya same maimaitawa yana tura qofar da qafarsa.

"Oh......inda ranka kasha kallo....duniya juyi juyi wai kwado ya fada ruwan zafi......dama idan bakayi sharar masallaci ba ai kayi ta kasuwa,kudi shu'umai......iska kuma na wahal dame kayan kara.....ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta". Wannan jerin gwanon habaicin suka fito daga bakin bibo wadda ta iso daura da wajen don zubda sharar sa ta kwaso daga dakinta.

Waiwayawa kawu rufai yayi yana dubanta
"Wai dukka wadannan gayyar gamayyar haibaicin akan waye kike?,indai da Sabrina kike aikin banza kikeyi,kinfini sanin halinta,uwa uba kuma a yanzu ita din me arziqi ce.....me arziqi kuwa baya fada da talaka......ni kuwa kinsan warki nike daidai qugun kowa.....to saiki banbance".

Tsaiwa tayi sannan ta waiwayo tana zabgawa kawu harara,wani irin tsanarsa da haushinsa suna cikata

"Magana kakeyi ne ko bakinka ne a haka?,aini rufai na jima da sallamaka cikin lamurana.....ashe da gaske aboki yana iya juyewa ya koma maqiyi?,dadin abun ba'a fimu iya 'yan shige shigen nan ba,to na meye ma zan damu banda abinka rufai?" Ta qarasa maganar tana yarfe hannu cikin son boye damuwarta da lamarin.

"To barkanki.....gwanda da kika gyara zancanki kika samawa kanki salama....".

Kunnuwanta ba zasu iya ci gaba da sauraron wannan quruciyar ta kawun da bibo ba,wanda har yanzu suka kasa dainawa,duk kuwa da cewa kansu da bakinsu a hade yake,yanzun ne abun duniya yake shirin hadasu,don haka suna tsaka da sa'insarsu ta tajuya tana takawa da nutsatsiyar tafiyarta dinnan da 'yan bani na iya suka sawa suna

"Maciji me tafiyar mutuwa" Nutsuwarta a tafiya a cewarsu sam bai dace da halinta ba a tasu fahimtar.

A falo tayi wurgi da jakarta ranta yana susa,tun komai baiyi nisa ba har kawun ya soma!shiga gonarta da kuma nuna mata iyakarta?. Dankwalin kanta ta zame sassalkar sumarta ta zare daga ribbon din data matse gashin,ta koma da zafi zafi ta zauna saman kujerar tana furzar da iska daga bakinta

"Ta yaya ma zata zauna a maida rayuwarta haka?,ya zata zauna ta rayu kaman haka?,dole ta matsa qaimin tattare komai dama kowa nata zuwa bigiren da zata ci gana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login