Showing 273001 words to 276000 words out of 557259 words

Chapter 92 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

468

kasalance ta maida kayan ta kuma rufe ta maidasu ma'ajiyarsu sannan ta dawo ta soma daukansu zuwa dining don yau kwata kwata ma bata bari zuwaira ta shigo mata ba. Batason doguwar magana,hakanan batason sanya idanu da wannan shegen binbinin kallon da take binta dashi a kowanne daqiqa.

Dab da zata isa dining din saita dinga ji kamar qamshinsa. Batasan ya akayi ba.....amma tun daga waccan ranar ta haddace wannan nataccen qamshin turaren nasa da har yanzu yake maqale jikin rigunanta guda biyu. Sosai takejin qamshin,to amma ta raba idanunta ko ina cikin parlor din bata ga wani alamun shigowarsa ko shigowar wani ba. Agogo ta sake kalla sanda take ajiye warmer din,mintuna kadan ya rage ayi sallar magariba.....wannan lokacin kuwa ba lokacin dawowarsa gida bane,don qarfi da yaji ta haddace lokacin dawowar tasa saboda yadda ta aza dukka damuwarta akan cikar burinta na yaci abincin.

Watsar da tunanin tayi,taci gaba da shirya komai ta kammala,ta tsaya kawai tana kallon yadda komai yake jere saman dining din.

"Inama ace yau daya burina ya samu ya cika?" Ta furta qasan ranta duk da tana jin wani sashe na zuciyarta kaman yana qyamatar hakan ya faru,sai kuma ta juya tana nufar hallway din da zai sadata da dakin. Dab da zata shige laila ta murda pivot door din tana shigowa falon tayi kwalliya sosai cikin wani silk material da aka tsarawa dinkin daya dace da shape din jikinta sosai. Red ne colour dinsa wannan ya sanya farar fatarta data samu gyara da pills na qara fari da allurai na qara hips da sauransu ya sake qawata shigar tata. Kome takeyi tana da cikakken goyon bayan hajja wadda a kullum burinta ta fita daban,ta kuma zama daban din ta kowacce hanya cikin mata.

Idanu suka hada,sai sabreen din ta dauke idonta kamar kullum,ta kuma taka a nutsenta tana wuceta,tana jin bata da wani lokaci nata sam sam.

Da idanu ta raka sabreen da wani irin kallo na qurilla,allurar kishi tana tsikararta,tana tambayar kanta da wanne irin products haka take amfani masu tsananin qarfi?. Tana ji ana cewa kowanne dan adam tara yake bai cika goma ba.....to amma ita sai take ganin tamkar a halittar sabreen goma take cif cif!.

Tsaki taja tana maida dubanta kan dining din. A yunwace ta shigo,ta samu zuwaira kuma bata nan,tabbacin a yau kenan saita shigo da kanta neman abinda zataci.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 41


_Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_
__________________________



Matsawa taci gaba dayi zuwa wajen dining din,tana cike da haushin yadda a kullum ake jigilar qawata wajen da warmers na alfarma wadanda suke bata tabbacin abinci ne lafiyayye.....to amma kullum idan ta tuna maganar da hajja ta gaya mata akan abincin sai ta maida qwalamarta bisa tilas. Asali ita din mutum ce da ba kasafai ta fiya bawa irin wadannan abubuwan muhimmanci ba. Hasalima tana ganin idan ba dominka aka shirya abu ba bazai taba tasiri a kanka ba.

A nutse ta isa wajen,ta kuma jawo warmer din farko ta soma budeta,budewar da ya qara adadin yunwar da takeji taji kuma bata da wata hanya illa ta toshe yunwar dake sakadar mata hanji kamar bata taba cin komai ba.

Yau gajiya takeji sosai a jikinta,wannan ya sanya data idar da sallah isha'i wanda duka zama tayi a wajen bayan magariba sai data yi isha din sannan ta tashi. Wannan Dabi'arta ce qwaya daya da har yanzu bata rabu da gangar jikinta ba,burbushin raino da tarbiyyar ummensu,bata wasa da sallah sam koda bayan gushewar ummen,kuma ita kanta ta hori 'yan uwanta sosai akai
(Ko hori yaranku da sallah.....tana da matuqar tasiri wajen hana bawa sabon Allah da kuma gyara halinsa,kamar yadda Allah ya fada cikin qur'aninsa me girma,tabbas sallah tana hana alfasha da munkari,Allah ya bamu dacewa ameen summa ameen). Tana shirin shiga wankan saita samu kanta da maimaita addu'o'in data karanta a littafin da anni ta bata wanda shi ya qara sanyata jin dadin zaman. Tana nanata addu'o'in suna tuna mata da zamanin da suke qananu......lokacin da ummee ke korasu makarantar allo ranakun weekend,ita hadiyya da sameeha. Qaramin murmushi ya kubce mata,tadan girgiza kai tana jin kewar lokacin quruciyar tata,tana jin inama tana da ikon dawo da wancan lokacin,ashe ba abinda yakai zamanin quruciya dadi.

