Showing 246001 words to 249000 words out of 557259 words

Chapter 83 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

558

shude ba tare da tasan komai game dasu ba.

Ta dauka yadda ta dokanta ta fita ne idanunta suke mata gizo sanda ta hangi babu ko burbushin kudi a wajen,amma data bude sosai sai taga gaskiya take gani.......ba komai a ciki kamar yadda ta gani da farko.

Mamakinta ya ninku akan mamakinta na kwanaki hudun da suka shude........ta sulale tana sake zama a saman stool din dake kusa da ita.

"Wai wa yake da alhakin aikata haka?" Ta sake tambayar kanta tana jin tantama akan tabbacin zargin farko da zuciyarta ta bata.

Duk wani karsashi na fitar saita rasashi......yaushe ya samu damar shigar mata daki?,dame dame ya bincika mata?,me zaiyi da wayarta?,dame dame zai bibiya cikin wayar?. Wadannan tunanin su suka sakata a gaba,ta kasa tuna komai ko abinda ya dace tayi,har sai da agogo ya alamta mata sha biyu dai dai na rana.

Cikin qarfafawa kai gwiwa ta koma toilet ta sake wanke fuskarta,ta dawo ta wuce closet ta dauki handbag da shoe da zai dace da shigarta sannan ta soma barin dakin tana jefa atm dinta a jaka da zummar idan ta fita ta samu wani guri ta cire kudi daga account dinta.

Wannan ce ranar farko kuma karan farko data fito daga cikin gidan a yanayi irin wannan. Faffadar haraba yalwatacciya me wani irin tsari me jan hankali. Kusan gurare da yawa an qawatashi da koriyar ciyawa a maimakon tiles marbles ko concrete da akafi yawan amfani dashi. Sai wasu irin fararen stone da aka zuba a wasu daga cikin hanyoyin da zaka taka ka wuce zuwa haraba ta biyu. Idanunta suna iya gane nata wasu qofofi da babu qofa a jikinsu face wani irin design da aka musu wanda batasan ainihin inda zasu sadaka dashi ba. Sosai harabar ta qawatar da wani irin yanayi da zakayi tsammanin ba cikin qasata nigeria kake ba.....saidai wutar dake can qasan zuciyarta ta danne burgewar da wajen yayi mata,taci gaba da tafiya cikin confidence zuwa qofar gate din da take da tabbacin zata sadata da waje.

Tsaye kawai tayi don bata fahimci ta inda zata ratsa ta wuce ba,sam qofar ba irin qofofin data saba gani bane. Gajiya tayi da tsaiwar ta kuma gaji da kallonta da tunanin ta inda zata fita din,don haka ta saka hannu ta soma knocking da tunanin zasu iya jinta.

Tun tana knocking din a hankali har ta fahimci ba kowa ke jinta ba,ta qara dada qarfinsa saidai a banza don ba wani motsi da taji da zai bara hope din wani na kusa zaiji ya kuma budeta,wannan ya qara hasala mata zuciya,ko a kurkuku take bangaren muggan laifin kisa ko fashi da makami iya horon da za'ayi mata kenan,don haka ta sake maida kai wajen buga qofar da kyau ba tare da tunanin cewa babu me jinta ba.

A hankali wani sashe kadan daga saman qofar ya zuge kanshi da kanshi. Fuskar jordan ta bayyana wannan karon sanye cikin uniform din daya zama kayan sawa ga duk wani ne aikin tsaro dake cikin gidan.

"Good afternoon maa". Ya furta da wannan matsananciyar girmamawar da yake mata wadda ba abinda take sawa zuciyarta sai wani irin qarin takaicinsa. Fuskar jordan fuskace da ba zata manta da ita ba ko kadan

"Open the door" Ta fada adan fusace tana kallonsa,tana jin kamar ta miqa hannu ta zabga masa mari. Cikin rusunawa da girmamawa kaman yadda ya saba ya fara mata magana da hausa

"Am sorry maa......boss bai bada umarni ba,idan ba damuwa ko zaki kirashi kuyi magana tukunna?". Idanunta ta janye kawai daga kan jordan din bacin ranta yana ninkuwa,abinda yayi mata a wancan lokacin shi ya maimaita mata kenan?,waishin me yake daukan kansa ne shi?,don yana da kudi?,yana da dukiya shi yasa yake tunanin zaiyi duk abinda yaga dama?,zai taka wanda takeso a duk sanda yaso?,zai wulaqanta mutane sannan kuma ya kwana lafiya?. Ta ina zata nemeshi bayan babu ko waya guda daya a tare da ita?,ta ina zasuyi magana bayan ya yanke sadarwar gidan gaba daya?,koda ma komai yana nan a muhallinsa ta rantse ba zata kirashi ba.

