Showing 27001 words to 30000 words out of 557259 words

Chapter 10 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

398

har ita ya danqara mata wannan sunan?" Wannan ba baqon abu bane a wajenta,saidai har yanzun mamaki da lamarin maza bai gama sakinta ba.


"SAMHG store" Ta amsa masa a nutse tana gyara agogon hannunta daya goce

"An gama ranki ya dade" Ya fadi cikin zumudi yana tayar da motar.

Sun jima akan hanya yana tauna abinda zaice da ita,don a taqaitaccen saninsa da ita.....mutum ce me matuqar tsari,nutsuwa da aje komai a bisa gurbi da muhallinsa. Bayaso ya kwafsa kaman waccan karon,bayaso damarsa ta sake kubce masa,duk da cewa har kawo yanzun baisan me ya aikata daya rasa wancan damar a wancan karon ba.

Yaji babu dadi ainun saboda ya qwallafa rai sosai a kanta. Ta yiwa zuciyarsa wani mahaukaci kamu a ganin farko. Yayi tsammanin kudinsa da ajin mataki na rayuwa zai saya masa ita cikin qanqanin lokaci,sanin da ya yiwa 'yammata kenan a yanzun,ballantana ita dake da kyau da aji irin wannan.

Sanda yake wannan tunanin nata nazarin da karatunsa duka a kansa yake. Yadda yaketa rejecting kiran dake fama shigowa wayarsa a jejjere. Duk kiran da zai shigo sai ya katseshi. Tuni hankali da kuma jikinta ya bata wanda ke kira.

Idanunta tadan lumshe,koda yaushe su dinne dai,cikin wahala,qasqanci,tozarta da kuma wulaqanta zaune cikin gidajen aure. Ko meye kuma zai fito yaje yazo su din yake afkawa.

"Zan iya cewa wani abu?" Ya tambaya a ladabce yana murza steering motar cikin qwarewa

"Kafin sannan ya kamata ka daga wannan kiran ko?" Ta fada idonta akan fuskarsa.

Motsawa kadan yayi yana duban wayar ta qasa idanu,bai zaci ma ta lura da hakan ba. Haushi ya soma kamashi akan kiran da take masan babu qaqqautawa. Yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,tunda bai jima da fita a gidan ba,yasan kuma abinda ya fito ya baro a gidan

"Tarin damuwa ce da matsaloli kawai take dauke dashi" Ya furta yana jan siririn tsaki.

Har tsakiyar ranta taji saukar maganar,ta lumshe ido kadan tana budesu. Yana nan din a haka,yana nan yadda ta karanta. Tayi qoqarin tureshi daga shiga layikanta,tayi qoqarin hanashi shiga cikin tarkonta don baya cikin irin mazan data zana bisa layi da gurbin rayuwarta,taso ta barshi ya samu me hukuntashi a gaba.....amma tunda har ya sake dawowa cikin rayuwartata cike da karsashi da zumudi,to tayi imani hukuntashi yana cikin qaddararta ne. Ba kuma zata qyaleshi ba,a wannan karon saita hukuntashin yadda ta saba hukunta maza irinsa. Maza irinsa basa tsira daga tarkonta......basa tsira daga kamunta,hakanan basa tsira daga hukuncinta.

Cikin salo na dabarar da yake gani kaman ba zata gane ba ya latse wayar,ya kuma jefo mata maganar da tafi damunsa

"Hanan.......wannan karon bazan bari ki kufcemin ba"

"Nima bazan bari ka tafi ba" Ta furta,a bakinta bisa mizanin ma'ana qwaya daya tak da hankali zai iya fahimta,amma kuma an aje ajjiyayyar ma'anar da ake nufi da maganar can qasan zukata.

Wani irin dadin daya sabbaba masa lafiyayyen murmushi ya ziyarceshi. Bai taba kawowa ko kusa a ransa samun wannan gwaggwabar nasarar a kurkusa haka ba,amma kuma,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa

"Duk kyau ko matsayinta zata sauko......a yanzun fa mata ke neman mazan aure idanu rufe" Hudubar data shiga kunnensa kenan,kuma ya yarda da hakan dari bisa dari.

"Amma hanan banga alama ba......bansa inane mazaunin da kike rayuwa ba,gida unguwa da sauransu"

"Gaggawar me kakeyi?,kada ka samu damuwa" Ta amsa masa tana jin ya ginsheta gaba daya,tana jin ta damu qarshen zamansu yazo,ta qagu su isa SAMHG store ya ajeta ya bata sarari.