Pyjamas ta saka baqaqe gaba daya da suka sake haska mata fatarta,sai ta dora qaramin farin Malaysian hijab saman kanta bayan ta nannade gashinta a tsakiyar kanta cikin ponytail holder,hakan ya sanya kan yadan tashi kadan kamar tayi acuci maza na.

Fararen flip flops ta zurawa fara tas din qafarta,wadda duk wani lalle ya fita a jiki,sai tsantsar haske daga qara da gogewa kamar jini zaiyi tsartuwa.

Hankalinsa na rarrabe akan wayarsa sanda yake qarasowa cikin falon. Daidai lokacin da laila ke saukowa daga dining din sai ya zamana mutum na farko da idanunta suka fada a kai. Cak ta tsaya ana zare duk wani noti na jikinta,wannan shine karon farko data taba gaba da gaba da muhammad jadda,kusan duka a baki ko cikin magazines da news paper take ganinsa.

Duk yadda tasha fasaltashi a zahirinsa ya wuce nan,wani irin ingarman namiji da a iya tafiyarsa kadai ta hangi izzarsa da kuma cikar isarsa.

Kaman a jikinsa yaji ana kallonsa,wannan dalilin ya sanya daga idanunsa yana duban sashen da yaji jikinsa yafi rinjaye. Suna hada idanu gaba daya kwarjininsa ya mata wani irin mamaya data gaza riqe kanta,duk wata zarra da jin kai da takeji tana dashi a matsayinta na diya mace ya sulale yayi nasa waje. Yadda ya kafeta da idanunsan nan masu qunshe da wani sirri sai taji komai yana kwance mata

"Barka da dare" Tayi namijin qoqarin furtawa bakinta yana son hardewa

"Yauwa" Kawai ya amsa mata dashi.

"Nice laila....'yar gidan hajja.....hajja harira ta maamah" Tayi bayanin a nata zaton hakan zai burgeshi ko kuma ya sake bata matsayi na musamman a matsayinta na 'yar aminiyar mahaifiyarsa.

Fuska yadan yamutsa kadan yana fahimtar inda ta dosa.

"Yayi kyau.....ban fadi muku banson kowa around us ba idan ina gida?" Yayi maganar fuskarsa na wadace da wani irin daurewa kamar baisan sunan wani abu waishi dariya ba,don dama da bacin rai ya sauko.

Kasaqe tayi tana mamaki,tabbas zuwaira ta shaida mata,amma ko a sannan kallon banza ta watsa mata ta wuce dakinta,don tana ganin ita ta wuce wannan dokar tayi aiki a kanta. Tana jin kanta tamkar ita din halastacciyar 'yar gidan ce,don haka bata ma wani tsaya amfani da dokar ba bare ta kiyayeta. Tana shigowa a duk sanda taso tayi abinda takeso ta fita,saidai da yake dukkaninsu ba ma'abocin zaman falon bane kowa sabgar gabansa yake shi yasa ba wanda ta taba karo dashi a cikinsu.

"Get out of my sight......and kada ki sake bari mu hadu" Ya fada cike da zallar umarni ba tare kuma daya kalli sashen da take ba yaci gaba da tafiya kansa tsaye zuwa dining din.

Ajiye wayoyinsa yayi bayan ya gama abinda yake,ya maida hankalinsa ga abincin yana dubansa. Yau zai kawo qarshen duka wannan drama din ya ayyana hakan a ransa,daidai sanda take fitowa daga parlor din zuwa ainihin falon da yake ciki.

Kai tsaye dama idanunta kan dining din suka fada,don ya zame mata wani aiki na daban kiyaye waye a wajen da kuma duba waiko ya zauna cin abincin?. Bataso yadda tashin farko suka hada idanu ba don zaya dauka ne kawai kallonshi takeyi,take tata izzar itama ta motsa,ta dauke kai sosai tana takawa zuwa qofar kitchen.

"Hey.....com here" Ya fada da matsakaiciyar murya. Tanason gwada masa tsiwar amma tana tsoron abinda zai biyo baya,dole ta dawo din fuskarta shimfide da kalar nata miskilancin.

"Serve me" Ya fada cikin basarwa yana bude wayarsa. Cak ta tsaya,tana jin kamar kunnuwanta ne suke jiye mata ba daidai ba. Ta zuba masa abincin fa ya buqata?,ta tambayi kanta tana neman qarin haske.