"Kawu ne ya jawo miki" Amsar data dawo cikin kanta kenan. Idan ma kira ne shine mutumin daya kamata ace ta kira,har yanzu tana ji a jikinta kan ta inda ake hawa ta nan ake sauka,kawun shine ya bada ita ya kuma saida mutuncinta.......don ta nata bangaren ba'a kan muhammad fu'ad bane farau shallakewa maza masu kudi da kuma hadari......don haka don shi kadai bazai zame mata matsala ba inda anbi karatun yadda ta saba. Har taji kamar ta sare,sai taga idan ta bari hakan ta kasance yasha da ita,don haka ta matsa bakin gate din

"Can you barrow me your phone?". Ta tambayeshi tana kallonsa. Jinin jikinsa yasha,yadan kalleta yana kokwanto. Yaya zata rasa waya tana a gida irin wannan?.

"Afwan madam.....amma me zakiyi da waya?" Idanunta da suke mata zafi ta lumshe

"Zan kira uncle dina ne.....i lost my phone". Dan jim yayi kadan,sai kuma ya amsa mata yana sanya hannu a aljihu ya fiddo wayar ya miqa mata bayan ya sake bude glass din ya qara girma.

Yadda yake bata wayar kamar tana a kurkuku ya sake matsa zuciyarta ya qara yawan adadin bacin ran da take ciki.

Wani sashe daban na gidan ta koma ta zauna saman wasu rukunin kujeru da aka qawata cikin wata rumfar bamboo dake bada iska me kyau da sanyi. Da qyar ta iya hada lambobin kawun don ba haddacewa ta taba zama tayi ba.....saidai kawai kira na yau da gobe daya bata daman kallonsu daya bayan daya suka kuma zauna a kanta.

Bugu biyu kawun ya daga da cikakkiyar sallamar data kusa sanyata jan tsaki

"Kamar gaske" Ta fadi a ranta tana amsa sallamar tasa a daqile.

"Wa nake ji kamar sabreena?" Ya fadi da annashuwa cikin muryarsa,zuciyars na bashi tabbacin lallai zama ya soma miqawa,wataqila wani alkhairinma ta bugo tayi masa

"Nice" Ta amsashi a hankali

"Kai madalla Allah.....ma sha Allah,amma fa naji dadin kiranki kin kyauta diyar albarka,dama inata zube kunne naji kiran naki......"

"Eh gashi na kira......na kiraka ne kuma na gaya maka.......wannan mutumin daka saida masa dukka 'yan cina da mutuncina ya kamata ka kirashi ka bashi labarin haihuwata akayi bawai a baiwa aka ribatoni ba.......ka fada masa abinda ke tsakaninka dashi daban da abinda ke tsakanina dashi,bazan iya daukan dukka wannan izzar tasa da izgilancinsa ba......ina da 'yance kafin zuwansa zan kuma ci gaba da kasancewa me 'yanci a rayuwata.....don har yanzu babu d'a namijin da zai dinga ruling dina yadda yaga dama ba tare da naso haka ta kasance ba".

"Kai jama'a.....waike wacce irin yarinya ce ne me butulci?,Allah yayi miki wannan babban gamo da katar din da miliyoyin mata ke fatan samu amma ki zauna kina shashanci?,yo Allah na tuba idan ranka ya dade baiyi mulki da izza ba meye zaiyi?,kudi ne dashi fa?,arziqi garai irin arziqin da gwamnati ma wani lokaci biyayya takeyi maka.......ina gani malam rufa'i?,to wallahi bada ni ba.....hasalima ni bamu taba waya dashi ba,dan uwansa kuwa farouqu bazan dauki sirrin gidan ma'aurata nakai masa ba Allah bazai la'anceni ba,in zaki nutsu kiyi biyayya ki tara abinda kika tara karki mana buqulu to,amma wannan jan kunnen bada ni ba.....wane mutum inji mutuwa,Allah baki da hankali sabreena" Har ya qare maganganun idanunta suna kulle saboda yadda yake mata magan da qarfi da hayaniya,uwa uba ita bataga dalilin dogon jawabinsa ba.

"Kawu" Ta kirashi a nutse.

"Yaushe su huda suka zama cikin kayan gado da har za'ayi rabonsu zuwa ga wata mace da basu hada alaqar komai dasu ba?".

"Wata mace?,Allah na yarda dai da gaske akwai sauran qarancin nunar hankali a tare dake.......kina magana akan hajiya mariyah surukarki?,mutuniyar kirki me yawan alkhairi da son zumunci?,yo wannan kika fadi mummunar kalma a kanta aisai Allah ya tsine miki albarka.......ni baza'a zageta dani ba,sai anjima sabreena" Kafin ta ankara ya yanke wayar,abinda ya sanyata a razani ta maida dubanta kan fuskar wayar tana kallonta cikin mamaki.