A hankali ya kutsa motar babbar harabar kantin saida dukkanin kayan buqatar rayuwa,wanda zaifi kyau ka kirashi da kasuwa a sauqaqe amma kuma a zamanance. Ba abinda basu hada ba na kayan buqatu,tun daga tufafi zuwa kayan masarufi. Wajen nada matuqar girman da idan ka kirashi da duniyar siye da siyarwa. Girmansa ya sanya yake da mashigu daban daban da kuma guraren fita mabanbanta.

Cikin tafkekiyar harabar wajen ya aje motarsa,ya kasheta cikin mutuwar jiki da kasala yana waiwayowa inda take zaune tana qoqarin rataya jakarta gami da daukar wayarta ta riqe wadda ke aje saman cinyarta.

"Idan ban damuwa zan dan tayaki tattaki zuwa ciki......don naga wajen kamar cike yake da maza da yawa......ni kuma ina kishin na barki ki fita ke daya a kallemin ke" Ya furta cikin kulawa da wani irin narkakken so dake ragargazar zuciyarsa.

Da wani sassanyan kallo ta jefeshi,qawataccen murmushin nan dake qawata fuskarta da kuma labbanta ta sakar masa. Ta rausayar da kanta gefe tana juya idanunta. So take ta sallameshi a iya haka,bata buqatar doguwar damuwa. A lokaci irin wannan da takai qarshen mission dinta,ko fita unguwa ba kasafai take damunta ba sai idan buqatar haka ta taso. To amma hakanan taji akwai buqatar ta fita din,akwai kuma buqatar ta fita tayi musu siyayya.

"Baka da damuwa akan duka wannan......wannan hanan din ba komai idanunta ke kalla ba ballantana su burgeta" Ta bashi amsa a nutse.

Murmushi ya saki yana qara narkewa a sonta,yana ji cewa zai iya yin komai don ya mallaketa,yana jin cewa muddin ya sake barinta ta subuce masa a wannan karon ya tafka babbar asarar da bazai iya maida madadinta ba,baya jin ma zai bari hakan ya faru dashi sam sam.....kai koda tuna hakan na iya faruwar bayason yayi.

"Na ga zahiri......na kuma tabbatar wannan halittar ta daban ce......gamu cikin neman sa'ar kasancewa da ita" Ya fada yana lumshe idanu. Kai ta kawar amma tana murmushin yaqe. Ya numfasa bayan ya gama qare mata kallo cikin shauqi ya dauki wayarsa dake aje tun sanda ya maidata silent ya bude.

Tarin miscall a qalla guda goma kyawawa daga gareta. Ya jawo maballin sama ya sharesu yana sakin tsaki can qasan ranshi tare da wucewa mobile app na banking da yake ajiyar kudadensa.

Sosai ta jingina da makarin motar idanunta a lumshe sosai,sai kayi tsammanin bacci ko kuma gajiya ne sukayi mata yawa,saidai a cikin biyun duka babu ko daya a ciki.

"A taimaka a karantomin account number na dan bada wani tukuici" Idanunta ta janye daga saman wayar nasa,saita tashi ta zauna sosai tana dan sakin murmushi

"No need" Ta amsa masa a yangance kaman yadda ta saba magana

"Please.......ba wani abu bane me yawa.....just tukucin bani damar ganinki da kikayi a yau ne" Bata sake ce masa komai ba,sai ta zura hannunta cikin jakarta,wani dan siririn card me ruwan zaibar gold ta ciro ta aje a gefansa. Ta dauke kai tana qoqarin bude murfin motar wanda ita kanta tasan ba zata budu ta sauqi ko dadin rai ba......ta kwana da sanin meta aiwatar mata.

Cikin qasa da minti daya taji ya furzar da iska daga bakinsa gami da cewa

"Done.....ina fata zakiyi appreciating"

"Why not?,godiya me kima......godiya nake qwarai......but motarka tana nema ta riqeni fa"

"Da zatayi hakan data taimakeni ai" Ya amsata yana sake lafewa jikin kujerar. Kyawawan sexy eyes dinta ta waro waje kadan,sai kuma ta daga hannunta tana duban agogo

"Akwai alqawari da nayi,bana so kuma na saba......idan ka sani na saba kuma......next time kafin na baka daman sake haduwa dani....." Katseta yayi yana dariya ta hanyar hada hannayensa biyu waje daya sannan ya saukesu ya juya yana buda side dinsa

"Lemme check meye ya riqemin amaryata haka".