"Zuba abincin nace" Ya sake maimaita mata ba tare daya dubeta ba. Wani irin abu taji ya tsargawa sassan jikinta. Ta dade tana fatan zuwan wannan ranar,ta dauka duk sanda taxo din zata kasance mutum da tafi kowa murna a duniya,amma kuma sabanin murnar mutuwar jiki taji.

Matsawa tayi sosai gaban table din,ta ware qananun luxury table mat din ta sake shimfidasu,sannan ya zari plate da bowl ta soma zuba komai tsaka tsakin quantity sannan ta jera masa a gabansa.

Wayar ya ajiye a gefansa,ya miqa hannu da kanshi ya ciro spoons guda biyu ya saka cikin abincin sannan ya dubeta

"Oya.... Let's eat together" Ya furta yana matso da drinks din da aka aje a wajen duk da ba abun shansa bane sam sam duk wani drink da company ta sarrafa.

Ba shiri ta bude idanunta a kansa,ji tayi kaman an dauko guduma an shirga mata. Cikin qasa da minti daya tayi qoqarin daidaita nutsuwarta dukka a qoqarinta na daidaita komai,ta girgiza kai tana fadin

"Na qoshi". Sake ware idanunshi sosai yayi a kanta yana dubanta,abinda ya sake sanyata kenan a tsilla tsilla,tana kyautata zaton akwai wani abu me nauyi da idanunsa ke dauke dashi,wanda muddin ya kama zuzzurfan kallo irin wannan sai kajishi har qashinka.

"I think kin fito ne ke debi abincin right?" Daburcewa tayi yanda ya kama abinda ya fito da ita din kansa tsaye kamar me gani har hanji. Bata saba qarya ba koda wanne irin hukunci aka tanadar mata,wannan ya sanya kai tsaye ta bashi amsa da eh.

"Good.....kinga wannan shi yafi kamata muci tare ko?" Ya fada cikin sigar saukar dakai yana turo abincin gabanta. Kanta ta sake kadawa,gaba daya yana birkitata ganin yadda yake matsantawa saita zauna sunci abincin

"Seat down!" Ya fada da wani irin husky voice yana buga hannunsa saman table din har abincin dake cikin plate din yana watsewa saman table din. Batasan sanda ta zauna ba kaman yadda ya buqata tana qoqarin kaucewa kallon fuskarsa da har hancinsa ya fara yin ja alamun tsananin bacin rai wajen farin mutum kenan.

"Kinsan abinda zan gaya miki guda daya?" Yayi maganar qasa qasa kamar ba shine yanzu ya buga wannan tsawar ba,bai jira ta amsa ba ya dora da fadin

"Duk sanda kika qara yimin girki a gidan nan saikin cinyeshi tsaf!". Gigicewa ta sakeyi da abinda yace,maganar daya fada kawai ta sanya hasashenta ya tsaya daidai inda take zatonsa

"Be warned!" Ya furta yana ranqwafowa sosai saman kanta har tana iya sheqar dumin numfashinsa da yake futarwa daga hancinsa. Baya yaja ga kwashe wayoyinsa,zuciyarsa na masa wani irin zafi ya soma sauka daga wajen yana dosar hanyar da zata sadashi da stair dinsa.

Maamah uwarsa ce,ba yadda zaiyi da ita,amma zaiyi dukkan abinda zai iya ya toshe kowacce qofa da zata samu nasarar budeta a kansa ko kuma waninsa muddin yana da iko da masaniya.

Koda ya koma saman duk yadda yaso yayi keeping kanshi busy ya manta da komai sai ya kasa. Mahaifiyarsa......macen daya biya kudade aka daura mata igiyarsa..... A duniya idan akwai wasu mata da sukafi kowa kusanci dakai suna sama da wadannan ne?. Me suke nema a tare dashi?,amsar daya kasa laluba kenan. Sosai abun ya dinga masa ciwo,shi yasa ko sau daya bai taba aminta da ita ba,ko sau daya bai taba jin ya gamsu da ita ba......takowacce fuska tana da qatuwar lam'a da tabon da shi shine babbar shaida......bayan tarin shaidun da ya samu har abinda be nema bama an bashi,ta yaya zai iya kallonta a matsayin wankakkiya?,ta yaya zai iya yafe mata?. Yanason ya zame mata lesson me girma a rayuwarta,zai kuma ganar da ita kuskurenta na shiga rayuwarsa hakanan kai tsaye.

Daga qarshe dai dole ya kunna karatun qur'ani daya karade ilahirin sassan nasa,yayi kwance kawai idanunsa a lumshe sautin yana shiga kunnensa,sannu a hankali kuma nutsuwa ta fara samuwa a jikinsa.