A wannan karon duk yadda taso tare kukan sai da hawaye ya sauko mata bayan ta maida wayar wa Jordan. Sai kawai ta soma tattaki da sassarfa tana komawa ciki cikin yankewar kowanne tsammani.

A falo na biyu ta zube don ta gaza isa bedroom din. Wasu irin hawaye masu zafi suka fara gangaro mata. Me yasa rayuwa zata juye mata da zazzafan yanayi irin wannan dare daya?,yanayin da ko s mafarki bata taba tunanin zaya risketa ba?. Ya cika mugu na gaske,ya rufe mata kowacce qofa ko hanya da zata samu sassauci......me ya rage ita kuwa tsakaninta dashi banda itama tayi duk yadda zatayi tayi nesa dashi?,me ya rage banda ta aiwatar da nufin maamah a kansa don ya gwada shiga halin mulkin mallakawa d'an adam yaji idan hakan da dadi?.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 27


27


β˜…β˜…Madaidaiciyar haraba ce wadda yanayinta yayi kama da gine ginen turawa ainun,irin gine ginen qasashen qetare,saidai kuma ba harabar kadai ba.....gidan dama sauran gidajen dake wajen dama unguwar gaba daya ba zaka dauka kana cikin abujar nigeria bane ba.

Tamkar shi daya ne cikin gidan saboda rashin hayaniyar jama'a da kuma motsi,saidai a yawancin lokuta yakan zabi yanayi irin wannan don bawa zuciyarsa hutu da kwanyarsa. Bayan doguwar gwagwarmayar tabbatuwar buduwar kamfaninsa ap lagos kwanaki uku da suka wuce,sai ya zabi tsaiwa a abujan don ya sanya ido game da gudanarwar kamfanin koda na sati guda ne kafin ya koma bakin nasa ayyukan da suma a yanzu suke buqatar hankalinsa.

Farin boxer ne a jikinsa da wata cotton shirt me gajeran hannu wanda ta bayyana ginuwar muscles na jikinsa,zubi da qirar qarfin da yake da ita.

Tataccen natural ruwan blood orange ne a gabansa da ba'a sirka masa shi da sinadarin komai ba kaman yadda yake dabi'arsa ce a haka. Yafison komai natural da za'a sarrafashi da hannu,duk irin dukiyar da yake da ita amma yana sarrafa kanshi wajen sanin abinda zaici,wannan ya sanya yake da wata irin cikakkiyar lafiya.

Wayoyin dake gabansa ya sake maida idanunsa akai,ya sake miqa hannu ya dauki daya daga ciki yana jujjuyata. Ba komai a ciki,baiga kuma komai ba. Dayar number maamah dince kawai akai,ba contact ko daya,kaman yadda ba massages a ciki,duk wani social app dake kai baya aiki ba'a budeshi ba,kamar yadda daya wayar take itama. Ba Facebook ba insta ba tiktok,ko watsapp babu duk da yana zaton an taba amfani dashi a kanta an rufe ne. Yanason ya zurfafa binciken sama da haka,amma sai wani sashe na zuciyarsa ya tunasar dashi haramcin zurfafa bincike akan dan adam......amma su ya halatta ya bincikesu har haka?,bayason maamah taci gaba da jefa qafafunta cikin halaka.....dole uwa uwa ce.....mutum daya ce duk duniya ke amsa wannan sunan......kamar yadda yayi imani yarinyar sai ya karanta mata menene rayuwa kafin ya sakar mata qofofin 'yanci ta yadda ba zata sake zama guba ga kowa ba.

Maida wayar yayi ya ajiye,yana jin kamar zuwa yanzu ya kamata ya wuce gida hakanan ko don hankalin anni ya kwanta. Ya fahimci kamar tana zargin bai taho da yarinyar ba,amma da yake gwanar kawaici ce ita bata ce masa komai a kai ba. Ya sani ma inda farouq yana nan zuwa yanzu da tuni ya tona mishi asiri,sai Allah yasa suka shiga wata seminar kwata kwata bashi da lokacin kanshi.

Wayarsa ya dauko ya lalubi saddiq

"Kana ina ne?" Kanshi yadan shafa cikin jin shakka da nauyinsa

"Katamfe extension" Ya amsa masa yana addu'an kada ya masa fada. Bayajin doguwar magana a kansa sosai,hasalima wata kasala ke damunsa,ruwan dumi yakeso yasha ya sake kwanciya,don haka kawai ya bashi saqon a dunqule

"Kayi magana da team su shirya flight,gobe zamu wuce gida"

"Okay in sha Allah" Ya amsashi yana jin dadin yadda bai matsa masa ba bare ya sanyashi baro soyayyar da yake raino a lokacin.

Wayar ya mayar aljihun boxer din nasa,sannan ya dauke sauran kayayyakinsa da suke wajen ya fara saukowa daga farfajiyar dake a matsakaicin tsaho,shi ba upstairs ba shi ba qasa ba,amma lallai saiya biyo ta cikin dab da qofar parlor sannan ya shiga parlor din ya wuce duk inda zaije.