Da lumsassun idanunta ta bishi da kallo har zuwa sanda yake zagayawa gaban motar zuwa daya side din da take zaune. Yayi dukan dabarunsa amma hakan baiba,don haka ya zagayo yana fadin

" Bansan me yake faruwa,lafiya lau qofar yake,bari nasa a duban.....am really sorry" Ya sake apologizing yana hade hannuwansa.

taka Kai kawai ta daga masa tana irgen lokutan cikar target dinta. Cikin saa kuwa ya juya ya fara takawa yana barin wajen,wanda hakan ya bata damar janye kallonta sannu a hankali daga kansa,ta kuma maida saman wayarsa dake ajiye a wajen tana bada haske,tabbacin yunqurin hanata komawa key yayi daidai kenan,saita katse kiran da takeyi daga tata wayar zuwa tasa don sanya wayar awake.

A nutse ta jawo wayar ta wuce zuwa ga maballin kira.

Tarin miscall dinne kuwa ta samu kamar yadda tayi zato,dukka kuma daga number dake ajiye cikin wayar da sunan MOM SUHAIL.

"SUHAIL" Ta ambata a fili,idan har bawai ta manta ba suhail din shine sunan first born dinsa kamar yadda T.j ya tabbatar mata.

Wani irin tausayin matar da batasan ko wacece ba ya fara ratsa ta. Tana shirin karkata akalar binciken nata zuwa wani sashe na daban saqon SMS ya shigo wayar.

MOM SUHAIL kamar yadda yake a rubuce ta bangaren kira. Bata tsaya dogon jinkiri ba ta bude,gajeran saqo ne kamar haka.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 18


_Nayita kiranka baka dauka ba,kome meye mukayi da kai kafin ka baro gida ai ya kamata ka tsaya kaji dalilin kiran da nake maka babu qaqqautawa,bayan ka fito ciwon suhail ya tashi,a yanxu haka muna asibiti,amma babu ko sisi a hannuna,baka barmin komai ba,already kuma account dina yana buqatar naje banki na gyara bare nayi hidimata da kudina yadda na saba_.

Wani abu me tauri taji ya tsaye mata a wuya,ta zura hannu a jakarta ta ciro wayarta,tanason taga nawa ita ya kashe mata?,nawa ya saka mata alhali ko sisi matarsa bata amfana dashi ba?.

Naira dubu dari ta tarar. Wani matsiyacin tsaki ta saki,cikin dukkan arziqinsa ya rasa da meye zaiyi mata kyauta sai naira dubu dari?. Bata tsaya batawa kanta lokaci ba ta sauka ta koma mobile app dinsa da bai jima da fita a kai ba.

Daga password har username dinsa fes cikin kanta,tamkar hadaka ko gamayya sukayi dashi wajen creating dinsu a sanda zai bude manhajar. Cikin qasa da second goma komai ya bude,tarin miliyoyin kudaden dake kwance cikin account din nasa suka bayyanarwa idanunta,sai ta koms ta jingina da kujerar motar tana kallonsu,kamar ma bata tsoro ko shakkar dawowarsa.

Numfashi take fitarwa d'ai d'ai qirijinta na sake quntata. Tarin zallar rashin imanin maza yana sake tabbatar da kansa a zuciyarta.

"Yana da wannan kudin ya fita yabar matarsa babu ko sisi?,yana da irin wadannan kudaden yabar yaronsa cikin halin ciwo?,yana da wannan kudin ya gaza siya masa abun hawan da idan lalura irin wannan ta taso baya kusa zata kaisu zuwa ga asibiti cikin gaggawa?.

Tsanar MAZA tsanar SOYAYYA da kuma tsanar AURE suka sake linkuwa cikin ranta. Irin wannan shaidojin na gani da ido ta din saidai ta bada labarinsu. Shi din ma ba komai bane a cikin maza......bata kuma san namiji na nawa bane shi din da a yau xai shiga makarantarta.......a yau zata sanyashi ya koyi darasi kaman sauran,saidai nasa darasin yazo ne a gaggauce saboda gamawa da babinsa da tayi,da kuma dadewa da tayi da sanin shi din wayeshi?.

Beneficiaries dinsa ta duba,cikin sa'a tun batayi nisa ba taci karo da sunan da yayi daidai da sunan matar
*ameena mu'azzam*.

Kai tsaye ta saka amount din da yayi mata ta kuma karkatasu zuwa ga account din.

Daidai lokacin data hangi tahowarsa,ta daga hannunta ta zare wania abu daga jikin qofar,sannan ta maida hankalinta kan wayar kamar ba me wayar ne yake dosota ba.

Hankali kwance ta koma ta goge alert massage din da kamfanin sadarwa suka aiko,ta kuma koma zuwa ga email a gaggauce ta goge nashi tayi minimize ta maida wayar mazauninta tana karanta sunan banking da yake amfani dashi,sannan ta zaro tata wayar tana duba ma'ajiyar lambobi dake cikin wayar.