Ko qwaqwaran motsi kasa yinsa tayi ballantana ta tashi daga wajen,batasan adadin lokutan data shafe zaune a wajen ba,har sai data daga idanu taga agogo yana gaya mata qarfe goma da rabi saura mintina biyar sannan ta iya miqewa.

Zuwa sannan hatta da qafafunta sunyi wani irin nauyi da sanyi,saita gaza shiga kitchen din ta zarce hallway din sannan ta fada dakinta. Rasa abinda ya kamata ta tuna tayi,ganinta yayi kenan koko yaya?. Karon farko da taji wata irin nadama na saukar mata. Ya akayi ta biyewa mamah din ta yarda ta ciyar dashi gubar da batasan ranar yankewarta ba?,wacece maamah din?,me kuma take qullawa?,me take buqata ne a rayuwarta sama da rayuwar da take ciki?.

Zafi sosai takeji cikin ruhinta,tunda take bata taba sha'awar ciyar da wani ko shayar d wani wani abu me illa irin wannan ba,koda sanda take shirya gyara zaman mazan da suka zabi harka da mata kuwa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 42


_Daba abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace "mafi falalar sallah bayan sallar farilla itace sallar dare_

*_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqaπŸ˜„,Allah ya bada ikon jurewa_*
____________________________


β˜…Qarfe tara na safiyar alhamis ce wadda aka wayi gari da lullumi qwarai,sakamakon hadarin farko daya fara hada jikinsa tun bayan sallar asubahi. Bai bada ruwa ba amma kuma ya yiwa rana shamaki daga fitowa tayi rawar gaban hantsi kamar yadda ta saba kowacce safiya saman sararin samaniya.

Yanayin sai ya haifar da yanayi me dadi da kuma sanyaya zukatan da suke cikin wani yanayi.

A irin wannan lokacin ne muhammad jadda mamallakin kamfanin jadda diamondchore resources yake saukowa a hankali daga samanshi. Cikin shigar aiki,saidai kuma yau zaka dauka juma'a ce saboda shigar kaftan yayi. Dinkin zamani daya zauna masa sosai,ya kuma fidda sigar kyan nan nasa da kana kallonsa zaka tabbatar tabbas halfcast ne shi din wato ruwa biyu.

Cikin parlor din ya samu tuni ameh ya kammala shirya masa komai na breakfast dinsa. Ameh din shi ya koma masa girki tun bayan wancan abun daya faru,yaja daya daga cikin kujerun wajen ya zauna ameh din ya gaidashi cikin rusunawa. Amsawa yayi da kulawa sannan ya fara serving nasa,yana yi yana dibansa da labarai,wanda kusan dukansu labaran da suka fita ne a jaridar safiyar. Ameh din yana da karance karance da yawan sauraran kafafen yada labarai,don haka a mafi yawan lokuta idan bai samu damar duba news paper ba shike bashi latest na cikinsu.

A nutse ta maida littafin amdatul ahkam da take dubawa,ta kuma d'auki zaduzzaujaini ta sakashi a ciki don yin alama akan inda ta tsaya din. Saman side bed drawer tayi masa kyakkyawar ajiya tana jin wata nutsuwa tana ratsata. Sati guda kacal kenan da fara karatunsu da rumaisa'u d'iyar malam amma wani nutsuwa takeji da gamsuwa da karatun. Rumaisa'u din da tayi tsananin mamakin ganinta a matsayin malamarta da ya dauko mata domin daukan karatun addini a hannunta. Zuwanta kusan uku tana rejecting tana qin fitowa......sai ana hudun ta fito da zummar yiwa malamin ko malamar bayanin ta daina wahalar da kanta tana zuwa......ta gayawa wanda ya aikota dalibar bata da buqatar wani karatun. Ganin rumaisa'u din sai ya zagwanye komai daga zuciyarta,ta cika da mamakin zuwanta gidan,saidai daga baya rumaisa'u din ta gaya mata

"Hamma muhammad tsohon dalibin malam ne"

"Gwara da kika ce tsohon" Sabreen ta furta a ranta. Don tako ta ina bataga ta inda ya dace ko ya cancanta mugu maqetacin mutum kamar fu'ad din ba ya hada alaqa da malam ba. Daga haka ba wani zance daya qara shiga tsakaninsu,sai hiran duniya kawai da kuma karatun daya biyo baya.

Da farko kawai dai tana sauraren rumaisa'u dinne,amma karatun kwata bayayi mata wani armashi ko burgeta. Saidai lokaci guda kuma a rana daya data arawa rumaisa'u hankalinta sai taji karatun ya fara shiga kanta,mafari kenan data fara hada hankalinta da zummar Tsintar abinda ta Tsinta,saidai tafi tafi sai ta fahimci karatun yafi qarfin ka tsinta kawai. Ita kanta rumaisa'u mamaki takeyi ainun....mamakin yadda karatun

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login