Sam hankalinsa ba'a wajen yake ba sanda yake saukowar,cikin wani irin mamaki qofar parlor din ta bude sannan ta bayyana gaba dayanta cikin ba zata.

Saura kadan ya hada jiki da ita,don ta shigo ne da wani irin zafin nama,banda shima me zafin namar ne yaja baya da sauri da ba abinda zai hana jikkunansu haduwa guri guda.

Cikin second biyu ya maido hankalinsa jikinsa,suka fara yiwa juna kallon kallo.

Fareeda,d'iya ga ambassador din nigeria a qasar china. Matashiyar da duniya ke gara mata fiye da yadda takeso,ta samu gata.....ta samu ilimi.....ta mallaki kyau......tana da tsananin wayewar da bata barinta fayyace daidai a addininta da ba daidai ba.......wayewar dake haska mata komai ya yiwa ranta dadi.....komai ranta keso daidai ne,wayewar da gatan da sukayi mata jagora tare da nuna mata kome takeso lallai zata sameshi ta kowacce hanya.

Doguwa ce fara sannan kuma siririya,wadda ke tattalin jikinta da amfani da mayuka da kuma supplement masu tsananin aji da tsada ba tare data bari zallar hutun da take ciki ya zama jagoran gyaruwar komai nata ba. Zai wahala ka kalleta ka kirata da mummuna kai tsaye......saidai bata cikin sahun kyawawan da kallo daya zai sanya ka gamsu kyakkyawa ce,tana mataki na kyau a middle class....duk da tana kai kanta high class a koda yaushe tana ganin ta cancanta da aje kanta a can.

Ta jima tana jin sunan muhammad fu'ad jadda yana gilmawa kunnuwanta.....wani lokaci daga bakin manyan friends dinta yaran gata irinta,wani lokaci kuma daga bakin mahaifinta. Saidai ko sau daya hakan bai taba jan hankalinta ba,saboda tana da wata izza akan namiji da saidai ya nemeta,don ta hada komai da take ganin babu kalar d'a namijin da bata zarce masa ba......in fact tana tunanin ma ita har yanzu cikin wannan duniyar da muke ciki babu kalar mijinta. Sau tari idan sunan ya gilma mata kawai tana surantashi kamar sauran alhazawan masu kudin dake hauka a kanta,masu shekaru,kai duka furfura ko kuma furfurar ta fara ketowa,masu qiba da ajiyayyen tumbi,masu matan aure uku hudu da tarin 'ya'ya.

Bisa rakiyar tilas data yiwa mahaifinta nigeria don zuwa bikin bude company din JADDA SPARKLE WORLD daga nan su qarasa garinsu gaisuwar mutuwar qanin mahaifinsa da ya kusa cimma wata uku da rasuwar amma bai samu zuwa ba. Kafaffe kuma tsayayyen yaya ga kakansu qwaya daya daga rage shi ya zuba bala'i akan fareeda,sam yarinyar ba wanda ta sani a cikin su kaf,saboda rabonta da garin tun batafi shekara biyar ba a duniya,basa qaunar zuwa kwata kwata,wannan ya sanya mahaifinta ambassador khaleed mustapha ya tilasta mata saboda rufe bakin mutane.

A karon farko da sanarwar bayyanar me kamfanin kan dandamalin jawabi ta ratsa microphone din,ta daga kanta daga kan wayarta da take qoqarin posting hotunanta a shafukanta,ta kuma saukesu akan muhammad fu'ad dake tsaye gaban abun magana yana daidaitashi yadda zai dace da bakinsa.

Wata lafiyayyar suit ce a jikinsa data tsone idon duk mutumin dake zaune a wajen. Suit din da musamman aka sarrafata tun daga qasar Italy saboda rana irin wannan. Ta sake fidda tsahonsa da murjewar jikinsa da wani irin mahaukacin kwarjini da ya zame masa garkuwa wajen karya maqiya da abokan gabarsa. Idanunsan nan masu wani irin kyau da bata taba ganin irinsu ba suna yawo saman fuskokin tarin al'ummar da sukazo wajen saboda shi yayi cikakakkiyar sallamar da duk wanda ya sanshi yasan wata abace da baya tsallakewa yinta ako ina koda wanne irin mutane ne a gabansa,ba ruwansa da banbancin addini qabila ko kuma yare.....ako yaushe yana yin abinda xai ci gaba da tuna masa....zai kuma ci gaba da bayyanawa ko waye suke tare cewa SHI MUSULMI NE.

Sanda ya fara jawabin taron da wani irin tataccen turanci da lanqwashewar harshen da zaka rantse cikin fadar queen Elizabeth

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login