Sunayen dake ajjiye cikin wayar ta fara bi,cak ta tsaya saman wani suna da yayi daidai da sunan banking nasa,ta danna malatsi na tura saqonni,ta kuma aika da saqon a gajarce

"Done" Ta jefa wayar a jaka daidai sanda ya iso bakin window din suna sake yunqurin buda motar.

Ja daya bakaniken ya yiwa murfin ya bude,sai ya waiwaya yana dubansa cikin mamaki,wanda shima cikin manakin ya iso

"Oga ina tunanin kaine baka jawo ta da kyau ba"

"Kai amma nayi mamakin faruwar hakan" Ya matsa yana kama hannun motar ya matsashi har sau uku. Mamaki yadan sake kamashi,amma kuma kiransa da tayi d nuryarta me laushi ya dauke hankalinsa daga nan.

"Okay na gode to" Ya fadiwa bakaniken yana cirar wani abu a aljihunsa adan gaggauce saboda kiran nata.

Bude mata qofar yayi,ta sako qafafunta ta fito tana gyara zaman abayar jikinta. Cikin nuna kulawa yake fadin

"Da alama motar bata gaji dake ba,kamar yadda me motar shima bai gaji da kallin wannan kyakkyawar surar ba......don Allah ayimin lamuni a bani exact gurin da zan sameki.......da gaske nake,banzo da wasa ba,ni din ba irin sauran samarin yanxu bane......da niyyar aure nazo" Ya qarasa maganar yana lanqwashe murya.

A nutse ta watsa masa idanunta da suke sake narkar dashi. Batajin daga rana irin ta yau ma zai sake samun damar tsaiwa da ita a muhalli daya irin yanzun. Wannan itace dama ta qarshe kuma lokaci na qarshe a wajensa tsakaninsa da ita.

"Ba damuwa......ka samu number dina ai.....komai zaizo da sauqi?"

"Are you sure?" Ya tambayeta yana kallonta cikin kokwanto. Saboda shi kansa yasan samunta din abune me wahala.....ta subuce masa wancan karon.....hakanan haka ya qaraci karakainarsa da nemanta amma ko me kama da ita babu ballantana ita karan kanta din. Kai kawai ta gyada masa sannan ta juya ta soma takawa tana barin wajen gami da cewa

"Godiya nake......fatan alkhairi"

"Nike da godiya kyakkyawa" Ya fada murya a lanqwashe yana binta da kallo da zazzafan so,yana jin kamar ya saceta ya gudu da ita ya mallakawa kansa ita.

A nutse take taka kowanne step da zai sadata da ainihin makeken store din. Murmushi ne kwance saman fuskarta ita daya,duk da bata juya ba amma ta tabbatar yana tsaye ne yana kallonta,tana hasaso yadda fuskarsa zata koma a sanda ya laluba asusun bankinsa ya taras da barnar datayi masa,tana hasaso yadda wannan tattausan kallon zai koma zazzafan kallo da kuma zurfin tunanin TA YAYA AKAYI HAKA YA FARU?.

Yadda take daukan hankula da idanuwan wasu daga cikin jama'an dake sabgoginsu a waje da cikin shagon bai dameta ba,don ba wani baqon abu bane a wajen ta. Itadai ta sani,akwai dubbai zuwa miliyoyin mata da suka zartata a kyau.....don bata tana daukan kanta ta sanya a sahu ko jerin kyawawan mata ba,amma batasan mene a tattare da ita me matuqar jan hankali irin haka ba.

K'annenta sune gaba da komai da kuma kowa. Buqatunsu kuma sune gaba da nata buqatun. Don haka duk list na abinda suke buqata ta fara dubawa. Tana tsinta tana jefawa a cart.

Ta kwashi a qalla minti ashirin tana nasu siyayyan sannan ta fara nata. Siyayyarta bame sauqi bane,tana da tsari tana zabi,ba komai yake burgeta ba kaman yadda a rayuwarta na zahiri ba kowa ke burgeta ba,komai nata yana da tsari,don haka ta bata lokaci sosai akan nata kayan,ta saki jiki kuma kamar ba zata bar shagon ba.

Sai data gama tsaf sannan ta gangara bangaren kayan maqulashe. A duk sanda ta samu kudi irin haka bata rabo da siya musu kayan taba ka lashe,harda ajiye wasu ma cikin daki. A duniya idan akwai abinda taqi jini shine taji sunce BABU ko BANI DASHI ADDA....kalma ce da bata yarda a yanzun ta shiga tsari da babin rayuwarsu sam sam.

Sashe ne

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login